Showing 66001 words to 69000 words out of 81601 words
Chapter 23 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
ta ga ya b'ata rai haka ta manta,amma wannan karon komai da gaske yake d'aukan shi.
Afrah ce ta shirya ta nemi izinin Abban ta zata gidan Mama, amince mata ya yi tare da bata dubu d'aya,yace ta tsaya a hanya ta d'an sai masu ko da lemo ne, godiya ta yi,ta fice, ta dad'e a bakin titi tana jiran abun hawa kafin wani matashin saurayi, mai matsakaicin kyau da haske ya tsaya a gaban ta, motar shi kadaran kadahan ba wata me tsada bace, shi ba talaka bane da alama kuma ba mai kudi bane, sallama ya mata ta kauda kai gefe tare da amsawa a hankali, qara gaba shima ya yi inda ta tsaya ya sunkuyar da kan shi daidai tsahon ta ya ce,
" Malama Afrah bismillah mana, kina tsaye rana zata maki illa ai"
Cike da mamakin sunan ta da ta ji ya ambata a bakin shi ta matsa gefen shi tace,
" Malam ina ka sanni?"
" ke ba qanwar Sulaiman bace? Sulaiman abokina ne ai, tare mukai makaranta, muka gama, naga hoton ki ne a wayar shi, ba Yousuf ne yayan ku ba, kuma kina da qanwa ne ko yaya me suna Ablaerh?,"
D'aga masa kai ta yi ta d'an murmusa lallai wannan ya san ta, bud'e mata motar ya yi ya ce ta shiga,
"Na gode matuqa, amma gaskiya ba zan shiga ba, na ji dad'in tayin da ka min, ba ya daga cikin dacewa mace ta shiga motar wanda ba muharramin ta ba a wannan zamani da muke ciki, domin kuwa kamar misalin kasancewar su ne a d'aki d'aya na ukun su zai iya zama shaidan,"
Ba qaramin burge shi ta yi ba, cike da jin dad'i ya bud'e motar ya fito, adaidaita sahu ya sama mata, ya biya kud'in, ta masa godiya, ta tafi.
Tin a hanya take tunanin fuskar ajnabin da bata tambayi sunan shi ba, data tuna murmushin shi sai itama tai murmushi, a haka suka isa ta sauka ta shiga, tana shiga ta tarda Mama da Atiyyaerh, Mama na wanke wa Atiyyaerh kai da kalkashi, da kwai, tare da man shampoo, sai dirza kan take tana mitar,
"Gashi sai uban yawa da tsaho baza ki gyara ba, gashi nan duk amosali ya danqare maki akan ai, in ba dan kina tare da tsohuwar da kullum ki ke tsokanar na tsufa ba wa zai baki wannan maganin amosalin dake danqare akan ki? "
"Kaiiii jama'a dad'i na dake mita, "
Dundu Mama ta d'ima mata,ta kuwa gantsare tana kukan shagwaba?dariyar Afrah ce ta sa su duba inda take tsaye ta na Jin dramar su duk da idon Ablaerh a rufe yake ta san ita ce, oyoyo ta fara mata, itama ta wuce daki ta yi ta cire kayan ta ta daura zani, tazo ta zauna a kujera 'yar tsuguno ta gaida Mama ,bayan sun gaisa ne tace,
" Mama nima a wanken da karkashin, kaina se ya yi ta qaiqayi ya na kuma karyewa,"
"To taho, kk min raki kisha d'ima kema, ai rashin sani ne, wanke kai da karkashinnan yana da amfani sosai, gyara kai yake da qarawa gashi tsaho, sannan ya yi maganin amosali, kuma yana sa laushin gashi,"
Bayan sun gama wanke kai ne, suka tafi d'aki suka fara drying gashin su da hand dryer, suka mulke shi da man kwakwa, mai had'in man rid'i da na alayyadi, da man habbatussauda, sai man zaitun, ba qaramin kyau gashin su ya yi ba se sheqi yake ya yi baqi sosai, ga santsi da yake, Ablaerh ce ta nade shi cikin shower cap ta shiga wanka, ta dirje jikin ta sosai, tare da shafe tsakanin cinyoyin ta da Alovera, dan ya yi haske, ( shafa alovera, lemon tsami, lemon zaqi, kindirmo asalin mai kyau, tomeric da lemon zaqi ahade, yana saka tsakanin cinyoyi ya yi haske, ko kuma duk inda yake baqi a jikin ka kana son ya yi haske mai kyau in ka shafa duk d'aya daga ciki ya yi kamar 30mnts yana haskaka wajen, amma tomeric da lemon zaqi hada su ake a shafa) fes ta fito kamar a dauke ta a gudu, Allah ya ma Atiyyaerh kyau mai ban sha'awa, sannan ga gyaran jiki natural da Mama ke mata kullum, Afrah ta gani tana ta murmushi ita daya,
" Hmmm who is the lucky guy?"
In ji Atiyyaerh na tabbatar da wannan Murmushi na tinanin masoyi ne
Dagowa ta yi da idon ta masu kyau ta kalli 'yar uwar ta ta, ta sake sakin murmushi bata ce komai ba, itama zuwa ta yi ta qara watsa ruwa, dan jikin ta ya dan baci da kumpa, bayan ta fito ne su ka yi kwalliya,sannan Afrah ta nisa tace,
"Ammm game da abinda kk tambaya dazu ki ka ji na yi shiru banda amsar da zan baki ne, domin ban san me zance ba, zan fada maki how stupid i am to fall in love with a stranger? Ko zan fada maki cewar ko sunan shi ban sani ba? Amma shi yasan sunan mu ya san Yah Sulaiman,"
Cike da murna, Atiyyaerh ta daka tsalle, ta rungume ta, ,
" U ar not stupid my love, so haka yake, banga laifin ki ba, fatan mu ubangiji yasa shine mafi alkairi a rayuwar mu, baki daya, ki fad'awa Yah sulaiman cewar kin ga abokin shi har ya taimaka kk samu abun hawa da sauran su ya mai godiya kinga in ma ya manta ki ai ya tuna ki, dan ba zamu bari ya kufce mana ba yanda naga alamar son shi a tare dake,"
Murmushi Afrah tai sosai daya bayyana haqoranta masu kyau, suna haka Mama ta shigo suka ci gaba da hira da ita, Afrah a gidan ta kwana dan kwata2 yanzu bata son bud'e ido ta ga Rasheeda, da ana canja uwa da ta canja ta ta amma ba a yi sai dai tai mata addu'ar mai canja zuqata daga mummuna zuwa kyakkyawa ya canzawa Umman nata halayen ta.
Tin safe suka gyarawa Mama gidan Afrah ta shirya komawa gida, a hanya ne Ablaerh na dawowa daga rakiya Tsohon saurayin ta Hassan ya tare ta, tayi mamaki sosai daya gane ta, gaisawa suka yi ya fad'a mata yana sane da mutuwar auren ta, yasha wahala kan ya gano inda take, yau dama ya so zuwa gaida Kakan nata ya gabatar da kan shi, sai kuma gashi sun hadu,
"Mu qarasa gidan dan na kula maganar ba ta tsaye bace ko malam Hassan?"
" wannan haka yake , bismillah na qarasa dake,"
" A'a ba damuwa, ai mun kusa,ba sai na shiga ba, muje kawai,"
A gefe ya yi parking d'in motar tashi sannan ya kulle ya bi bayan ta......
*Hahaiiiii casssssss, Malam Hassan samawa kan ka lfy muna da miji a hannu*🙄
[07/07, 6:15 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅🏼
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
Page 29:
Parlour ta bude mishi ta mai izinin shiga sannan ta shiga ciki ta sanar da Mama, kafin ta d'ebi zobo mai sanyi da meatpie da suka yi ita da Afrah ta kai mishi, sai da ta koma ciki ta d'an bashi waje sannan ta dawo, ya d'an ci kad'an dan shi damuwar shi bai wuce tazo su yi magana ba, ita kuma ta rasa ta yanda zata b'ullo masa, zaman ta keda wuya Yousuf ya yi sallama ya shiga, ganin baqo kuma ga Dimond d'in shi a zaune ta sha kwalliya ya sa ya yi kicin2n da rai, fuskar nan kamar bai tab'a dariya ba, hankalin ta in ya yi goma ya miqe tsaye, a daburce ta furta,
" Sasssannu.. da zuwa Yayah,"
ko kallon ta bai ba ya amsa, idon shi na kan Hassan, yana jiran qarin bayani, daga tsayen ya harde hannayen shi a qirji yana kallon su,
"Ammm dama wannan shine Hassan.."
Se kuma tai shiru, Yusouf yace ,
" Ehemmm? Sai yazo yin me?"
Hassan ne ya miqe tsaye ya je ya ba ma Yousuf hannu dan su gaisa, kamar ba zai miqa masa nashi hannun ba, ya miqa mai ya koma d'aya daga kujerun parlourn ya zauna ya hard'e qafa, qasa ta yi da kan ta, da a ce zasu kasa kunne da sun ji yanda zuciyar ta ke bugawa, Abbah ne ya yi sallama a tsakar gida, nan da nan ta yi wata ajiyar zuciya me qarfi, fit ta tashi da sauri ta fita waje, zuwa ta yi ta kama hannun Abba suka shige dakin su, tana shiga ta fara buga qafa irin na shagwab'ar da ta Saba yi wa Abban,
" Abba tin d'azu nake jiran ka, Hassan yazo ga Yayah can yana ta b'ata rai , yayi fushi, ni kuma bani na kawo Hassan ba, ganina ya yi a hanya muka gaisa, na zo da shi dan bana son mu tsaya a waje, ina son na masa bayani, akan ina da wanda nake so, amma Yayah kamar ba zai gane hakan ba gaba d'aya ya b'ata rai,"
Hawaye ne ya gangaro mata, Abba murmushi ya yi dan ya gane a rud'e take sosai,
" kwantar da hankalin ki ina shi Yousuf d'in yake? Muje na gan su"
Noqe kafad'a ta yi ta zauna gefen Mama da ta fara bacci,
," A'a Abba ni dai bana son na sake ganin Fuskar Yayah sai ya sakko, tsoro nake ji,"
Dariya ta ba Abban ya fita, ta kama hannun ta ta saka a baki tana cisgar farcen ta tare da qurawa qofa ido, ta kasa kunne sosai dan ta ji me za a ce, Abba ne ya musu sallama ya Samu waje ya zauna suka gaisa da Hassan ya bashi baki akan ga abinda ke akwai na auren Yousuf da Atiyyaerh, hankalin shi ya yi matuqar tashi a karo na biyu, hawaye ne suka zubo ya yi saurin d'auke su, amma ya makara a kan idon Yousuf, jikin Yousuf ya yi sanyi, dan ya tabbatar ba qaramin so yake wa qanwar tashi ba, amma sawun giwa ya take na raqumi, shima in ba ita rayuwar shi zata shiga hatsari, hakuri ya ba Hassan cike da dakewa ya nuna masu ya gode zai wuce amma yana son a mai alfarmar ganin ta ko da sau d'aya ne, kishin Yousuf ne ya motsa ya dan had'e rai, ya ce,
" Minti 5 na baku danni sauri nake zan tafi nima,"
Murmushi Hassan ya yi dan ya gano Yousuf d'in kishi ke damun shi, se ya dafa kafad'ar shi yace ,
"Ni minti 2 ma ya ishen,"
Abbah ne ya yi murmushi ya miqe ya shiga ciki, tana ganin Abba ta miqe tana zaro ido da son Jin me ya faru, cikin tsokana Abbah ya ce,
"ki je yayan ki na can na fada akan kin kawo wani,"
Hawaye ta fara tana yarfa hannaye, Abba dariya ya saka yace,
"Matsoraciya waya fad'a maki ana tsoron miji? Ba tsoro tsakanin ma'aurata sai dai biyayya, da ladabi, in kina jin tsoron namiji sai ya ci kashi akan ki, amma in kina mai biyayya sai rayuwar ku ta zama abin burgewa, kin ji ko, share hawayen ki wasa nake maki,"
Sharewa ta yi, maganar Abbah ta shige ta sai ta samu gwarin guiwa ta fita, a waje ta tadda Hassan, Yousuf kuwa d'an d'aga labule ya yi yana leqen su, Atiyyaerh ta hango shi, amma shi bai kula ba, he is busy wajen kallon Hassan,murmushi ta yi mai sauti, har haqoran ta suka fito, Hassan yace,
"Wato kina murna zaki auri dan uwan ki ba ni ba ko?"
Cikin sauri tace
" A'a ba haka bane, kawai naga yanda ka fahimci Abba da sauri ne,"
" To ba dole ba, wannan yayan naki kamar zai doke ni, sai muzurai yake,"
Dariya suka saka, a tare, ya taka zuwa wajen motar shi, ya d'akko wata leda da kwali a ciki ya bata ya mata fatan alkairi ya tafi, yana shiga mota ya kifa kan shi ya fara zirarar da hawayen rasa ta a karo na biyu, da kan shi ya rarrashi kan shi ya tafi, tana shiga ciki ta gan shi ya had'e rai sosai, itama jiman tawa Hassan take, kan ta tsaye ta je ta zauna akujerar dake kusa da tashi, miqa masa ledar hannin ta ta yi tace,
" Yah kaga Hassan ya ban ya tafi, sai na ji ya ban tausayi,"
" Eh shiya sa naga sai dariya kuke kamar kema kina son shi kar ya tafi ko?,"
Dariya ce ta kama ta amma ta dake,ta ce
" Laaa Yah ya akai ka gani?"
"Ina tsaye jikin labulen nan na ga komai ai,"
Dariya ta saka sosai harda duqawa, tin yana tsumewa shima ya saka dariyar,ya ce,
" kinga laifina ne? Na sani ko ya yi yunqurin gudar min da amarya?"
Dariya suka dad'a sawa,
" kai jama'a ayi ai auren nan na huta, ina qailula gaba d'aya kun cika mana kunne da dariya, haba,"
"In kin gaji da ganin mu gobe ma a daura mana aure ki ga in ban d'auke mata ta mun tafi ba"
Haka suka yi ta zolayar juna kafin daga bisani ta basu waje su ka sha hirar su ta masoya.
Auwal ne a qofar wani gida, na masu qaramin qarfi, yana tsaye da alama wani yake jira, wata budurwa ce da zata kai sa'ar su atiyyaerh , ko ta girme su da kadan, ta fito tasha kwalliya, anyi daurin ture kaga tsiya, sai taku take cikin isa da rausaya, tana leqowa waje sosai naga kyaun ta ba laifi,ta hadu, ga shape mai kyau, murmushi Auwal ya yi, ciki naga ta masa jagora suka shiga, a soron gidan an shimfida tabarma da abinsha a jug, da qaramin cup, sai flask da alama abinci ne a ciki,cikin zazzaqar muryar ta ta ce,
"Sannu da zuwa," washe Baki Auwal ya yi ya ce,
"Ke za a yi wa sannu da qoqari, sai kace wani babban baqo ko Wani saurayi zaki min wannan tarba ta musamman haka,"
Dariya ta yi mai cike da jan hankali sannan ta ce,
"Ai kai saurayi na ne, dama ba na kowa ba,"
Se ta yi wani farrr da ido,habaaaa suman xaune Auwal ya yi, (Hahaiiiii cassssss Auwal ya je zance💃🏻💃🏻💃🏻)
A haka dai suka gama hirar su Auwal ya bata kud'i ta qi amsa, shi kuwa ya matsa da kyar ta amsa, ta masa godiya ta shige gida, Auwal ma ya ja motar shi ya koma gida cike da farin ciki, Rasheedah ya gani tsaye ta riqe qugu, cikin rashin kunyar ta da ta Saba ta ce Masa,
"Wai ni ban gane maka ba kusan yau sati biyu kenan, sai ka na kaiwa dare, in ka fita, ko kana zaune ka shirya ka ci kwalliya ka fita Ina ka ke zuwa? "
Ko ci kan ki bai ce mata ba, dan har yanzu baya kula ta, domin ya kula sam bata risina ba sai ma abinda ya yi gaba, cire kayan shi ya yi ya shiga wanka ya fito ya juya mata baya ya kwanta abin shi, ta yi ta bambami bai ce mata bari ko ci gaba ba.
Washegari da yamma ,Sulaiman ne ya shiga gidan shi da wani abokin shi,se da ya nuna ma baqon nashi wajen zama sannan shi kuma ya shiga ciki, dakin Abban su ya kwankwasa, Rasheedah ce ta fito, ya ce mata Abban su na nan, fuskar shi ba walwala, kallon shi ta yi na wasu 'yan sakonni sannan tace masa yana ciki, kafin ma ya ce mata komai Abban ya fito cikin shiga ta kamala, yace,
"Mu je ko,"
Gaba Sulaiman ya yi shima Auwal ya bi bayan shi, Rahseeda ce ta kama haba, ta ce,
" Yau nake ganin ikon Allah, akan waccan shed'aniyar yarinyar kowa ya juyan baya, lallai dani take zance,"
Juyawa ta yi ta koma dakin.
Bayan Abokin Sulaiman mai suna Qaseem ya gaida Abba ne, ya gabatar da kan shi a matsayin wanda yake son Afrah, kuma yana aiki da Aminu kano Teaching Hospital tare da Sulaiman, sannan iyayen shi suna nan a unguwar Kabuga, bayan ya gama ma Abba bayani ne, Abba ya masa izinin ci gaba da zuwa wajen Afrah dan su fahimci juna, kuma in da hali yana son had'a auren ta dana dan uwan ta, Qaseem ya yi matuqar farin ciki da hakan,dan godiya ya dinga yi kamar zai kwantawa Auwal,Suna gama tattaunawa Auwal ya miqe ya koma ciki, Auwal d'in na shigewa Qaseem ya miqe ya daka tsalle, ya fad'a kujera ya na murna,Sulaiman ya Kai masa duka a kafad'a ya ce,
"Kaiiii shegen a gidan surukai kk dai a rage wannan rawar kan,"
"Kai ka ga haka, ni yanzu na gama zama d'an gida, je ka kiran masoyiya ta mu gana,"
"Tab yaro ni yayan ka ne ai ba wai qanin ka ba,"
Durqusawa Qaseem ya yi a qasa yace,
"Dan Allah yayah kiran qanwar ka na zanta da ita,"
D'age kai sulaiman ya yi ya dora qafa d'aya kan d'aya, yana kad'a qafar shi a dole ana neman alfarma wajen shi, kwafa Qaseem ya yi ya miqe tare da zama a kujera ya ce,
"Kar kaje d'in nima za ka zo zance wajen walida na ga uban da zai kira ta, ni haka nake maka?"
Ai da sauri Sulaiman ya miqe ya shiga dakin Afrah ya sanar da ita zuwan Qaseem,
" Yah wane haka?"
" Abokina da kk ce ya taimaka maki kwanaki, shine yazo, Abba ya masa izinin ganin ki,"
Cikin tsallen murna ta sakko daga gado, ta rungume Sulaiman, tana murna, kiss ta masa a kumatu ta fad'a toilet, hab'a ya kama, sannan ya kama qugu ya tokare qafa d'aya ya bud'e baki yana kallon qofar da ta shige, Murmushi kawai ya yi sannan ya fita waje,wato dai kenan itama tana son shi, kad'a kai ya yi ya sanar da abokin nashi tana zuwa shi ya shiga in sun gama ya masa waya.
Tana can ta rasa ma wacce kwalliya zata yi, daga qarshe ta yanke kawai bari ta shafa powder ta shafa mai a bakin ta da kwalli, dan bata son bata masa lokaci, tana gamawa ta saka doguwar riga ta yane kan ta da mayafin rigar, ta fesa turaruka masu sanyi ta fito, ta zo ta same shi, kan ta a qasa sai murshi take shima haka, zama ta yi a kujerar da ke d'an nesa da shi sannan suka gaisa, ya qara jaddada mata me ya kawo shi, ta yi na'am da shi, suna cikin hira ne Rasheedah ta fito, ta gan su, kallon inda