Showing 42001 words to 45000 words out of 81601 words
Chapter 15 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
San me yasa ki yin abinda ki ka yi jiya, kin ga kenan duk wahalar da ki ka sha jiya Baki samu lada ba,ba lada ba la'ada, kin Yi asarar lokacin ki da energy din ki wajen kyautata min na qarya da yaudara, ke ba dan Sakeenah ce da kan ta ta yi wasiyyar ki kula da Atiyyaerh ba saboda tana maki kwadayin samun Rahamar Allah akan Wanda suke sada zumunci ai ganin yarinyar nan ba me barin ki kiyi muguwa azzaluma kawai, wato ke naki yaran su je makaranta su samu ilimi ita da kud'in uban ta da uwar ta ta zauna da jahilci ko? Sannu muguwa"
Zagaye ta ya yi ya wuce ta gaban ta zai shige d'aki, har ya gota ta ya dawo baya ya ce mata,
"Rasheedah ki sauya halin ki da wuri da gaggawa, kar ki zo ki na danasanin da bashi da amfani,"
"Ba zan sauya halin nawa ba, azzalumi me cin amana kawai, ta je makarantar na ga yanda ilimin zai zauna a Kan ta, aikin banza kawai "
A fusace Auwal ya juya Dan ya lallasa ta ta na ganin ya na biyo ta ta zura da gudu qasa ta shige kitchen ta rufe, tare da ci gaba da fad'a masa baqaqen maganganu, kwafa ya yi ya koma d'akin su ya kwanta a gado ya rintse idanun shi Yana Jin qiyayyar Rasheedah na samun wajen zama a zuciyar shi, be fita ba ranar se da aka tashi yaran ya wuce ta a parlour har ta zabura zata gudu taga ko kallo bata ishe shi ba, ya wuce d'akko Yara, ya biya da su restaurant suka ci suka sha suka qoshi, sannan ya dawo da su gidan, da kan shi ya yi wa su Afrah da Atiyyaerh home work, sannan ya fita ya bar gidan tare da mummunan gargad'in daidai da harara aka wa yarinyar in ya dawo Shima zai d'au mummunan mataki sannan ya fita, Rasheedah kuwa ji ta yi kamar ta yi bindiga, shi yasa ta Saka hijabi ta fita zaga unguwar da qafa Dan ta rage baqin cikin da ke ran ta.
****************************
Kusan wata biyu kenan suna zuwa makaranta batare da wata matsala ba,yanzu mutuniyar ku Atiyyaerh in za ta yi magana sai da turanci take yi dik da dama sun Saba yi da iyayen ta, amma lokacin bata da Wani wayo sosai yanzu ne take gane komai dalla dalla turanci ya zama second language d'in da ta ke ji ta Kuma kware akai sannan larabci dan ana yi musu shi a makarantar, Afrah kuwa bata san bihim ba da ake koya musu dan bata Wani Maida hankali akan karatun, kullum taje daga kukan banza sai bacci, in kuwa aka matsa za ai karatu a gida sai ta gudu wajen Umman su,ta ce ita bata so, Rasheedah ko ji take kamar ta mata dukan tsiya dan haushi kullum gori take mata da cewa,
"Shiritacciya kawai,ke ba zaki Maida hankali ki yi abinda zai amfane ki ba kin tsaya shiririta, ga waccan mara galihun ma tana karatu balle ke, so kk ta girma ta fi ki ilimi tana aiki ke kina zuwa maula ko? To ki tsaya ki ji da kyau daga yau se yau, bana so na sake ganin ki na wannan wawancin so nake ki fita komai da komai ma ni ba karatu kad'ai ba kin ji ko?,"
Ita dai Afrah sai dai ta tsotsi hannu ta ci gaba da kallon ta kawai.
Yau Lahadi, zasu je gidan kitson dake maqotaka da su, Atiyyaerh bata son zuwa ko kadan, duk da yawan gashin dake kanta, bata qin kitso, amma dalilin yaron gidan kwata2 ta tsani kitson da zuwa gidan, yaro ne sa'an Yousuf,mai suna Ahmad, ba qaramin son ganin Atiyyaerh yake ba shi kuma a rayuwar shi,dan yara abokan shi ma cewa suke budurwar shi ce,ya yi ta jin dad'i kuwa, in ya ganta ya je ya yi ta mata surutu,kala2, gashi baya zuwa makaranta shi, se ball da wasa a unguwa dad'in dad'awa kuma qazami ne , haka gidan da suke zuwa kitson ma qazamai ne matan gidan, Suna shiga gidan Atiyyaerh ta labe bayan Yousuf daya rako su shida Sulaiman, aiko Ahmad na hango su ya tashi ya je inda suke,yana jan hannun ta Atiyyah, kallon Yousuf ta yi ta kyab'e baki zata yi kuka, aiko yana ganin haka ya kaiwa hannun Ahmad duka yace,
"Dalla sake mata hannu, wani qazami da kai,"
Aiko da jin haka Ahmad ya saki hannun ta ya kaiwa Yousuf naushi, dambe ya kaure a tsakanin su, Afrah ta matsa gefe tana tsotsar hannu tana kallon su, ita ko Atiyyaerh saka hannu ta yi aka fara damben da ita sosai, Ahmad ya fisu qarfi, Sulaiman mugun matsoraci ne, baya ya yi yana ta zare ido, idon shi sunyi jawur yana son yin kuka, wani abokin Ahmad ne ya taso suka hadu suka zane Yousuf, ana gama damben Ahmad ya fizge hijab din Atiyyaerh aiko gashin ta da ke dunqule a matsattsen hijab din ya baje, kuka take sosai da qarfi, wanda ya ja hankalin matan gidan suka leqo soron, Maman Ahmad ce tace,
"Me zan gani haka, Yousuf waya fasa maka baki? Me ya faru haka?"
Kan ta gama tambaya Ahmad ya kwasa da gudu da abokin shi sun bar wajen, Sulaiman ne da yanzu ya fara kuka ya fad'a mata komai, Yousuf ya kumbura sai nishi yake, bai ce komai ba, ya d'aga Atiyyaer, ya kama hannun ta suka yi gida, Maman Ahmad na ta kwala mai kira yaqi juyowa, suka shige gida Afrah ma bin su ta yi, sannan Sulaiman, suna shiga Rasheedah na kitchen ta fito, ganin fuskar Yousuf da jini ga shi sun yi biji biji shi da Atiyyaerh sai mamaki ya kama ta ta ce,
" Ah kunyi saurin dawowa lafiya? Me ya faru na gan ku haka?"
Sulaiman ne ya mata bayani, aiko kan ya qarasa ta gane Atiyyaerh ce ta ja aka ma Yousuf haka, wani irin Mari na rashin Imani ta sakar ma yarinyar da ke kuka, ta kamo ta ta hau duka ba ji ba gani tana fad'in,
"Dan uban ki da ya gudu ya bar min wahala kashen d'an ki ke so a yi? dubi yanda jini ya ke zuba a bakin shi,shegiyar yarinya tin yanzu kin fara hulda da maza ko, to bari kiji in aure ne ki bari ki tasa aurar dake zamu yi da wuri mu huta da wahala, shegiya mai kama da mayu,"
Ta wurga ta gefe ta shige ciki ta na Kiran yaran nata, Yousuf kuwa kuka yake sosai, duk abinda aka masa bai ji kuka ba sai da aka dake ta, ranshi ya yi mugun b'aci da hakan, d'aki ya kwasa da gudu ya shige, Sulaiman ma ya bi shi, kallo Rasheedahn ta bisu da shi,
"Shashashai in ban da ku ma,kuna gani yanda kowa ke nuna yafi son ta akan ku, kuke manne mata, har wani haushi ka ji kenan dan na hukun ta ta akan dukan da ta sa aka ma? Kai ka sani wawan yaro kawai,"
Ta yi shigewar ta kitchen ,ta ci gaba da aikin ta, kuka sosai Atiyyaerh take, Afrah ta je ta zauna kusa da ita, tana shan hannu, bata ce mata komai ba amma sai kallon ta take,idon ta ya cika taf da hawaye itama.
Da daddare bayan Auwal ya dawo sun gama cin abinci Suna kallo,se na ga Yousuf na yi wa Abban su rad'a a kunne, cikin fushi sosai kuwa ya shiga d'akin shi, tana kwance ta yi d'aid'ai a gado tana kwasar rab'a , aiko ya samu qaton hannun shi na magina ya yanka mata duka a cinya, a gigice ta farka,
"Wayyo Allah,waya d'anan Iron a cinya me zafi haka?"
Tana kuka ta na murza wajen tana yarfe hannu,
"Ni ne nan na dake ki, mai shegen son kai kawai, ke wace irin mata ce da baki san Annabi ya faku ba? Meke damun ki ne, wannan yarinyar marainiyar Allah me ta ci maki? Ki shiga hankalin ki ina fada maki baki ji ko? Zan mummunan saba maki akan ta,"
"Kan uban can akan waccan yarinyar ka daken? To bari kaji, wahala a hannuna yanzu ta fara shan ta kala2, indai ni ce Rasheedah, sai dai ka kashe ni inna dake ta, ta zabura tai waje da gudu har zanin ta na kwancewa, bin bayan ta ya yi shima,tana zuwa ta samu Atiyyaeh na home work, ta dauke ta da mari, ta sake dauke ta da wani, yarinya ta gigice gashi marin da bata san da zuwan shi ba, ta kasa ma kukan, bude baki ta yi tana qaqalo kukan ya qi zuwa, Rasheeda bata ankara ba itama ta ji maruka na sauka a kuncin ta, yana dukan ta tana dukan Atiyyaerh tana zage2, d'aga ta ya yi cak, ya yi d'aki da ita ya rufe ya shiga kirbar ta, kamar an aiko shi,
"In kince ba zaki fasa dukan ta ba baki haifu ba, ko bana nan kika dake ta na dawo sai kin karbi naki dukan kema tinda kin zama baqar jaka, muguwar banza kawai,"
kuka take sosai, tana jin wata muguwar tsanar Atiyyaerh sabuwa na sake kama ta,
" Lallai Auwal ka ja mata, ka ja mata d'and'anar azaba a wajena kala2, baka san me zan iya aikatawa da wanda ba zan iya ba har yanzu,"
Ta tashi da kyar ta fada toilet tana kuka......
*Hummmmmmmm*
[01/07, 8:47 pm] asiyahabibu93: 💅🏼 KAI NE JARUMI 💅
Page 20:
Tin daga wannan ranar, ko hanya ce ta biyo da Atiyyaerh ta inda Rasheedah take sai dai ta bar wajen da kuka, danko sai ta mata wani abun muguntar da zai saka ta kuka, kullum Yousuf dayasanin fad'a ma mahaifin shi abinda ya faru yake, sannan ya qudurta a ranshi sai ya kama Ahmad ya baje qarfin shi akan shi, tinda shine silar abinda yake faruwa da Ablaerhn shi .
Kwance take a d'akin su bayan sun dawo daga islamiyya, ko kayan ta ta kasa cirewa, ashe da empty lunch box ta tafi ranar, sai da ta je zata ci abinci taga wayam, gashi da safe iya tea ta sha, tea din ma ba wani had'in kirki aka masa ba, Auwal tin da ya kula the more yana shiga harkar su the more Rasheedah na qara haukacewa da musgunawa yarinyar sai ya ja baya da shiga lamarin nasu,saboda ya kula idan zai jinyata Rasheedah ne akan Atiyyaerh da ta samu dama sai ta ninka abinda ya mata akan yarinyar,kawai sai ya koma yi mata addu'ar shiriya,dan haka lokuta da dama yana ji Kuma ya na ganin ta tana mata mugunta amma haka zai kasa tanka mata,yau har ya tashi zai Saka wa Atiyyaerh extra cake a jaka sai ya ga ta saka mata lunch box a jakar sai ya fasa aiwatar da qudirin shi,hakan kuwa shi bahaushe ke Kira da rashin sani ya fi dare duhu dan kuwa ba komai a cikin lunch box d'in,ko da suka dawo Atiyyaerh ta tambayi abinci Rasheedah ce mata ta yi ta je d'aki ta cire kaya tazo su ci da 'yan uwan ta, tana shiga ta biyo ta d'akin, tace in ta sake ta koma parlourn sai ta ji a jikin ta,ta zauna har sai ta kira ta, su Yousuf basu gane komai ba, suka zauna jiran ta,
" Afrah ku ci abinci mana ko kun cinye akwai da yawa a kitchen zan qara maku na zuba mata wani, maza kuci,"
Fara ci suka yi, amma Yousuf kwata2 bai jin dad'in ci ba tare da Atiyyaerh ba, a haka ya tura suna gamawa tace su je daki su yi wanka, su huta kafin lokacin islamiyya ya yi,'yan mazan tashi suka yi suka tafi d'akin su, Afrah ma ta nufi d'akin su ita da Atiyyaerh, se ta ga Atiyyaerh kwance tana kuka, ta riqe ciki, yunwa duk ta gama rarake mata ciki, Afrah ce ta je ta zauna a gefen ta ta tambaye ta meye, cikin kuka ta fad'a mata yunwa take ji,
" Umma tace mu cinye zata zuba maki wani,ki je ki ci naki a wajen Umma"
Cikin jin dad'i da kuma tsoron me zai je ya zo Atiyyaerh ta miqe ta fita, zaune ta ganta ta d'ora qafa d'aya kan d'aya ta na kad'a ta, rara gefe ta fara cikin sanyin jiki da murya tace,
" Umma yunwa nake ji, kamar zan mutu,"
" Laaaaa kaji munafukar yarinya,yanzu ke a ina kk san mutuwa? Iyyeee, waya fada maki ana mutuwa in an ji yunwa, wahala kawai zaki sha ba zaki mutu ba in ma tsoron mutuwa kk kar ki bi uwale, matsa ki ban waje munafuka ki je ki shirya, ki saka kayan ki,na islamiyya lokaci ya kusa,"
"Umma abincin fa? Yunwa nake ji yau ban ci abinci ba fa"
"Dan uban ki Adnanu ba Zaki bar nan wajen ba se na b'ab'b'alla ki? Dan munafurci salon Wani ya ji a ce bana baki abinci ko? Kin b'ace min da gani ko se na mammake ki?"
Tini hawaye ya gama wanke fuskar Atiyyaerh, hankalin ta a matuqar tashe, dan ba qaramin yunwa take ji ba, haka ta koma d'akin,ta fara saka kayan ta na islamiyya, tana sharce hawaye, Afrah ma kukan ne ya kama ta, dan ta ji komai, haka suka gama shiri suka fita, Afrah ce ta gaya ma Yousuf komai, hankalin shi ya tashi sosai da jin haka, gaba d'aya tausayin qanwar tashi ya gama lausasa zuciyar shi,dan bai san ya zai ya bata a binci ba tare da Umman su ta gane ba, dabara ce ta fado masa,yace su yi gaba zai taho.
Sallama ya yi ya shiga gidan ya riqe ciki, da gudu ya yi band'aki, ta bi shi,
"Yousuf lfy? Meya same ka? Ko gudawa kk ne?"
" Eh Umma, inna fito zan bi kitchen na sha magani na koma makaranta,"
"To Allah ya sawaqa, ni nayi d'aki ka tabbatar ka ja min qofa sosai kan ka fita,"
" To Umma"
Murmushi ya yi, bayan ta haye sama da dan mintuna kamar biyar ya fito ya yi kitchen ya nemo leda, ya d'ebi abinci, da ruwa a roba, ya d'au maganin gudawa ya fice da gudu, Atiyyaerh ta jingina a jikin windon ajin su tana hawaye tana kallon waje yunwa take ji ba ta wasa ba,can ta hango Yousuf na gudu, da leda a hannun shi, mamaki ne ya ishe ta,bata gama tambayar kanta meye a ciki ba ta ga ya shiga ajin su yana neman izinin an aiko shi wajen Atiyyaerh dan ta taho bata ci abinci ba aka ce ya kawo mata,
" Ablaerh ki taso yayan ki na neman ki a waje kar ki dade," in ji malamin su da ke tsananin son ta, saboda qoqarin ta, bayan haka Atiyyaerh yarinya ce Mai shiga rai, sannan Kuma ba Wanda ya qi yaro me kyau ai.
Cikin hanzari da rashin kuzari ta isa, suna fita ya bud'e mata abincin a wata 'yar kwana a yunwace ta hau d'iban girkin ta na ci idon ta na kwalla, haka ta cinye abincin tas ta sha ruwa, Yousuf kuka yake har da majina, ba qaramin tausayi ta bashi ba,samu ya yi ya goge mata bakin ta sosai da ya yi maiqo,
"In mun koma gida Umma ta baki abinci ko kin qoshi ki karba, in ba haka ba zata gane na baki abinci ta dake ki ta dake ni, kin ji,"
kad'a kai ta yi alamar ta ji,sannan a hankali cikin sanyin murya tace,
" Na gode Yaya,"
Murmushi suka yi wa juna sannan suka tafi ajujuwan su, Yousuf sai da ya sha bulalar latti, sannan aka barshi ya shiga.
*Bayan shekara bakwai*
Atiyyaerh an fara zama budurwa ita da Afrah, Sulaiman da Atiyyaerh na JSS 2, Yousuf Kuma ana SS 2, Afrah na JSS 1 daga baya ta Maida hankali a karantun ta dik da cewa har yanzu bata Kai Atiyyaerh hazaqa ba amma ta fi da fahimtar abinda ake koya musu a makaranta, Atiyyaerh ta zama budurwa me cikar halitta da haiba, duk da cewar ba qaramar wahala take sha ba a gidan duk wanda ya ganta zai d'auka ta fi shekarun ta, tana da girman jiki, Afrah ma hakan take a bangaren ta ba laifi sun yi gadon kyau wajen iyayen su maza da mata, duk wani aikace aikacen gida Atiyyaerh ke gabatar da su kama daga kan wanke2 share2, wankin kayan ta na gida da uniform, watarana har na Rasheedah da Afrah haka za a sa ta yi dole, dik da cewa akwai washing machine a gidan, wataran in za su gidan Mama gaida ita, in ta ga ta je can musamman a week end sai ta ce ita a barta zata yi mata weekend to anan take samu ta huta da aikace2, ta samu ta maida hankali a kan hardar ta ta Qur'an da karatun bokon ta.
Kayan kwalliya wajen Afrah ba a magana, ko abun wankan ta daban ne, daidai misali Auwal harka ta bud'e masa ga aiken kud'i da baya yankewa daga wajen Adnan, kudin da Adnan ya bar masa ya kula da Atiyyaerh ma juyawa yake yi Yana yin blocks da Saida siminti tinda ya fi kwarewa a wannan harkar, dan haka Yana qoqarin wadata iyalin nashi da duk Wani abu da suke buqata, Atiyyaerh kam har ta cire rai da amfani da kayan kwalliya, domin tasha gargad'i wajen Umman su akan kar ta sake ta ganta da kwalliya, ko ta ji ta yi amfani da tirare ko abun wankan Afrah, roll on kawai take sai mata Shima acewar ta kar ta kashe su da warin balaga, duk qoqarin Afrah na ganin Atiyyaerh tayi amfani da su ko a boye ne amma inaa Atiyyaerh taqi Sam domin ta ma riga ta Saba da rashin kwalliyar, in ta matsa sai tace mata
"Afrah kar ki damu, ni Kwalliya bata gabana yanzu, fatana na gama da duniyar nan lafiya ko so kk na saba umarnin Ummana? Wace irin yarinya kk so na zama kenan an hana ni yin abu Kuma na aikata? A haka ma alhamdu lilLAAH bana buqatar Kwalliya na gode da nuna kulawar ki a gare ni, best friends for everrrr,"
Sai ta Kai wa Afrah runguma ta na dariya,lokuta da dama da sabulun wanki take wanka, sannan ta shafa basilin, har cikin ranta bata Jin Wani damuwa akan hakan,duk randa