Showing 132001 words to 135000 words out of 155423 words
Chapter 45 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
na ganin zumudin da take ya kira ta, ta je gaban shi, ta na dariya, zama yayi ya na nannade hannun rigar shi, wanda hakan ya zamar masa kamar wata al'ada,
"Shin ba ki bari a d'aura auren su Barira sannan ku tai?"
Dafe goshin ta ta yi, sannan ta ce,
"Kashhh, ka ko ga na mance wallah, qarhe goma kacce limaman da kun ka samo za a kawo su ko? To wa zai tsaya a matsayin waliyyin su Bariran?"
"Wai yaran ga sun ce ni suka so, ni Ko ban san wad-da ake ba, kunya suke son bani cikin mutane"
Dariya sosai Sultana ke yi, saboda yanda ta ga damuwa sosai a fuskar shi, to shi daurin auren wata ibada ce me wahala? An bayar na karba ne fa, tsokanar shi ta dinga yi, ya na daure fuska, dan shi da gaske yake bai san ya ake yi ba.
Da misalin bakwai daidai, matasan suka shiga gari, dan shigo da Limamai guda biyar da suka roqa arziki, za su daura musu aure, cikin rashin sanin ina za a je limaman suka amince, sai da aka dakko hanya suka ga ana nausawa daji hankulan su ya tashi.
Wasu masu raunin zuciyar har da kuka.
Ko da aka iso, suka ga waje masha Allah, an gyare shi, ya yi tass, kowa cikin kwalliya mazan da matan, ga abinci da abun sha, sai hankula su ya fara kwanciya, amma sun dasa wa zuqatan su ayar tambayar me ya kawo mutane cikin wannan surquqin daji?
Kamar yanda Lawwali ya ce, da misalin qarfe goma na safiya, aka daura auren mutum goma sha huɗu,a kan sadaki dubu talatin talatin.
Lawwali ana gama daura auren ya bar wajen, wani waje ya nufa da ba mutane ya zauna shi kadai, ya na hawaye, tunanin rayuwar shi tun daga farkon ta zuwa yanzu yake yi,daga gobe zai bar wannan dajin ya koma zama a cikin gari kamar kowanne mutum mai 'yan ci, sai yanzu ya gane su aka sa a kurkuku, ba su suka sa a kurkuku ba, tunani ya ke, shin tuban da ya yi ya karbu kuwa? Ko dai har yanzu Allah na hushi da shi? Abubuwan da ya aikata manya ne, masu girma ne,tunanin kalaman Mubarakan shi ya yi, a duk sanda take masa nasiha, ta na sanar da shi cewar,
'Yah Auwal ka tuba ka dena wanga harkar, ka samu aiki na halal ka yi, in ka tuba Allah mai yawan gafara ne, mai son bayin shi masu yawan tuba ne, kar ka yanke tsammani daga rahamar Allah'
Nan da nan ya ji wani qarfin imani da Allah na ratsa shi, ya na jin tabbas Indai tuba da yarda da Allah na sa Allah Ya yafewa bawan shi, to tabbas ya na saka rai Allah ya yafe masa.
Ya na nan zaune ya ji kan reshen da yake kai ya yi qasa,alamar an zauna, kafin ya duba gefen shi qamshin ta ya sanar da shi wace ce, kwantar da kan ta tayi a kafadar shi tare da zira hannun ta a nashi.
Za ta yi magana ya ce,
"Shiiii, kawai mu yi shiru,mu saurari iska, da karar busassun ganyayyaki, mu saurari kukan tsuntsaye da bugun zuciyar mu, ina so na zauna da ke a haka na wasu mintuna kahin ku tahi"
Kissing din hannun shi ta yi, ta sake qanqame hannun, ta kwanta a jikin shi sukai shiru.
Suna nan zaune Mubaraka ta same su, murmushi ta yi, da ta ji sun yi shiru, ba abinda suke fadi, manne da junan su, a hankali ta taka, duk da qarar ganye da ke qoqarin tona asirin zuwan ta, ta na isa daf da su ta sanya hannayen ta ta rungume su a tare ta baya, Lawwali lumshe ido ya yi, sannan ya kama hannun ta ta gefe ya sumbaci yatsun ta,
"Barakana ya akai kin ka san muna nan?"
"Duba ku muke kawai sai na samu nasarar ganin ku anan"
Murmushi suka yi, a tare dukan su,
"Yah Sultan na jiran ki ku tai"
Kamo su duka biyun Lawwali ya yi, ya rungume su a jikin shi da kyau, suka fara takawa a hankali,sannan ya yi kissing goshin kowaccen su, ya ce,
"Ina son ku, ina qaunar ku, ku ne rayuwa ta, ina hwata mu dawwama a tare cikin hwarin ciki, duk da na san hakan ba lallai shi kasance ba, dan kuwa a rayuwa ta kaff na koyi wani abu sabo, ka na naka shirin duniyar ne, Allah shi na maka shirin komawa gare shi,kai d'an Adam, ba zaka taba gama naka shiri ba, shi ko Allah ya gama nashi Shirin akan ka Dan Adam,lokaci ne kawai da ya yi zai kire ka gare shi, kuma dole ka amsa kira nai, ina muku nasiha ku had'a kan ku, ku so junan ku, kuma ku riqe gaskiya da amana, kar ku ha'inci kowa a rayuwa, kuma ku nemi sanin Allah kahin ku bauta masa, da ace nasan Allah yanda ya kamata, da duk abinda ya hwaru bai hwaru ba, amma sai na aje neman ilimin sanin Allah, na nemi duniya, ina roqon Allah ya bar mu tare har a aljanna"
"Ameeen Yah Auwal /Auwal"
Suka hada baki suka fada, Lawwali ne ya sake Sultana ya dan tura baki,
"Ni dai gaskiya Sultyna ban yarda ba, wai shin ke ko dan sweetheart dinnan ko dan honey din nan baki iya ce min?"
Haba me za su yi banda dariya, shi kuwa tafiyar shi ya fara, ya na ta fadan rashin jin dad'in shi akan kiran shi da Auwal da Sultana ke yi, ba dan sunan soyayyar nan.
Bin shi ta yi da gudu, dan ya kusan isa filin wajen nasu, ta kama hannun shi ta ce,
"Zan fada maka wani suna mai daaadii, amma ba yanzu ba, sai mun koma gidan mu"
"Ni dai yanzu nake so"
"Ah ahh ba yanzu ba"
"To ke Aunty Sultana ki sanar da shi mana, ba a fa jinkirta bayyana soyayya, sai wata ta kwace miki shi"
Kukan shagwaba Sultana ta saka, ta na nuna Mubaraka,
"Ka gan ta ko? Har ta hwara yi min fatan kishiya ko shekara ban yi ba"
Dariya kowa ya ke yi a wajen,Sultan kuwa hankalin shi ya tashi, dan maganar da Mubaraka ta yi sai ya ji kamar da shi take, duk da bai ga alama ba,abinda bai sani ba kuwa shi ne, Mubaraka da shi take, amma ta yi kamar bata san ma ya na wajen ba, ta na so ta san shin hasashen ta gaskiya ne? Ya na son ta ko dan ta na son shi ne ya sa take ganin kamar ya na son ta?
Sallama Lawwali da Taheer suka yi, Taheer na qoqarin barin motar Mubaraka a nan, Lawwali ya ce ya je da ita, ya dinga kai yara makaranta, godiya ya dinga yi sosai, sannan ya cire yar qaramar jakar shi daga motar da za akai shi tasha ya mayar a wadda suka zo da ita.
Sallama ya dinga yi da mutanen wajen d'aya bayan d'aya,sai da ya zo kan Sultan ya rage murya ya ce,
"Kar ka tsaya kallon ruwa kwado ya maka qahwa wallah"
Kada kai Sultan ya yi, cikin yaqe, dan gaba d'aya hankalin shi ya tashi, ga dai Mubaraka ba wata babba ba, amma kwarjinin ta ya cika masa ido matuqa........
*Washhh na gaji,amma ya kuke gani mutanen kirki, shin ya kamata Sultan ya bayyana soyayyar shi a dajin Oga, ko kuma ya bari sai sun shaqi iskar gari???*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 59:
Taheer ya tafi da rabin awa, Sultana ma su ka yi haramar tafiya, zaune suke a cikin mota ita da Sultan, sai wanda zai kai su, dan ba za su gane hanyar fita ba.
Ido Sultana ta zubawa Lawwali kamar ta ce masa su je tare, ba ta so su rabu ko na awa guda ne, amma ta san ba ta da wannan damar, in ba shi ya sakko da kan shi daga fushi da Gwamna ba, ba wanda ya isa ya ce ya sauka din, to wataqila sai Mubaraka .
Mubaraka ta gama yadda da cewar hasashen ta na Sultan na son ta qarya ne, hasashen farko na ita din bata kai wadda zai so ba shi ne gaskiya, sallama ta musu, zuciyar ta na matuqar quna, ta bar wajen, za ta koma dakin ta, dan a yanzu ba ta so ta bude baki ta yi magana, za ta iya fashewa da kukan da ya tokare mata wuya.
Muryar shi ta ji a bayan ta, cikin sanyi ya kira sunan ta,
"Mubaraka"
Bata gasgata kunnen ta ba, dan haka bata juya ba, a zaton ta gizo Muryar shi ke mata, saboda ta na tsananin so ya kira ta din dan ya furta mata kalmar so.
Tafe take shi kuwa binta yake, tun da ta juya ta fara tafiya ya kasa samun sukuni, kasa jurewa ya yi, ya ce a jira shi, Sultana da Lawwali na tsaye su na kallon shi ya bi ta da gudu.
Maimaita kiran sunan nata ya yi, Ita kuwa a yanzu ta tabbata ba gizo Muryar shi ke mata ba, dan haka tsayawa ta yi cak, bakin ta dauke da murmushi, da hope din son jin kalmar so daga bakin shi,idanun ta taf hawaye,
"Mubaraka, na kasa tafiya ba tare da na bayyana maki saqon da zuciya da gangar jiki na ke ta bani ba, Mubaraka ina son ki, I love u so much, tun randa na fara dora ido na akan ki a gidan mu, na ji wani baqon lamari ya darsu a zuciya ta game da ke, ban fahimci ko me ne shi ba, saboda ni baqo ne a fagen so, tun daga lokacin nan ba ranar da za ta zo ta wuce ban tuna ki ba, amma na bar wa zuciya ta, dawowar ki daga Kano, na ga kin qara girma, kin qara nutsuwa sai na ji abinda nake ji game da ke ya na nunkuwa a rai na, a yanzu na tabbatar da cewa, ke kadai nake so, ke ce macen da na ke jira, shi ya sa na kasa kula kowacce mace da sunan soyayya"
Wata ajiyar Zuciya suka sauke kusan a tare, Mubaraka ta ji dadi kwarai, wanda ba shi da misali,Sultan kuwa ji ya yi kamar an sauke masa wani babban nauyi da ya jima ya na dauke da shi akan shi.
Juyawa ta yi a hankali suka hada ido, cikin jin kunya ta sauke nata idon,sannan ta saki murmushi, shi ma ita yake kallo, cike da so da qauna,amma ya tabbata da ta na kallon shi ne tun dazun da ba zai iya furta kalaman da suka dinga fita daga bakin shi ba kamar ruwa.
A hankali ya ce,
"Baki amsa min ba, kin karbi soyayya ta, ko dai ban miki ba ne?"
Da sauri ta kalle shi, daga sama har qasa, sannan ta ce,
"Wacce mace zaka ce wa ka na so ta ce bata son ka Yah Sultan?"
"Macen da ba ta son na miji mai kama ta, ko mai irin halaye na mana Mubaraka"
"To ni dai kamannin ka, da halayen ka duk sun yi min, ba ka da makusa a iya sanin da na maka"
"Hakan na nufin ki na so na kenan?"
Daga kai ta yi, ta juya cikin sauri ta nufi hanyar dakin ta, kallo ya bi ta da shi, Lawwali ne ya dafa shi, ya ce,
"Tau baban soyayya, tunda ka qare aman zucciyar ka, yi hankuri ka dena kallon qauna ta haka nan, kar ta faɗi"
Dariya Sultan yayi,ya ce,
"To babban Yaya za a bani?"
"Shi kadai ne buri na tun farko ,kuma gashi kun had'a kan ku, ya na daga cikin sharadin da nake da burin mahaifin ku ya cika min, sai ga shi kun hada kan ku da kan ku, Allah shi sanya albarka cikin wanga lamari"
"Ameeen, ina godiya, waccan matar taka ta matsu na san taji me ke hwaruwa, bari mu tai, sai ka iso,"
"Tau ya yi, Allah shi kiyaye hanya"
"Ameen"
Mota Sultan ya shiga cike da farin ciki,ya bayyana wa Sultana me ya faru,ta yi murna kwarai da jin hakan.
Mubaraka kuwa leqawa ta dinga yi ta window ta na kallon Sultan, bayan tafiyar su Lawwali ya kira kowa da kowa, ya fidda makullan gidajen da yake da su a hannun shi, wanda ba shi da su kuma a wajen shi Sultan ya ce zai bashi in sun hadu a cikin gari.
Miqawa wasun su makullan yayi sannan ya sanar da su, ba zai yu kowa ya samu gida shi daya da matar shi ba, wani gidan sai dai mutum biyu, wani gidan ma sai dai mutum uku, daga baya duk wanda Allah ya horewa ya tashi.
Godiya suka dinga yi, tare da addu'a da fatan alkhairi,wasu daga cikin matan har ma da mazan kuka suka dinga yi, sabo kenan, turken wawa.
Suna nan su na jajanta rabuwar su da juna mazajen da suka maida Limaman da suka daura musu aure suka dawo, nan aka sanar da su me ya faru, sun yi godiya sosai, sannan suma sun jimanta rabuwa da junan su.
Lawwali dakin su ya je, ya aika a kira masa Mubaraka.
Ita ta taya shi hade kayan su shi da Sultana, ya bada umarnin kayan gadon a kai masa gidan su, can dakin Mubaraka za a saka.
Su na gyara dakin ne ya bijiro mata da maganar Sultan, kunya ce ta kama ta, shi kuma dariya ya yi, ya ce,
"Ohhh rayuwar duniya kenan, wai Mubaraka 'yar qararramar nan ce yanzu ta girma har ta kai ga saurayi, Allah to shi sanya alkhairi, "
"Kaiii Yah Auwal ni fa ba yanzu za ka yi min auren ba, ni dai ba na so na rabu da ku"
"Tabbb ai kuwa ya zama dole, ko ba aure ai akwai mutuwa ko? Ballantana mace dama ita ba mazauniyar gidan iyayen ta bace, komai daren dad'ewa za ta yi aure, sai wadda Allah ya nufa ba zata taba aure ba a rayuwar ta"
"Haka ne, Allah ya sa mu dace,...Yah Auwal yau za mu bar nan?"
"Ahh ahh, sai gobe ko jibi ma, sai an kai kayan ga gida, an gyara miki d'akin ki, sannan zan maishe ki da hannu na, na damqa musu amanar ki,na gaji da faɗa da kowa ni yanzu, ba na son tashin hankali da kowa, in kin koma ki sanya wa zuciyar ki hankurin zama da su, tunda kin dai san yanda halin su shike,"
"Haka ne Yah Auwal, in shaa Allahu, za ka same ni mai hakuri"
"Allah ya miki albarka Barakana, dama can ke mai hakuri ce,Allah shi qara maki hankuri akan duk abinda zai same ki"
Ameeen, Yah Auwal dina"
Haka sukai ta hirar su, su na tattara kayayyakin Sultana.
*************************
Wata mata ce a tsaye a jikin mota, a gaban wani babban super market ta na waya, kaya aka debo niqi niqi za a saka a bayan mota, ta danna key din hannun ta, ma'aikatan super market din suka zuba kayan, Laminu na can gefe ya na kallon ta, ya jima ya na bin matar tun safe da ya fito daga gida, har yamman nan.
Su na gamawa ta sallame su,ta shige motar ta, ta tada ta, ta hau titi, Laminu ma bin ta ya yi a baya, wata hanya ta dauka, wadda take shiru ba mutane sosai, shi ma binta ya yi, ya sha gaban ta, wani burki ta ci, tare da daga kai, a tsorace, ta kalle shi.
A tare suka fito daga motocin su, Laminu ne ya nufe ta da fuskar tausaya wa, da ban hakuri, ya shammace ta ya shaqa mata wani tsumma a hanci, dauke numfashin ta tayi, ta kama hannun shi ta juyar da shi ta murde shi, ya fadi qasa da guiwowin shi, su na haka wasu motocin jami'an tsaro suka qaraso, su ma tafe suke su na bin su a boye dama.
Sake numfashin ta tayi, ta shaqi iska, duk da haka sai da d'an wanda ta shaqa ya sa ta jiri.
Kamata wani daga jami'an tsaron ya yi, suka sa ta a mota, Laminu kuwa tuni an danna shi a motar 'yan sandan, nan suka dunguma baki dayan su, sai police station, ana zuwa dakin tuhuma aka miqa Laminu.
Binciken da jami'an tsaron suka yi akan mutuwar yaron da suka kama dan ya bada shaida akan wanda ya sa su sace Hajiyan Hansatu ya nuna musu cewa akwai sa hannun Laminu, dan haka suka had'a masa wannan tarkon da jami'ar tsaro mace, suka samu nasarar kama shi.
Laminu ya qi bayyana abokan ta'addancin shi da fari sai da ya ci na jaki, ya ga za su masa lahani a banza, shi ne kuwa ya bayyana sunan Isah, nan da nan kuwa aka kira Yaya Musa aka sanar da shi su na buqatar su a station din, dan jin yanda ta kaya.
Hajiya na ta murna ta shirya ta ce ma Yaya Musa su je,a hanya ta kira Hansatu ta sanar da ita an kira su a police station, an ce a samu wani mahimmin bayani, da ya kamata su sani.
Fatan alkhairi ta musu sannan ta ce in su Ameenatu sun taso daga makaranta za su zo.
Su na isa station din aka sanar da su mummunan labarin da ya sanya Hajiya kuka wiwi, da idanun ta, sai lallashin ta ake ta kasa denawa, ta dauki soyayya mai tsafta ta sanya a zuciyar ta wa Isah ashe mutumin banza ne.
Har wajen Laminu aka je da su, ta kalle shi ta ce,
"Allah wadai da samuwar irin ku cikin al'ummar Annabi Muhammad, Allah ya shirya masu hali irin naku, yanzu ka dube ka, yaro kyakkyawa, wa ze ce za ka aikata wannan mugun abu? Yanzu shi abokin naka kuna waya ne? Dan tun da ya tahi bai kire ni ba, wancan karon kuwa ya na kira na"
Cikin jin kunyar dattijuwar Laminu ya ce,
"Hajiya Isah bai dawo wa yanzu gaskiya, dan kuwa abokin harka ta ta saida koken wani