Showing 27001 words to 30000 words out of 155423 words

Chapter 10 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx

26 Oct 2025

420

riqe da jaka, da wayar ta a hannu.

Sultan ma cikin shiri, ya fito, dan su na son su je su ga inda Foundation din nata yake.

Hajiya Ikee an sha ado na alfarma ita da gwamna , sai qamshin turare masu tsada ke tashi,

Sultana ta yi mamakin ganin irin motar da aka ware domin kai ta da komowa da ita daga duk inda za ta, tsohuwar motar ta ta kalla, ta ga batai komai ba, last year aka sai mata, ta so yin magana, amma bata son ta bata moment din, ba komai, zata san ya da ta yi da waccan din.

Qamewa ta yi a lokacin da ya bude mata qofar shiga mazaunin da ya dace da mace mai aji da kima kamar ta,qamshin turaren shi ta shaqa cikin salo mai burgewa, ta kuwa burge Lawwali,idanu suka qurawa juna.

Wata iriyar faduwar gaba ce ta kama Sultana, abinda tunda take a rayuwar ta ta duniya bata taɓa ji ba game da kowa, idanun ta ta lumshe a daidai lokacin da ya furta,

"Ran ki shi dade, Bismillah"

Tsigar jikin ta ce ta kowanne kusurwa da kafa ta jikin ta ta miqe,

'Waye wannan?'

Shi ne abinda zuciyar ta ta furta a hankali, uniform din shi ta kalla,ta rasa gane a wanne bangaren tsaron yake, bayan ta zauna ne ya shiga mazaunin driver ya zauna shima ,motocin su Gwamna ne a gaba, sannan ta su, sai ta masu tsaron lafiyar su na take masu baya.

"Wane ne kai?"..........

*Wane ne shi ? In ji Sulty Babu*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 17:

"LAWWALI DAN TALO"

"What?"

"Eh suna na kenan, Ni ne sabon drivern ki, kuma guard din ki,"

"Ok, kuma sunan ka kenan? LAWWALI DAN TALO?"

Murmushi Lawwali ya yi, ya ce,

"Eh sunan kenan Ranki shi dade, ko akwai matsala na?"

"Ah ah , tambaya d'ai Ni kai, amma zan iya kiran ka da Auwal?"

Wani irin murmushi ya yi, mai sauti, wanda ya narkar masa da duk wata gaba ta jikin shi, nan da nan ya ji ran shi ya haskaka, Mubarakan shi na kiran shi Auwal, ga Sultana...na neman izinin kiran shi da Auwal, cikin sauri da alamar bada hakuri Sultana ta ce,

"I am so sorry pls, ba niyya ta na sauya maka suna ba, na ga kamar Auwal da Lawwali daya ne, shi ya sa, i can call u with whatever u want me to," (zan iya kiran ka, da duk abinda ka ke so na kira ka da shi)

Shi ma cikin hanzarin da zaquwa ya ce,

"Ran ki shi dade, ki kira Ni da Auwal, sunan da nih-hi so na wallah, qauna ta dai ka kira na da wanga suna ,shi nas-sa kin ka ji na yi shiru"

Sultana ta ji dadi da ba ta bata masa rai ba, dan haka sai ta daga kai kawai, ba ta son ta yi maganar da zata sa ta yi dana sani, ta rasa dalilin da ya sa ta ke ta surutu da mutumin da ta fara gani yau, har da qoqarin sauya masa suna.

Tafiyar awa daya da wasu 'yan mintuna ce ta kai su unguwar da Foundation din yake, motoci sun tsaitsaya, Gwamna da Hajiya Ikee da Sultan suna tsaye su na jiran ta fito, ta tsaya mamakin ganin motocin 'yan jarida da police su zagaye wajen, ga mutane mabuqata an tara su a wajen, dama Daddyn nata ya yi wannan shirin ne? Lallai da gaske yake yi, amma abinda bai mata dadi ba shi ne, yan jarida da ta ga suna tsaitsaye su na jiran fitar ta, ba haka ta ke son gudanar da qungiyar ba, ba ta buqatar sanar da duniya abinda take yi, ta na son yi ne domin Allah.

Kamar Sultan ya karanci tunanin ta, kurdawa ya yi cikin mutanen, ya ɗan taba kafadar Lawwali da ya bude mata mota ya na jiran ta fita, matsa wa ya yi, ya tsaya a gaban ta, cikin murya mai taushi ya ce,

"Sulty baby fito mana, kar ki damu da mutanen nan, ki fito kawai abin ki ki ga waje, sannan ki bawa wadannan mabuqatan abincin,da ke a can wajen, an yi haka ne dan wasu mabuqatan su ga wajen su zo gare ki neman taimako ke gane?"

Daga kai ta yi, amma a qasan ran ta, da an barta, shi mai neman taimako ai ba ya buya, a duk inda suke za ta nemo su.

Cike da jin kunya ta fita, dan bata saba da irin wannan abubuwan ba, shi kan shi Sultan bai ji dadin yanda mahaifin nasu ya tallata abun ba, da ya san za ai haka da bai zo ba, yanzu hotunan su da video din su zai ta zaga gari.

Yanka dan kyallen da aka Saka a bakin qofar shiga building din ta yi da almkashin da ya sha ado da kyalle, addu'a ta yi a zuciyar ta, ta neman sa'a, da nasara akan abinda ta sa gaba, tare da kariya daga dukkan sharri, sannan ta sanya qafata ta dama ta shiga, har cikin offices din guda bakwai, sai manyan store rooms guda hudu, wajen kamar dan irin buqatar ta aka riga aka gina shi,tabbas abinda take buri kenan n biyu a rayuwar ta bayan koyarwa, to ga dama ta samu.

Hawayen farin ciki ne ke son saukar mata, ta maqale su, Hajiya ta rungume, itama ta rungume ta, nan da na kuwa aka hau daukan su hotuna, ji ka ke kyas kyas kyas, Gwamna Halliru ne ya dafa kan ta, sannan ya rada mata wani abu, da hanzari ta daga kan ta, suka fita zuwa farfajiyar wajen, Lawwali na can daga nesa ya yi zooming din ta a wayar shi ya na mata video ,fuskar ta cike da annashuwa da annuri ta ke rabawa mabuqata abinci.

Buhun shinkafa ,qaramin buhun sugar, sai omo, sabulu, mangyada, man ja, indomie da gishiri, su ne abubuwan da sultana ta dauki awa biyu ta na rabawa.

Shiri na musamman aka dauka live ana yaɗawa a gidan talabijin n garin Zamfara ,nan da nan kuwa wasu mutanen suka ji qaunar sultana ta shige su, wasu kuma banda zagi da tsinuwa ba abinda suke mata, wasu zagin ta suke da mahaifan ta har su na fadin.

'Dubi kayan jikin su, shi kadai ya isa wani talakan ya ci da kan shi na wata uku, a haka suke son taimakawa'

Kowa da abinda ya ke fadi, domin shi ɗan Adam kayan Allah ne, ba mai iya masa, ba tare da sun san me ne ne a zuciyar ta ba, sun yanke mata hukunci.

Yanda Sultana bata gaji ba haka ma Lawwali bai gaji da ɗaukan ta ba, domin kuwa gwamna da Hajiya Ikee da suka ga abun ba na qare bane, tafiya suka yi, suka bar ta, Sultan ya so zama, Hajiya ta tisa shi a gaba suka koma gida tare.

Mutane kuwa kamar ingizo su ake, qara zuwa wasu suke, su na layi, Ita kuwa miqawa take, cike da farin ciki, da murmushi, da za a bude qirjin ta wataqila hasken dake ciki sai ya kashe na wani ido, saboda tsabar haske, da farin cikin da ke ciki, tabbas dukkan mai bayarwa domin Allah farin ciki ya tabbata a zuciyar shi .

Sun bar wajen da azahar, ba dan sultana  ta so ba, sai dan komai ya qare ne, har da kudin dake jakar ta sai da ta bayar.

Mutane na ta mata addu'a, wasu har ran su, wasu kuma yi kawai suke, a gefe su na zagin ta, da iyayen ta, su na fadin na munafurci ne, dan an kusa zabe ne, ya ke son ya yi amfani da ita, dan ya zarce.

Sultana na ta daga ma wata dattijuwa hannu ta fada motar ta, Lawwali ya mayar ya rufe.

"Ran ki shi dade ina muka nufa?"

"Gida"

Shi ne abinda ta fadi, ta kwantar da kanta a jikin motar, fuskar ta dauke da murmushin da ya kasa gushewa, ko gajiya bata ji a jikin ta, saboda jin dadi.

Lokaci zuwa lokaci Lawwali na satar kallon ta, a duk lokacin da zai dora ido akan fuskar ta, sai ya ji jinin jikin shi ya tsinke, ya qara gudu, ba qaramin kamu son ta ya masa ba.

Har suka isa gida bata daina fara'a ba.

Bude mata motar ya yi, ya tsaya dan ta fita ya rufe, bata san ya na yi ba, dan durqusa wa ya yi daidai kunnen ta kadan ya ce,

"Ran ki shi dade mun iso,"

A firgice ta kalle shi, fuskar shi ta kalla, ta ga ba wani alamar wasa, ko murmushi, sanar da ita kawai ya yi, ya kalli gefe, ajiyar zuciya ta sauke mai qarfi, ta masa godiya zata fita, har ta fara taku za ta shige ta dawo baya, ta kalle shi, shi ma ita ya kalla, idanun su cikin na juna ta ce,

"Sultana,...ka kira Ni da sultana"

Cikin hanzari ta bar wajen, bin ta ya yi da kallo, cikin wani irin yanayi, domin kuwa ta gama kashe masa duk wata laka ta jikin shi .

Jiki ba kwari ya rufe motar ya gyara parking , sannan ya kashe ya tafi gidan shi ,tun a hanya ya kira Mubaraka ya na bata labarin yanda komai ya kasance, ta na ta taya shi farin ciki, ashar din Lamishi ne ya katse mata wayar da take da Yah Auwal din ta.

Komawar su kenan, ta hangi tukunyar tuwon su na zubewa, rude ya tafasa ya malale a qasa.

"Dan uwar ki bani wayar nan, dama Lawwali ya d'ai sai wayar ga ne, amma na san watarana sai ke yi min ba daidai ba, garin uban ki ka samo shi ko muwa? Mu ka tahiya da zahi, da rani, da damina mu nema, mu kawo a ci ba Dan Talo ba, yanzu da kin ka bari ya tude ki na da abinda zaki dahwa muna? Bani...bani wayar nan, yau sai na liqa Maki kashin wahala (sai ta mata dukan wahala)"

Mubaraka miqa wayar ta yi, ta hau qoqarin guduwa, Mai Buruji na fadin,

"Du Allah dai ki kyale diyar ga Lamishi, dubi fa wanga aiki da tayyi Ita dai, ko ina qal qal qal, dan dai ta tussuwa talge? Ana iya yin wani, ballantana ma ga abinci mun zo da shi"

"To radio uwar zance, tunda niyyi niyyar liqa mata kashin wahala sai na buga in ji dadi, da ki ka hwadin abinci, nan nan wannan mijin naki me mutuwar zuciya mun ka wuce da abukkai nai waje, su na jiran mu kunce su canye"

Wata zabura ta yi da ta sa kajin gidan da Mubaraka, da Mai Buruji tsere, shigar Yabbuga kenan ta ga ana tsere, Mubaraka na ta ihu ta na bada hakuri, Mai Buruji ta maqale qofar dakin ta su na dariya ita da Kameelu, Yabbuga ce ta sheqe da dariya ta ce,

"Yau na ga ikon Allah ma daki kusa, mace ci nesa"

Ai ta na fadin haka zuciyar ta ta tuno mata Lawwali, wani irin tsoro ne ya kama ta, in ya shigo ya ga ana dukan Mubaraka, gaba dayan su sun shiga uku.

Cacima ta kai wa Lamishi ta na son kare Mubaraka daga dukan ta, cikin rashin sa'a Lamishi ta fadi qasa, qafa ta gurde, salati ta zabga, tare da rusa ihu, Dan Talo ne ya keta cikin gidan a guje ya na fadin,

"Mi an kai, wam-mutu? Shin mi na na yah-hwaru wanga salati har garka ana ji"

Ya na cikin maganar ya lura da Lamishi uwar gidan shi a qasa, ga Yabbuga da Mai Buruji na qoqarin daga ta, bayani Yabbuga ta masa daga qarshe ta ce,

"Walle Dan Talo da ta ba Mubaraka kashin wahala Lawwali ya yi ajalin mu har lahira gwanda ta qalle qawahu na baro qohwata na yi jinyar ta, ina nika iyawa da bala'in Lawwali ?"

Har daki suka kai Lamishi ta na ta rusa kuka, mai gyara aka kira ya je ya duba qafar, aka yi addu'o'i aka shafa man shanu da kade, mai gyara ya ce,

"Lamishi ki kula da qahwar ki turmushe na kin kai, kar ki zan ka aikin da zaki wahal da ita, nan da sati kina warkewa, Allah shi bi da lahiya"

(Turmushe, targade)

Lamishi baccin wahala ne ya dauke ta, Mubaraka kuwa ta san ta ja wa kan ta dukan da ita ma in ba ai sa'a ba sai ta kwanta, dan haka kuka ta fara, ta na addu'ar Allah ya mantar da ita me ya faru ya ba wa zuciyar ta hakuri.

Haka Lamishi ta kwana qafa ta yi haushi, ta kumbura,miqo min dakkon kuwa har Dan Talo ranar bata bar shi fita ko ina ba.

Washegari......

*Cassss ga washegari mutuniyar ku 😅*

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAEH

PAGE 18:

Washegari da sassafe bayan Mubaraka ta yi sallah, ta ɗora abin karya wa, ta share gidan tsaf, ta wanke bayi, zuwa bakwai da arba'in 7:40am, ta gama komai, wanka ta shiga a gurguje, da niyyar ta shirya ta gudu zuwa makaranta , ba tare da sanin kowa ba.

Sai da ta tabbata ta aje ma Lamishi komai na buqata, sannan ta tafi ta sanya uniform ,ta rataya jakar ta, ta na saka takalmin ta ta ji kiran Lamishi, cikin faduwar gaba, tare da saddaqar wa akan ba zata makaranta ba yau ma ta tafi amsa kiran Lamishin,

"Na'am Umma gani"

"Dan uban ki Dan Talo ina kk Shirin tafiya? Kin nakasa ni sannan ki tafi zuwa makaranta? Baki wallah zuwa ko ina, je ki shirya ki bi Mai Buruji,"

Wani irin kuka Mubaraka ta fashe da shi ,a rayuwar ta ta tsani duk abinda zai hada ta da gidan gwamna, kuma ta na hango alamun Lamishi na son ta maida aikin gidan kamar na gado, tunda suna yi itama se ta yi shi.

"Dan soyayyar ki da Annabin rahama Umma kar ki aika ni gidan can, ki barni na tai zuwa makaranta, na kwana biyu ban tai ba, Umma..."

"Ki na ruhwa min baki ko se na fashe shi? ....Mai Buruji...ke Mai Buruji...in ke qare ku tai da wannan lalatacciyar, ta maye gurbi na, kin san sultana ta fara zuwa aiki,"

Mai Buruji da aka kwalawa kira ce ta shiga dakin sannan ta ce,

"Na ko ga Sultana na son Mubaraka, ya kamata mu tafi lokaci na wucewa"

Cikin kuka Mubaraka ta shige gaba, ko uniform din ma qin cirewa ta yi, suka tafi.

Sun isa gidan tara da rabi ta yi, Lawwali na tsaye jikin motar Sultana ya na jiran ta, uniform din nan sun sha guga sai sheqi suke, ga qamshi na tashi a jikin shi, waya yake da No 3 ya na sanar da shi duk abubuwan da suke faruwa, tare da neman sani akan wasu abubuwan da ya kamata su yi, rashin shi a wajen ba shi ke nufin tsayawar ta'addancin su ba, ta waya ya ke sanar da su duk wasu dabaru da makirce makircen nakasa mutane bayin Allah.

Tsayawa ya yi da maganar da yake, a daidai lokacin da mata guda biyu masu matuqar mahimmanci a rayuwar shi suka tsaya a gaban idanun shi.

Sultana ce ta fito cikin simple shigar ta mai kyau, da ɗaukan hankalin mai kallo, a daya gefen Mubaraka ce saye da uniform idanun ta sun yi jawur saboda kuka.

Wayar shi ya soke a aljihu ya nufi Mubaraka, cikin tsananin damuwar da ta bayyana a fuskar shi, jijiyar gefen goshin shi ta fito, cikin Muryar shi ta asalin dan daba ya ce,

"Wane ne? Wane me qarar kwanan ne ya sa ki kuka?"

Hawaye ne suka gangaro mata, Mai Buruji ce ta sakada za ta wuce ya mata wani mugun kallo ta koma ta tsaya cak, tare da fadin,

"Lawwali ina ni ina tabin Mubaraka? Ai ba karen maguzawa na yaccijen ba, walle ba ni ta ba, Lamishi ce ta hana ta zuwa makaranta, tace nan za ta taho, ta yi wa Sultana aiki, jiya ta samu turmushe"(targad'e)

Rintse idon shi ya yi, cikin baqin ciki ya kama hannun Mubaraka, sannan ya kalli Mai Buruji ya ce,

"Ke ki yi wa Sultana aiki, makaranta take so, makaranta zata je, so kuke ta zauna ta zama jahila kamar ni?"

Sultana na tsaye ta na mamakin abubuwan da ta ji kuma ta gani, dama Lawwali dan su Lamishi ne? Sai yanzu da ake magana ta ga kamannin shi da Mubaraka, duk da ba sosai bane, amma akwai kama ta jini, har yanayi ya mata da Lamishin ma.

Waje ya nufa dan sama mata adaidaita sahu duk da ya san hakan zai wahala a irin wannan unguwar, amma ba zai damu da nisan inda zai je ba, dan farin cikin qanwar shi.

Sun dan yi nisa Sultana ta daga murya ta ce,

"Auwal..ku shiga Mota mu aje ta makaranta ,sai mu wuce daga can"

Hanyar mota Sultana ta nufa, su ma suka juya suka koma wajen motar, durqusawa Mubaraka ta yi, ta gaida sultana ta amsa cikin kulawa, bude ma Mubaraka Lawwali ya fara yi, sannan ya zaga zai budewa Sultana, ta daga masa hannu, ta bude da kan ta ta shige .

Sai da ya dauki hanyar makarantar su Mubaraka sanan fushin shi ya fara tafiya, ba zai bari a tauye ta ba, ba zai bari a lalata rayuwar ta a tagayyarar da rayuwar ta kamar yanda aka yi wa tashi ba.

Sultana na kula da yanayin shi, tare da jinjina irin qaunar da yake ma qanwar tashi, ya kuma yi matuqar burge ta, sai ta ga qimar shi da darajar shi a idon ta.

Cikin murya mai taushi Sultana ta ce,

"Ashe Auwal Dan uwan ki ne? ...Auwal ashe ita ce qanwar ka da ka ke fadin ita kadai ke kiran ka da Auwal?"

Wata ajiyar zuciya ya sauke mai qarfi, tare da sakin murmushin da ya bayyanar da irin son da yake ma qanwar tashi.

"Eh Ran ki shi dade, ita ta qauna ta da nika batu akai jiya"

"Allah Sarki, ashe ku din yaran Lamishi ne, na ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login