Showing 153001 words to 155423 words out of 155423 words
Chapter 52 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
tai ban koma ba da nayi aure ne ma Asshibi ta tai, dan mu na gaisawa ta waya da ita, jehi jehi, bata sanar da ni wannan babban rashi da an kai ba, Allah shi gahwarta mai"
Mubaraka na son Hansatu, saboda mace ce mai kirki, ta ji dadin yanda ta nuna kulawar ta, kallon mutumin dake mata ta'aziyya ta yi, sannan ta ce,
"Aunty Hansatu wanga na Yayan nawa?"
"Shi na Mubaraka, shi na wanda iyaye na sun ka so na aura tun kahin Isah, Allah be nufa ba sai yanzu"
"Allah Sarki, matar mutum kabarin shi,Allah shi sanya alkhairi aunty,"
"Ameeen na gode, Ahmad mun ka kawo ganin likitan yara ba shi da lahiya, bari mu tai, sai na shigo shiyyar"
"Allah shi bi da lahiya sai kin zo din, na gode"
Shafa kan Ahmad Mubaraka ta yi, ta ce ya gaida su Ameenatu, dan ya san ta sosai, Islamiyya daya suke zuwa, ita a babban aji take, murmushi ya yi, har da daga mata hannu ya tafi, Sultana ta shiga ganin likita, Sultan ya zo ya tsaya a gefen mubaraka, da ke kallon inda su Hansatu suka bi dauke da murmushi, dan dukan kafadar ta ya yi kadan, da tashi, sannan ya ce,
"Da ace za a kawon ke yau, kema nan da wata tara ko goma za ki haifa mana baby, nan da shekara bakwai ya zama kamar wancan yaron,"
Kunya ce ta bi ta lullube Mubaraka, ta rasa ina za ta sanya kan ta, su na nan tsaye suka ga an gunguro da gado, Sultana na kai, da sauri Mubaraka da Sultan suka yi kan ta, gani suka yi ta na ta yatsina fuska, kamar za ta yi kuka.
"Me ya hwaru?"
"Daga duba ta naquda ta taso, zamu kai ta dakin haihuwa, ku je ku kawo kayan haihuwa"
Cikin sauri kuwa Mubaraka ta duqa gaban Sultana ta ce,
"Sannu Aunty Sultana, Allah shi sauke ki lahiya, Allah shi kawo miki haihuwar da sauqi, bari mu tai mu doko kayan,"
Shafa kan Sultana, Sultan ya yi, Sannan suka tafi.
A dakin haihuwa kuwa banda kiran sunan Allah ba abinda sultana ke yi, irin azabar da take ji ba ta da misali.
Cikin ikon Allah kafin Mubaraka su je su dawo, ta samu haihuwar yaron ta namiji, sambalele, dan lukuti kamar OO.
Duk ya cika dakin da kuka, Midwife din da ta karbi haihuwar sai tsokanar shi take da kiran shi ragon maza, a ido gashi kamar namiji, amma sai kuka, Sultana kuwa kuka kawai take, zuciyar ta ta shiga wani irin yanayi wanda ba shi da misali,tun Nurses na ganin kamar kukan Murna ne, har abun ya basu mamaki,
"Boyar Allah kukan ga ya yi yawa, ke da zaki godewa Allah, sai ki zanka kuka haka?"
Mubaraka ce ta leqa kan ta dakin,riqe da kayan baby, kamar yanda aka buqata, Sultana na ganin ta, ta sake bare baki da kuka, Mubaraka ta fahimci kukan me take, kawai sai ta ji hawaye ya na gudu a nata kuncin, qarasawa ta yi, ta duqa ta rungume Sultanan, ita ma rungume ta tayi da duk wani qarfin da ya rage mata, kuka sukai ta yi, kamar ranar ne Lawwali ya tafi ya bar su.
Da kyar Nurses din wajen suka raba su, cikin kuka Mubaraka ta ce,
"Ku yi hankuri dole mu yi kuka, mahaifin yaron ya rasu,tunawa da shi ne ya sa mu kokawa, da ace shi na nan da na tabbatar sai ya maku kyautar da za ku san kun karbi haihuwar matar so, na tabbatar da ya na nan da kun tabbata kun jima baku ga uban da ke son matar shi da d'an shi ba kamar shi,da za ku yi mamakin shin waya hi so a tsakanin mu ukun nan, matar shi? Dan shi? Ko qauna tai? Zuciyar shi cike take da soyayya, wadda in ya na wa mutum,sai mutum shi zaci shi kadai ya ke so,wannan dalili ne ya sa muke kuka, mun rasa wani bangare na jikin mu, kuma a yau mun samu wani bangare na jikin mu"
Wata midwife a wajen ce ta share hawayen ta ta ce,
"Allah Sarki, ku yi hankuri, Allah ba shi barin wani dan wani shi ji dad'i, Allah shi raya,"
"Ameeen"
An gyara jariri, da mahaifiyar shi, Sultan ya yi wa yaro huduba da suna Muhammad Auwal,Sultana kuwa qin bari ta yi a aje yaro nesa da ita, in ba Mubaraka ce ta dauke shi ba, kowa ya dauke shi za ta yi ta magana a miqa shi, ba kunya ba tsoron surutun mutane.
Kwanan su biyu a asibitin aka sallame ta, ta koma gidan Hajiya Ikee, nan fa Sultana ta ga gata, Mubaraka ba tare da wani tunani ba ta tattaro kayan su, ta taho gidan Hajiya Ikee, Sultan ya ji dadin hakan matuqa.
Ranar suna mutanen Tudun faila sun samu halartar sunan, an yi suna ba laifi, ba yabo ba fallasa.
Bayan Suna Lamishi ta tattara sauran kayan Mubaraka ta aiko mata da su, tare da yi mata aiken Fatan alkhairi daga wajen Jameelu, yana ta mata dariya yake bata saqon, ya ce,
"Mama 'Yabbuga ta ce dama haka ki ka so, ki koma gidan mijin ki, tunda ba su kai ki ba to gashi ke samu dama"
"Kaiiiii ya Salam, matar ga ta iya sheri wallah,"
Sultan ne da ya shiga dakin da Mubarakan ke da zama a gidan ya ce,
"Ai Jameelu na ke hwada maka harda roqo na ta yi wai na ce su Mama 'Yabbuga su maishe ta dakin ta"
"Innalillahi Yah Sultan yaushe mun kai haka da kai"
"Rannannn, ki tuna mana, rannan"
Dariya Jameelu ya dinga yi, ya na jin dadin ganin farin ciki a fuskar yayar tashi ,sallama ya musu ya koma gida, Sultan kuwa cewa ya yi,
"Tooo amarya ta, tunda yanzu kowa ya nutsu, mu ma ya kamata mu nutse cikin dausayin soyayyar mu ko? Yaushe za ki koma dakin ki? Nan dai dakin baqi na"
"Ba rana, ba dai ka yi min sheri ba?"
Dan tura baki ta yi ita a dole ranta ya ɓaci, ba tare da ta ji takun shi ba, ta ji an sumbaci lips din ta da ta tura gaba, da sauri ta kalle shi, dariya ya mata, sannan ya mata gwalo zai gudu, take masa baya ta yi, suka fita su na gudu su na dariya, dakin shi ya fada, ya na sane ya bar qofar a bude, ta na shiga ya mayar ya rufe, ya maida ta jikin qofar ya mata rumfa, kallon ta ya ke daga saman idanun shi har zuciyar shi, ya na haddace duk wani tudu da kwari na fuskar ta,Itan ma da kallo ta bi shi, cike da wani irin yanayi da bata taba shiga kalar shi ba a rayuwar ta, murya can qasa Sultan yace,
"Gudun mi ki ke yi haka?"
"Ramawa zan yi"
"Me za ki rama?"
Shiru ta yi ta maida kan ta qasa, ta na wasa da rigar ta da ta kama ta gefen dama
"Gani tau rama"
"Na yahe maka"
"Ni kuma ban yahe ba sai kin rama"
"Ni dai nace na yahe"
"Ni kuma na ce ban yahe ba"
"Allah na yahe maka, ka ga ka bari na tai aunty Sultana na can qasa ita da Hajiya su na jira na na tai na goyi Yaya"
"Ni kuma ga ni mijin ki ina so ki rama abinda na miki, ko ki bari na rama miki, sai ki koma"
Shiru ta yi ta na kallon shi, cike da so da qaunar shi,
"In rama miki ko?"
Daga kai ta yi, a hankali,tare da runtse idanun ta, babu bata lokaci kuwa Sultan ya dora lips din shi saman nata, tun Mubaraka bata mayar masa, har sai data maida hankalin ta, da nutsuwar ta wajen rama abinda yake mata.
A yammacin ranar Sultan ya samu angwancewa da amaryar shi Mubaraka.
Hajiya da Sultana tunda suka ji shiru ba su bi sahun su ba, sai bayan da magariba ta yi, ba su ga Mubaraka ba, kawai sai suka yi sallar su, suka ci abincin su, suka bar musu nasu,ita da Sultan.
Sultan ya so ya kira Sultana ta taimaka wa Mubaraka, amma ta qi sam, ta ce za ta iya kula da kan ta kar ya manta ba na farko bane ba, wanda shi ji ya yi kamar ba a taba mata wata hanya ba shi ya fara sanin ta 'ya mace (aikin d'inkin bature da cin kaji da kayan marmari kenan) , dan haka da taimakon shi ta gyara kan ta, ta gasa jikin ta da kyau da ruwan dumi, dan akwai komai da take buqata a dakin Sultan din, kayan ta ne kawai ke can dakin da baqin.
Sai da ya bari qafa ta dauke, kowa ya haye sama, ya shiga dakin baqin ya tattaro komai na Mubaraka ya mayar dakin shi.
Kafin ta gama shiryawa ya tafi debo musu abinci, ya na dumama abincin a microwave ya na murmushi, ya na nan tsaye Sultana ta fito diban ruwan zafi a flask da take sha.
Ganin shi ta yi ya nata zabga murmushi dariya ta yi, ta ce,
"Ango ka sha qamshi, ni da na ji qamshin jikin ka ma na zaci Mubaraka ce, ashe kai ne"
"Sultana baki da kunya ko?"
Dariya suka kwashe da ita sannan suka tafa,
"Bari kawai, Allah ya ma yarinyar can albarka, amma ni ina mamaki, an ce an taba mata fyade, amma ban ji wata alama da ta nuna hakan ba, ko dai dan ban san kan abun bane?"
"Wataqila dan baka san kan abun bane, and akwai matan da suke da baiwa, kamar wadda ka ke fada yanzu ba zata taba komawa da budurcin ta ba, amma fa ba za a ji ta a bude ba sosai, sannan ka san matan garin ga dai da gyara ko? Na tabbata an gyara ta sosai, musamman da sun ka san me ya hwaru da ita a baya"
Jinjina kai kawai Sultan ya yi, dan ya san me ya tarar, tabbas to iyayen ta sun masa qoqari matuqa.
Abincin ya haɗa musu, ya mata sai da safe, ya ce ta shafa masa kan Auwal.
Murmushi ta yi,ta na jin wani irin dad'i da farin cikin ganin annuri a fuskar yayan nata.
Bayan sun ci abincin su,sukai kwanciyar su, Sultan ya rungume amaryar shi kamar an ce masa ga masu kilinafin matan mutane nan.
**************************
Sai bayan wata biyu da haihuwar Sultana Hansatu ta samu zuwa can Tudun faila, dan yi musu gaisuwa, ta samu labarin an yi wa Mubaraka aure, nan ta nemi adireshin gidan aka bata, daga nan mijin ta abin son ta, ya kai ta gidan tsohon gwamna Halliru, ba ya jin nauyi ko ganin bata lokaci,in zai kai ta unguwa, ko ina ne kuwa.
Mubaraka ta ji dadin ganin ta sosai, sun sha hira matuqa kafin Hansatu ta tafi.
Tunda Hansatu ta je gida take bawa Hajiya Labarin Sultana, har sai da Hajiya ta ce,
"Gaskiya da za su bamu ita Musa shi aure, da mun gode musu, maganar yaro kuwa ai shi d'a na kowa ne,na tabbata Musa zai riqe shi kamar shi ya haihe shi,"
Cike da murna Hansatu ta ce,
"Kwarai kuwa, ki duba ki gani, yanda Yah Abdullah ke son su Ameenatu, yanzu hwa ba ya so na kira shi da kowanne suna sai da Baban Ahmad,diyan nan gaba daya sun mance da uban su, tunda daidai da rana guda ba na iya tuna sanda ya dauki dayan su, balle har ya musu wasa, amma shi har da su goyo, su doki, duk haka yake musu wasa indai shi na gida baya gajiya "
"Allah Sarki, Allah shi yi muku albarka"
******************
An sha fama sosai kafin Sultana ta yarda ta auri Yaya Musa, abinda ya sa ta yarda ganin irin yanda yake son Muhammad kamar shi ya haife shi, shi ya ja ra'ayin ta, ta tabbata ba soyayyar nan bace da ake cewa, in zaka so bazawara ka so dan ta, ta tabbata wannan soyayyar gaskiya ce, dan wasu za su nuna suna son dan bazawara, sai bayan aure su yi ta rashin mutunci.
Ba a wani ja dogon lokaci ba aka sha biki, amarya Sultana ta tare a gidan Hajiyan Hansatu, zama suke na mutunta juna, da karrama juna, tare da so da qaunar juna.
Sultana bata taba ganin wani a gidan ya nuna wa Muhammad banbanci ba, daga manyan har yaran, hasali ma wata soyayya yake samu ta daban,saboda yaro ne mai kyau, da kazar kazar kuma ba shi da qiwa.
Yaya Musa ya samu kulawa da soyayyar da yake fatan samu a rayuwar shi,ji yake kamar auren saurayi da budurwa suka yi da Sultana tsabar kulawar da take bashi.
Sultana kuwa a koda yaushe qoqari take ta danne soyayyar Lawwali da ke binne a qasan ran ta dan faranta wa mijin ta mai tsananin son ta.
**********************
Bikin suna ake ta yi, a gidan Hajiya Ikee, Sultana da Hansatu sune akan komai, Dan haka komai ya kayatar ya wadatu, ba wanda ya taba zaton Mubaraka za ta yi qiba, sai ga shi haihuwa daya ta zama masha Allah, wata yar kubul kubul da ita, gwanin sha'awa ,ta samu yarinya mace, an sa mata suna Ayshaa, sunan da Lawwali ke buri ya sanya wa diyar shi, in mace ce, Sultana tai ta shagwaba ta na fadin an riga ta, dariya suka dinga mata, Mubaraka kuwa ta bata hakuri ta ce,
"Next time ke kuma sai ki haifi Humairah"
Dariya aka sake sanyawa cikin farin ciki, haka sukai ta nishadi, angon qarni na can tare da abokan shi,su na cin abunci.
Tsohon gidan su Sultana da Lawwali kuwa, an maida shi islamiyyar matan aure, an saka mata Suna Muhammad Auwal Qur'anic recitation school, Mubaraka ce ke kula da makarantar da wasu malamai da suka d'auka.
Su Mai Buruji da Lamishi da 'Yabbuga kullum da yamma Jameelu ke kai su ya maida su in an tashi.
Tammat bi hamdu lillah.
Nan na kawo qarshen labarin Oga Lawwali, ina fatan kuskuren da ke ciki Allah ya yafe min,ya shafe shi cikin rubutu na da zuqatan wanda suka karanta, alkhairin da ke ciki Allah ya bani ladan shi, ya sa al'ummar musulmi su amfani da shi,Allah ya zaunar da ƙasar mu lafiya ya biya wa kowa buqatun sa na alkhairi daga kan 'yan qasar Nigeria zuwa shugabannin mu da su kan su 'yan ta'addan dan a daina kashe kashen da ake yi Ameen.
*Haermeebraerh ce*
(Hamibrah)
*Haermeen Hammah❤️🙈*
*Hameedah Sanusi Ahmad*
*Ummu Fateemah wa Muhammad Muzakkir* ❤️