Showing 42001 words to 45000 words out of 155423 words
Chapter 15 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
su gina masallatai, noma, samar da ruwan sha da sauran ababen more rayuwa, tallafa wa gajiyayyu da marasa lafiya, sune suka zama ayyukan da ya sa a gaba, ana yi ana dauka a hoto da video ana yad'awa jama'a.
A wannan lokaci ne na qaratowar zabe,lamura ka yi ma wasu daga cikin mutanen qasa wahala da tsanani, tare da qunci , wasu kuma lokacin ne suke cikin walwala, da nutsuwa da yalwa, harkokin samun su ta bude, rayuwar su ta yalwatu da dukkan abinda suke burin samu.
Gidan gwamnati Hajiya Ikee ta koma da zama, mutane na zuwa, wannan ya shiga wancan ya fita, watarana har fita take da muqarraban ta unguwanni dan kai masu taimako, mutanen mu kuwa dake a hannu suke, ana buqatar abincin da wasu kayan masarufin duk sun manta da wahalhalun da suka sha abaya, da rashin kula su da gwamnatin bata yi ba a baya, ta na da manyan mata a unguwanni daban daban, da ke rabon kayyaki da abinci, tare da kudi wa mata a gidaje, domin a sai quri'un su, ko me ya sa da ba a tallafi matan ba sai zabe ya zo a bi su da dubu ko dari biyar da atampa oho.
Motoci ne masu numfashi, da qoshi ke yawo a saman hanyar qauyen da duk titin ya farfashe, mutanen qaramin kauyen kuwa, sun yi babban shirin tarbar Gwamna da muqarraban shi.
Motocin na tsayawa, securities suka zagaye motar Gwamna, 'yan jarida na tsaye na jiran fitowar shi su fara daukan rahoto, manyan motocin abinci da suka zo da su ne suka qaraso, qatti na ta sauke buhunan abincin, mutanen qauyen natsaye su na kallon su, sai da suka bari Gwamna Halliru ya fito an fara daukan shi,tare da fadin rahotanni na son rai da zuciya, sukai ta fitowa da gorori, da bulalai, tare da duwatsu, dukan motocin suka fara, tare da jifan su da duwatsu su na fadin
"Ba ma yi ! Ba ma yi !"
A gurguje Gwamna ya fara qoqarin komawa motar shi, cikin rashin sa'a wani matashi ya maka masa gora a goshi, babu bata lokaci kuwa daya daga cikin masu tsaron gwamna ya zari bindiga ya harbe matashin, qarar bindigar ne ya sanya mutane rudewa, wajen ya kacame da hatsaniya, wasu na qoqarin guduwa, wasu na ganin ko za su rasa ran su sai sun cimma abinda suka yi niyya.
A guje motocin gwamnatin ke guduwa, wasu daga matasan kuwa sun hana a dauki manyan motocin abincin, sun kakkare ko ina.
Haka wasu daga muqarraban gwamna suka gudu da qafafun su.
Sultana ba ta jima da komawa gida ba, ta idar da Sallah ta kwanta, ta na hutawa ta ji qarar motoci, dan tsaki ta ja ta daki pillow ta toshe kunnen ta, tare da yin goho a gadon, ta na dukan gadon, cikin dan kukan shagwaba ta dauke pillown daga kan ta ta miqe, idanun ta lumshe take tafiya, kafin ta isa motocin sun shiga gidan, labule ta daga ta leqa qasa, ta na hamma, tare da murza idanun ta, ba shiri ta wattsake daga baccin da ya taru a idon ta.
Mahaifin ta ta gani cikin jini, farar babbar rigar shi ta gaba tayi faca faca da jini, da sauri ta bar jikin window ta zari rigar ta ta saka, ta manta gaba daya kanta ba dankwali ta fita parlour ,securities na waje, gwamna ya shigo, ciki, cike da bacin rai, wani daga securities din ne ya shiga ya sanar da zuwan doctor, Dr zama ya yi a kujera ya na fidda kayan aiki, Gwamna Halliru na tsaye ya na bada mummunan Umarnin da ya sanya Sultana kusan suma a tsaye, da wa mahaifin ta yake waya haka? Wanne azzalumin ke taya mahaifin ta aikata mummunan aiki irin wannan?
Zama ya yi ya na fitar da wani irin hucin bacin rai da baqin ciki, Dr ya fara gyara masa ciwon shi, ko zafi bai nuna alamar ya na ji ba, tsabar yanda ran shi ya kai qololuwa wajen ɓaci, tsoro ne ya kama Sultana, har ta kasa qarasawa wajen shi .
Hawaye ne kawai ke zuba a idanun ta, bakin ta na rawa, zuciyar ta na bugawa da qarfi, hannu ta sa ta shafi kan ta, ta juya sama da gudu, wayar ta ta dauka, ta na kallon ta, shin Hajiya za ta kira? Ko Sultan? Ko kuma......
Lawwali ne ya fado mata a rai, lokuta da dama in mutum na cikin damuwa, ba wanda ke fado masa a rai sai masoyin shi, wannan dalilin ne ya sanya Sultana tunawa da mahaifiyar ta, da d'an uwan ta, qarshe ta dire akan lawwali, (hakan na nufin Sultana ta kamu da son Lawwali?) cikin hanzari ta kira shi, ta jima ta na ringing bai daga ba har ta katse, sake kira ta yi, ya na fara ringing ya dauka, a gaggauce ya ke magana, daga baya ya tsaya cak, saboda jin kukan Sultana da ya yi.
"Ran ki shi dade lahiya? Me ya hwaru ki ke kuka?"
Ta kasa magana sai kuka take, da kyar ya samu ta nutsu.
"Daddy ne...Daddy ne na ji ya na waya....wai za a je wani qauye a tashi garin,....ya na so a kashe kowa...har mata da qananan yara...ba ya so a bar kowa ya rayu, saboda sun zubar masa da jini...ya bada umarnin a sa wa garin wuta..Auwal ya zan yi? I need your help pls"
Kuka ne sosai ya kwace mata, fita ta ɗan yi waje ta tsaya jikin bene, ta na hango Gwamna Halliru ya na bada umarni ga 'yan jarida kar su kuskura su saka abinda ya faru a zuwan su qauyen a kowacce kafa ta yada labarai, har kuma abinda zai faru washegari.
Sultana sanar da Lawwali tayi abinda taji ya na faruwa, Lawwali kuwa ya jima da dauke wuta, ya na cikin tsaka mai wuya, shin wa zai bi? Gwamna ko Sultana? Ta na neman taimako a wajen shi,ba tare da sanin shi ne wanda aka bawa Umarni ya je da yaran shi su tashi qauyen ba.
Amma zai jira ya ji wanne irin taimako take nema a wajen shi.
"Ran ki shi dade sanar da ni irin taimakon da ki ke nema a waje na"
Cikin kuka sultana ta ce,
"Ban sani ba...Ni ma ban sani ba...just stay with me on the phone, har sai Sultan ya dawo, ina jin tsoro, ba na son kasancewa ni kadai, ina jin tsoro"
Takure take a jikin matattakalar benen, a gaban idon ta mahaifin nata ke ta abubuwan da ba ta taɓa zaton zai aikata ba, Lawwali na sauraron kukan ta, har cikin qoqon zuciyar shi, yaran shi na tsaitsaye su na jiran umarnin shi.
Jin zuciyar shi yake kamar wuta, kiran Gwamna ne ke shiga wayar shi, cikin sanyin murya ya ce,
"Ran ki shi dade, ina da wani kira mai mahimmanci na shigowa, ki yi min hankuri na daga, zan sake kiran ki"
Shiru ta yi, bata amsa ba, banda kuka ba binda take yi, kashewa ya yi ya dauki wayar Gwamna, cikin tsawa da fada yake magana.
"Shin kun tahi ko kuwa?"
"Mun shirya yanzu za mu tai"
"Ku kashe kowa, kar ku bar kowa da rai,"
"Tau ranka shi dade"
Ya na gama magana da gwamna ya sake kiran Sultana, bata dauka ba, ta na zaune a wajen ta na kuka, komai ya tsaya mata cak, tsoro da mamaki duk sun kau daga zuciyar ta, gata nan ne dai kawai.
Jin bata dauka bane, ya sa Lawwali bawa yaran shi umarnin tafiya, nan da nan kuwa suka fita, suka shisshiga motocin su, dauke da muggan makamai, da bindigogi, da bama bamai,basu shiga kauyen ba sai da suka je dajin su suka tsara komai, sanan suka qara mayaqa, cikin dare suka shiga garin, mutanen garin sun sakankance, su na ta murna, da jin dadin samun kayan abincin da suka yi, tare da korar azzalumin gwamnan nasu.
Kwatsam suka fara jin harbi ko ta ina, da tashin qananan bama bamai.
Gari fa ya rude, da tashin hankali da iface iface, duk wanda ya san Lawwali a zahiri ba zai gane shi ba a yanzu, gaba daya wannan mutumin ba shi da digon imani, ba tausayi a zuciyar shi.
Kashe mutane kawai yake kamar ya na kisan kiyashi.
Basu suka bar garin nan ba sai da suka maida shi kamar toka, daidaikun mutane ne suka samu guduwa, suka bazama daji, da wasu qauyukan da ke kusa da su.
Qarfe sha biyu na dare, suka bar qauyen, direct gida Lawwali ya nufa a motar shi,ya na zuwa ya yi wanka ya ci abinci, ya kwanta, juyi ya dinga yi, wanda ya rasa dalilin yin shi,a hankali tunanin Sultana ya fara mamaye zuciyar shi mai kama da dutse, soyayyar ta da soyayyar mubaraka ne kadai ke raya zuciyar shi, banda su ba shi da wani abu da ke narkar da zuciyar shi.
Wayar shi ya dauka ya dinga kallon hotunan su, ya na sakewa, ya rasa yanayin da yake ciki, ko kuma abinda yake ji a zuciyar shi .
Bai san sanda ya danna kiran Sultana ba, ya kara a kunnen shi, cikin shaqaqqiyar Muryar da ta ci kuka ta gode Allah ta dauka.
"Ran ki shi dade, baki bacci ba?"
Kallon qur'anin da ta gama karantawa ta yi, ta lumshe idon ta hawaye suka zuba, ta ce,
"Eh ban yi bacci ba, kai me ya hana ka bacci?"
Shiru ya yi, tare da gyara kwanciyar shi, ya lumshe idanun shi ,sanan ya ce,
"Na kasa bacci, ban san me ke damu na ba, Sultana ina da wani babban al'amari a tattare da ni, wanda ni ka jin matuqar tsoro akai"
"Me ne ne wannan al'amarin? Ko zan iya sanin shi?"
Da sauri ya kawar da maganar ta hanyar tashi zaune ya ce,
"Ran ki shi dade, ya kamata ki kwanta ki bacci, akwai gajiya a tattare da ke sosai "
"Humm Auwal kenan, kai a ganin ka zan iya rintsawa? Bayan zuciya ta da ƙwaƙwalwa ta su na hango min abinda ban gani ba? Zuciya ta na hango min kukan yara ƙanana, da mata,da mazaje, zuciya ta na hasko min yanda jini ke malala na dan Adam ba dabba ba,ba tare da haqqin su ba, anya mahaifi na mutum ne kuwa? Anya wadan da suke aikata kashe kashe da zubar da jinin al'umma mutane ne kuwa?anya akwai zuciya a qirazan su kuwa?anya suna tunawa da cewa kamar yanda suke daukan rayukan bayin Allah suma watarana ran su za a dauka? Anya su na sane da cewa akwai wuta akwai aljannah? Anya su na tunawa da cewa su na da mahalicci wato Allah, mai yawan rahama, da kuma yawan azaba? Anyaa????"
*Makaranta Sultana na neman amsa*
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 24:
Wata iriyar zufa ce ke karyo mishi, wadda ta sanya shi tunanin anya ya kunna AC ma kuwa, kallon saitin AC din ya yi, ya ga a kunne take, tashi ya yi ya kunna fan, sannan ya koma ya zauna, ya na sauraron yanda Sultana ke karanta masa abubuwan da ko Mubaraka mai yi masa nasiha da wa'azi kullum, bata taɓa fada masa wadannan kalaman masu matuqar taba zuciya ba.
Cikin tsagaita wa da kuka sultana ta ce,
"Allah shi ne mafi sani game da mutanen nan da Daddy ke aiki da su,su ke lahanta mutane, suke kassara su, suke illata su,in masu shiryuwa ne, Allah ya shirye su, in ba masu shiryuwa bane Allah ya musu abinda suke wa bayin shi, "
Shiru Lawwali ya yi, dan bai isa amsa wa da ameen ba, tunda ya san mene ne suke wa yaran wasu, jijiyoyin kan shi ne suka tashi rudu rudu, qit ya kashe wayar,gaba daya ya kashe ta.
Yawo ya fara yi a dakin, me zai sa Sultana ta musu wannan addu'ar , in wani abu ya samu ahalin shi fa? (Na wani bnza na ka dukiya kenan).
Ranar Lawwali bai samu bacci ba sai gaf da suba, bacci kuwa ya sha me kyau, bai tashi ba sai qarfe goma na safiyar ranar.
Sultana kuwa dama ta yi waya NGO akan ba zata je ba, bata jin dad'i, su kula da wajen, da duk wanda ya je neman taimako, abinda ya fi qarfin su su sanar da ita.
Lawwali ma sai da ya tashi ya ga message din ta, ji yayi hankalin shi ya tashi, me ke damun ta? Dole ne ya je ya duba ta.
Wanka ya dauka, ya sanya wasu riga da wando,na shadda sun yi mishi kyau sosai, ba hula, wayar shi da yan kudi, sai makullin mota ya dauka, ya fita, kafin ya je wajen ta, sai da ya shiga gari, ya siyo mata kayan kwalama na Bature, duk ya ma rikice ya rasa me ya kamata ya siya, haka dai ya siyi banza ya siyi wofi ya ja mota sai gidan Gwamna.
Ko da ya isa ya tarar da securities da yawa, sanin ko shi waye a wajen gwamna ne ya bashi damar shiga ba tare da wani bincike ba, gwamna Halliru da Hajiya Ikee ba su gida, Sultan ne da Sultana sai masu aiki, ranar Mai buruji da Lamishi duk sun samu zuwa, har a sannan qafar Lamishi bata qarasa warkewa ba, dan haka Sultan ya hana ta yin komai, sai godiya take, ya ce ta ci gaba da turo Mubaraka, ba se ta zo ba, tunda ba lafiya.
Sultana na zaune kusa da Sultan, ya yi tambayar duniya ta qi sanar da shi abinda ke ran ta, saboda ba ta son ya tsani Daddyn su kamar yanda ta tsani ganin shi,ba ta so ta b'ata kowa a rayuwar ta, ta fi so ta fadi alkhairin mutum, in ba ya zama dole se ta fad'i sharrin mutum ba, wannan ba yanda zata yi,balle mahaifin su, bata fatan Sultan ya sani, zuciyar shi zata karye sosai, saboda yanda yake son mahaifin nasu sosai.
Hawaye ta share sannan ta yi murmushin yaqe ta ce,
"Yah Sultan ba abinda ke damu na, ciwon kai ne kawai, in ina da matsala ka sani kai ne mutum na farko a duniya da ke fara ji"
"Haka ne, amma Ni ma kin san na fi kowa sanin ki, ba ciwon kai bane kadai damuwar ki, akwai wani abu da ya ke faruwa, wanda ki ke boye min"
Bude baki ta yi dan yin magana wayar ta ta dau qara, ko da ta ga sunan Auwal, sai ta samu kan ta da jin dad'in hakan,domin a daran jiyan ta yi ta sake gwada kiran shi bai shiga ba, har da safen nan ma ta kira bai shiga ba.
"Assalamu alaikum,"
"Wa'alaikumussalam, Ran ki shi dade ya ki ke? Ya jiki? Ina hwata dai kin samu lahiya ko? Na taho na duba jikin ki, tunda kin ce baki da lahiya"
Miqewa ta yi da sauri ,ta isa gaban window'n da ake hango farfajiyar gidan, ganin shi tayi tsaye da ledar shopping a hannun shi, murmushi ne mai kyau ya kwace mata, ta jingina da ginin wajen, sannan ta ce,
"Lallai ka iya zuwa dubiya, haka ake zuwa dubiya an sha gayu? What if mara lafiyar ta rikice fa?"
Waige waige ya fara ya ga ta ina zai hange ta, bai gani ba, cikin sa'a ta sake leqa shi suka hada ido, dariyar shi da ke rikita mata kwanya ya saki, sannan ya shafa kan shi, tare da lumshe ido ya sauke su fess akan ta,
Sultan ne ya isa gaban ta, ya harde hannayen shi a qirjin shi, ya na kallon ta da mamaki, dazu fa kuka take.
Su na hada ido, ta bar wajen za ta hau sama, ya riqe hannun ta, a hankali ta ce,
" ka shiga parlour na baqi gani nan zuwa"
Kashewa Lawwali ya yi, ya shiga gidan ya shige har inda aka ce masa, ya zauna zaman jiran ta.
Ita kuwa qoqarin gudu take Sultan ya riqe ta,
"Ina zaki je baki min bayanin sauyawar ki ba a lokaci qanqani? Na fi qarfin awa biyu ina tare da ke, kina ta hawaye, kin kasa fadan komai, yanzu daga amsa waya sai ki fara dariya?"
Shiru Sultana ta yi, dan ko me zai faru ba zata sanar da shi mummunan sirrin mahaifin su ba, gwanda ta tonawa kan ta asiri, akan ta fada masa gaskiya.
"Yah Sultan, i am in love, ....i am in love with my driver, amma ban sanar da shi ba, shi ma kuma da alama ya na so na, bai sanar da ni bane kawai, Yah Sultan ina cikin damuwa ne saboda na san ba wanda zai goyan baya a gidan nan,labarin soyayya ta ina hango qarewar shi tun kafin ya fara"
Bilhaqqi yanzu kuma kukan hasashen da ta yi take yi,
"Sultana tabbas zabin ki ba mai karɓuwa bane a wajen su Hajiya da Daddy, amma a waje na karbabbe ne, in dai ki na son shi, ya na son ki, zan tsaya a gefen ki, har sai kun cimma burin ku"
Qanqame hannun shi ta yi cikin nata, tare da fadin,
"Na gode,"
Shafa kan ta ya yi, sanan ya ce,
"Wannan shi ne abinda zan miki, duba da yanda iyayen mu suka maida ni mara mamora a cikin al'umma, ba na aikin komai, ana kulle na kamar mace, ba na baki wata gudunmawa a matsayi na na yayan ki"
"Yah Sultan kar ka ce haka, soyayyar ka a matsayin dan uwana ta wadatar da ni komai,"
Cikin ran ta kuwa cewa ta yi,
'Dole iyayen mu su yi kullen mu, domin sun san me suke aikatawa, su na tsoron kar wani abu ya same mu,'
Sai da ta ɗan gyara fuskar ta ta sanya sutura mai kyau da ta rufe jikin ta sosai, sannan ta isa wajen Lawwali, sassanyan qamshin ta ne ya fara yi masa maraba, kafin kyakkyawar fuskar ta ta masa sallama.
Sake baki ya yi ya na kallon ta, anya da gaske bata da lafiya? Shi be ga alama ba,
"Kallon nan na ka na neman ya yi min yawa wallah"