Showing 81001 words to 81601 words out of 81601 words
Chapter 28 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
me ke faruwa ba ita dai zaton ta ya bata mafarki take, muryar Amarya ta ji a kan ta ta na fad'in,
" Malama ya ya dai naga har yanzu kina kwance ki na bacci baki soma qoqarin had'a mana abin karyawa ba, ko so kk in ya dawo daga masjid ni da nake amarya na fito had'awa? Sarai kin san, ban da lfy, qafafuna ciwo suke,sai na sake shiga ruwan zafi tukunna,zan ji dama dama saboda yanda baby ya hana ni bacci jiya, gaba d'aya gabb'ai na ciwo suke"
Hawaye ne ke Malala a idanun Rasheedah da ta gama tabbatar da cewa idon ta biyu ba mafarki take ba, Wani abu ne mulmulalle take ji ya tokare mata wuya tsabar baqin kishin da take ji na dawainiya da ita,gashi wani kwarjini yarinyar ke mata har wani tsoro tsoron ta take ji, Auwal ne ya shigo, amarya na ganin shi se ta yi kamar miqewa ta yi daga tsugunnon gaida Rasheedah, da sauri ta saki wata 'yar qara, Auwal na ganin haka ya yi sauri ya nufe ta ya qarasa d'aga ta,
"Sannu, ni bana ce maki kar ki fito bane, sai kin gama warke wa? Gashi nan zaki qarawa kan ki ciwo ai, wuce mu je na sake sa maki ruwan zafi ki shiga wataqila za ki fi Jin dad'in jikin ki, sannu Allah ya sawaqe,"
Cike da shagwaba ta fad'a qirjin shi, ya tallabe ta yana shafa bayan ta,cikin kissa da maqale murya ita a dole ga mara lafiya ta ce,
"Wai da zuwa na yi mu gaisa da Yaayaah, se na ga kuma kamar sallah ta ke shine na Jira ta idar na gaishe ta,"
Baki Rasheeda ta saki dan tsananin mamaki, lallai akwai aiki a gaban ta babba ashe?..........
*Woo ke Woo ke Amaryar Auwal, sha sha'anin ki duniya ce samaaaa*💃🏻💃🏻💃🏻👄👄👄
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: Ta bangaren Rasheedah da amaryar ta kuwa komai ya wuce kamar Wani saba'ni be tab'a shiga tsakanin su ba, girmamawa sosai Khadeejah ke Yi wa Rasheedah, yaran amaryar ma gaba d'aya Rasheedah ke kula da su, a kullum bata da aiki, sai yiwa qanwar ta Sakeenaah addu'a da fatan samun rahamar Allah, ta tabbatar da cewa Sakeenah na can ta samu ladan gyara zumuncin da ta yi sanadin shi, ta gode wa Allah da ya bawa Sakeenaah JARUMIN miji kamar Adnan, Wanda ya yi hakuri ya jure rashin 'yar shi a kusa da shi dik da labaran da yake ji na azabtarwa da ta yi mata, ta gode wa Allah da ya sa ta gane halayyar da take na hassada da kyashi da kishi ba abu bane me kyau tin kafin ta mutu, a yanzu rayuwa suke Cike da so da qauna da girmama juna ita da Auwal tabbas Auwal SHINE JARUMIN ta na har abada, ba zata gaji da gode masa ba a bisa hakuri da ya yi da halayen ta marasa kyau.
Ahmad kuwa na can ya Maida hankali wajen neman ilimi da kasuwanci, ya na matuqar kewar Atiyyaerh wannan dalilin ne ya sa ya kasa neman mata da kan shi ya aura, sai Hajar ce ta sama mashi mata cikin qannen ta aka aura masa, Yana da Yara biyu Shima mata dika, ta farko ta ci sunan mahaifiyar shi, ta biyu Kuma ya Saka sunan Atiyyaerh, gaba d'aya gidajen ana zumunci da juna daidai misali.
*Alhamdulillah....Nan na kawo qarshen novel dina mai suna,KAI NE JARUMI, ina riqon Allah daya gafarta min kuskuren dake ciki,alkairin da ke ciki ya yad'a shi a dika duniya ya bani lada, ya bama makaranta ikon amfani da saqonnin dake ciki na alkairi Ameen.*
*A cikin mazajen nan na labarin KAI NE JARUMI wanene Jarumin ki/ka?*