Showing 63001 words to 66000 words out of 155423 words

Chapter 22 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx

26 Oct 2025

430

/>
Da sauri ya bar wajen, ya nufi motar shi, dan ba ya son ya ga me No 1 ze aikata a gaba, gashi lokacin tashin Sultana na ta gabatowa, wataqila ma ya na isa time ya yi, a dayan bangaren ma ba zai so rusa plan din shi ba na wajen Sultanan, dole ya na ji ya na gani ya hakura.

Ya na tafe ya na sauke wani irin numfashi,kamar wani mayunwacin zaki, duk wanda ya san wane ne asalin Lawwali, a wannan lokacin is not a good idea ka bata masa rai, dan yanzu zai ma lahira sabon baqo da mutum.

Gudun da yake zubawa har ya wuce misali, wataqila da a qasashen turawa ne da tuni an tsaida shi .

Birkin da ya ci ne ya janyo hankalin mutanen da ke wajen, cikin su har da sultana, da ke saka hannu a wata takardar da za a fitar da buhunan shinkafa domin mabuqata.

Ta na kallon idon shi ta ji wani irin yanayi da bata taba ji ba game da Lawwali, wato tsoro,sai dai ta bangaren Lawwali, su na hada ido sai ya ji bacin rai da baqin cikin shi ya ɗan ragu, har murmushi ya ɗan yi mata.

Ganin murmushin shi ne ya sanya ta sakin nata, ta kawar da tsoron da ke ran ta, amma tabbas fuskar da Lawwali ya sanya a baya, bata fatan sake ganin irin ta har gaban abada.

Kafin ta zo ya bude mata qofar,ta na shiga ya mayar ya rufe da qarfi,sai da ta ɗan razana, shi din ma da qarfi ya shiga ,ya kuma rufe da qarfin, cikin sauri ya tada motar dan ya na buqatar leqa sansanin su, ya ɗan huce haushin shin shi a can.

Ba tare da ta yi wani tunani ba ta miqa hannun ta zuwa kafadar shi, a hankali ta shafa saman rigar tashi kafin ta matsa kafadar tashi sannu a hankali, wata iriyar ajiyar zuciya lawwali ya sauke mai qarfin gaske, tare da gangarawa gefen hanyar ya tsaida motar, kifa kan shi ya yi a jikin sitiyarin motar, ya na sauke numfashi, quncin da ke cikin zuciyar shi ba shi da misali, ya na ji ya na gani qanwar shi take a wulaqance, kafin ya gano ta ya zaci ba tashin hankalin da ya fi rasa ta da ya yi, amma yanzu ji yake wannan tashin hankalin ya fi na rasa ta da ya yi, shi ba qarfin shi aka fi ba, ba komai ba, amma ya ke azabtuwa.

Bai san sanda ta zauna a gefen shi ba, sai jin hannun ta ya yi a saman qeyar shi ta na shafawa a hankali, idanun ta na zubar da hawayen tausayin masoyin nata, ta san duk damuwar shi ba ta wuce ta rashin Mubaraka ba.

A hankali ya daga kai suka kalli juna, gaban ta ne ya yi wani mummunan faduwa, Lawwali kamar ba shi ba, fuskar shi ta yi jawur, idanun shi ma haka, ga wani dagawa da komawa da qirjin shi ke yi, cikin sauri ta zame hannun ta, ta sunkuyar da kan ta qasa, ba za ta iya jurar kallon shi ba.

Muryar shi na rawa, ya ce,

"Sultana....qauna ta a duk inda take ta na buqata ta, ina ji a jiki na, ta na cikin matsala,"

Tsigar jikin ta gaba daya ta miqe, sakamakon kiran sunan ta da ya yi, bata taɓa zaton bayan iyayen ta da suka saka mata suna sultana ba, akwai wanda ya iya fadin sunan ya yi daɗin saurara kamar Lawwali ba, ga wani matsanancin tausayin shi da ke addabar zuciyar ta, cike da raunin murya ta ce,

"Allah na tare da ita ko ba ka nan, zai kula da lamarin ta, baka cutar da d'an kowa ba, kai ma ba za a cutar da taka qaunar ba"

Da sauri ya kalle ta, sannan ya ce,

"In kuma na cutar da wani fa? Sai a cutar da tawa qaunar ki ka nuhi?"

Yanayin yanda ya yi maganar ya sa ta jin kalaman ta ba su yi dadin saurara ba a kunnuwan shi, cikin sauri ta ce,

"Nooo ba haka ni ka nuhi ba, mu je gida mu sake wa Daddy magana, Ni kai na na damu da rashin Mubaraka,"

Cikin kauda maganar, dan gujewa bacin ran da ta hango kwance a fuskar shi, ita abun ma ya fara bata tsoro, ba ta taba ganin wanan Auwal din ba.

Ba tare da ta koma baya ba suka tafi, har suka isa ba wanda ya sake magana, ta so kunna ko da rediyo ne dan kawar da shirun amma gaba daya bata ga fuska ba, ita da motar ta, ta najin tsoron driver,zuciyar ta ce ta mata tuni da cewar,

'Shi din ba wai drivern ki bane kadai,ya riqi babban matsayi a zuciyar ki Sultana, matsayin da babu wani mahaluki da ya taba riqe irin shi, a kaff tarihin rayuwar ki, shi ne namiji na farko da ki ka fara yi wa so irin na soyayya, kuma shi ne namijin da ki ke ganin za ki qarasa rayuwar ki da shi, har abada'

Ji ta yi motar ta daina tafiya, ko da ta dawo daga duniyar tunanin da ta shiga sai ta gan su a cikin gidan su, baya ta leqa dan ta tabbata ma'aikatan gidan na ta gaishe ta ma bata kula ba.

A tsaye yake a jikin qofar ya bude mata, ita kawai yake jira ta fita ya kama gaban shi, da yau har ita din ma haushi take bashi,in ba ganin shi ya yi a daji ya na ragargazar mutane ba ba zai ji dadi ba.

"Ran ki shi dade, mun iso"

Cikin yanayi na jin kunyar ya kama ta ta na kallon shi, ta fita, ya rufe, baya ta bude ta dau jakar ta, da wayar ta, duk ya na tsaye,

"Dan Allah ka kwantar da hankalin ka, duk da na san abu ne mai wahala, amma ka jaraba karanta hasbunallahu, wa ni'imal wakeel, inshaa Allahu komai zai yi daidai, za a gan ta,"

Daga mata kai kawai ya yi da fake murmushi, Wanda ta san fake ne, amma ita sai ta mayar masa da kyakkyawa kuma mai kwantar da hankalin,amma ba irin hankalin Lawwali ba, dan kuwa ya dai ji dad'in ganin murmushin nata, amma bai rage masa rad'ad'in da yake ji ba a ran shi.

Ya na qoqarin tafiya Mai Buruji na qoqarin fita itama, su na hada ido ta gigice ta yi baya a guje, ta koma bangaren masu aiki,ba ita ta bar gidan ba sai ana kiran la'asar.

************************

Gidan ya yi wa Lamishi shiru yau, ba wanda ya je mata jajen ma da ake dan yi, ga qawar ta tun jiya da ta keta da gudu, har yau bata dawo ba, ga Mai Buruji bata koma ba, shi kuma wannan lalataccen mijin nasu dan wahala sai zarya da sintiri yake kamar dan agaji, da aikin agajin ma yake da al'umma ta amfana da shi.

Shigowar shi ta biyar kenan, cikin dan had'e fuska ya ce,

"Ke ga wannan lalatacciyar bata dawo ba ko? Tunda kin ka bar zuwa ta samu wajen tafiya yawon shashancin ta, sai ta ga dama ta ka dawowa gidan ga"

"Kar ka kuskura ka zage ta, yo akwai lalatacce da ya wuce ka? Baka nema ba, ba ka bada jallin nema ba, amma ka ishi mutane da dumin banza, kai ba ka damu da jimawar da tayyi ba, amma ka damu da rashin dawowar ta dan ka ci abinci kai da lalatattun abukkan ka, Ni ka ga tahiya ta ma gidan 'Yabbuga, in ta zaka kace ina can"

Yaqe baki ya fara ya na mata kirari na uwar gida, ita kuma ta tsuke fuska gam, ta yafa mayafi ta bar gidan.

Zaune ta tarar da 'Yabbuga a saman turmi, ta kasa kunnuwan ta gidan Isah ta ji me suke ciki, Lamishi na ganin haka, ta kwashe da dariya ta rafka gud'a, sannan ta ce,

"Ahayyyeeee, Allah gani, in ji gurmuwa (gurguwa) gulma ajali, in ba ai ba a mutu,ki na nan zaune ke d'ai ga gida ba ki hitowa a sha hira? Ke tsaya kasa kunne shigifar (katanga) maqota,"

Hannu 'Yabbuga ta sa a baki ta na ma Lamishi nuni da ta yi shiru, jan hannun ta tayi, suka bar wajen, suka zauna a bakin qofar parlourn 'Yabbugan, Lamishi ce ta kalli 'Yabbuga hannu da qafa, ta ga bata ga komai ba, cikin rashin fahimta ta ce,

"Shin ina lallen da nis-sa miki jiya?"

Tsaki 'Yabbuga ta ja mai qarfi, sannan ta tura dankwalin ta gaban goshi ta na sosa cinyayyar qeyar ta,

"Ina ko kigganai? Lalle dai ba lalle na ba, miyak-kad'i ta wallah (kuka)"

(Lalle dai ba lalle bane kuka ce wallah)

"Miiii? Wanne irin miyak-kad'i?"

Fari 'Yabbuga ta yi, kamar wata 'yar daudu ta ce,

"Miyak-kadi dai da kis-sani, ita mun ka kwaba, mun ka daura, niyyi awa da wanni zaune ina sharar bacci wahala, nic-ci gudun wahalar banza akan lallen ga na banza, dan da ban kai wannan lokacin gidan ku ba da ban hadu da qanin shedan din can ba, ya hirgita ni, duba, duba, nace duba nan ki gani"

Wani shafcecen yanka ne a sharabar ta, kamar ta ji shi da icce ko langa langa,

"Ke ga yanda na here qahwa, ban ci lalle ba na ci gudu, dake jikin tallaka na ko jin yankan ban ba sai dazu da zan wanka da rana nijji zahi, nicce too Allah gani gare ka missamen? Ina dibawa nigga qahwa ta here,"

Lamishi na son yin dariya ba hali, dan yanzu sai su raba hali, ga dariya ta mata yawa,

"Yi dariyar ki, yanzu wannan dan rainin hankalin ya hita shi na yi min dariya,"

Ai kuwa kafin 'Yabbuga ta rufe baki,Lamishi ta fara keta dariya, tunano irin zaman da 'Yabbugan ta ci akan lallen da irin gudun da ta sha kawai take.

Tun 'yabbuga na bata rai, har ita ma ta sake sukai ta dariya.

Daga baya suka jajantawa juna rashin mubaraka, wanda har a wannan lokacin abun ba wai ya shiga jikin Lamishi bane, kamar yanda kowacce uwar kirki ya kamata ya shige ta ba.

************************

Lawwali na isa sansanin nasu, ya kira No 2 da No 3 suka tara masa mutanen da suka kama last 2days ,aka fitar masa da su tsakiyar daji,  No 4 na ganin haka ya san tabbas Lawwali ya ga wani abun da bai ganshe shi ba, ya na son zuwa ya bada hakuri ya na tsoro, kar laifin ya koma kan shi,dan ya tabbatar wadannan mutane goma da aka fidda ba daya da zai dawo a raye...........

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 32:

Kukan bayin Allah kawai ke tashi a dokar daji, ba gida gaba ba gida baya, daga su sai Lawwali da yaran shi, kowannen su dauke da bindigogi, an gama loda wa Lawwali alburushi a bindigar shi, ya na tsaye cikin qunar rai da baqin ciki, ya na karba ya saki alburushi a kan mutum na farko da ke a gaban shi, haka ma ya yi wa na biyun shi, ya saita bindigar akan mutum na uku da ke gaban shi, kalaman Sultana suka bijiro a ƙwaƙwalwa da zuciyar shi,

'Allah na tare da ita, ko ba ka nan, zai kula da lamarin ta, baka cutar da d'an kowa ba, kai ma ba za a cutar da taka qaunar ba'

Hannun shi na rawa, kamar zai ajiye bindigar,amma dake zuciyar shi ta riga ta bushe, bai samu sauqin baqin cikin da yake ciki ba sai da ya kashe mutum biyar a cikin su, ya sa aka maida saura, a wajen aka haqa rami, ba sallah, ba addu'a aka binne bayin Allah.

Ko da suka koma sansanin su No 1 ya hango cikin 'yanmatan da ke wajen, ya na hira da su,ya na wani karairaya kamar tsohuwar karuwa, wani malolon baqin ciki ne ya taso masa, kujera ya bada umarni a saka masa a filin wajen, kamar qiftawar ido kuwa aka ajiye masa kujerar shi, ya zauna cikin isa da mulkin da yake ji kamar an bashi mulkin qasar baki d'aya ya kalli mutanen dake wajen,wanda gaba d'aya a qarqashin shi suke, matasa ne da magidanta, wanda adadin su ba zai wuce  sha uku zuwa sha biyar ba, mata da maza,dattijai da matasa, sai yara wanda shekarun su na haihuwa  ba zasu wuce sha uku zuwa sha biyar ba, akan yaudari mutane da su, dan a yi garkuwa da mutanen.

Kiran su ya yi gaba d'aya, nan da nan kuwa suka isa kowa ya riqe bindigar shi, suka tsaitsaya kamar wasu horarrun sojoji,hakan ya yi matuqar birge shi, ya kuma sanya ya ji ya na da ikon da a yanzu in ya ce a kama masa No 1 a harbe wata kafa a jikin shi ba zata yi saura ba, ba tare da alburushi ya huda ta ba, amma bari ya yi playing game d'in su na cin amana shima.

Murmushi kawai ya musu, saboda duk a tsorace suke, sun san labarin batan qanwar shi, sun san shi ne dalilin fushin shi, wasun su har fata suke ya gan ta da wuri saboda Ogan su ya dawo kamar da, mai fara'a, walwala, da basu nishadi.

"Mun jima ba mu yi wasanni ba a wajen nan, yau ina so a yi wasan dambe,amma banda cuta, kowa ya yi da wanda yake bi,misali, kai...(ya kira wani matashi da ba zai wuce ashirin da biyar ba, sannan ya kira wani da yake sa'an shi) kai ma zo nan, kunga shekarun ku kusan daya ne, kuma muqamin ku ma  anan wajen, kusan d'aya ne, to ina so a yi dambe, sai d'aya ya gaji ya ce ya isa haka, amma in ku na ganin ku ragwaye ne, duk zan halbe ku na sake sabon zubi"

Kafin Lawwali ya gama rufe baki har sun fara kasa kan su, kowa da wanda zai kara da shi.

"Habaa ba kowa ne zai yi ba, in an ka ce kowa ne zai yi tau su waye 'yan kallo?"

Mutum hudu kawai ya zaba, wato No 2 da No 3,sai No 4 da No 5.

"Wadanga, su ne manya wajen ga ko?"

Cikin d'aga murya da ihu suka amsa, da

"Ehhhh su na Oga"

"Tauuu su na zasu nishadantar da mu yau,...kaii Yakubu, taho kai na alqalin wasa, kai zaka bada damar farawa, sharadi daya ne, banda halbi, amma komi ana iyawa, a yi dambe har sai d'aya ya buga qasa so uku, sannan za a qare"

Habaa mana waje fa ya dau harami, sai ihu da murna ake, su kan su wanda za su yi damben ba alamar bacin rai a tattare da su, nan da nan kuwa suka shirya, No 2 da No 3 suka shiga tsakiyar fili, Lawwali na zaune ya na taune cikin bakin shi, idan plan din shi ya tafi daidai, daga yau No 1 ze fara cin qaniyar shi a hannun shi.

Mai kula da wasa tini ya harba bindiga bayan ya sanar da wasan ba wani doka, ana iya amfani da komai dan kare kai, amma banda bindiga.

Kokawa kuwa da naushi, tare da harbi da qafa kamar 'ya'yan jakkai tuni ya kaure a tsakanin su,sun jima suna fafatawa kafin No 3 ya buga qasa ya na haki da fidda numfashi da kyau,

Ihu da murna tare da tafi ne ya kaure a wajen, No 2 ne ya je gaban Lawwali ya duqa ,shi kuma ya daki kafadar shi cikin jinjina, da karrama wa, ihu wajen ya sake dauka, a fuskar No 3 babu alamar jin haushi ko hassada dan an samu nasara akan shi, tabbas har cikin ran su wasa suka dauki abun.

No 4 da No 5 ne suka shiga fili, aka fad'a masu sharadin wasa, tare da harba bindiga, nan da nan suma suka kaure, ana yin nasu ne, wani  matashin da Lawwali ya radawa abinda yake so ya yi, ya fara bi d'aya bayan d'aya ya na fada wa mutane magana a kunnuwan su.

Cikin rabin awa No 4 da No 5 sun jigata, ba wanda ya samu nasara akan dan uwan shi,amma fa kowanne a cikin su ya daku, banda jini ba abinda ke fita a jikin su su dikan.

Cikin hargowa wajen ya dauki sunan, Oga da No 1, cike da mummunan tashin hankali No 1 ya fara kada kai, ya na ja da baya, kamar wani tsumma haka wani gabjeje a wajen ya wurga shi tsakiyar fili, No 1 ji ya yi kamar zai fitsari a wando tsabar tsoro, kowa ya san Lawwali a wajen, ba shi da na biyu a qarfi, ba shi da Mahadi a qarfi a wajen, to akan me za su hada su? Indai ba so suke a kashe shi ba.

Wani irin fushi ne ya bayyana a saman fuskar Lawwali na irin quncin da ke cikin ran shi, cikin qanqanin lokaci ya kawar da fushin ya fara nuna kawai a bar wasan, kar ya cutar da No 1, dariyar yaqe No 1 ya fara, tare da fadin,

"Oga ya ce a bar wasa haka nan, sai wani lokaci"

A gaggauce Lawwali ya kalli matashin da ya yi wa rad'a, ai kuwa matashin ya yi tsagal ya ce,

"Bamu jiya ba mu dai, mu na so mu ga hwadan manya, zai fi dadin kallo,"

"Muna so, mu ma mu na so, mu na son ganin fadan manya!!!!"

Shi ne abinda mutanen wajen ke ta ihu su na maimaita wa, har suka jawo hankalin mutanen da ke rufe a wajen, ta window da duk wata kafa da za su samu damar kallon me ke faruwa suke leqe, ai kuwa cikin daga hannu d'aya wajen ya yi tsit.

Lawwali ne ya isa gaban No 1 ya ce,

"Kar ka damu aboki na, kawai ka dage, wataqila ka samu nasara akai na, ka ga ba ni da wani qarhi Mubaraka ita ta qarhi na ka sani, gashi ban gane ta ba, za ka iya nasara akai na cikin sauqi"

Wata iriyar zufar saman hanci da saman lebe No 1 ke yi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login