Showing 24001 words to 27000 words out of 155423 words

Chapter 9 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx

26 Oct 2025

419

/>
Ta na tafe ta na masifa da harshen turanci.

"Ku yi hakuri da halin Azizah, in baki manta ba, akwai wanda muka zaba Maki ki aura a baya, qanwar shi ce, yanzu haka su na da hannun jari mafi yawa a kamfanin mu, yayan nata ke riqe da kamfanin, mutumin kirki ne matuqa, amma Aziza dake renon qasar waje ce, tarbiyyar ta da tamu ta bambamta, a haka ta fara barin wasu munanan halayen mutanen can, ku ci abincin ku, ku rabu da ita, a qasan ran ta, mutuniyar kirki ce, ba ko da yaushe take haka ba"

"Ba bu komai Hajiya,Allah ya sa ta gyara halayen ta gaba daya, domin ku ci gaba da jin dadin zama da ita"

"Ameeen" shi ne abinda yayan ta ya riga kowa fadi, ya na mutuwar son Aziza, amma halayen ta na baqanta ran shi.

Bayan kammala cin abincin su ne, Bilkisu ta ga Hajiya ta goge bakin ta da tissue ta ɗora a kan ragowar abincin ta, ga qashin da ta ci ta tauna duk ta zuba a sauran abincin, tashi ta yi tsam ta dauke, sannan ta kalli Hansatu ta ce,

"Umma ai dai ba kyau wulakanta abinci ko? Hajiya ki dena bata abincin da kika rage, kar watarana ki rasa abinda za ki ci, Umma bari na samo leda mu qulle sauran mun dumama gobe"

Kunya ce ta kama Hansatu matuqa, Hajiya kuwa da Yayah yi sukai kamar ba su ji me Bilkisu ta ce ba, kwashe wanda suka zuba a saman plate din suka yi kawai, suka tara a wani empty mazubi dake wajen,

"In Allah ya yarda daga yau ba zaku sake zama da yunwa ba kunji?"

Daga kai yaran sukai suna kallon Uncle din nasu cikin farin ciki.

Basu suka fara shirin komawa gidan su ba, sai bayan isha'i,Hajiya ta haɗa masu ashirin ta arziki,dan kuwa sai da bayan mota ya qi rufuwa.

Kayan sawa ne, na Hansatu da yaran, da na Isa kan shi, Isa kuwa bayan sabbi shi da Hansatu har da kwance na Yayah da Aziza da Hajiya suka samu, yaran ne kawai aka sai masu sabbi tun kan su je.

Har qofar gida motar ta tsaya, Yabbuga na jin qarar mota ta diba da gudu ta labe a zaure, ta na leqen su, Dan Jumma kuwa mamaki ya gama kashe shi,gulmar ta ta har ta kai, su na tsaka da hirar su ta zabura ta yi waje haka?

Sai da ta gama ganin kayan da Isa ya shigar shi da Hansatu sannan ta koma ta labe a katanga, daidai inda ta kan ji maganar su, ta na tsaye ta ji maganar Isa,

"Bubbude mu ga meye a ciki, dan iskanci shi ne dazu ku ka tafi cin abinci kuka bar ni zaune ga dan iska, na je gidan su Mata ta cin azziqi ko?"

"Ka yi hakuri ba haka bane"

"Dalla Malama bude naga me aka saka a ciki,"

Ganin abun azziqin ne ya yi yawa, nan da nan ya fara washe baki, ya na zuba, har zama ya samu waje ya yi, ya na ma Hansatu hira, mamaki ya gama kashe ta.

Ranar Isa sai da ya gwada mata soyayyar da suka dade ba su yi irin ta ba.

Ta ji dadin hakan matuqa, addu'a ta dinga yi Allah ya tabbatar da su cikin azziqi mai albarka.

Yabbuga kuwa ta nade komai jira take washe gari ta yi ta guntsawa qawayen ta na gulma, duk yanda ta so ta yi maganar abu da Dan jumma ya qi bata hadin kai, tai ta Masifa ita daya, har bacci ya dauke ta.........

Sai mu jira uwar gulma ta tashi daga kwana😅

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 16:

Da misalin 8:12am, Yabbuga na tsaye a qofar dakin Hansatu, riqe da jug din da ta ciko shi da wani tsinkakken kunun da ta tsulawa ruwan zafi, sai sallama take wage baki ta na dokawa, Isah ne ya fito ya na miqa, rigar shi a kafada, ko kauda ido Yabbuga ba ta yi ba, ta fara gaida shi ,

"Ango na Hansatu, an kwan lahiya?"

"Lahiya lau, qaqa an kayi yau kittaho gidan ga da swahiya haka?"

"Ohhh ni Yabbugan Dan jumma abin arziqi dai be amshi kare ba, wagga tambaya awab-ba a son zuwa na?"

"Ni ban ce ba, na ga dai ba ki saba taho wa da sahe ba, Ni rabo na ma da na gane ki gidan ga na mance"

Sai a sannan kunya ta kama Yabbuga.

"Yo jiya ina zaune na kunna gidan redio nijji Mallam na wa'azi akan zama da maqwacci lhiya, shi na nicce bari mu gyara, rayuwar ga ba tabbas"

Isah dai kurkure bakin shi ya yi, ya fice.

Hansatu ce ta qarasa fita tsakar gidan, dan dama ta na tsaye, ta nutsu ta yi shiru ne kar a ce kuma ta yi laifi.

"Barka da sahiya Yabbuga,"

"Barka dai Hansuwa, shin ina 'yan yara ban gane su ba"

"Su na ciki, karatu Ni ka masu, ke san abinda ya hwaru, ina tsoron barin su sake hita,kuma dama basu zuwa boko, to mu na karatu a gida "

"Allah Sarki, tauu ga wanga nikkawo musu, a gasa hanji, ko da dai na ga jiya kun tai gari a mota,"

Cikin dariyar son jin gulma ta yi maganar, Hansatu murmushi ta yi ya karba, ta na godiya, a zaton ta Yabbuga tafiya za ta yi, sai ta ga ta na qoqarin binta ciki, kasa hana ta shiga ta yi, suka shiga ciki, kayan da Yabbuga ta gani jibge sun so tsorata ta, amma ta dake,

"Ah ahhh wanga abin arziqi hwa, daga ina?"

Murmushi kawai Hansatu ta yi, ta nemi tsohuwar tabarmar ta ta shimfidawa Yabbuga, tunda suke a unguwar wannan shi ne zuwan Yabbuga na Shida har ta zauna a dakin ta.

Tun ta na farko farkon zuwa, lokacin ta na da abubuwa,sai kuma yau.

Abu kamar a mafarki kawai Hansatu gani ta yi yabbuga na bude buhuna ta na leqawa, mamaki ma ya hana Hansatu magana, Ita kuwa ta na budewa ta na Suratu, tare da yaba abubuwan da ta gani.

Isah ne ya shigo, tare da fadin,

"Ku jira Ni ina zuwa,"

Dakin ya fada ba ko sallama, Yabbuga kuwa qamewa ta yi a gefe, dan tun da ta ji Muryar Isah ta daina leqen buhunan.

"Ke miqon wannan buhun da na ware jiya,"

"To"

Shi ne kawai abinda Hansatu ta ce,gashi ga buhun ya dauka amma ba zai dauka ba sai ya sata aiki.

Da kyar ta ke jan buhun, ta kai waje, kayan abinci ne danqare a ciki, da suturu masu tsada, ya tattare, a cewar shi ba ya so su saba da abin duniya ,shi kuwa ba shi gare shi ba, kuma da iyayen ta suka tula musu kayan abinci ba na cefane da shekarun shi zai sai kayan miya?

Maza ne a tsakar gidan guda uku, daya mai gwanjo ne, daya mai shago ne, daya mai sai da kayan abinci ne na awo.

Sai da Hansatu ta fitar da buhu uku, sanan ta koma ta na maida numfashin baqin ciki, da gajiya.

Ta na tsaye ya gama siyar da komai, aka bashi kudin ya kalmasa a aljihu.

Ya kalli Hansatu da ke tsaye ,

"An jima ki dafa taliya, mun kwana biyu ba mu ci ta ba, kwai ragowar manjan nan ko? Ki soya, ga hamsin a siyo yaji, wannan ashirin din ki sai Maggi, kin San taliya da manja akwai dad'i,se na dawo"

Miqa mata saba'in ya yi, ya fice, amsa ta yi ta na masa addu'a har bakin qofa, ta koma ciki, a zuciyar ta ta ji dadin kudin da ya bayar, a qalla an samu sauyi, tunda da ko kwandala baya bayarwa (to kudin da ya saida abincin fa?)

Mamaki ya gama kashe Yabbuga, amma cikin ran ta fari kwal, domin yau ta guntsi gulma me dumi a bakin ta, jira take su Lamishi su dawo daga aiki a zauna majalisa ta guntsa musu suma.

Sallama ta wa Hansatu ta tafi, ta na shiga Dan Jumma ya fara tambayar daga ina take.

"Gidan makwatta nittai, ko an hana ziyara ne a hadissan da kk karanta min kullum?"

"Ah ahhh ni ban ce ba, amma ziyara ba halin ki bane sai kin so gulma"

"Dan Jummaa Ni ka ka kira magulmaciya?"

Bai amsa ta ba ya fita, tare da sanar da ita ga dari uku nan a sai kayan miya, shi ya tafi.

Masifa ta dinga yi, kamar akwai me sauraron ta, ta yi ta kuma ,ita a dole an fada mata sunan da ba halin ta bane.

***********************

Yamma ce liss, garin na fitar da hucin zafin ranar da ya kwankwada da rana,wanda ke waje, kuma a unguwa irin ta yaku bayi, shi ya ke dandana kudar shi, dan kuwa ba shi da abubuwan more rayuwar da zai sanyaya jikin shi, balle ya samu ruwa mai sanyi ya sawa tumbin shi ya ji dadi.

A gidan gwamna Halliru kuwa Hajiya Ikee ce ta shiga dakin Sultana, Wanda ta kashe fitilu tsaf, ta ke kwance cikin duhu, idanun ta da suka kumbura na kulle, ta takure waje guda hawaye na zuba a cikin su.

Sanyin da ke ratsa dikkan wani sashe na jikin ta ya sa ta rawar dari, Hajiya Ikee ce ta dau remote din AC ta rage sosai tare da fadin,

"Haba Sultana, wagga wace rayuwa kin ka ɗorawa kan ki ta jidali? Ke zauna ke dai a daki, awar wata mayya, ke ware kan ki, rayuwa kuwa za ta yu a haka?"

Juyar da fuskar ta gefe ta yi, sannan ta goge hawayen ta a hankali, fitilun dakin Hajiya Ikee ta kunna, da sauri Sultana ta kulle idon ta, saboda hasken da ya gauraye dakin ta.

"Tashi mu je, Daddyn ku ka kiran ki,"

Kamar ba za ta tashi ba, amma ta miqe da kyar, cikin tsananin gajiya da zaman da ta ke a daki, bude wardrobe din ta ta yi, ta dauki wata riga jallabiya mai kyau, kalar ja, ta sanya a kan qananan kayan nata.

Mayafin ta yafa, ta fita, ba tare da ta jira Hajiya ba.

Su na isa katafaren parlour'n da ke dauke da manya kuma fararen kujeru,sai manyan hotunan shugaban qasa, mataimakin shi, gwamna da mataimakin shi, sai daya gefen hoton ahalin gidan ne, su na dauke da farin ciki, da nishadi ,sultana na rungume a jikin Sultan su na dariya, iyayen su ma na rungume da junan su.

Parlour'n komai fari ne, sai carpet mai kalar green da ratsin baqi, glass table babba a tsakiya da gefe da gefe, sai suka qayata kwalliyar wajen.

Sultan na ganin qanwar shi ya miqe, ya tarbe ta, kanta a qasa ta gaida shi, y amsa, duba fuskar ta ya yi, ya ga ta na murmushin yaqe.

"Sulty baby me ke damun ki ne haka?"

"Me zai dame ta kuwa? Banda tunanin talakawa da tassa ga rayuwar ta, ka san diyar Daddy akwai tausayi, taho nan wajen daddy kin ji Sultyn Daddy"

Cike da shagwaba ta zube a kujerar da yake zaune, shi kuwa ya rungume ta ta gefen shi na dama.

Cikin kulawa, da lallashi ya fara magana, kamar wani na Allah.

"Sulty na, ina so ki sani, ita rayuwa ta na zuwa ma kowanne bawa ne ta yanda Allah yasso, sannan shi wanga abu da kin ka ga shi na hwaruwa iko ne na Allah, ba lehin mu na ba shuwagabanni, lehin talakawa na, domin kuwa da damar talakawa da ki ke gani sun hi masu kuddi iskanci, sun ji masu kuddi sabon Allah, shi nassa Allah ke jarabtar su, ba komi na ba, amma masu mulki na da lehi suma, wajen qin tallafawa talakawa, ta yanda za su samu abin yi har su taimakawa wasu, to wanga tunani da niyyi yassa nacce, daga yanzu zan bude maki gidauniya, da zaki zanka taimakon talakawa, ki na shiga duk inda kk so, dan ki tallafawa talakawa, na amince maki na yarje maki, Amma da sharadi "

Hamdala kawai take jarawa, tare da share kwallar farin ciki, cikin sauri da azama tace,

"Daddy fadi sharadin ka, in Allah ya so ina cika shi"

"Sharadin shi na, office zan bude mi ki, ba na son yawan yawo, ki nemi ma'aikata da kan ki, shi ma shi na cikin taimakon da zaki hwara, Sannan akwai driver da na samo maki, ban yarda ki hita ko da da bakin gate na , ba tare da shi ba,ya zame maki tamkar inuwa, duk inda kin ka sa qawahun ki shi aje na shi nan, har office ina so in kittai, shi zam shi na tsaye bakin gambu, ba driver bane kadai, yanda zai kula da rayuwa ta haka zai kula da taki, ina ji da shi cikin masu yi min aiki gaba daya, ki yarda da shi ba zaki wahala ba"

Maganganun shi duk sun shige ta, kuma ta riqe su kaff a kwanyar ta, dan haka tace,

"Daddy na yi ma alqawarin kula da dukkan sharudan ka, na gode na gode na gode Daddy na"

Sultan ma farin ciki ya kama shi, ganin farin ciki a fuskar qanwar shi.

Hajiya Ikee ce ta ce,

"Tau yau dai ki na hitowa cin abinci damu ko?"

"Eh, yau da Ni za a ci abinci, Ni zan serving kowa, na hutar da masu aiki"

"Hhhhh sai ka ce ke ki ka dahwa, dan dai serving abinci, ai ba aiki na ba"

Cike da shagwaba ta kalli Daddyn su da ke danne dannen remote dan sauya tasha, hankalin su na kan hirar shi kuma ya ga ana nuna wani mummunan ta'addanci da aka yi ma wata rugar Fulani, wanda abun ya bashi mamaki, dan ba shi da hannu a lamarin, to waye ya aikata hakan?

Ya na sauya tashar ya ji Sultana na fadin,

"Daddy ka ga Yah Sultan kooo"

Murmushi ya ɗan yi a takaice, sannan ya ce,

"Sultan za ka sha mamaki duk sanda Sulty Baby ta maka abinci mai dadi ,sai ka bani ajiyar kunnen ka guda"

Dariya sukai ta yi, cike da nishadi suka ci gaba da hira.

***********************

Gwamna ya sanar da Lawwali duk wani tsare tsare da shirin shi, ya kuma damqa amanar sultana a hannun shi, ya nuna masa mahimmancin kula da lafiyar ta, da bata kariya, ya yabe shi akan irin jarumtar shi, da ganin zai iya kula masa da gudan jinin shi.

Lawwali kuwa ya sanar da gwamna zai kula da Sultana da rayuwar shi,kafin wani abu ya same ta sai ya fara samun shi,gwamna ya yarda da Lawwali matuqa.

Lawwali ya koma gida cike da murna da farin ciki, wayar Lamishi ya kira dan a hada shi da farin cikin ran shi wato Mubaraka.

Ko da ya dauka sai ya ji haniya,tsaki ya ja, dan ya san ta na can majalisar tasu ta gulma ne.

"Lamishi ya da ai a hada Ni da Mubaraka ne? Na san ki na can majalisar ku ta gulma,"

"Lawwali za ka ci uban ka, Ni ka ka hwadi ma magana haka ba ladabi? Tau dan uban ka Ɗan Talo, ko shi be isa hwada min ba sukari ba"

"Shi kin ka ce, dama tsoron ki shike"

Cikin dariya ya yi maganar, dan kuwa hango ta yake ta karkace ta qanqance idon nan zata fara zabga masa masifa, tunawa ya yi ashe ya sai ma Mubaraka waya,kit ya kashe wayar, Lamishi kuwa dai zuba ruwan masifa take, tare da yi masa alqawurran rashin mutunci duk sanda ya je gidan.

Ko da ta kula ya kashe wayar ma bata dena wayar qarya ba, dan kuwa Yabbuga ta hanga ta ga yanda tai shiruuu ta nutsu, kamar ba ita ke zuba masu gulmar gidan Hansatu ba, tsoron da Yabbuga ke wa Lawwali ya shahara, ba tun yau ba ko waya ya kira Lamishi in su na tare, tari wannan bata so ya kwace mata,wani ashar Lamishi ta danna kamar ta na yi da Lawwali, ware ido Yabbuga ta yi, ta na kada yatsa, alamar Lamishi ta bari.

Sai da Lamishi ta gama wayar qaryan ta sannan ta ce,

"Dan babbar butar me gari kai, aza shi kai dan shi na tantiri a waje, Ni ma za ze gagare ni, to ni na ci uwar dan iska na yaga zani, Allah shi maido shi gidan lahiya, zan nuna masa Ni na haihe shi,Ni uwar shi ce a dabanci"

"Um ummm Lamishi, ki dena Jan Lawwali da hwada, in kai nai ya juye walle shi na manta ke uwatai ta shi yanka maki dukan wahala"

"Ke arrr, matsoraciyar banza, nan nan ko tari Lawwali ya yi gudu kike, sai ka ce ke ba qawar uwatai ta ba"

Yabbuga da ko dogon labarin Lawwali ba ta so a yi ce ta kalli hanyar da mijin ta ke dawowa ta ce,

"Ohhh yau Dan jumma ko ina ya tsaya, bari in shiga gida in zuba mai ruwan arwalla ga buta"

Habaa me su Mai Buruji za su yi, banda dariya,yau Yabbuga ke son zubawa miji ruwan alwala, saboda tsabar an kirayi sunan dodon ta, bata kula su ba ta fada gida, ta na shiga ta rufe gambu ,(qofa).

Hijabin ta ta cire ta hau mita,

"Bahaushe ya ce hanyar lahiya, a bita kullum kullum (a bita da shekara ) ina nika yarda uwa tai ta je ta ambaci suna na gaban wannan me danyen kan shi biyo ni har gida shi yi min aikin ganganci? Ban wallah daukan kasada,"

Butar ta dauka zata zuba ruwan, me ta yi tunani kuma oho, ta fasa ta fada dakin ta.

***********************

Yau mutan gidan Gwamna Halliru sun tashi da bayyanannan farin ciki, dan kuwa Sultana farin cikin su ce, a duk sanda take walwala, to suma su na walwala, sanda kuwa take cikin qunci, suma fa ba za su zama cikin farin ciki ba, har sai ta koma normal.

Hakan ce ta sa gwamna yi mata abinda zai sanya ta farin ciki.

Cikin doguwar riga baqa mai fadi mai stones kalar blue da farare su na ta walqiya kamar fuskar ta, ta fito,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login