Showing 78001 words to 81000 words out of 81601 words
Chapter 27 - KAINE JARUMI BOOK COMPLETE Hausa Novels BY HAERMEEBRAH.txt
labulayen a haka iska zata shiga ta na kad'awa gwanin dad'i, ita kuwa Fauziyya zuwa balcony d'in ta ta tsaya ya zame mata kamar ibada,kullum sai ta je balcony d'in nata ta tsaya ko zata ga bawan Allahn nan me kyau da ta gani rannan, takan Sanya kaya masu mutunci wani lokacin harda mayafi dan bata so ya sake ganin ta a yanayin da ya gan ta a baya,to her biggest disappointment Adnan ya dena zuwa wajen,a kullum ta je bata gan shi ba tana shiga matsananciyar damuwa,a ranar sai ta zama wata iriyar shiru shiru bata son kula kowa bata son Kuma a kula ta.
Adnan ne sanye cikin qananan kayan da suka matuqar karbar jikin shi rigar shi ruwan chakulan wando Kuma baqi, sai qamshi ke tashi a jikin shi sakamakon feshe jikin shi da ya yi da turarukan shi masu dadin qamshi da tsada, se ya qawata kyakkyawar qafar shi da baqin takalmi, ya d'auki wayar shi ya fita, balconyn shi,da niyyar shan iska, ( Daddyyyy da niyyar dai ganin Fauzy🤣) yana zuwa da minti kamar 4 sai gata, ta fito, sanye cikin riga da wando, sai ta yafe kanta da mayafi, fuskar ta ba walwala ta fito ta tsaya ,dan a zaton ta yauma bazata gan shi ba, amma bata cire rai ba, kallon wajen shi ta yi cikin yanayin da ke nuna saddaqarwa akan ba ganin shi za ta yi ba yau ma, amma mamakin ganin shi da farin cikin ganin shi ya sa ta kusa sake wayar ta a qasa, wani murmushi ta saki mai nuna tsantsar farin cikin ta, d'aga masa hannu ta yi ba tare da ta sani ba, sai da ta kula da abinda ta aikata ta yi saurin saka d'aya hannun ta sauke wancan, dariya ya yi irin ta manya,ya d'aga mata hannu shima, alamar gaisuwa ta masa, da kai da hannu, shima ya amsa, nuni ya yi mata da yana son ya zo wajen ta,itama ta masa alamar amincewa, cikin kunya ta juya tai dakin ta da gudu,tana shiga ta haye saman gadon ta tana tsallen murna, a haka maman ta da take kira Mum ta shigo, tana ganin Mum d'in ta ta tafi da gudu ta maqalqale ta tana murna,cikin 'yar dariya mahaifiyar ta ta ce,
" Meye haka Baby zaki balla ni fa,"
"Mum ya zo yau, har munyi magana, ya ce zai zo anjima,na amince masa da ya zo, mom I can't wait to see him, I want to hear his voice, I want to know him mommy,"
Cike da fara'a mahaifiyar ta ta ce,
"To Alhamdu lilLAAH na maki murna Baby, fatana Allah ya sa ya zama alkairi a rayuwar ki, ya sa SHI NE JARUMIN KI da ki ke Jira, lallai a cikin kaff Wanda suka nemi auren ki ki ka qi su to wannan ya yi sa'a dan da alama da za a bar ki ke Zaki je neman auren shi da kan ki,"
Cike da shagwaba ta ce,
"Mommyyyyy! Ko da yake gaskiyar ki ne fa,nice na yi sa'a in kk ganshi tabbas zaki fi gane dalilin da ya sa na shiga wannan yanayin akan shi, he is so handsome and gentle, ya hadu Mum, i think i am deeply in love with him, Ya Rabby Allah kasa shine alkairi na,in ba alkairi bane a rayuwata da addini na, Allah ka min sauyi cikin sauqi ba tare da na wahala ba,"
A sanyaye ta qarasa addu'ar ta, Mahaifiyar ta ce ta shafa kanta, tare da sumbatar goshin ta ta ce,
" Allah ya amsa baby, ki kwantar da hankalin ki, rabon ka baya tab'a wuce ka,sannan abinda ba rabon ka ba baya tab'a samun ka,in Allah ya yarda alkhairi ne a gare ki shi yasa Allah ya had'a ku a airport Kuma ya Sanya kuka zama maqota"
D'aga kai ta yi ta na Murmushi da Kuma gasgata maganar mahaifiyar ta,suna tsaka da hira ta zabura ta ruga toilet tare da fad'in,
"Mum i have to look beautiful Ina zuwa na yi wanka na zo ki min kwalliya,"
Dariya maman ta ta yi tace,
"Baby ai ke dama can kyakkyawa ce baki buqatar makeup, sannan ma ke me Zaki da Kwalliyar tsofaffin, ki gama ki dai zo ki yi da kan ki tinda kin fini iyawa nima watarana ke kike mini,"
Tashi ta yi ta shiga duba ma yarinyar ta ta kayan da ya kamata ta saka,wata doguwar riga ce,Fara sol,da ratsin golden color a jiki,ta sha aiki ta wajen wuyan ta da hannu, ta tsuke ta sama sai ta yi fad'i sosai ta qasan ta, sai mayafin rigar shima kamar rigar ya sha ado ta d'akko mata, ta feshe mata rigar da turaruka masu sanyin qamshi, ta d'akko mata wani golden color takalmi, mai dan tsini amma ba can ba,ta aje mata,sannan ta yi murmushi tace,
" Allah ya bada sa'a Baby bari na je na had'a maku abun motsa baki kafin ki kammala, na fi so na yi da kaina kar mu fara da bashi abincin masu aiki ko"
Tana gama magana ta fita,Fauziyya kuwa ta na can tana qalqale fata, kamar ance mata tabawa zai yi ya ji ta fita ko da datti, bayan ta gama ta fito d'aure da towel tana ganin kayan da Mom d'in ta ta fiddo mata sai ta yi murmushi tace,
"Thanks Mum,"
Gaban mirror ta je,ta hau gayu, kwalliya ta yi sama2,wadda ta qara fitar da sirrin kyan ta, gyara gashin ta ta yi, sannan ta saka kayan ta, Masha Allah, duk wanda ya kalle ta dole ya yi marmarin qara wa,tana zira takalmi, Daddyn ta ya kwankwasa d'akin nata tare da sallama ya bud'e qofar ya shiga, kallon ta ya yi daga sama har qasa ya ga yanda ta yi masifar kyau, sai kawai ya tsaya a kan qafar shi d'aya ya na bin ta da kallon tuhuma,hannun shi d'aya a qugun shi sannan ya ce,
"Wannan gayun fa, ko dama can kina da masaniyar zuwan baqo wajen ki ne?"
Cike da jin kunya ta rufe fuskar ta, murmushi ya yi ya bata hannu akan ta je gare shi, miqa masa hannun ta yi, suka fita a tare, sai da suka je babban parlourn nasu sannan ya zaunar da ita kujerar dake d'an nesa da ta Adnan,da Auwal, dan ya sanar dashi zasu zance,Auwal ya yi ta tsokanar shi, daga qarshe yace in sun gama da nan shima zashi yaga tashi budurwar, kallon ta kawai suke,kamar sunga sabuwar halitta, Daddyn ta ne ya zauna kusa da ita suka qara gaisawa da su, itama ta gaida su, sannan Daddyn ta ya fara magana kamar haka,
" Alhaji Adnan, da Alhaji Auwal,naji dad'in zuwan ku matuqa, da kuma abinda ke tafe da ku,kamar yanda na sanar da ku d'azu in dai ta b'angare na ne ban da matsala akan hakan, sai ma fatan alkairi da zan yi a gare ku,amma ina son ku san wani abu d'aya,dik yanda zan baka goyon baya in baka nemi soyayyar ta ba lamarin ba zai yuwu ba dan ba zan yi mata dole ba,duk duniya bayan mahaifiyar ta, ita nake gani na ji dad'i, itace sanyin idaniya ta, ka ga kuwa duk yanda na kai da son ka in Fauziyya ba ta yi na'am da Kai ba gaskiya sai dai na baku hakuri, ina fatan zaka riqen amanar ta, kuma bazaka tirsasa min ita ba?"
" Inshaa Allah Alhaji ba zaka samu sabanin abinda kk so ba daga wajen mu,kamar yanda na Sanar da Kai nima ina da Yara ka ga ba zan so na yi wa taka ba daidai ba, Allah ya shige mana gaba a wannan lamarin,"
"Ameen, to ni bari na shiga daga ciki"
Sallama ya musu ya basu waje, kunya a wajen Fauziyya kuwa kamar tace qasa bude na shige,duk jin ta take a takure, ta saba zama gaban maza ayi hira ayi karatu amma wannan karon sai take jin ta wani iri,gaishe su ta sake yi suka amsa ta ja baki ta yi shiru,masu aiki ne suke shigo da kayan motsa baki, bayan sun gama ajewa sun tafi, Auwal ya gabatar da kan shi sannan ya gabatar da Adnan a matsayin Wanda yake son ta da aure ba da wasa ba, bayan kammala yad'a manufar su da Auwal ya yi Adnan na ya karb'e ya qara jaddada mata manufar shi akan ta sannan suka yi shiru suna jiran jin ra'ayin ta, cike da kunya ta ce,
"Na amince da Kai da Kuma abinda ke tafe da Kai waje na,Allah ya tabbatar mana da alkhairi,ya kare dikkan abin qi a lamarin"
Ta na gama fad'in haka ta rufe fuska da siraran yatsunta,
"Ameen"
Shine abinda suka had'a baki suka amsa mata da shi cikin murmushin ganin yarintar ta,hira suka ci gaba da yi a nan ne ta ke Jin taqaitaccen tarihin shi,se dai ya b'oye mata kamannin da yake ganin ta na Yi da marigayiya gudun kar ta yi zaton ko shi yasa ya zab'e ta, ba zata ji dad'i ba, kowacce mace ta na so a so ta dan ita d'in ake so ba dan wata alaqa ba, Fauziyya ta tausaya mashi sosai, dan ta kula akwai soyayyar matar shi sosai a ranshi,ta yi masa ta'aziyya sannan Kuma ta masa uziri rashin masoyi tabbas ba dad'i,daga baya suka mata sallama suka tafi, bayan ya aje mata tsarabar daya kawo mata, na turaruka.
Gidan budurwar Auwal suka je daga nan, ta sha kwalliya da atampa kalar red da fari, sai ratsin baqi,ta yi kyau sosai itama ba laifi ba makusa,se ta yafa farin mayafi a saman Kwalliyar ta, ta qawata qafarta da farin takalmi, dan Auwal ya sanar da ita dawowar Adnan da yake yawan bata labarin shi,dan haka ta san komai game da rayuwar su, bayan sun gaisa itama ta masa ta'aziyyar rashin Sakeenaah, yaji matuqar dad'in hakan,suka taba hira kafin su tafi itama Adnan ya bata ledar da ya yi mata tsarabar turaruka,sannan suka rabu kowa ya yi gidan shi.
Rasheeda na zaune ido tarwai bata ko Jin alamun bacci a cikin su, qarfe goma daidai ya yi sallama ya shiga gidan,
"Daga ina kk malam? Ohhh daga wajen karuwar da kk son kawo min cikin gida a matsayin kishiya ka ke ko? To bari kaji na fad'a Maka Auwal, ba zan zauna da kishiya ba, sai dai ka zab'a,ko ni ko ita,"
Ta kame hannu a qirji tana girgiza qafa,sanye take da doguwar rigar bacci mai santsi da ta daurawa zani a saman ta.
"Ke dai zaki zab'a zama dani ko tafiya gidan Abbah, ni dai na wa qanwar ki 'yar aljannah da yardar Allah alqawarin ba saki tsakanin mu, amma in kina ganin zaki tafi ko kina son sakin zan iya baki, aure kam kamar na yi na gama, yanzu ne zaki tantance a Ina ake yin kishi Rasheedah,a tsakanin soyayyar zumunci da soyayyar miji, sannan da wasa kk sake ce ma matar da zan aura karuwa tabbas sai na barar maki da haqora, in yaso kin ji dad'in yin kishin da b'ab'urarren baki, sokuwa kawai,"
Kuka ta d'ora hannu aka ta rusa, yaran su na d'aki suna jiyo su, kowa dariya fal ciki, Afrah da take ita d'aya a d'akin ta kasa jurewa ta yi,ta kuwa hau kwasar dariya abin ta, dan ji take kamar ta matso da ranar auren Abban nasu, Yousuf bai son ya yi dariya saboda Sulaiman ba'a sirri da shi dan ya na fasa dariya zata Jiyo su,in kuwa ta ji su se sun sha jarabar ta akan su zata juye haushin uban su, ai ko suna had'a ido suka fashe da dariya a tare,Sulaiman da ba a sirri da muryar shi har waje, tana ji kamar mahaukaciya sabon kamu ta yi hanyar d'akin tana zage2 ta na fad'in sun raina ta,ba laifin su bane laifin ubansu ne daya sai mata raini a wajen su, kafin ta idasa shiga d'akin Yousuf ya yi tsalle ya datse qofar ya rufe da key, ta gaji da fadan ta a bakin qofa tai gaba, dariya suka ci gaba da yi,suna maida zance.
A lokaci d'aya, Adnan ya shigo masu da lefe,har na Atiyyaerh shi ya had'a tinda Allah ya hore masa arziqin yin hakan, sadakin Atiyyaerh da Sulaiman Auwal ya d'auki nauyi, Adnan ya sanar dasu, dukkan su a gidan shi sabo da ya sa aka gina tin kan ya dawo zasu zauna, har Abbah da Mama duk zai dauke su daga nan tsohon gidan,mijin Afrah ne kawai zai dauki matar shi ya Samar mata muhalli dan kar su ga an musu katsalandan a lamuran su,dik da cewar Adnan ya fara yi wa mijin nata tayin komawa sabon gida amma ya nuna masa ah ah ,ya fi so su zauna a inda ya gina da kan shi,dake yana da zuciyar nema shima, ya ce A'a yana da gida,in dai Afrah zata iya zama, d'aki uku ne, kitchen da toilete a kowanne daki, ga toilet a tsakar gida,sai babba parlor da dinning area, ga parking space, da ba zai wuce wajen zama mota d'aya ba, ba laifi, gidan ya yi sosai,Afrah ta aminta, inda ta nuna mai ita ko da gidan qasa ne zata zauna da shi,albarkar auren suke nema.
Sati biyu da kai lefe aka d'aura auren su, gaba daya, an sha shagalin biki ba kadan ba, nera kam ta koka, kuma sun koka rashin Sakeenaah a wannan rana, wanda Rasheedah ce ta fara kokawa har abun ya ba su mamaki, har ma ta dinga yi mata addu'a, mutane ma akai ta yi mata addu'a, 'yan uwan Adnan ma sun nuna bajinta a wannan gagarumin ruguntsumin bikin aure me dimbin tarihi da aka gudanar na tsahon kwana hud'u,bayan kammala dinner da aka gabatar a rana ta hud'u mutane da dama suka koma gidajen su,Wanda za su Kai amare da Kuma Wanda za su kwana washe gari su wuce suna nan ana ci gaba da harkokin azziqi.
Amare da angwaye ne zaune a qasa a gaban Abbah ya tara su a babban parlourn shi dan yi musu nasiha da addu'o'i kowa zaune kusa da matar shi,amare sai 'yan koke koke suke na al'ada, Atiyyaerh kuwa kukan ta ya had'a ma'anoni da yawa, tinawa da auren ta na fari, rashin mahaifiyar ta,da murnar samun auren zab'in ran ta.
Abbah da Mama sun ce za su bar angwaye da amare su gama amarcin su kafin su koma sabon gida, Dan haka ba da su za a tare ba.
Rasheedah kuwa kamar zata mutu haka take jin kishin nan na tab'a qoqon ranta,cike da takaici ta shige motar Auwal ta na jiran shi ya je ya ja su ya Maida su gida, a gaba ta qame qam ta na jiran ta ji an ce ta koma baya ta sauke kwandon rashin mutunci, ba Wanda ya kula ta, Auwal ya bud'ewa amaryar shi baya ya Saka ta ya koma mazaunin driver ya ja su suka wuce gidan su.
Adnan kuwa da motocin shi akai ta zirga zirgar Kai amare da shi kuwa da kan shi ya ke son ya Kai amaryar shi gidan ta, dan daga wajen Dinner a gidan Abbah dik suka taru har Baffanin shi da Kawunan su akai addu'a da Sanya albarka.
Bangaren Rasheedah kuwa ko da suka Isa gidan qin fita ta yi a motar ta na so ta ga kwal uwar daka, Auwal be kula ta ba ya je ya kulle gate ya yi addu'a, sannan ya ja hannun amaryar shi ya ce ta kulle gidan in ta shigo suka shige suka barta a wajen,a tsaye ta tadda Auwal ya qanqame amaryar shi kamar za a kwace ta sai Wani shinshinar ta yake yi, amarya kuwa kunya duk ta hana ta kwakkwaran motsi,bakin shi ya Kai saman nata ya sumbata a hankali narkewa ta yi a jikin shi ta na b'oye Kan ta a qirjin shi, motsin Rasheedah ne ya sa amarya ta janye jikin ta daga nashi,tana kallon Rasheesah da ta cika ta yi fammm, Abba ne ya yi masu magana akan yana son ya yi magana da su, ganin irin kallon da Rasheedah ke wurga wa amarya se ya bawa Amarya haushi, dama ta na da labarin Rasheedah kaff Dan haka sai ta koma ta sake lafewa jikin Auwal cikin shagwab'a ta ce,
"Gaskiya ka bari sai gobe ka yi mana maganar please baby, saboda ni dai ....ni daiiiii Ina buqatar mijina yanzu ka ji baby,"
Cike da shagwaba ta qarasa maganar kamar wata 'yar qaramar yarinyar da bata gama Iya magana ba, gaba d'aya Auwal ya rud'e, ya susuce, janta ya yi kawai suka fad'a d'akin su, Amarya ce ta rufe qofar, tare da watsawa Rasheedah mugun kallon da ta ga ta na bin ta da shi itama, sannan ta ce mata
"Yah dai na ga ki na biyo mu ko da ke za a shiga d'akin amarya da angon ne?"
Ta ja guntun tsaki sannan ta doka qofar ta shige,wata qara Rasheedah ta sake, ta durqushe a wajen tana kuka, da kan ta ta rarrashi kan ta ta yi shiru,ji ta yi sun tada sallar su ba Wanda ya kula ta,daga nan taji Auwal na yi wa amarya addu'a suka ci kazar da bata San sanda aka siya ba balle sanda aka Kai ta d'akin,to Ita Ina tata kazar? Amma dai Auwal bai da adalci in dai haka ne, sai hirar su take ji sama sama, dik da dai Auwal ne ke ta zuba amaryar ta koma Jin kunyar shi, can Rasheedah ta ji ya sauya salon nishin shi da kalaman shi, da gudu ta bar wajen ta yi daki ta na mugun gunjin kuka tare da fad'in,
"Na shiga uku ni Rasheedah, dama wannan ne kishi, kenan da gaske Hassada nake wa qanwata uwa d'aya uba d'aya, a da bana jin wannan qunar zuciyar da na ke ji a yanzu, wayyo zuciyata , Sakeenaah ki yafe min, tabbas kin yi gaskiya,abinda kk so na gani na gane a yanzu na ganshi Kuma na gane wayyoo ni Rasheedah na shiga uku na lalace,"
kuka take kamar ta had'iyi zuciya take ji, kanta kamar zai cire qasa dan ciwo, a nan qasan ta yi baccin wuya, kamar a mafarki ta ji an bud'e qofar d'akin ta an shiga, dukan qafar ta ta ji ana yi kamar tashin ta ake Daga bacci, bata gasgata ko