Showing 27001 words to 30000 words out of 81601 words
Chapter 10 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
hankalina ya tashi,na zaci Wani abu ne ya same ki"
" kwantar da hankalin ka Mine gani na dawo ai ko? Jiki na ne ban gane masa ba shine na tafi na San in na Sanar da Kai kana Iya barin aikin ka ka taho bayan zan iya Kai kaina, ai hakan be Kamata ba ko? Alhamdulillah zuwa na ya yi amfani dan kuwa na samu shawarwari masu mahimmanci daga wajen likita, na samu kwarin guiwa da kwanciyar hankalin da nake buqata, amma har yanzu Ina da damuwata guda d'aya,"
Cikin sauri ya ce,
"Meye damuwar ki?"
Murmushi ta yi mai ciwo,
"Damuwa ta ka riga ka santa ka qi kawai ka karb'e ta ne, bama ka so na dinga fad'a, kuma ina kyautata zaton in ban samu wannan alfarmar daga wajen ka ba ko mutuwa na yi ruhina ba zai samu nutsuwa ba,"
Kuka ta saka sosai harda shessheqa,
"Ki daina kuka mana, amma kin san abinda kk nema a wajena mai wahala ne, kar ki manta fa nima banda kowa makusaci a yanzu sai ku, ya zan iya hakuri ina kallon abun da na san nawa ne zai wulaqanta kuma na kasa tab'uka komai, dan na yi imani da Allah zuri'ar ki ta shiga hannun wannan muguwar yarinyar ba za su ji da dad'i ba, sannan wa ya fad'a maki ma zata yarda ta riqe maki yaro ko yarinya? Kuma wama ya Sanar da ke ba Zaki rayu da abinda Zaki haifa ba? Kar ki manta fa ni da ke abu d'aya ne, ba ke kad'ai ke so na ba, nima Ina son ki, to ta ya ya Zaki dinga yin maganganun da za su kassara zuciya ta, ko so ki ke Nima na kamu da Wani ciwon?"
Cikin kuka ta ke kad'a Kai alamar Ah ah, rungume ta ya yi ya na shafa bayan ta a hankali ya ci gaba da fad'in,
"Haka aka ce maki daga haihuwa d'aya mutum zai mutu ko me? ko kuwa mutane nawa ne masu hawan jini kuma sike haihuwa su rayu? Ni ki daina ma wannan maganar dan Allah kina sawa ina shiga damuwa sosai,"
Share hawayen ta tayi sannan ta qoqarta tashi zaune da kyau ta shige daki, sai magana yake mata bata kula shi ba,ai kuwa hankalin shi ya tashi, ko dai da gaske mutuwa zata yi ta bar shi? komawa ya yi ya zauna ya fasa bin ta, hannun shi biyu ya Sanya ya tallabe fuskar shi ya saki kuka mai d'aci, zuciyar shi ya ji ta matse masa waje d'aya ta na quna,
" Ya Allah kar ka raba ni da mata ta, ina son ta, Allah ka sauke ta lafiya da abinda ke cikin ta Allah ka fini son ta Allah ka mana zab'in alkhairi,"
Abinci ta fito zata deb'o ta Jiyo kukan shi da addu'ar shi, sai ta koma da baya ta jingina da gini,itama kukan take,daga baya ta share hawayen ta ta fita, kitchen ta wuce ta fara diban abinci,zuwa ya yi ta bayan ta ya kwantar da kan shi a bayan ta cikin matacciyar muryar da ba a son yin magana da ita ya ce,
"Na amince da buqatar ki ki daina saka damuwa a ranki, Allah ya sauke ki lafiya"
Murmushi ta yi ta juyo ta hau sumbatar shi, sai da ta dangana shi da jikin gas sannan ta sake shi tana ta godiya, yaqe kawai yake haka ta debi abincin ta suka koma parlour ta na ci ta na sake nuna masa dalilin da ya sa take son aikata hakan, Wanda shi Sam be dauki hakan a Wani babban dalili ba Banda takurawa abinda zata haifa da Sanya shi cikin damuwa da baqin ciki kamar yanda ta rayu a cikin su saboda yayar ta ta.
A kwana a tashi yau cikin Rasheedah da Sakeenaa ya shiga watan haihuwar su wato watanni tara cip2, wanda Sakeenaah ko alamar naquda bata ji, amma Rasheedah kam tin kwana biyu da suka wuce take fama da ciwon baya da mara, yau abun ya tsanan ta, cikin taimakon Allah Auwal ya kaita asibitin da ta saba haihuwa,bayan gumurzu da artabu a d'akin haihuwar ta sillub'o diyar ta mace mai kama da ita sak kyakkyawa masha Allah, labari ya iske ma su Sakeenaah, inda cikin zumud'i ta hau girke2 da shirin zuwa asibitin dan ganin jinjirar, Adnan kamar ya hana ta amma dai ya yi shiru, dan bai son ya b'ata mata rai a wannan stage d'in,haka ta gama ta shirya ya kaita, da sallama ta tura qofar suka shiga tare da Adnan, Rasheedah na bud'e idon ta ya sauka akan cikin Sakeenaah, wani uban ashar ta saki sannan tace
"Me nake gani kamar ciki a jikin ki Sakeenaah?"
Adnan cikin qasaitaccen murmushi yace,
" kwari kuwa, da yake Allahn da yake bayarwa ba ta hannun oo yake miqa abun ba sai gashi muma ya bamu,"
Sakeenaah ce ta dan dungure shi da hannu kan ya yi shiru , qarasa shiga suka yi,aiko Rasheedah ta had'e fuska, tana sababin ita bata son gayya haba abu a dami mutum daga haihuwa sekace ya yi shela? Ba wanda ya kula ta, Sakeenaah ta had'a mata tea mai kauri ta zuba mata farfesun naman kaji da yasha dankalin turawa, carrot, da green beans da kayan qamshi nan take wajen ya kuwa kaure da qamshi, yawu Rasheedah ta had'iya sannan ta leqa kwanon, tana miqa mata ta amshe tana wani yatsina,ta hau ci kamar mayya, sai Wani zaro ido take, dariya Adnan ya kunshe, Sakeenaah ta harare shi, Auwal ne ya so magana shima tare da yin dariya Sakeenaa ta hana da ido, haka suka qunshe dariyar su, har ta gama, ko kwana basu yi ba aka sallame su dan Suna cikin qoshin lafiya ita da jinjirar.
Yau kwanan Rasheeda hudu da haihuwa, Sakeenaa ta tashi da matsananciyar naquda mai tsananin azaba, gaba d'aya Adnan ya rasa jarumtar shi da kullum Sakeenah ke Kiran shi da JARUMIn ta kuka ya ke wiwi kamar shi ne ke naqudar, tausayin ta ya gama ragargaza naman jikin shi da tinanin shi
Bangaren Sakeenaah kuwa........
Ku d'an Jira ko zuwa anjima mun ji mi nana ka hwaruwaaaa....
[30/06, 10:40 am] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 12:
Wata iriyar wahalalliyar naquda Sakeenaah ke yi,ta wani fannin ta sanya matsanancin tsoro da fargabar shin zata rayu da abinda take ta fata Allah ya bata shekara da shekaru ko Kuma mutuwa za ta yi? Wannan dalilin ne ya janyo jinin ta ya yi bala'in hawa, ba abinda take sai addu'o'i, wanda kusan rabin addu'ar tana nemar wa kanta rahamar Allah ne, sai kuma daidaito a tsakanin zumuncin ta ita da yayar ta, anyi inducing din ta kafin ta samu haihuwa, kukan jaririyar su ne ya karade ko ina, na dakin har da Wani sashe na asibitin ma.
Dik halin nan da Sakeenah ke ciki Adnan na gefen ta ya na riqe da hannun ta ko yatsina fuska ta yi sai ya mata sannu,in ko ya ga hawaye a idon ta na gangara haka Shima nashi idon zai ta zubar da ruwa addu'a kuwa bai San Iya adadin abinda ya roqar mata ba da abinda zata haifa, sai da naqudar ta taso gadan gadan ne aka tada shi d'aga wajen ta ya tsaya a gefe, ma'aikatan lafiyar suka duqufa dan taimaka mata ta haihu.
A lokacin da kukan jinjirar ta su ya shiga kunnuwan shi kuwa rikicewa ya yi da murna da kuka, ba b'ata lokaci ya dora goshin shi a qasa dan godiya ga Allah, ya na d'agowa ya je jikin gadon ko gama gyara Sakeenaah ba a yi ba ya rungume ta ya hau sumbatar ta yace,
"Sannu my love dama na fad'a maki ke Jaruma ce, kin ga qoqarin da ki ka yi ko?Allah ya miki albarka, Masha Allah Atiyyah (Kyauta )ta iso Allah ka raya mana ita da imani,ka ba maihaifiyar ta lfy, ni kuma ka qaran arziqin kula da ita,"
Murmushi Sakeenaah ta yi mabayyani, bayan an dora mata yarinyar tasu a jikin ta ta kalle ta ta sake murmusawa a karo na biyu sannan ta ce,
"Tabbas Ablah(cikakkiya daga kyaun halitta) ta iso, Masha Allah ka ga yarinyar nan ba inda ta baro mu,"
Ta daga kai tana kallon mutane hud'u dake dakin, Doc. Midwifes biyu, da mijin ta Adnan, dan ta samu tabbacin maganar ta, gaba dayan su kad'a kai suka yi cikin yarda da maganar ta sosai,
"Tabbas wannan gaskiya ne madam, barakallah yarinyar nan ta na da kyau anya mun tab'a karbar kyakkyawar haihuwa irin wannan kuwa?" inji likitan,
"Gaskiya tinda muke bamu taba karbar haihuwar kyakkyawa irin wannan ba, kalar ta daban ne, Allah ya raya maku ita da imani," in ji d'aya d'aga cikin midwifes din,
" Ameen"
Suka amsa dika, nan take Adnan ya karbe ta ya mata addu'oin da suka zo a sunnar Annabi Muhammad ana yi wa jarirai, sannan ya miqa ta ga Sakeenaah ta tauna dabino ta bata, nan danan ko ta tsotse shi tass, tana gamawa aka bata nono ta sha, sannan Doc. Yace su bada ta ai mata wanka a kawo masu ita, dai dai nan Mama da ta gaji da Jira a bakin qofa ta shigo, itama ta na ganin yarinyar sai da ta yi sujjada dan godewa Allah, sannan tace a basu su dika su tafi ba maganar wani wankan asibiti tinda sun goge ta tas, haka kuwa aka yi Sakeenah da baby na gama cika awannin da ake bayan an haihu a asibitin aka sallame su suka yi gida, gidan ta aka wuce da ita, dan basu shirya tafiya wankan gida ba, Adnan tuni ya sanar da ita baya so, shi a barshi komai a nuna masa zai mata Mama ta ce inaaa zaman biqi ba aikin namiji bane, ya dai bari a mata anan d'in tinda baya so ta je gidan ita ta zauna mata dan Maman ta kula da gaske baya son ta yi nesa da shi,suna isa kuwa ya daura ruwa a qatuwar tukunya, Mama ta shiga ta mai sannu tana tsokanar shi angon qarni, yana sunkuyar da kai yana shafe qeya, fita ya yi yaje d'aki, ya isko Sakeenaah na ta bacci, tea ya hada mai kauri ya tada ta ta amsa tasha,su Shamsiyya kuwa dama ba yau suka Saba ganin yanda yake wa matar tashi hidima ba, Adnan mutum ne da ke kyautata wa matar shi kwatankwacin yanda take kyautata masa koma a ce fiye da hakan.
Kitchen ya sake komawa ya bud'e fridge da freezer dan ya tabbatar in akwai komai da suke da buqata ko Kuma akwai buqatar qarowa, ya na tsaye ya na nazarin wajen ya hango wata roba da aka shaqe da farfesun kayan ciki dakkowa ya yi ya bud'e ya ji yanda qamshi ke tashi Shamsiyya ya kwalawa Kira ta zo cikin hanzari ta durqusa ya miqa mata tare da bata Umarnin ta dumamawa Sakeenaah.
"To uban gida na ni ai da Ina Jira in ka fita ne ma in sama mata abinda zata ci, amma tinda ga wannan shikenan,"
"Kar ki damu a dumama wannan din ma ba komai, anjima sai a yi sabo,"
Mama na can na wanke jinjira, shi Kuma ta cikin matar shi yake, wata tukunyar ya gani ta tafaso ya ji qamshin abubuwan be tab'a Jin irin shi ba, tambayar Shamsiyya ya yi menene wannan? Amma dai ba matar shi za a bawa ta sha ba ko?
Murmushi ta yi sannan ta ce,
"Uban gida na wannan ai ba na sha bane, na zama ne, ruwan wanka tinda dama akwai na zafin a tolas d'in ku ba se an d'ora ba shine Hajiya Mama da ta zo se ta dora wannan d'in, tinda cikin Uwar d'aki na ya Kai wata takwas Hajiya Mama ta aiko da su"
"To amma dai ba a tafashen zata zauna a ciki ba ko?"
"Ah ahhhh Uban d'aki na, se ya huce daidai yanda zata iya zama"
Sanda aka gama dumama farfesun Adnan da kan shi ya karb'a dan ya Kai mata, ruwan tea Mai kauri da ya sha kayan qamshi Shamsiyya ta dafa ta sake had'a mata ta d'ora masa saman trey ta bashi, ya na Kai mata kuwa ba b'ata lokaci ta gyara zaman ta a saman gadon,yunwa ta ke ji sosai dama, sannu ya yi mata ya zauna gefen ta ya fara bata a baki be bari ba sai da ta qoshi sosai.
Doc. Ya bada Umarnin kar a sa mata ruwan wanka mai zafi sosai saboda hawan jinin ta dan haka ruwan da baida zafi Mama ta had'a mata ta taya ta wanka suka fito, Adnan na can d'ayan d'akin d'auke da jinjirar ya na ta kallon ta Cike da so da qaunar yarinyar,Kafin awa uku Baby da mama sun yi fes sun fito shar da su.
Adnan da Mama waya suka dinga yi wa 'yan uwa da abokan arziqi Suna Sanar da haihuwar, cikin qanqanin lokaci gida ya cika da dangi da ke kusa da su both na Adnan d'in da Sakeenaah,har su Rasheedah sai da aka sanar wa ta hanyar Kiran Auwal da Adnan ya yi amma daidai da Allah ya raya bata San ta ce ba, ta dai tambayi abinda aka haifa aka Sanar da ita, can se ta kyab'e baki sannan ta cewa Auwal da ke mata albishir d'in haihuwar,
"To da ka ke Wani fad'a min barin tawa jinjirar zan na tafi wajen tata jinjirar kenan ko me? Ni fa bana son jaraba haba"
Kallo Auwal ya bita da shi, dan yanzu abin nata ya d'auke shi a matsayin bugun mugun baqin aljani ba yin kanta bane, magani ya Kamata ya nemar mata ko Allah zai sa a dace.
Babyn Rasheedah taci sunan Farhah, bayan kwana bakwai itama Sakeenaah babyn ta taci sunan Mama, Haleema, inda Baban ta ke kiran ta Atiyyah, maman ta ke kiran ta da Ablaerh, Mama tace wannan sunan sai su ita ba ruwan ta Hali dubu zatana kiran takwarar ta, Abba yace Matas zai na kiran masoyiyar shi, Sakeenaah kam sai dai tai dariya, domin gata da so ba wanda bata gani wajen miji da iyayen ta, ga shi Kuma 'yar ta ma ana nuna mata soyayya Mai qarfin da ta fi wadda ake mata
" Mama ya kamata ki je wa Rasheedah, kin ga zaman da kk min zai dad'a ja min qiyayyar ta, amma ki hakuri inna Fad'i ba daidai ba,"
"Zan tafi na je mata, amma da na je ba jimawa zan yi ba zan koma gidana tinda kin ga ita haihuwa ta uku ce fa ta San Kan komai,ke din ma tinda dai ga masu aikin ki dattijai biyu da Shamsiyya sun Iya komai Suna da amana Suna qaunar ki ga kuma mijin ki da yake Jin zai iya komai ma da kan shi dik za ku Iya kula da wannan mai manyan idon, Rasheedah kuwa tin da ta haihu na je wajen ta ta nuna bata buqata ta, amma shikenan ai bana biye mata ba, zan je d'in kamar yanda ki ka ce, Allah ya miki albarka,"
"Ameen Mamana, sai dai akwai wata alfarma danake son na nema a wajen ki,"
Qasa ta yi da murya sosai ban ji me tace ba, amma naga Mama ta miqe cikin fushi,
"Dama jira nake ki min wannan maganar banzan da Abban ku yace kin masa tin wata biyu da suka wuce,shi ya hane ni da tinkarar ki da maganar duba da rashin lafiyar da ki ke fama da shi, idan shi ya maki alqawari, to ni ban yi ba, kuma ba zan taba yi ba, sanin kan ki ne Rasheedah ta tsane ki, da duk wani abu daya dangance ki, hauka kk da zaki ce haka,"
Kuka ta fara sosai, harda shessheqa, hankalin Mama ba qaramin tashi ya yi ba,dan ko kad'an bata son damuwar Sakeenaah, Sakeenah irin yaran nan ne da ke da shiga rai saboda tsananin biyayyar su da kyawawan halayen su, shi ne dalilin da ya sa suke son ta ainun, cikin sassauta murya Mama ta ce,
"Abun har ya kai haka,to tsaya, ki bar kuka mu yi magana, fad'an dalilin ki kwakkwara na aikata hakan?"
Hawayen ta ta share ta fuskanci Maman ta ce,
" Maa ni nafi son koma meye dalilina daga baya kun gani, ni bana son furta meye uzurina, alfarmar nan kawai zaku min ku nuna min soyayyar ku cikakkiya a gareni bayan ba ni a doron qasa, Ina so wannan abun da zan yi ya zama wasiyya a gare ku kin ko San Mama wasiyya indai ta alkhairi ce dole ne a cika ta ko?,"
" Akul na kuma jin maganar idan bake dinnan kina karyan zuciya sosai Sakeenah, wa ya ce maki Zaki mutu yanzu? Dan Allah ki dena wannan maganar mara dad'in ji"
murmushi ta yi kawai sannan ta rungume Maman,hawaye na bin kuncin ta, a haka ta samu ta fara gyangyadi, Adnan ne ya dan leqo ya gaida Mama, da hannu ta masa nuni da ta yi bacci, a hankali ta zame jikin ta daga na Sakeenah ta gyara mata kwanciya shi Kuma ya gyarawa Baby Atiyyah kwanciya sannan suka ja masu qofa suka fita, daukan Mama ya yi a mota dan ya Kai ta gidan Rasheedah,ya zauna a qofar gida dan tace a yau zata koma gidan ta ba zama za ta yi ba,
" Aaa Mama ce a gidan namu yau Kuma,to sannu da zuwa, ya kuma kk bar mai jego da jikar so,"
Baki Mama ta saki ta bi Rasheedah da ta yi maganar da kallo, lallai wannan rashin kunyar ta ta na buqatar gyara,har da ita abun zai tab'a ashe
"Gidan ku Rasheedah, ni kk kalla ki fadawa haka? A jikokina wa na ware, haihuwar ki nawa? Ita haihuwar ta nawa? Meyasa kk haka? Ke yanzu ba zaki daure ki sawa zuciyar ki salama ba,to sai anjima dama leqowa nayi a gaisa naga jaririya, Allah ya raya mana da imani"
Cikin maganar shi ta yara Yousf yace zai bita, daukan shi ta yi ta fice tabar Rasheedah na mata Allah ya kiyaye, dan ita a ganin ta ta fadi abinda ke ranta, dama lokaci zuwa lokaci Yousuf kan je mata ya yi kwanaki, duk da ba safai Rasheedah ke yarda ba.
****************
Atiyyaerh da Farhah na da saurin girma da ga wayo, sai dai Atiyyaerh tafi Farha girman jiki, kamar itace babba, in Mama ta fada ace ai ta yi