Showing 9001 words to 12000 words out of 81601 words
Chapter 4 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
ya cafke ta ta baya,qara ta saka, sannan ta yi ta dariya, sama ya yi da ita yana fad'in
" Wa na kamaa?"
"Please Mine ka kyale ni,ka fa yi alqawarin ka yafe min"
" Yes na maki alqawarin ba zan rama ba, amma ai ban maki alqawarin hana ki soyayya ta ba ko?"
Yana fada yana dorata kan dinning table dake cikin kitchen din yana dariya, dariyar ta ta rage tana jifan shi da Wani mayataccen kallon da ya sake birkita shi, nan da nan zuciyar shi ta hau tsananin bugawa, idanun shi sun nuna zallar yanda ya ke Jin ta a zuciyar shi, gani na yi kamar ba layin Yara suka fara d'auka ba se na ja qofar kitchen d'in na koma kallon cartoon a parlour.
Washegari da misalin qarfe takwas na safe jirgin su ya tashi daga Ciro international airport zuwa Nigeria,tafiyar awanni biyar ne da 'yan mintuna ta iso da su Aminu Kano international airport,cikin baccin da be jima da daukan ta ba ta ji ana sanar masu isowar su gida Nijeria, zasu sauka ta garin kano, dad'i ne ya kamata, cikin zuciyar ta take jin dama ace tana sauka taga mutanen gidan su da Rasheedah da babyn ta, inama ta bude ido ta ganta gaban ta ta rungume ta ita da abinda ta haifa da Yousuf.
"Tinanin me kike?"
"Tinanin Mama da Abba da Rasheedah da iyalan ta nake, ba qaramin son na gan su nake ba,"
"karki damu ko da dare ne zan kai ki wajen su in baki gaji ba ,"
Maqale hannun shi ta yi dan murna, ji ta yi in ya mata haka ya gama mata komai,suna sauka drivern shi ne ya zo daukar su, bakin shi yaqi rufuwa dan murnar ganin iyayen d'akin nashi, koba komai suna cin mai kyau, suna shan mai kyau sanda Hajiya na nan,amma tin da suka tafi sai dai su saya su ci, ko su ci girkin masu aikin ta mata, a cewar su kuwa basu Iya komai ba.
Wanka da sallahr azahar kawai Sakeenah ta yi ta hau bud'e akwatuna da jakunkunan da ta yo wa mutanen gidan su tsaraba, ta hau ware na kowa ta na sa wa a inda ya dace lokacin da ta gama qarfe uku na rana ta yi, gani ta yi da sauran lokaci kafin su fita, gashi ta Saba wa Adnan da cin abincin ta, tashi ta yi ta fad'a kitchen sai hana ta yake ya na cewa ta zauna ta huta, ta ce,
"Se kace wadda ta tuqo jirgin? Ni da na sha bacci na ma ka bari kawai na sama mana abu me sauqi yanzun nan"
Cikin ranta ta na ayyana ai dole ne ta kyautata masa duba da yanda yake kyautata mata da iyayen ta Shima, ko a can waje da suka je, ita ke masu girki, har abokan shi na can yake kawowa, suci su qoshi Kuma su na yaba mata sosai.
Dama da suka dawo ta tarar da gida a share a goge fes, sai dakin shi da nata ne kawai ba a gyara ba, saboda basu bar ma key ba balle a gyara, da niyyar in ta gama girkin zata shiga ta gyara ta na zuwa da kayan shara da goge goge ta ga har ya sauya zanin gado, ya wanke bathroom, godiya ta masa sannan ta ce ya bata waje ta qarasa shi Kuma ya qi, ya ce sai dai su yi tare, ba yanda ta iya da shi haka suka had'u suka gyara dakunan su tare, har mamaki Adnan ke bata in ya na ayyuka irin wannan a gida, kamar ba shi ne hamshaqin Mai kud'in nan ba, Wanda ake nunowa a TV ya na baza babbar riga da baza turanci, lokuta da dama in ta masa qorafi akan yanda yake mata aikace aikace sai ya ce mata,
"Sakeenah dik dukiya ta da d'aukaka ta da Wani qasaita ta bata Kai ta fiyayyen halitta ba, ni ba kowa bane a Kan shi amma Yana yi wa iyalan shi hidima, shi ne Wanda ya fi kowa kyautata wa iyalan shi, ni Kuma Ina so na yi koyi da shi, ko da ace ban yi komai da yake yi Sak da Sak ba Ina so na kwatanta, sannan in ban miki ba wa zan yi wa ban da uwa banda uba bani da Yaya bani da qanne se kawunai da baffani ke shaida ce Ina kyautata musu Ina sada zumunci na da su, amma ke ce a yanzu ya zama dole na ba wa kulawa sama da kowa a rayuwa ta"
Duk sanda ya fad'a mata haka ta kan ji wai shin ita me ma take masa ne a rayuwar zaman su na kyautatawa?
Su na kammalawa suka yi wankan su a tare, kamar ko da yaushe doguwar riga ta saka da ta siya a can Ciro,ta yi rolling Kan ta da mayafin rigar ruwan Zuma da ta sha adon stones da saqa me kyau a jikin ta,ta yi matuqar kyau, baqin ta irin mai sheqin nan ya na ta d'aukan Ido sosai, duk wanda ya kalle ta sau daya sai ya yi na biyu,niqab din ta ta daura, ta samu waje tana jiran shi ya idar da sallah, su na wanka ta ga baqon ta ya zo (period) se kawai ta ke tasbihi daga zaunen, subhanallahi wa bihamdihi subhanallahil azeem, astaghfirullah wa'atubu ilaik ya rahman, subhanallah, Alhamdu lilLAAH, Allahu Akbar, subhanallahi wa bihamdihi adadakhalqihi waridhanafsihi wazinatu arshihi wamidadakalimatih,su take ta maimaitawa,dama Sakeenah ta riga ta Saba da yawan tasbihi ko aiki take ana samun ta tana hailala, da hauqala,ko hira take a ka dan yi shiru to fa za a ga ta na tasbihin ta( hakan na sa mutum ya zama mai kwarjini bayan ladan da zai samu, Allah zai so shi, dan shima yana son Allah, sai kana son abu kk ambaton shi, sannan Allah zai sa bayin shi na gari su soka kaima, akwai fa'idodi marasa adadi wajen ambaton Allah, wadda ta ke yi Koda yaushe zata fi gane me nake fad'a)tana zaunen ya shigo kallon' kina burge ni Sakeenah ta' ya bita da shi, dan ba qaramin kyau ta masa ba a hakan, hanun ta ya kama ya miqar da ita su na Yi wa junan su Murmushi, sannan ya dauki akwatuna biyu da jakar ta suka fita
Gate me gadin gidan su ya bud'e wa Adnan ya fitar da mota shi ba su tsaya a ko Ina ba sai a qofar gidan su Rasheedah, da sauri Sakeenah ta bud'e motar ta shige ciki tana kwalawa yayar ta ta kira dan gidan Rasheedah ya fi kusa da gidan ta akan gidan iyayen su shi yasa suka fara zuwa nan, yousuf na zaune yana cin tuwon masara miyar kubewa d'anya, ta ji kifi, ai ko ta d'aga shi sama ta yi tana masa wasa, yana ta dariya, dik da lokacin da suka tafi yana qarami, shekarar shi bata fi daya da watanni ba, dan haka ba wani gane ta ya yi sosai ba,
"Ina baby Sulaiman yake? Da kewar ku na dawo Yara na a ban Sulaiman na gan shi, gani na dawo a bani yaro na in ganiiiii"
Yatsina fuska Rasheedah ta yi ganin irin shigar alfarma da kyaun da qanwar ta ta sake yi kamar wata baqar balarabiya,miqa mata shi ta yi ta na yatsina, Auwal kuwa na mata sannu da zuwa tare da miqa mata yaron da ke hannun shi ya na bacci, Rasheedah ce ta kasa boye yanda take ji game da kyan da Sakeenah ta yi, madadin ta yabe ta Kai tsaye se cewa ta yi,
"Ko dai ciki ne da ke naga kin qara kyau,"
Murmushi Sakeenah ta yi ta d'an rungume Rasheedah da gefen hannun ta na dama ta ce,
"Ba ciki bane, dan yanzu ma bani da tsarki"
" kaiii Sakeenaa halin ki na yarinta na damuna ni dan Allah sake min kafad'a kar ki karya ni ki takaici Yara na, tinda kin d'auke shi gashi nan ki gan shi kafin ya yi fushi ya ce se yau kk zo ganin shi"
Sakeenah dai bata kula ta ba, dan yau Cike take da farin cikin ganin su,ba zata biye mata ba ta b'ata mata rai a banza, sake rungime yaron ta yi ta sumbace shi a chiks din shi both side,fuskar ta na dauke da murmushin da ke bayyana hushiryar ta, itama dai Rasheeda yau duk baqin halin ta sai da ta murmusa, ganin yanda qanwarta ke son yaran ta kamar ita ta haife su, wata mummunar zuciyar ta ce ta ce mata,
'ke mara wayo ja can dan bata taba haihuwa bane take son yaran ba dan wai tana qaunar su ba har ran ta, da ace ta na da nata ko kallo basu ishe ta ba, yanda suke cikin daula ba ganin ta ma ba Zaki na Yi ba, ki duba ki ga jimawar da suka je suka yi a qasar waje kamar ba za su dawo ba'
'Dan gajeren tsaki ta yi ta zauna, Sakeenah kuwa waje ta yi ta miqawa Adnan yaron ya ko yi masa addu'a Auwal ma bin ta ya yi dan su gaisa da Adnan d'in, yana isa ya washe baki ya ce,
"Larabawan makka da Madina barka da dawowa yallabai, ai na zaci ba Zaku dawo ba na ce dan Allah a kawo min qanwata ta zo ta ga d'an ta, .....ya ka tsaya a waje Bismillah malam Adnan mu shiga ciki,"
Adnan kad'a kai ya yi ya na dariyar barkwancin Auwal sannan yace,
"Da azahar muka dawo fa qanwar nan taka Mai rikici ta kafe ita se ta ga Mama da Abba da yaran ta, ni Kuma ka San burin ta kamar umarni ne a gare ni, dole ne na cika mata shi....amma da ka fara shiga kaga yanayin wajen zai yu na shigo kai tsaye?"
Auwal yaji daɗin hakan dan ya San halin gimbiyar tashi, ya baro ta zaune da daurin qirji dama haka take yawan zama a gidan, ko a same ta da riga daban zani daban kamar mara tufafi, ko da baya samun d'inka mata kaya masu tsada, amma baya rabo da sai mata kayan sawa daidai qarfin shi, Kuma a gida ma ana mata sutura Sakeenah na kawo mata, ta saka complete ne take ganin asara.
Shiga ya yi ya mata magana za su shigo da Adnan,dan kwalin ta ta ware ta yafa tana qunqunin za a hana ta sakewa ita da gidan ta, dan rowa da son abun duniya irin na masu kud'in yanzu, su barta ta je masu oyoyon shine ba za su bari ba, sai da suka biyo ta dan kar ta je ta dangwali arziqi, kan ta rufe bakin ta da mitar ta ga an jawo akwati an shigo da shi, cike da takaici Sakeenaa ta kalle ta dan kuwa ita da Adnan ba abinda basu ji ba.......
Rasheedah a sauya hali......
.
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
*ZINARIYAR MACE⚡*
*Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.*
Na gyaran nono.
Na sanyi.
Dilka tare da hadin sabulu.
Duk Wani nau'in maganin mata.
Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani.
*08089965176*
*07084653262*
Page 6:
Wani yawu ta had'iya ji ka ke "maqawat" se zare Ido take,idanun ta akan akwatin da ke hannun Adnan, kallo suka bita da shi jin maganganun da take sun tsaya cak, ba kunya ba Jin nauyin kowa Rasheedah ta miqe daga inda take zaune ta Isa gaban su,hannun ta na rawa fuskar ta d'auke da murmushi da zumud'i ta durqusa gefen Adnan tana masa sannu da zuwa, tare da qoqarin karbar akwatin hannun shi,nan take Auwal ya watsa mata wani mugun kallon da yasa ta ja baya tana zumburo baki, Adnan da Sakeena kad'a kai suka yi dan tsananin takaicin halayen ta, miqa mata akwatin Adnan ya yi har tana tuntube da qafar Yousuf ta karb'e,kuka Yousuf ya sa dan taka shin da ta yi,ko ta kan shi bata bi ba, ta kama akwatin ta yi parlour ta dora saman kujera, qoqarin budewa ta hau yi abun ta, ba godiya ba komai, ba tambayar na waye? Adnan ne yace mata,
"Ga tsarabar ku nan Daga Sakeenah ta had'o harda kayan bbyn ta da aka haifa bata nan, Allah ya raya ya sanya albarka, ni kuma ga nawa a sai wa yaro wani abu,"
Ya zaro kud'in da ban gane ko nawa bane, ya miqawa Auwal, zumbur ta yi ta matso da niyyar karb'a taga har Auwal ya karb'a, wani haushin ta ne ya kama dikkan su, a wannan lokacin ko Sakeenaah idon ta ya cika fam da hawaye, qoqari kawai take wajen riqe su, tin da ta zo fa duk d'okin ganin yayar ta ta, ita ko a jikin ta ba ta nuna ma tana farin ciki da ganin ta ba, kuma bata mata kyakkyawan sannu da zuwa ba, amma da ganin abun duniya ta rud'e, anyaaa????
"To mu zamu wuce dare na yi asuba ta gari,dan a yau muka so duba su Mama ma, amma da alama se dai mu bari zuwa gobe saboda dare ya yi"
Adnan ne ya furta hakan ganin yanda matar shi take gab da fashewa da kukan baqin ciki, kamo hannun ta ya yi, a hankali ta furta masu,
"Sai da safen ku Yayah Auwal ...
My boy kayi bacci lfy ko Allah ya muku albarka,"
Kuka Yousuf yasa sosai da zasu tafi,ya maqale ta, sai zabga ihu yake yana fad'in zai bisu, Sakeenaah ce ta ce,
"Yayah Dan Allah ku bamu shi mu tafi da shi mana, in ya so gobe in zamu je gidan Mama sai mu kawo shi"
Cikin Jin dad'in yanda Sakeenah ke son yaran su Auwal ya ce,
"Dakko mai kayan shi ya bisu,dan kin san shi da kafiya ko sun tafi ba zai daina kukan nan ba ya samu abin yi kenan yau,"
Wani mugun kallo Rasheedah ta watsa wa Auwal, sannan ta kalli yanda Sakeena ta kwantar da yaron a kafadar ta yake ta ajiyar zuciya, ita kuma tana shafa bayan shi cikin lumshe ido da kaunar yaron,
" A'a a ,a bar min d'ana a gidan uban shi domin shi bai saba da gidan masu akwai ba, da gidan talakawa ya saba,haka kawai ya je ya ji dad'in gidan masu arziqi nan gidan ya gagare shi zama, ba zai yu ba,"
Cike da rashin mutunci na ba sani ba sabo take maganar, cikin kuka mai qarfi Sakeenaa ta dire yaron ta fita da gudun ta, tana kuka, Adnan ji ya yi kamar ya shaqe Rasheedah, wani mugun kallo ya watsa mata ya matsa daf da ita ya na nuna ta da yatsan shi manuni ya ce,
"Wai ke wace iriyar mahaukaciyar mata ce wadda bata San menene zumunci ba, bata San mene ne so da qauna irin ta 'yan uwantaka ba? Anya Rasheedah ki na da zuciya a qirjin ki kuwa? To ga d'an naki nan an bar maki Dan Allah ki jiqa shi ki shanye shi idan ana sha wawuyar banza kawai, kuma in Allah ya yarda in dai ni ne mijin Sakeenaah ba zaki qara ganin ta taka qafar ta ba a gidan ku, sai dai in kin canja hali, Allah ya cece ki na ga qafar ki Kuma a gidan masu halin ki ga yanda zan maida ki, shashasha kawai,"
Cike da fushi ya fice, Auwal kuwa daskarewa ya yi a wajen , kunya, tsoron halin matar shi, da kuma tausayin Sakeenaah ne danqare a zuciyar shi, kasa ce mata komai ya yi, dan yana ganin in dai ya yi magana ta mai shirme sai ya kirb'e ta kamar kubewa a turmi, d'aukan Yousuf ya yi da yake ta tsala kuka, ya zaro alawa a aljihun shi ya b'are masa ya bashi, da qin karb'a ya yi da fari, amma da wayo da dabara ya hakura ya karb'a ya yi shiru, nan da nan bacci ya dauke shi, a haka ya dauke shi suka je tare ya rufe gidan sannan ya wanke masa hannu da baki, daya ci tuwo dazun, ya kai shi ya kwantar da shi a shimfidar shi, ya dakko Sulaiman ma ya kwantar, sannan shima ya bi lafiyar gadon su ya yi masu addu'a dika ya fara bacci, gimbiyar na can tana d'aga wannan ta aje, ga murnar samun kaya, ga baqin cikin sanin Daga inda kayan suka fito danqare a ranta, wannan wai tsarabar su ce daga qanwar ta, Allah kada'i yasan ita wanne irin kaya ta lodowa kan ta, oh duniya, taya za a ce qanwarta ita ke da arziqi sai dai ta na sammata, amma ita tana zaune hmmm Allah ya kyauta,
Hassada kenan, kana nuna wa Allah be Iya rabo ba, subhanallah, to Duk me wannan halin ya shirya shiga tashin hankali duniya da lahira, hassada yanzu ta yi wa mutane yawa da katutu a zuciya, d'an uwa na yi wa d'an uwan shi hassada, miji ko mata na wa juna hassada, maqoci da maqoci hassada, yanzu a social media ma da baka tab'a ganin mutum ba, da ka ga Wani ci gaba ya same shi se ka