Showing 15001 words to 18000 words out of 81601 words

Chapter 6 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt

26 Oct 2025

313

na ce Allah ya jiqan iyayen mu da suka gabata ya kyautata makwancin su ya sa su yi alfahari da samun ka a matsayin d'a na gari Ameen"

"Dama ai ba godiya nake so ba, Dan nima iyaye na ne, addu'ar ki kawai nake buqata Dan kuwa addu'ar ki a gare ni haske ce, Kuma alkhairi ce, Dan tinda na had'u Dake alkhairai kala kala ke bibiyata wadannan addu'o'in naki na daga cikin abinda ke qara min ci gaba a rayuwa, kin ga kuwa ni ne ma zan maki godiya ko?"

Lips din shi ta kama da yatsan ta ta Dan ja, ta miqe ta gudu d'aki, da qarfi ya furta,

"Invitation aka bani in zo kenan? To Gani nan zuwa" da sauri ya bi ta d'akin suka rufe qofar abin su, Bai fito ba sai da aka kira magariba, ya wuce masallaci.

Sallah ta gabatar da azkar ta sake gyara abubuwan da suka b'ata, ta Dan watsa ruwa ta saka rigar baccin ta Mai kyau, ga tirarukan da  ta Sanya masu sanyin qamshi, sai ta Dora hijabin ta ta na jiran a yi isha'i, bayan ta idar da sallar isha'in ne ta shiga kitchen ta sama masu fruit salad da  chicken and potatoes salad sai Dan abun sha da ta had'a na abarba  qarfe tara na dare ya shigo, ya na hamma,

"Wai kin San ana idar da sallar isha'i kawai se bacci ya dauke ni, maqocin mu ne da zai tafi ya tashen shine muka taho"

"Ai dole bacci ya dauke ka, ka wuni aiki, ka dawo ban barka ka huta ba, I am sorry mine"

Kamo ta ya yi ya na Murmushi ya ce,

"Ni fa da na gan ki da qaton hijabi haka na San akwai wata harkar a qasa, zo nan in gani ba wata I am sorry,"

Guduwa ta yi suka hau zagaye kujerun Suna dariya, da kyar ya kama ta suka zube a kujera su na dariya,

"Dan Allah zo mu je mu ci abinci yunwa nake ji, na San kaima yunwa ka ke ji"

Da kyar ya barta suka jera ya na riqe da qugun ta, sai da ya fara ja mata kujera ta zauna sannan ya zauna Shima, ta zuba musu abinci suka fara ci.

Bayan sun kammala a tare suka gyara waje Wanda suka rage suka saka a fridge ya taya ta wanke kwanukan, suka kashe kayan kallo suka wuce d'aki, ni dai ban bi su ba dan lamarin su Adnan in kana binbini se ka ji kunya.

Bayan ya tafi aiki da safe ita Kuma da hantsi ta shirya ta ja motar ta ta yi gidan su ta sanar da iyayen su game da tafiyar da Adnan ya ce za su yi zuwa Hajji, ba qaramin murna suka yi ba, cikin tsananin farin ciki Mama ta sa waya ta kira  Rasheedah ta Sanar da ita abin farin cikin da ya same su dan ta taya su murna,wayyo Allah, Rasheedah ji ta yi kamar ta mutu dan baqin cikin daya kama ta, tana kashe wayar ta hau kuka,  Auwal ne ya riqe ta yana tambayar waya mutu cikin tashin hankali, banza ta yi da shi sai da tai kukan ya ishe ta sannan tace,

"Wannan banzar yarinyar ce zata makka,da su Mama, zan so ace ni na fara kai su, ba ita ba, amma dubi yanzu sabida auren talaka qanwar bayana ita zata kai iyayen mu makka,"

Ta qarasa cikin kuka, wani haushin ta ne ya kama shi kamar ya shaqe ta, ya na mamakin yanda bata Iya b'oye baqin ciki da hassadar ta har se ta yi kuka,anya Rasheedah ba 'yar tsuntuwa bace a gidan? Dan shi yanzu ba safai ya ke Jin haushin zagin da take masa na talauci ba, Cikin Jin haushin maganganun ta ya yi tsaki ya fice daga d'akin, d'aga kan ta  ta yi ta kalle shi ta murguda baki tare da hararar shi, sannan ta ce

"Ni ba dan son da nake maka ba na rantse da tini na bar gidan ka na auri mai kudi, haba namiji ace yau ko atampa super ko Holland din nan ba ka tab'a siya ka ce na Kai gida ba, balle shadda me d'an maiqo, kamar Kai ka kawo talauci duniya"

Yousuf ne ya shigo yana kuka yayi kashi, wani haushi ne ya qara kamata kamar ta kama yaron ta yi ta duka, da mai kud'i ta aura yanzu ai da tana da masu aiki, ga Sakeenah nan masu aikin ta kusan biyar, wai a haka ma bata son masu girki, gyara parlourn ta guda uku da sauran dakuna kawai ake mata se kula da tsakar gidan da fulawowi da wankin su da sauran abubuwa, amma dik wata hidimar Adnan da kanta take yi,cikin fushi ta miqewa ta daka masa tsawa akan  ya bar mata kuka kan ta doke shi, aiko qara b'are baki ya yi, tako kama shi da jibga,ba ta yi aune ba ta ji maruka masu lafiya ta kowanne gefen fuskar ta, ihu ta kurma ta hau bori,

"Dan iskanci kina nan kina shashanci da muguwar hassada yaro ya dakko po zai hau ya kasa cire wando har yayi a jiki shine zaki hau d'a da duka,ke wa ya dake ki a jakancin da kike wa mutane",( makaranta kuji fa har jaka mijin ta ke kiran ta sabida tana mai halayen su) kuka ta ke sosai, ga baqin cikin da ke cin ta in ta tina tafiyar su Sakeenah,ga duka taci a hannun miji,sannan ya sata gaba ta wanke kashin dole,ta na kuka take  wanke masa ta shirya shi, ta koma ta kwanta, tinanin wannan tafiyar da zasu yi take ta yi anyaa zata bari a yi tafiyar nan kuwa?...........

*Readers barkan mu da safiya, anya Rasheedah na da head kuwa?*
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAINE JARUMI 💅🏼







WRITTEN BY HAERMEEBRAERH





*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani,  ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra   3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da  kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*


Page 7:




Kafin washegarin ranar aman da ta yi ya fi uku, duk ta fita hayyacin ta, da asuba sallah kawai Adnan ya yi ya kwashe ta sai asibiti, suna zuwa aka hau duba ta, nan take suka gane zazzabi ne kawai ke damun ta, saboda damuwa da ta yi mata yawa, qara mata ruwa aka yi saboda ta samu kwarin jikin ta dan aman da ta yi ya galabaitar da ita, se aka had'a mata da magungunan da za su saukar da zazzabin, likita Kuma ya bata shawarwari na ta qoqarta ta yi avoiding duk Wani abu da zai sa ta shiga damuwa saboda kiyaye Kan ta daga kamuwa da cutar hawan jini, daga baya ya ce wa Adnan ya biyo shi office d'in shi ya na so ya yi magana da shi.

A tare suka shiga office din , Dr. Uwais ya zagaya ya zauna a kujerar shi sannan ya wa Adnan nuni da kujerar da ke gaban shi ya ce ya zauna, zama ya yi Suna fuskantar juna likita ya cire gilashin shi ya kalli Adnan ya ce,

"Alhaji Adnan a iya sanin da na Maka na San Kai me kula da lafiyar ka da ta iyalin ka ce, amma garin yaya ka bari wannan ciwo ke qoqarin kama matar ka? Ka sani fa matar ka na gab da kamuwa da hawan jini, binciken mu da Kuma tambayoyin da na mata ya nuna akwai matiqar damuwa a tattare da ita, wataqila akwai abinda kk mata na rashin jin dad'i ya sa hakan ke Shirin faruwa da ita, Wanda in haka ne zan yi matuqar mamaki, Iya sani na da Kai Kai mutum ne Mai kula da dik Wanda ke qarqashin shi ballantana matar da kowa ya shaida kana so Kuma kana kula da ita fiye da Kan ka na sani tsakanin miji da mata sai Allah, amma dai dan Allah ka duba kai qoqari ka gyara, ka dinga faranta mata kamar yanda ka saba, ka ci gaba da  kula da amanar da Allah ya baka, in kuma ta wani wajen take samun damuwa ka qoqarta kaga ka toshe mata wannan kafar damuwar, gaba ake gudu,ina fatan ban yi maka katsalandam a harkokin iyalin ka ba,shawara ce a matsayi na na d'an uwan ka Kuma likitan iyalin ka,wadda Ina ganin in kabi a sannu zata samu sauqi da wuri Kuma za a gujewa wannan mugun ciwo na hawan jini,"

kad'a wa likitan kai Adnan ya yi cikin sauri da kuma gamsuwa da bayanan shi,

"Sam Uwais raina be b'aci ba,ta  ya zaka bata min raina akan gaskiya? na ji dad'in shawarwarin ka ainun, amma ina mai sanar maka daga yau damuwar ta zata kau da yardar Allah,Kuma Ina so ka sani bana daga cikin silar damuwar ta amma na san musabbabin hakan Kuma zan d'au mataki akai, haba Kai ma ka San yanda nake son Sakeenaah ba zan cutar da ita ba, na gode Uwais in ka je gida ka gaida su Baffah bari na koma wajen ta,Ka wuni lfy"

Uwais cousin d'in Adnan ne, Baban Uwais Yaya ne ga mahaifin Adnan,anan asibitin suke ganin likita, Kuma suke zuwa medical check up.

Sallama suka yi da juna, ya wuce d'akin da aka ajiye ta,ya tarar da ita waje d'aya ta dafe kai,tana ta tinani kala2 bama ta san ya iso ba,

"Kin gani ba, yanzunnan aka maki maganar rage damuwa amma kin zo kin takura kan ki anan, haba Sakeenaah so kk ki kamu da ciwon da ni zai zame wa masifa da bala'i? Tinda sanin Kan ki ne dik halin qunci ko rashin lafiyar da ki ke ciki na fi ki shiga damuwa, in Kuma ba so ki ke ki rasa ni ba gaba d'aya Dan Allah ki Dena shiga damuwa"

  Cikin hawaye ta gyada kai,

"To in dai baki son rasa ni ki daina damuwa, komai da ya faru ki d'auka bai faruba ba zan yafewa kaina ba idan wani abu ya same ki,?"

Dr. Uwais be sallame ta ba sai yamma,kafin a sallame tan Adnan be Sanar da kowa halin da suke ciki ba shi da masu aikin su ne sukai ta dawainiya da ita, kama Daga Kan abinci ne da Duk wata kulawa dai da take buqata har aka sallame su da la'asar.

Bayan sun dawo gida wanka ya mata da ruwa mai dumi sosai jikin ta ya gasu sosai, ta ji dad'in wankan, shima yayi, qananan kaya suka saka dan su sha iska daga nan se suka koma parlor,amfani ya yi da comb ya hau taje mata gashin ta suna ta hira ya na bata labarai na abun dariya, ita Kuma ta na ta sheqa dariya abunta kamar bata da wata sauran damuwa a duniya,da kanta ta sa band ta daure Kan nata ya dawo gaban ta ya kalle ta ya qara ya ga yanda ta yi kyau se qamshi take budawa,rungume ta ya yi ta na mishi dariyar yanda yake ta yabon kyan ta daga baya ya sake ta ya je ya kunna mata kallo ya sunkuya ya sumbaci goshin ta sannan  ya wuce kitchen,bayan shi ta bi da kallo ta na yi masa addu'a a zuciyar ta,murmushin ta mai kyau dake bayyanar da hushiryar ta ta saki,ya na juyawa suka had'a Ido kuwa ,ya ji dad'in ganin wannan tsadadden murmushin nata, hakan na nuna masa ta fara warewa kenan, a qasan ranta tana qoqarin mantawa da komai, daga zancen haihuwar har abinda yayar ta ta ke mata,so take ta fifita farin cikin mijin ta da ita Kan ta akan kowa yanzu,yanda Adnan ya damu da halin da take ciki ya na bata tausayi sosai dan har  'yar rama ya yi a dare d'aya, tana wannan tinanin ya iso dauke da faranti babba a hannun shi, tarkacen kwalamar ta da ta Saba ci ya deb'o mata dan kawai ranta ya yi fari, dangin su Chocolate da biscuit ne da ice cream, sai Apple,shi dai kawai ya lodo komai da ya Kan ga ta na ci dan bai san me zai fi faranta mata ba a yanzun da bata da lafiya,aiko tana gani ta hau masa dariya, dan ta fuskanci gaba daya bai ma san me zai kawo mata ba,

"Ko kina son wani abu da ban saka ba ne a cikin nan? ko banana kk so, ko kina son juice ? Aikuwa kin ga na manta ban dakko ba bari na kawo miki,"

Miqewa ta yi ta amshi farantin ta aje a center table, ta je gare shi, d'afe shi ta yi kamar wata mage haka ta shige jikin shi, ya d'aga ta da kyau ita ko ta saqale qafafun ta a qugun shi,ta kwantar da fuskar ta a wuyan shi, a hankali, numfashin ta na dukan wuyan nashi, kama ta ya yi da kyau sannan ya samu waje ya musu masauki a kujera, a hankali ta ke masa rad'a a kunnen shi,

"Ina son ka mijina,ina qaunar ka, Allah ya faranta maka yanda kk faranta min, Allah ya jiqan iyayen ka ya sanya su a aljanna,Allah ya kyautata makwancin su, kafin a samu namiji kamar ka a wannan zamanin sai an sha wahala, KAI NE JARUMI na ni Sakeenah Allah ya barmu tare har abada, Allah ya bani iKon kyautata Maka sama da ya da ka ke kyautata min"

Wani irin dad'i addu'o'in ta ke masa tare da narkar da zuciyar shi a kogin qaunar ta da girmama ta,lumshe Ido kawai yake ya na bin ta da kallon qauna,Sakeenah na kashe masa gab'ob'in jiki da addu'ar da take wa iyayen shi iyayen shi shi kad'ai suka haifa amma samuwar Sakeenah a rayuwar shi ya sa Yana Jin kamar su biyu suka bari a duniya, bata gajiya da yi musu addu'o'i a kowacce Rana ta duniya ko Mai ya mata in ta ji dad'i sai ta musu kyakkyawar addu'a,ya tallabo fuskar ta ya dago ta sosai suka fuskanci juna,magana yake son yi ya kasa furta komai, ji ya yi ta ce masa

"Dauke ni mu je d'aki miji na"

Murmushi ya saki ya manna fuskar shi a jikin ta, ba musu Adnan ya sungume ta sukai d'aka abun su Suna dariya, tin a hanya ta fara gigita shi, dana ga haka nace tabbas ba wani rahoto daidai ni bari na cinye kwalamar ta ta☹

(To jama'atul musulmi Dan mace na period ba shi zai hana ta shiga aza room da mijin ta ba, saduwa ce take haramun, dik abinda za su yi da be sab'awa Allah ba suna Iya abun su Dan faranta ran junan su)

***************************

Rasheedah ce ke ta sharar baccin ta tin daren jiyan bata farka ba balle ta yi wankan tsarki ta yi sallah, ko kuka yaron ta ya yi Auwal ke Kara shi jikin Nono ya sha ya koma bacci se kace wadda tai aikin qarfi,ta na nan kwance har sai da Yousuf ya tada ta ya yi kashi a poo ya na so a wanke masa sannan ta miqe, ta je ta wanke masa ta yo wanka ta sa kaya ta tada sallah rana na kallon ta gatso gatso,a hanzarce ta jejjefa sallar ta ninke sallaya  ta zo ta dafa masu taliya, da manja da yaji, ta duba kayan da aka kawo mata jiyan, wasu qananan kaya ne masu matuqar kyau riga da wando kalar orange, masu matuqar kyau da tsada ta dauka har zata saka, can wata zuciyar ta ce mata

'ke me zaki saka kayan qanwar bayan ki kiyi da su? Kawai kije ki siyar ki sai wasu sauran kudin kin kashe wata hidimar da su'

Ta yi amanna da shawarar kuwa dan haka ba b'ata lokaci ta samu Sulaiman ta masa kwaskwarima Yousuf ma ta masa,ta saka masu wasu kayan ta dau wad'anda take ganin zata siyar suka rufe gida su ka yi gaba, suna fita wani babban shago ta je a layin nasu da suke saida yan kayyaki haka,taje ta masu bayanin kawo mata akai jiya ita kuma ba ta son sawa tace bari ta saida, aiko yana gani shima dan son banza ya hau d'aga wa ya na kalla, wasu riga da wando ne suka dauki hankalin shi ya riqe wandon ya na kallo, tambayar ta ya yi nawa zata siyar masa wandon, ta ce ko nawa ne ya bata dan ba sanin kud'in su ta yi ba,iya wandon dake mahad'in rigar zaiyi k, amma haka ya hada dika da rigar da wandon ya bata 4k, sauran ma haka ya yi ta musu siyan wulaqanci, a haka ta tashi da 37k dad'i ne ya kama ta kamar ta suma,   kasuwa ta wuce daga nan ta siyo atampopi uku, ta saiwa yaran suma yan kayan da ba Wani tsada gare su ko quality ba, ta hado kan sauran canjin ta ta yi cefane har da kaji biyu, tayo gida.

A qofar gida ta ganshi ya cika ya yi fam,sai a sannann gabanta ya fadi, dan kwata2 ta manta da shi, salati ta hau yi, kan ta iso qofar gidan itama ta dake ta b'ata rai sosai kamar yanda ta ga ya yi, yana ganin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login