Showing 36001 words to 39000 words out of 155423 words

Chapter 13 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx

26 Oct 2025

435

kudi ba, ta yi alqawarin biya, suka bata account No,ta tura musu, sannan ta ce a sanar da yaran su ci gaba da zuwa makaranta, za ta dawo ta duba ko sun dawo,sallama ta musu ta tafi

Lawwali mamaki ya hana shi ma bin ta su tafi, anya Sultana jinin Halliru da Ikeelima ce kuwa?

Tsayawa ta yi a gaban shi ta ce,

"In ka qare kallon nawa mu je ko?"

Murmushin gefen baki ya mata, sannan ya ce,

"Ai ke din ce Ran ki shi dade, bayan kyau da ki ke da shi,har da kyauwun zucciya, "

Kunya ce ta kama ta, ta sunkuyar da idanun ta daga kallon shi, su na tafe su na dan yin hira, ta na jin dad'i in ya yabi kyawun ta, bata sani ba ko dan bata saba jin haka bane oho, kawai dai ta san ta na jin dad'i.

Har suka isa mota, yaron na riqe da hannun Sultana,

"To yanzu ina ne asibitin da Baban ka yake?"

"Babban asibiti ne, amma ban san waje ba, Inna Rabi ta tassan waje,Ga gidan ta can, wancan me buhun"

Bata gaji ba, sallama ta yi suka gaisa da matan gidan, gida ne na haya, mai dakuna da yawa ciki,

Har qofar Innar shi Rabi ya kai ta, suka gaisa, ta mata bayanin haduwar ta da yaron, sai a sannan ne ta tuna bata san sunan yaron ba, Innar shi ce ta sanar da ita sunan shi Huzaifah, sultana sanar da ita tayi ta na son ta je duba mahaifin yaron a asibiti, ya za a yi?

"Dama an jima kadan zanna kai musu abinci, mu tai na rake ki"

Nan da nan ta shiga ta saka hijabi, ta kulle qofar ta, suka fita, motar da ta gani su na nufa ce ta dan tsorata ta, Sultana ta ce,

"In ki na ganin akwai matsala ki min kwatance, zan bide su"

Kunya ce ta kama Rabi ganin Sultana ta gano ta.

Nan dai ta shiga suka tafi har asibitin, ta ga mahaifin Huzaifah, ta biya duk wani abu da ake buqata, bayan nashi ma har da na wasu mutum shida.

Alqawarin sake komawa ta yi, watarana asibitin dan taimakawa masu jinyar.

Sai da suka isa office din su, Sultana ta ke nazarin abubuwan da suka faru, tabbas masu neman taimako na asibiti, da irin unguwannin su Huzaifah, unguwannin talakawa, lallai yau ta samu wata babbar nasara a abinda ta ke da buri, alqawarin taimakawa mabuqata da ta dauka da yardar Allah za ta yi qoqarin cika shi duk da ta sani ba zata iya taimakon kaff mutanen garin Zamfara ba, amma zata qoqarta taimakawa wanda ya samu.

(Shin irin su Sultana ne kawai ya kamata su dinga taimakawa talakawa? Ke me kike aikatawa na taimakon wasu? Kai fa? Mu tambayi kammu, a rayuwa kar mutum ya ce sai ya ci ya tada kai sannan zai bawa wasu, da kadan din da muke da shi da shi za mu taimaki wasu, masu kidnapping har gida wasu masu qarfin halin suke zuwa su yi su tafi, masu asiri da maita har gida suke bi su cutar da mutane, me ya sa masu taimakawa mutane ba su bi gida gida? Ba riya bane dan ka yi abu wasu sun gan ka sanda ka ke yi, niyyar ka ita ce ladan ka, baka sani ba da loma daya da zaka bawa wani ya ci Allah ya maka rahama ,mu kyautata niyya yayin yin aikin alkhairi, in dai mugaye za su bi gida gida su kashe, su sace, su cinye,to kuwa kai mai aikin alkhairi kai ka fi cancanta da ka bi gida gida dan kyautatawa, zamanin magabata na gari har gida suke bin wanda za su taimakawa, me ya sa muka daina? Ladan ne Bama so?)

*Tambaya a gare mu baki daya*

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 21:

Tafiya ya ke a cikin duhun dajin da suka yi wa hanyar mota da kan su, saboda yawan shiga da fita, babu hasken komai, sai hasken futilun motar, qarar tsuntsaye, da wasu dabbobin kawai ke tashi, bai tsaya a ko ina ba sai ginin da yake maboyar su, cikin hanzari ya fita daga motar ya shiga wajen, tun daga bakin qofa har ciki masu gadi ne riqe da muggan makamai, gaisuwa kawai suke miqawa wajen Ogan su da suka yi kewar gani kwana biyu, ya so ko da murmushi ne ya musu, amma bacin ran da ya ke ji ya hana shi sake musu fuska, sun kuma fahimci hakan.

Qofar da za ta sada shi da inda aka ajiye Tsohon Gwamana No 5 ya bude masa, bayan ya gaida shi, daga masa kai ya yi kawai ya shige, a wata kujera da aka tanadar masa ya zauna, tare da harde qafar shi daya saman daya, kallo ya kafe mutanen dakin da shi, ya jima ya na kallon su,daga baya ya ce,

"Wab-bud'e shi?"

(Waye ya bude shi)

Shiru wajen ya dauka, cikin bacin rai Lawwali ya zari bindigar qugun No 3 ya harbi qafar Tsohon Gwamna, wata iriyar qara ya saki, tin qarfin shi, jijiyoyin kan shi da na wuyan shi sun fita rudu-rudu, ya na so ya riqe qafar amma ba hali, saboda an daure hannayen shi, cikin rawar murya ya ce,

"Wata yarinya ce, ......na mata ...alqawarin....million goma....in ta kunce ni.."

Wata dariya Lawwali ya saki sannan ya ce,

"Ku je ku kawo min su Sa'adatu, na ji a cikin su wacce mai qarar kwanan ce tab-bude shi"

No 2 ne ya fita cikin sauri, Lawwali kuwa fada ya fara yi,

"Meye amfanin ka a nan Inuwa( No1) kai ne fa babba yanzu, ka na mi da an ka bude shi, ko ka san hitar shi daga nan, daidai yake da tonuwar asirin mu! "

'Yan mata ne guda uku suka shiga kowaccen su sanye take da kaya kamar mai shirin fita yaqi,a cikin matan da ke wajen, su aka bawa horon fita da mazan in za a je cikin gari sato mutane ko wani fada ko wata hatsaniya dai.

Daya daga cikin su sai rawar jiki take, hankalin ta a tashe, lokaci zuwa lokaci ta na daga kai ta kalli No 1, da alama ta na neman agaji ne a wajen shi, shi kuwa kauda kai ya yi kamar bai taba ganin ta ba.

Su na qarasa shiga Lawwali ya yi ido hudu da budurwar da ke rawar jiki, ya ce,

"Yaseerah kin bata wayon ki, shin kin manta million nawa Excellency ya ce mu karba wajen mutenen ga? Kudi na hwa masu yawa, me ya sa zaki zagaya ki aikata haka?"

"Oga.... Dama...."

Cikin sauri No 1 ya kalle ta, ya ce,

"Oga butulci ne irin na mata, bai kamata a barta ba, ya kamata a hukunta ta saboda  ya zama izina ga na baya"

Kafin Lawwali ya bada umarni, ko ya yi magana, No 1 ya harbi Yaseerah, qarar bindigar da qarar ta kusan a tare suka karade wajen, gaba daya kallo kan No 1 ya koma, shi kuma ya fara wani murmushin jin dadi ya ce,

"Oga a min afuwa, irin haka ba za ta qara faruwa ba, zan sa ido sosai, ba a koma samun maci amana wajen ga na yi ma alqawari"

"Wa ya ba ka izinin yin halbi?"

"Oga a min afuwa, na zaci za ka yi hwarin ciki na kawar da maci amana, duk da ina son Yaseerah  ba zan taba bari ta ci amanar mu ba,"

Yanda ya yi maganar ya sa Lawwali zaton ko No 1 na jin haushin cin amanar da Yaseerah ta yi ne, shi ya sa ya harbe ta.

Umarni ya bada akan a ɗauke ta, a binne ta a daren, sannan ya miqe kamar zai tafi ya saita Tsohon Gwamna ya saki kunamar bindigar a qirjin shi, sannan ya fice, No 2 na biye da shi a baya,

"Oga ka sani fa dangin shi ba su aiko kudin nan ba, sun ce su na nan suna haɗawa ne, yanzu da aka kashe shi ya za a yi?"

"Ko sun kawo, ko basu kawo ba dama ba komawa wajen su zai yi ba,"

Motar shi ya fada, sannan ya wurga ma No2 bindigar shi, ya ja motar shi ya bar wajen.

Ko da ya isa gida wanka ya yi, ya nemi abinci ya ci, ya kwanta, nan da nan bacci mai dadi ya dauke shi.

***********************

Sultana ta kasa rintsawa, tunanin fuskar Lawwali ta hana ta sukuni, duk wani motsi da za ta yi ganin shi take, har a yanayin ma da bai taba zuwa mata ba, fuskar shi ta ke gani daf da ta ta in ta rufe ido, da ta bude se ta ga kamar da gaske shi ne a tsaye .

Miqewa ta yi ta shiga bayi, ta daura alwala, ta tada sallah, raka'a biyu ta yi, ta hau addu'a.

"Ya Allah ina roqon ka, dan kyawawan sunayen ka tsarkaka, ya rabbi, ka tausaya min a cikin halin da zuciya ta ke ciki, ban san me ne ne hakan ba, Allah ka bayyanar min da ma'anar abinda nake ji,ya Allah ka sanya ya zama alkhairi ne, Allah ka kawar da sharrin abinda ke cikin rai na"

Salatin Annabi ta yi, daga qarshe ta miqe, ta nade carpet din sallah ta kwanta, addu'ar bacci ta yi, ta shafe jikin ta, sannan ta kwanta da bangaren hannun ta na dama bakin ta dauke da tasbihi.

Lumshe ido ta fara yi, cikin ikon Allah kuwa bacci mai dadi ya dauke ta.

(Wannan shi ne amfanin addu'a, ka roki Allah mai duka, sannan ka yi imani, da yaqin cewa Allah ya ji, kuma ya amsa, lokaci kawai kk jira komai ya daidaita. Ba wai ka yi addu'a ba kuma ka ci gaba da damuwa, ya zama da kai da wanda bai yi addu'a ba baku da maraba)

***********************

Washe gari da safe mutanen Tsohon gwamna suka aika da 300m cash, suka aika Zuby ta karba, No 2 da   No 3 na can nesa sun yi ready ko da an zo da 'yan sanda, Zuby kuwa sanye take da hijabi da niqabi, ta yanda ba mai iya gane ko ita wace ce, ta na karba motar su No 2 mai baqin gilashi ta tsaya a gaban ta, ta fada suka wuce a guje suka tada qura.

Dan Tsohon Gwamna da qanin Tsohon gwamna na ganin an wuce ba a fiddo masu da shi ba suka bi motar da gudu su na ihun kiran su, motar tini ta bace kamar walqiya, yaron durqusawa ya yi ya fashe da matsanancin kuka, baffan shi ne ya dafa shi shima idanun shi na zubar da hawaye, kusan wata daya kenan rabon su da yayan na shi,suna cikin wanan mummunan halin wayar Qanin Gwamnan tai qara ya duba kiran.

Hannu na rawa ya dauka, cike da jimami da tsoro,

"Ka duba bayan dutsen nan za ku ga dan uwan ku"

Ai be gama jin me za a ce ba ya yar da wayar ya kwasa da gudu bayan dutsen, gawar tsohon gwamna ce ta masa maraba, salati ya saka da qarfi y fadi a wajen, da gudu dan gidan tsohon gwamna ya isa dan tare shi amma inaa, kafin ya isa ya fadi qasa, gawar mahaifin shi da ya gani cikin jini ta kidimar da shi, ihu kawai ya fara, ya na kiran a taimaka musu, ga shi wajen daji ne ba mutane, in ya diba a guje dama, sai ya koma hagu da gudu, da kyar y samu natsuwa ta zo masa ya yi inda suka aje motar su, domin sun hana su shiga da mota, a guje ya ke keta dajin har ya isa wajen motar su, kunnawa ya yi ya koma wajen gawar da baffan shi, ya ɗebe su ya mayar motar sai gida.

Ranar wannan ahali sun shiga cikin matsanancin tashin hankali, masu kuka nayi, masu suma na yi, masu addu'a na yi, masu ihu da kururuwa na yi, nan da nan kuwa labari ya baza garin Zamfara da kewaye ,mutane sun shiga tashin hankali da firgici, Indai manyan qasa ba su tsira ba su kuma gama gari fa?

Direct gidan Lawwali suka nufa da qatuwar jakar kudin, ya shirya tsaf dan tafiya gidan gwamna Halliru, sai qamshi ya ke bugawa, zuciyar shi fess kamar ba abinda ya aikata mummuna, fatan shi ya cimma burin shi na sace zuciyar baiwar Allah Sultana.

Bugun gate din gidan sukai ta yi, shi kuma ya na tsaki da ihun fadin

"Wane na ya ka son balle min gambu?"(wane ne ke son karyan qofa)

"Oga"

Shi ne kawai abinda suka fadi, ya gane su waye, ya na bude qofa suka miqa masa jakar suka koma motar su suka wuce, shi kuma a motar shi ya saka jakar ya bude gate ya shiga mota, bayan ya fidda motar ne ya rufe gidan ya nufi gidan Gwamna Halliru.

Ko da ya isa time din 7:12am ne, ya sanar da gwamna zuwan shi, ya na isa ya tarar da gate bude, motar shi ya shigar ya aje ta a parking lot, ya bude ya dauki jakar, ya zaga ta baya, dakin da suke zama su tattauna mugayen abubuwan su, shi da gwamna, da sauran miyagun mutanen da suke harkokin banza tare.

Sultana ta yi mamakin ganin Lawwali da sassafe haka kuma ya zaga ta baya inda mahaifin su ne kaɗai ke zuwa da baqin shi,gashi dauke da qatuwar jaka, to ko gidan aka ce ya dawo da zama ne? Wataqila ya dawo gidan da zama ne.

Murmushi ta yi mai kyau, dan jin dadin hakan, tare da fatan Allah ya sa hasashen ta ya zama gaskiya.

Ta na mamakin yanda yanzu ta koyi leqe ta window, hakan ba halin ta bane, a baya ba ta tuna sanda ta taɓa bude labule ta kalli qasa ba, amma a yanzu kullum sai ta kalli qasa, musamman kafin ta fita, da kuma in sun dawo.

Fitowa ta yi daga wanka, daure da towel, ta shirya, cikin kwalliyar da ta fi ta jiya daukan hankali, ta sauka qasa, a gurguje ta ci abinci, sannan ta fita, tsaye ta gan shi jikin mota ya na waya, ya na ganin ta ya kashe wayar ya bude mata mota, idanun shi akan ta, bakin shi dauke da murmushi, Itan ma haka, tsayawa ya yi kafin ya rufe qofar su na kallon juna

"Shin ki na sane ki ke kwalliyar ga dan ki gusar da hankali na ga jiki na ko kuma ki na sane ki ke satar zuciya ta ba tare da jin tsoron zan rasa ta ba gaba daya?"

Cike da jin kunya Sultana ta kauda kai ta na jizar lips din ta na qasa, bai tsaya jiran amsar ta ba dama, Ita kuwa a zaton ta ya na nan tsaye ya na jiran ta amsa masa, sai kawai ji ta yi mota ta fara tafiya,kallon shi ta yi ta madubi, su na hada ido kuwa ya kashe mata ido daya, tare da d'aga gira daya, kunya ce ta kama ta sosai sai da ta rufe fuskar ta da tafukan hannun ta.

Sallama suka yi da mai gadi, mai gadi na gaishe da sultana ba ta ji ba ma, har suka hau kan babban titi ba ta dawo normal ba, tabbas ta gama yarda a yau ta kamu da matsanancin son Lawwali, ita da take kwalliya dan ta ja ra'ayin shi, shi ya ja ra'ayin ta da kallon shi da kalaman shi.

Har suka isa ba su sake magana da juna ba, sai da ya je bude mata mota zata fita ne ya ce,

"Ran sarauniyar kyawawan matan Africa gaba daya shi dade, ina neman izinin ki zanna, gida wajen qauna ta,"

"Dan Allah Auwal ka dena sani jin kunyar ka,...and zaka iya zuwa, in ka je ka ce ina gaishe ta, ina gaishe da....(shiru ta yi, dan ta na jin nauyin ce wa Lamishi kuma a gaban shi, daga baya ta ce,) ina gaishe da Umman Mubaraka"

Wata iriyar siririyar dariya mai sauti ya saki, tare da duqar da kan shi, hakan ba karamin kyau ya yi wa sultana ba, zuciyar ta ta ji ta tafi wajen shi gaba daya, kafe shi ta yi da idanu, cikin yin qasa da murya yace,

"Ko ran Ran ta ya dade za ta iya sammin Lambar wayar ta, saboda in ta na buqata ta se na dawo?"

Miqa masa hannu ta yi, ta na nufin ya bata wayar shi, hannun shi ya miqa, sauran kadan hannayen su su hadu,da sauri ta janye hannun ta cike da shagwaba ta ce,

"Wayar ka fa za ka bani"

Shi kuma 'yar dariyar da ke tafiya da ita ya yi, ya ce,

"Ohh na zaci gaisawa za mu yi"

Hannu ya sa ya zari wayar a aljihun shi, ta bi qirjin shi da kallo, yanda rigar ta zauna a jikin shi, kamar a jiki aka dinka ya mata kyau, yawo ya yi da wayar a gaban idanun ta ya na murmushi, tare da lumshe idanun shi.

"A gaskiya ran ki shi dade in ki na yi min irin wanga kallo, sai ke gano muni na da ni ke ta boyewa kar ki gani"

Sultana ta gama kamuwa da matsananciyar kunya ,kasa amsar wayar ta yi, sai shi ya zare tata a hannun ta ya sanya lambobin shi ya danna kira, ta ta No ya yi saving, sannan ya miqa mata wayar ta, ya kulle motar ya raka ta har office, sannan ya tafi.

Bai tsaya a ko ina ba sai bakin titi, tun kan ya isa ya yi waya ya sanar da su inda za su dauke shi, ya ɗan jira su kadan kafin suka isa, mota ya shiga suka ja Sai gidan Gwamna Halliru......

*Dan Allah ku dan min hakuri da wannan, ban sani ba ko za a samu ci gaba nan kusa na yi baqi na yi busy sosai, ko wanan ma da kyar na samu nayi*

A GARIN MU

WRITTEN BY HAERMEEBRAERH

PAGE 22:

A mota ya bar su, zai shiga No 1 ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login