Showing 6001 words to 9000 words out of 81601 words
Chapter 3 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
ya hau godiya ba iyaka, sai can yamma aka sallame su suka wuce gida.
Sun isa gida lafiya, nan da nan Sakeenah ta Maida hankali ta dora ruwan wanka, Rasheedah na d'aki ta saka baby a gaba ta na kallo, cike da so da qauna irin ta d'a da mahaifiya.
Can gidan iyayen su kuwa tinda maman su ta ji an sauka lafiya, se ta yi musu girki mai rai da lfy ta aiko masu da shi, Sakeenaa ita ce ta ke wuni a wajen ta tin da akai haihuwar dan gidan d'aki d'aya ne ba zai Yu ta kwana ba shi ya sa sai dare ta ke tafiya, komai da ya kamata a ce ta tanada kan haihuwa ashe babu, ran Auwal ya yi matiqar baci, ashe duk 'yan kud'in na shi da take tattarewa ta ce zata sai abu saboda haihuwa ba siya take ba? Qwafa ya yi yace Allah ya basu rai da lfy se ya yi maganin ta.
Ranar suna Sakeena akwati daya qarami ta yi musu na kaya a shaqe yake da kayayyaki na jariri da na uwar, sai dubu ashirin da ta kawo ta ba wa Rasheedah, har yanzu ta kasa reading face din yayar ta ta, fatan ta Allah yasa daga wannan lokacin qiyayyar da take mata ta tafi, Allah ya maye gurbin qiyayyar da son ta a zuciyar 'yar uwar ta.
Yaro yaci suna Yousuf, ya ci sunan mahaifin Auwal se dai mu ce Masha Allah yaro ya ci sunan dan kuwa akwai kyau, mahaifin Auwal mutumin kirki ne sanda ya na raye shi yasa ya Masa takwara, Auwal saboda maraici ya sha wuya a rayuwa sosai, ga ba wani ilimin zamani sosai,gwanda ma na addinin, yana da shi, shima ba wani sosai ba, a qalla dai ba za a kira shi jahili ba, yace suna kiran yaro da sunan shi bai son wani iyayin b'oye suna, haka ko ake kiran shi da Yousuf din shi.
Yau kusan shekara ɗaya da rabi kenan da haihuwar yousuf, Rasheeda na dauke da wani cikin ba tare da ita Kan ta ta kula da hakan ba, Yousuf ya yi wayo sosai, yawon shi yake ko ta ina, ga surutu Dan dik abinda ya gani ya San sunan shi, zai iya baka labari tsaf ka fahimci abinda yake fad'i kowa na mamakin wayo da qoqari irin na Yousuf.
Sakeenaa kuwa a wannan lokacin hankalin ta in ya yi dubu ya tashi, saboda rashin haihuwar da bata samu da wuri ba har qasashen waje sun je, ance lafiyar su qalaou su dika,a dik sanda Adnan ya gan ta cikin damuwa ya Kan zaunar da ita ya ce,
" Haba my love ki daina kukan nan haka ya isa, ki zama mai tawakkali ga Allah kar ki nuna wa Ubangiji ke kinfi qarfin ya jarabce ki, haihuwa ta Allah ce fa, in ma tsoro kk zan qara aure na maki alqawarin ke daya kin ishe ni rayuwar duniya, ni har qasan zuciya ta ban da sha'awar tara mata da yawa, sai dai in Allah ne ya qaddara min, ki yi hakuri kin ji My love?"
Kukan ta kan ragu amma ba dan ta daina ba ba kuma dan ta daina jin zafin rashin haihuwar da batai ba.
Hankalin ta bai qara tashi ba sai wata rana da ta ziyarci Rasheedaa ta gan ta, ta tabbatar ciki ne da ita, a cikin zuciyar ta ta hau godewa Allah da neman gafarar shi sannan ta yi wa yayar ta addu'ar Allah ya qaro mata zuri'a ta gari me albarka.
Hira suka ta sha wanda gaba d'aya akan qorafin Babu da talaucin Auwal ne, qaiqayin baki ya Kai Sakeenah da fad'a wa Rasheedah hasashen ta na ko dai Wani cikin ne da ita? Shiru Rasheedah ta yi ta na tinanin rabon ta da period da Kuma hali na kasala da yawan amai da zubda yawu da take, Wani irin tashin hankali ne ta ji ya mamaye ta,nan da nan ta fara zage zage da qudirin zubar da cikin,Sakeenah ta yi data sanin Sanar da Rasheedah hasashen da ta yi, tin Rasheedah na fad'a da zage zage Sakeenah na gane wa har ta dawo ta dena gane komai, kalmar Rasheedah ta qarshe ce ta daki kunnen ta, da sauri ta kalle ta da kallon amma baki da hankali ko? Sanan ta ce mata,
"Kin kuwa San me ki ke fad'a? Wai ke me ya sa a kullum ki ke adawa da dik wata ni'ima ko jarabawa da Allah ya ke maki a rayuwa? Kin kuwa San hakan da ki ke babban laifi ne? Ki kalle ni mana ban ishe ki misali bane, tare fa aka mana aure amma ko b'ari ban tab'a yi ba, ga qawayen mu da aka wa aure a bayan mu dik sun haihu, shine ke dan kin samu Allah ya baki ki ke so ki masa butulci?"
"Dalla malama rufe min baki, tinda Allah ya wanke miji d'an gaske ga dukiya ya baki dole ki ce haka mana, ni da ni ke cikin daular da ki ke Kuma bana haihuwa me zai damen, ba se kawai na ci duniya ta da tsinke ba, amma ki dube ni fa ki gani, dik gayu na da kyau na na b'ige a auren magini, maginin ma qaramin magini talaka, haka kawai se na hau tara Yara tsufa ya kamani da wuri, ga babu ga tsufa nan da an kwana biyu ya ce zai qara aure ko? To ba zai Yu ba,idan ba zaki goyi bayana ba ki kama gaban ki dama ban gayyace ki ba, ni banda baqin naci ma ban ga me ya sa ki ke min sintiri a gida ba, mtsww aikin banza"
Sakeenah na zubar da hawaye yau ma ta bar gidan yayar ta ta, ta na qudirta anya ba zata bi shawarar Adnan ba ta dena zuwa tinda ba ta San darajar ta ba.
Tafiyar Sakeenah ba jimawa Rasheedah ta hau kukan baqin ciki da data sani ta yi tsarin iyali, a qalla Yousuf ya qara wayo Kuma wataqila Kan nan arziqi ya same su, se ta ji dad'in sake jiki ta haihu, amma ga talauci ga taron Yara kamar a idi, inaaa ba zata Iya ba.
Auwal na shiga gidan ta je da gudu ta fad'a jikin shi, se kuka take ta na shagwaba tare da buga qafa a qasa, ya na mugun son wannan bangaren nata na shagwaba da runguma da narkewa da take a jikin shi, ya na sa ya ji kamar shi kad'ai ne Wanda ta jingina a jikin shi take neman ya warware mata wata matsala ko damuwar ta, qara rungume ta ya yi shima tsam a jikin shi, ya ja ta suka shiga d'aki, a bakin gado sika zauna ya hau tambayar ta meyake damun ta,
" Auwal na kasa cin abinci yau, zuciya ta na ta tashi, ga jiri danake yawan gani, wai shine fa daga zuwan yarinyar nan ta kallen wai ciki garen,"
Ta qarasa cikin matsanancin kuka, murna ce ta kama Auwal, ganin haka yasa ta tsagaita da kukan ta, ta kalle shi,
" Ya naga kana murna?" Amsa ya bata da,
"Ba dole ba Allah mai kyauta da qari ya qaran, Allah na gode maka, Allah ka sauke ta lafiya ka raya mana abinda ke cikin ta"
yana ta zabga addu'o'in shi ta ture shi tana bin shi da wani mugun kallo,
"To ni yaushe ma na warke da zan sake wata haihuwar? dika2 ko shekara biyu ban ba da haihuwa na sake wata? Ehhh tin da ba da duwawun ka za ai haihuwar ba kuma ba a cikin ka za a kwanta ba kayi murna mana"
Cikin kuka ta fice tana surutai, shidai bai ce mata komai ba, dan tabbas ya san ta wahala, ci gaba da cire kayan shi ya yi yana ta murna,ita ko parlor taje ta kwanta tana ta rusa kuka,har Yousuf yazo yana kuka sosai shima dan ganin ta na kuka, daka masa tsawa ta yi ta kore shi, shiru ya yi yaron yaqi tafiya kuma yana ta kallon ta, daga baya haka ta yi bacci a wajen, Auwal gyara mata kwanciya ya yi ya rab'a mata Yousuf ya fiddo mai cikakkun nonon ta ya bashi ya yi ta sha,har shima baccin ya dauke shi.
*****************************
Sakeenaa ce kwance ta yi zugum idonun ta sai tsiyayar da hawaye su ke, ko dai zuwa za ta yi wajen Maman ta ta sanar da ita rashin haihuwar ta wataqila zata sama mata wata mafita, Kai koma ba ta samu mafita ba a qalla zata samu ta yi sharing damuwar ta da Wanda zai damu da damuwar tata, ba kamar Rasheedah ba da bata damu da dik Wani hali da take ciki ba, shawara kawai take da zuciyar ta wani tinanin ya fad'o mata........
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Page 5:
Duk wani qoqari da yunquri na Hana tafiyar nan Rasheedah ta yi ta gaji, dan kuwa bata samu nasara ba, har nuna wa Abban su rashin dacewar karbar tayin tafiya makka da Adnan ya musu sai da ta yi,ta ce kar mutane su ce sun aura mashi 'yar su ne saboda abun duniyar da yake da shi, da ta ga Abban zai gano irin hassada da kyashin da take wa qanwar tata, sai ta fake da cewar wai a ganin ta tinda shi Abban na da azziqin shi shima ai be Kamata ya bari har Adnan ya ce ze biya masa ba, sannan ai ba yau ya fara zuwa hajjin ba, Abba kuwa ya ce mata,
"Rasheedah ai Adnan ko a hanya muka had'u ya biya min makka na koma Hajji da gudu zan karb'a ballantana ya na auren 'ya ta, Kuma ni ban banbanta a tsakanin surukai na da yaran da na haifa ba, musamman da abun ya zo da dikkan su marayu ne, dan haka mu yanzu ranar tafiya kawai muke Jira mutane kuma sai su yi ta fad'an abinda suka ga dama, ni dai Ina maki nasiha da ki riqe zumunci domin Allah, ki so 'yar uwar ki kamar yanda take son ki ko sama da haka, Allah ya had'a min Kan ku ya muku albarka"
Cike da yaqe dan ba haka ta so ba, ta amsa addu'ar shi sannan itama ta hau musu addu'o'in Allah ya Kai su lafiya ya dawo da su lafiya, har lokacin tafiya ya yi Kuma ba ta yi magana da Sakeenah ba akan tafiyar, har gidan ta Sakeenah ta je dan yi mata sallama da ta d'akko maganar tafiyar se ta kauce, ta hau yi mata Wani maganar, ko Kuma ta yi shiru ta qi cewa komai.
Ranar da zasu tafi kuwa ko gida bata je ba dan yin sallama da iyayen ta, ta waya ta kira su ta maqale murya ta ce bata da lafiya ba zata samu zuwa ba, fatan samun sauqi suka mata, suka yi sallama ta waya, Sakeenah na karb'a dan su yi sallama ta kashe wayar ta ta na zage zage.
Auwal kuwa ya ce mata,
"Shi yasa ma har yanzu ki ke a haka cikin talaucin da ki ke zagi, ke ce me qashin tsiya shi yasa har yau ban kudance ba, hassada Kuma ga Mai rabo taki in ji bahaushe" hararar shi ta yi suka ci gaba da fad'i in fad'a a tsakanin su.
Ko da suka Isa qasa Mai tsarki babu wasa babu kama hannun yaro dikkanin su se suka dirfafi ibada da yin abinda ya Kai su, Sakeenah ta dage da neman gafarar Allah da Kuma fatan Allah ya bata zuri'a mai albarka, Allah ya gafarta wa iyayen ta da dikkan musulmi, tayi addu'a sosai har wataran takan kasa furta me take so ta roqa se kawai ta fashe da kuka, Allah ya san abinda bawa ke so kafin ya furta.
kwanakin su na cika suka hau haramar dawowa Nijeria daga Makkah,inda su Mama da Abba suka dawo su kuma suka qara gaba yawon shaqatawa da bud'e ido, dan ya mata alqawarin jin dad'i matuqar yana raye da rai da lafiya kuma da arziqin shi, spain suka fara zuwa dan Sakeenah na son qasar ta na gani a TV yanda masoya ke shaqatawa, inda suka yi sati d'aya ji ta yi kamar kar su bar qasar, daga nan suka wuce Cairo, anan ne suka samu waje suka yi zaman su dama ya na da gida a qasar tin Wanda mahaifin shi ya siya musu saboda in sun je hutu su sauka a muhallin su ba hotel ba, rabi da kwatan kasuwancin Adnan dama a nan ya fi yawa, su na nan zaune har sai da Rasheedah ta haihu,mutanen gida na ta tambayar ta yaushe za su dawo ne? Sai ta ce musu su na nan tafe, a hankali ta fara gajiya da zaman qasar tinda watarana in ya fita ya na jimawa kafin ya koma gida sai ta yi ta kewar shi ta ji gidan ya mata girma ita kad'ai, a hankali ta fara masa kukan ita ta na so ta dawo gida, ganin hankalin ta ya yi gida ne ya Sanya shi siyan ticket din komawa Nija, Sakeenah dai na qaurnar dawowa qasar ta ta gado Nigeria (Allah ya qara mana lafiya da zaman lafiya a qasar mu ta gado ya zaba mana shugabanni na gari) shiri take cike da murna da doki, ta matsu ta ganta a gida she really want to see her family ta yi kewar su da yawa.
Adnan ya lula duniyar tinani Sakeenah na ta had'a musu kaya, a da yaqi su koma gida, so ya yi har sai ta samu ciki ta haihu, sannan su koma da jariri ko jinjirar su a hannu, ba dare ba rana kullum yana kan yin abu daya, kawai dan ya samu ta samu ciki ko hankalin ta ya kwanta ga addu'a su na ta yi amma shiru, a kullum tinanin me zai dan ya sama mata farin ciki yake,a wannan karon ya tabbatar da cewa komai son ya faranta mata Allah ya fishi son ta, kuma shi ya gadama bai bata ba dan haka sai ya ja baya ya barwa Allah ikon shi, har ta gama had'a kayan be sani ba ya na riqe da rigar ta da ya d'auka dan ya taya ta ninkewa,ta kalle shi ta jinjina Kai, dan ta san wannan dogon tinanin ba ya rasa nasaba da halin da take ciki, ita Kan ta ta San ta yi dacen miji Wanda kowacce mace a duniya zata yi fatan ace mijin ta ne, amshe rigar ta yi ta aje a saman gado, sannan ta raba qafafun ta ta zauna a jikin shi tare da saqale hannyen ta biyu a wuyan shi, ta hade goshin su waje d'aya ta ce,
"Tinanin me kk bayan gani kusa da kai, daka miqa hannun ka kuwa zaka tab'o ni, ni kuma daka tab'o ni zan taso willingly to give u what ever it is u desire from me,"
Murmushi suka yi a tare, ya lakace hancin ta, a binda bata so kenan ya lakace mata hanci shi Kuma sarar shi kenan, ai ko kan ya sauke hannun nashi ta kama ta ciza ta sauka da sauri ta gudu parlour,tabbas ya ji cizon ya shige shi,dan haka be b'ata lokaci ba ya bi bayan ta yana yarfe hannu kamar wadda ta gutsure wa yatsan, yana raki,
" Ka dena abu kamar wani karamin yaro mana please, se kace Wanda na cire wa yatsan? Maganin ka kenan tinda baka Jin magana....my love ka ga gobe zamu koma gida ka yi hakuri kar ka rama sai mun isa gida please ,"
"Lallai ma yarinyar nan, ni Zaki yi wa wayo? Se da ki ka cijen ki ce Zaki bani hakuri? Lala lala in ji larabawa, anan ki ka min anan zan rama"
Bin ta ya yi suka fara kewaye gidan,ga Sakeenah da gudun tsiya da zamiya,kullum suka fara irin haka sai dai ta basshi ya kama ta kawai in ta ga ya wahala, amma ba dai ya kamo ta da kan shi ba, ai ko gudu ta saka suna ta zagaye gidan, tana mai dariya yana mata warning ta tsaya shi ba abinda zai mata, tace tabb in ba abinda zai mata meyasa yake bin ta,kitchen ta shige ta boye a qasan dinning table da ke ciki,
" My love ki fito ki ji, ya isa wasan haka, kin shige nan in iska ta maki kadan fa,na yafe maki, i promise ba abinda zan maki,"
"Ka yi alqawarin?"
" Yes na yi alqawarin,just come out kin ji na yafe miki"
A hankali take tashi dan ta San halin shi be San inda take bane shi yasa yake mata wayo da ta fito ya kama ta, haka kuwa aka yi,dan tana fitowa ta na waige waige ta ga ta Ina ya tsaya ta ji