Showing 48001 words to 51000 words out of 155423 words
Chapter 17 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
oga Lawwali ya gano kai ka ɗauke ta, kar ka kira suna na, ina da iyali, ina da mahaifiya da tai yi min saura, ban shirya mutuwa ba ni da dangi na"
Wata tsawa No 1 ya sake ma No 4,
"Wai kai me ye haka? Kana wani tsoron shi kamar ba namiji ba? Yanda ya ke jin shi shege ne mu ma muna jin kan mu, kuma ka na ganin da mun tsaya diba wadda nika batu ka na ganin ba za a kama mu ba? Dallah be a man, yanzu ka tai zuwa samo musu abinci mu kulle gida mu koma daji, kahin a kula bamu nan"
No 4 dai bai gama daukan wannan maganganun ba, a mugun tsorace yake, gani yake kamar zai ga Lawwali a gaban shi, cikin rawar jiki ya tafi ya samo masu binci, da ruwa, da duk wani abu da ya kamata su yi amfani da shi, dayan dakin dake can lungun gidan suka maida su, dakin na dauke da bayi, da babban gado, su na wurga su suka rufe gidan, sannan suka tsorata su da fadin akwai masu gadi, in suka ji kwakkwaran motsin su, sun bada umarnin a shiga a harbe su.
Ko da suka fita daga gidan, ina dubawa sai na ga wajen sabuwar unguwa ce,ba gidaje sosai, Bus suka shige suka dauki hanyar da zata sada su da maboyar su.
***********************
Lawwali ya firgice ya haukace wajen neman Mubaraka, tsakanin makarantar su ta boko da islamiyya da unguwar su ya yi zuwa ba iyaka, daga baya gida gidan yan makarantar su ya dinga bi ya na tambayar sanda suka gan ta na qarshe, jikin Lamishi kan ta sai da ya fara sanyi, Dan Talo kuwa ya na can yawon bin abokai, bai san me ke faruwa ba, sai wajejen sha daya da ya dawo ya ji Muryar Lawwali cikin maye ya na ta ashar tare da alwashin in ba a gan ta ba a gobe sai ya yi ajalin Lamishi, mugun bakin ta ne da tsanar da take wa Mubaraka ya ja ta bar gida.
Lamishi fa yanzu tsoron d'an nata ya gama shiga kowacce kafa ta jikin ta, basu taba ganin shi cikin matsanancin hali irin wannan ba, ya farfasa musu abubuwan amfani, ya jiwa kan shi rauni kala kala, ga shi ya kasa kokawa, banda huci ba abinda ya ke fitar wa kamar wani damisa.
Dan Talo qin shiga gidan ya yi, ya labe a waje, (uban banza kenan) jira yake ya samu Lawwali ya shiga dakin shi ya afka gidan, in ya so a nutse ya tambaya ya ji ina Mubarakar ta tafi.
Da misalin sha daya da rabi na dare Lawwali ya gama yanke shawara, makullin motar shi ya dauka,ya ja qofar shi zai fice, Dan Talo na maqale ya ji motsi, kwanar gidan ya sha a guje, Mai Buruji da Yabbuga na tafe su na tattauna tashin hankalin yau da Lawwali ke ta yi a unguwar, Yabbuga na fadin, da an sha kwana za ta koma, bata fatan had'uwa da shi ya na lafiya ma balle yanzu da yake a fusace.
A guje suka ga Dan Talo, su ma diba suka yi a guje Yabbuga ta yarda yar kwabirar wayar ta rakani kashi, sai ihu take ta na kiran Dan Jumma tare da zagin shi ta na fadin ya na sane ya qi raka su.
Dan Talo ya riga su fad'awa gidan su Yabbuga, dafe da qirji suka same shi ya na maida numfashi, Dan Jumma ne ya fito a tsorace ya na tambayar waye.
"Mi na na kun ka shigon gida haka a guje kamar wad'anda aka biyo? Yaqi akai halan?"
"Yaqi ake amma a gida na, wannan shegiyar yarinyar ce ta tafi yawo, bata dawo ba, ta ja muna bala'i, hatta da gambun gidan nan bai tsira ba, sai da Yaron nan ya ɗebe shi yau, komi ya hwashe ya lalata, na jiyo ya na fadawa Lamishi gobe in ba a ga Mubaraka ba sai ya yi jalin ta, ban ko wallah shiga shi gama da ni"
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una, anya Dan Talo kun yi addu'a kuwa? Yaro awa diyan shedannu? Bashi jin maganar kowa sai dai a ji tashi?"
"Ke Yabbuga shige ciki, kai kuma, dan Allah ka kama matar ka ku tafi gida, kuma da ka ke fad'in Mubaraka ta tahi yawo, ka hini sanin halin ta, iya sani na da ita ba za ai mata shaidar yawo ba, yarinya ce me hankali ,ko tunanin wani abun ne ya same ta baku yi, ku kam Allah ya yi muku sauqi, (gyara tsayuwar shi Ɗan jumma ya yi, ya na kada hannu, ya ce) zan ruhe gida"
Cikin sanyin jiki Mai buruji ta bi Dan Talo da jiki ya wa sanyi, sai yanzu maganar batan Mubarakan ya fara shigar shi, tabbas ita ba me yawo bace, kawai dai yawan fad'a da Lamishi ke yi ne ya sa shi ma yake fada.
Su na shan kwana suka tsaya cak, sai da suka tabbatar motar Lawwali bata nan, suka qarasa.
Su na shiga suka ga Lamishi na hada kayan ta, cikin tashin hankali, Dan Talo na tsaye a bakin qofar shiga dakin ya ce,
"Ke kuma mi na na ki ka yi haka? Ina zaki da wanga tsohon dare?"
"Gidan iyaye na zan tafi, tunda d'an da na haifa da ciki na ya ce sai ya yi ajali na akan qaunar shi, diyar da ni na haihe ta da ciki na, wanga wanne irin bala'i na? Ka dai san yadda Yaron nan shike ko?"
"Tau in kin tai can an ce maki barin ki zai? Kin ga kin ja musu musiba, gwanda ki zauna, gobe mu tai bid'ar ta gaba dayan mu, ki yi tunani dai"
Shiru ta yi, ta na nazari,to ina Mubaraka ta tai? Ita din ba me yawo ba ce, (sai yanzu ta san ba me yawo bace, duk sunayen da take kiran ta da su).
***********************
A hargitse ya shiga dajin, kowa ya san Oga ba lafiya a daren,dan haka kowa ya nutsu, No 1 da sauran yaran shi na kusa ne suka bi shi a baya, dakin da suke ajiye mutanen da suka sato, 'yan uwan su sun kasa biyan kudin fansa ya shiga ,firfito da su ya sa aka dinga yi, sai da ya fidda wajen mutum biyar sannan ya jera su a filin wajen, idanun shi kadai abin tsoro ne, bindigar da aka cika da harsashi ya karba ya dinga kai musu harbi, sai da ya harbe su tass, sannan ya koma dakin shi da ke wajen, ma'ajiyar giyar shi ya je ya bude,ya jima kwarai rabon shi da shan giya ,dakko kwalba ɗaya ya yi, ya kafa kai, bai aje ba sai da ya sha ta kusan rabi, wata iriyar razananniyar qara ya saki, ya buga kwalbar a qasa, wannan qarar ta firgita No 4 ba kadan ba, hankalin shi ya yi bala'in tashi, tsoro ya hana shi tunanin mafita.
In ya ce ze sanar da gaskiya,ya san bai tsira ba, in ya bari har Lawwali ya gano da kan shi nan ma bai tsira ba, ya zai yi??????
*Ina nissani?*
[6/21, 5:15 PM] HAERMEEBRAERH ❤️: 💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 27:
Sati biyu ya wuce ba Lawwali ba bayanin shi, ba Sultana kadai ba, hatta da Gwamna Halliru ya fara shiga tashin hankali akan lamarin Lawwali.
Duk wata barna da ta'asa da Lawwali ke aikatawa ta na komawa kunnen Gwamna Halliru, ga zabe ya gabato sauran kwana goma sha uku, lamarin ya tabarbare fiye da tunanin Gwamna, domin kuwa a yanzu Lawwali ko cikin gari bai cika shiga ba, sai jefi jefi dan ya ji halin da ake ciki game da neman qanwar shi da ya sa a yi.
Lawwali ya koma kamar mahauci, akan neman Mubaraka, ya yi kuka har ba iyaka, ya zama kamar wanda ya rasa iyayen shi da dangin shi a dare daya.
Duk wata motar da ta yi tsautsayin bi ta kusa da dajin su, to sunan su matattu, ko kuma ya sa a kame su, ayi ta azabtar wa, ko ya sa a yi ta amsar kudi wajen dangin su, madadin batan Mubraka ya risinar da shi,sai ya sake ruruta masa wutar rashin imani a zuciyar shi.
Sultana kuwa duk ta fige ta rame saboda rashin Lawwali, ko ta je Foundation din ma watarana da kuka take komawa gida, rashin ganin shi a idanun ta ba karamin azabtar da zuciyar ta yake ba.
Duk ta dora laifin akan Hajiya, domin a tunanin ta maganar da Hajiya ta yi ne ya sanya shi yin fushi ya tafi.
Ta gwada No shi ya fi sau shurin masaqi amma ta qi shiga, kullum sanar da ita ake a kashe wayar take, ta yi kuka ta godewa Allah, ta yi sallah ta yi addu'a akan Allah ya dawo mata da shi in da alkhairi, in babu Allah ya sa mata hakuri da dangana, hakan da ta yi ne ya sa ta ɗan samu sauqi kadan a ran ta, har ta ci gaba da aikin alkhairin da ta sa wa ran ta.
Shiru shirun ta, da rashin shiga mutane da take ya bawa Gwamna damar yada abubuwan da take na alkhairi a gidajen talabijin da rediyo, da duk wata kafar sadarwa, mutane kuwa na ta yabawa, wasu na qara neman taimako a wajen ta, ita kuwa hakan na mata dadi, ganin aikin da take ya na ta bunqasa.
In ta na aikin ta na samun nutsuwa da kwanciyar hankali,da ta dawo gida komai sai ya kwance mata ,ba abinda take gani a idon ta in ba Lawwali ba, tsayuwar shi a jikin mota, da murmushin shi mai sauti, yanayin yanda yake kafe ta da ido, ya na kallon ta, sai ta ji kamar a wannan lokacin ya ke kallon nata, har lumshe ido take, watarana ta yi murmushi in ta tuna, watarana ta fashe da kuka.
An shiga sati na Uku Lawwali be bayyana ba, sai wata safiyar Lahadi, ya shiga gari, direct wajen aski ya nufa,a ka yi masa aski me kyau, aka masa gyaran qafafu da hannuwa, sannan ya sayi turaruka, da kayan abinci ya nufi gidan shi,ko da ya shiga gidan duk ya yi qura, kallon ko ina ya yi, cikin sanyin jiki ya ajiye ledojin hannun shi ya kalli ko ina, wasu irin zaratan hawaye ne masu zafi suka dinga zubar masa.
Mubaraka ce ke masha shara, in ta biyo shi, ta yi wanka ya maida ta gida, ko gyaran da akai wa gidan na qarshe ita ta masa, har ta dinga mishi fadan ta ajiye wani flower vase a tsakiyar table, ta koma ta gan shi a qasa, ya kama kunnen shi ya na bata hakuri, ta na ta tura baki ta na shagwaba, ta ce ta hakura kar ya sake, ta mayar ta gyara komai, ta yi wanka ya maida ta gida, ya na gama tunawa ya sanya wani irin kuka mai ban tausayi, sannan ya ce,
"Barakana ina kin ka tai na? Wanne hali ki ke ciki? Kin ci abinci? Kin yi wanka kuwa? A wanne irin waje ki ke kwana? Barakana, ki yafe wa yayan ki, na kasa kare ki, na kasa nemo ki, baraka na ki dawo gare Ni, ke ce sanyin idaniya ta, na rabu da Sultana duk da son da nake mata, na kasa cire ta a zuciya ta, dan Allah ki dawo ki taya Ni neman soyayyar ta, ba zan iya ba Ni dai,ke Ni ka jira ki sa Sultana ta so ni, Barakaaaa"
Kuka ya dunqule a waje guda ya na yi, kamar qaramin yaro, ya na son dika qannen shi, amma mubaraka ta daban ce, ita kadai ce ke son shi, ita ke kula da shi, ita kadai ta damu da rayuwar shi, tun ya na da burin ya dawo na gari, har ya kangare, ba wanda ya damu da wace iriyar rayuwa yake ciki, kudi kawai iyayen shi suka sanya a gaba, yau kuwa zai kai musu kudin da zai haukata su, amma sai suma sun bayyana masa Barakan shi, ko ya sawa kudin fetur a gaban su ya qona, hakan sai ya fi masu ciwo sama da yanda yake ji a ran shi.
A haukace ya debi kudin da ya koma da su, masu dimbin yawa a jaka, ya zari makullin motar shi, da wayar shi da ya bari a gidan, bai je ko ina da ita ba, motar shi duk ta yi qura.
Ya na shiga ya fitar da ita, ya koma ya kulle gidan, ya na qoqarin fita daga layin, motoci guda biyu da ke kai Sultana Foundation a yanzu su ka shiga unguwar suma,kamar an ce ta daga kai, Lawwali ta gani fuskar shi ba walwala, idanun shi jawur kamar ba shi ba, ya na tsula gudu,gashi duk ya yi duhu,
"Auwal? Dama Auwal na nan? Shi ne ya daina zuwa? Driver bi motar Auwal duk inda ya yi,"
"Tau Ran ki shi dade"
Dayar motar masu tsaron lafiyar ta na ganin an juya suma suka bi su, ta waya ta sanar da su me ke faruwa, kwantar da hankalin su suka yi suka bi su a baya.
Saboda damuwar da Lawwali ke ciki, be ma kula ana bin shi ba, har sai da ya shiga unguwar su, ya tsaya a qofar gidan su, sannan ya kula da motocin Sultana.
Wani irin yanayi ne mara fassaruwa ya shige shi, kewa ne, tsantsar soyayya ce, da kuma neman taimakon ta, duk sun had'u sun game masa waje daya.
Ita kuwa bata san sanda hawaye ke gudu a fuskar ta ba, ga alama nan, Lawwali na shaye shaye, amma bata duban wannan, domin dama dan Adam tara yake, be cika goma ba, ita dai a kowanne hali yake ta na son shi, ita kadai ta san ya take ji.
A hankali suke takawa zuwa ga junan su, Sultana ji ta yi kamar ta kwantar da kan ta a faffadan qirjin shi, ko abinda take ji zai ragu, Lawwali ji ya ke kamar ya isa ya rungume ta, ta shafa kan shi da siraran yatsun ta, tare da fada masa cewar 'Komai zai wuce, zai yi daidai' a cikin kunnen shi.
Sun jima su na kallon juna kafin Sultana ta yi qarfin halin cewa,
"Why? Me yasa? Me ya sa za ka tafi a lokacin da zuciya ta, ta amince, ta yarda, ta kuma gamsu da ta kamu da matsanancin ciwon son ka? Me ya sa ka tafi, a lokacin da nake tsananin buqatar ka, ka kuwa san ya nake ji a nan dina? (Ta sanya hannu, ta nuna saitin zuciyar ta, cikin kuka,) ba zaka gane ba, saboda baka san me ne ne soyayya ba ga dukkan alamu,"
Cikin sauri ya dakatar da ita, dan kalaman ta na sake harzuqa zuciyar shi, ta na hango masa mugunta kala kala.
Cikin cije lebunan shi a cikin bakin shi ya shafa kan shi, da hannu daya, sannan ya ce,
"Sultana, ba ke dai ka jin duk abinda kin ka lissahwa ba, ni ma ina ji dika, wataqila har da dori ma, amma sultana ba ke d'aya zuciya ta ke so ba, qauna ta ita ce rayuwa ta, ban da komai banda kowa sama da ita,ita kad'ai ce gata na a duk qasar ga, ba mai so na tsakani da Allah, sama da ita, a yanzu haka ji na nake kamar duk duniya sun juyan baya, ni kadai ne, ban da kowa banda komai,"
"Wait a minute,me ya samu Mubaraka?"
A cikin tashin hankali Sultana ta masa wannan tambayar, a cikin qasa da minti bakwai ya bayyana mata me ya faru dangane da batan ta,da kuma irin neman da yake mata, bai samu ba.
Cikin kuka Sultana ta juya ta rufe bakin ta, ta jima a haka ta na kuka, Lawwali ma ji ya ke kamar ya yi kukan, sai daga baya ta juya gare shi, ta na share hawayen ta, motar ta ta fara budewa zata shiga,sannan ta ce,
"Mu je gida Daddy na nan yau, mu sanar da shi,a sanya neman ta, duk inda ta shiga, i love her, she is a gud gurl, I can't let anything happen to her, she is like a sister to me, mu je gida Auwal, maza shiga mota mu je,"
Kallon gidan su ya yi, cikin takaici, ya na jiyo muryoyin mata ana ta zabga hira, ya ji haushi da be shiga ya tarwatsa su ba, qanwar shi ta bata amma suke hira haka ana dariya har waje ana ji, ya so ya shiga ya gan su, da duk sai ya musu rashin mutunci d'aya bayan d'ayan su, amma ba komai next time.
Kwafa ya yi, ya shige motar shi, ya bi ta su Sultana.
*************************
Gwamna Halliru na ganawa da su No 1 da 4, su na tattaunawa akan yanda Lawwali ya haukace.
Sultana ta je za ta shiga parlour wasu masu tsaron wajen ne suka dakatar da ita, tare da sanar da ita cewar Gwamna ya ce kar a bawa Kowa damar shiga, sai da izinin shi, d'aya daga cikin su ta kalla tace,
"Ka je ka sanar da shi ni ce, na ke son magana da shi, ya na da mahimmanci na gan shi yanzu"
Har security din zai tafi, Lawwali ya qarasa shiga wajen, su na hada ido, security ya ja baya, tare da fadin,
"Ran ka ya dade Oga, Barka da zuwa"
"Gwauna hwa? "
"Shi na ciki Oga"
Mamaki ne danqare a cikin Sultana, an hana ta shiga amma an budewa Lawwali ya shige,me kenan? Lawwali ya fi ta matsayi a gidan Uban ta kenan?
Ko da suka shiga shiru wajen ya dauka, ba No 4 da ake tausa ba, ana nuna masa ba abinda Lawwali zai yi, as long as bai gane ina qanwar shi take ba, har Gwamnan kan shi sai da hankalin shi ya tashi ainun.
Cikin rawar murya, No 4 ya ce,
"O....ogaa, kai ne da rana haka?"
Lawwali ko kallon No 4 be ba, ya samu kujera ya zauna, tare da harde qafa,No 1 ne