Showing 33001 words to 36000 words out of 155423 words
Chapter 12 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
dafa shinkafa da wake, ya ji yaji mai dadi, ga man ya samu matsayi har albasa aka saka masa.
Nan dai Yabbuga uwar kwadai ta hau yaba qamshin girkin, Ita kuwa Hansatu jin haka ya sa dole ta debar musu, haqqin su ne sun ji qamshi tunda akwai ta zuba musu. (Da damar mutane rowa ta saka ba su damuwa da haqqin maqoci, a yi girki mai dadi, me qamshi a lashe a sude hannu, wasu ma maqotan su talakawa ne, amma ba za su sammusu ba, duk da dai yanzu duniya ta sauya, ka na iya bawa mutum dan Allah da haqqin maqotaka, ya ce dan a san ka na cin dadi ka bayar, amma ka tsarkake zuciyar ka ka bayar, mutum shi ya sani da ya maka sharri, sannan wasu in suka ga ana basu, sai su fara zaqewa da roqo, har mutum ya koma boye abu ya na rowa, da ace kowa zai gyara da an zauna lafiya)
Su na kai loma su na zuba hira, rabi da kwatan hirar bata wuce ta auratayya ba, Isah na daki ya na jin su, ya na kuma jin dadin hirar saduwar auren da suke ta yi, Hansatu kuwa sai fada masu take, su yi a hankali mijin ta na ciki, Matar Yahai na bude baki kuwa, sai da ta fadi maganar da ta sa Hansatu shiga wani irin hali na matsananciyar kunya, su kuwa suka sheqe da dariya, Asshibi kuwa sai ta ji matan sun kwanta mata a rai,dan kuwa wajen hirar banza ta fi kauri dama.
Hansatu ta gaji da jin maganganun su, masu sanya ta kunya, cikin tattausan lafazi ta ce,
"Wai ku in tambaye ku? Me ne ne jigo a rayuwar aure ne?"
"Saduwa mana heeeeee casssss"
Suka yi shewa tare da tafawa, Isah kuwa dake daki, har sake gyara kwanciya ya yi, ya na sauraron su.
Zama Hansatu ta gyara ta ce,
"Tabbas saduwa daya ce daga jigon da ka sa a yi aure, amma ba ita kad'ai ba ce jigo a gidan aure ba, abubuwan na da yawa, su din ginshiqai na da ka riqon aure, in babu su da tuni aurarraki da dama sun watse.
Na farko akwai yin auren ma shi kan shi domin Allah, sannan Yarda, riqon amana, saduwa, ladabi, biyayyah, soyayya, qauna, tausayi, ciyarwa,tufatarwa, wajen zama,girmama juna, qimanta juna, mutunta juna, tausayawa juna,iya girki,da wasu mahimmai dai.
Wa'yanga abubuwa in suka hadu, aure ya ginu, ya zauna kenan sai dai in ajali nai na ya yi.
Na fahimci me ya sa kuke ganin kamar saduwa ita ce kad'ai abinda ka riqe aure, ba komai na yasa ba saboda fadi da ankai cewar,Aure shike hada wata alaqa, tsakanin mace da namiji, wannan shi na nufin hade rayuwarsu ta zama daya haka nan kuma makomarsu ta kasance guda daya. Kowacce irin al'ummah akwai irin matsayin da ta ba wa aure, Aure a musulinci wani daurine da shike halatta wa ma'aurata mace da namiji jin dad'i da junansu, ta hanyar saduwa irin ta jima'i,da sauran mu'amaloli na jin dadin saduwa, Allah (subbahanawu wa ta'ala) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu.
Wannan babban dalili ne da zai sa ku ga kamar saduwa tahi komai a aure, amma duk wadda bata iya kula da miji ba, ta hanyoyi da dama, musamman iya girki, tsafta, kwalliya, ladabi da biyayya, bata iya magana ba, komi yattaho bakin ta hwadi takai, to wallahi mace na da saura a gidan aure ba ta iya komi ba"
Gaba dayan su har Isah da ke kwance, hansatu ta basu mamaki, ba mace ba ce me yawan Suratu, amma sai gashi yau ta yi magana cikin ilimi da nutsuwa da fasaha.
Mai Buruji ce ta fara yunqurawa ta miqe ta na sude hannu,
"Tauuuu, Mallamar gidan aure mun gode da wanga ilimi da munka samu, bari mu tai mu dora a gidan mu mu ma ko mun zam matan so ga mazajen mu kamar ke, mun gode da wake da shinkahwa ke iya girki, shi yasa Isah ba shi iya cin abinci ko ina, sai gida "
Dariya suka kwashe da ita, da shewa, dan kuwa magana Mai Buruji ta gaya wa Hansatu, ita da ake jibga kuma ake zagi kowa na ji, ita ke musu bayani haka.
Murmushi mai ciwo Hansatu ta yi, sannan ta ce,
"Ai duk abinda na fad'a maku ba qarya ciki, ballantana ki fad'a min magana, kuma ko da na fad'a ban ce ni ina aikata su ba,sannan ban ce ina da wani cikakken matsayi a wajen miji na ba, ballantana ya zama abin yi min arashi,"
Yabbuga ce ta taimaka wa Lamishi ta miqe, sannan ta kalli Hansatu ta ce,
"Keee wagga kwantas kin ga gida munkai yanzu, shiga daki ki lallaba Isah dan kuwa duk ya walqita ya ga ba shinkahwar ga se ke mance da kin taba sanin mi na na ma'anar aure a musulunci"
Dariya suka fita su na mata, kafin su rabu sai da suka yi ta gulmar ta, Yabbuga na basu labarin yanda yake dukan ta da zagin ta, akan abu qalilan.
*Shin a maganganun Hansatu akwai gyara ne mutanen kwarai? In akwai gyara ko qarin haske akan zamantakewar aure a qaro mana ilimi*
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 20:
Mata kala kala ne a duniya, musamman ta bangaren kwalliya, da gyaran jiki, kowacce mace da hanyar da take bi dan ganin ta yi kyau.
Akwai wacce za ta yi gyaran jiki da kaya irin namu na gida da muke amfani da shi yau da kullum, kamar su lalle, dankalin turawa, sugar ,kwai, cucumber, tumatur, gwanda, Madara, lemo, zuma da sauran su, wadannan kadai sun ishe ta ba tare da ta yi kwalliya ba.
Wata ta kuma kayan wanka na Bature kawai sun ishe ta, ba tare da kwalliya ba.
Wata kuma ta na haɗawa duka , ta kuma qara da kwalliya.
Sultana na daga cikin matan da basu damu da gyaran jiki da kayan amfanin yau da kullum ba, ta fi amfani da kayan gyaran jiki na Bature, masu gyara asalin fatar mutum ba tare da ta sanya shi fari ba, (wannan shi ne aji da waye wa, bleaching qauyanci ne da zubar da kuma da mutunci ga mai hankali amma tare da nuna wa Allah be iya ba, ya tauye ki, ke bari ki wa kan ki abinda ya gaza wa'iyadhubillah).
Yau tun da Sultana ta fito daga wanka,ta ke tunanin wanne kaya za ta saka dan ta yi kyau, me za ta yi wa fuskar ta dan ta qayata ta?
Ta jima zaune a dan qaramin table din, ta na shafe shafen mayuka da turaruka masu sanyin qamshi, yau ce rana ta farko da ta fara shafa kwalli, tare da shafa powder har dikin wuyan ta, jan baki ta jera a gaban ta ta na tunanin wanne za ta shafa, kalar purple mai haske ne idon ta ya sauka akai, dauka ta yi ta goga kadan, sannan ta hade kyawawan labban ta, kallon kan ta tayi a madubi, ganin yanda ta yi kyau ne ya sanya ta sakin murmushi mai laushi.
Maskara ta shafa ma gashin idon ta mai yalwa, ta gyara girar ta, abun shafa powder ta sake dauka ta gyara ko ina na fuskar ta.
Kallon wayar ta ta yi, ta ga ta na ringing, Sultan ne ke kiran ta, amsawa ta yi cikin sallama, da gaisuwa.
"Ok ina nan tafe ,bani minti biyar,"
Kashe wayar ta yi, cikin sauri da zare ido, ashe ta dauki lokaci mai tsawo haka? Lallai masu yin kwalliya su na cin lokaci, anyaa za ta dore kuwa? Kayan ta ta nema wanda ta saba sawa ko da yaushe, wato doguwar riga irin ta larabawa, in ta saka irin su su na amsar ta sosai, duk da ita din ba wata fara bace sosai, amma ba za a kira ta baqa ba, fatar ta na da haske sosai .
Ta na kammala shirya wa ta dauki jakar ta, ta sanya takalmin da ya zo da jakar ta ta, wayar ta riqe a hannun ta, ta na sake duba time din da ta bata.
Ta na daf da sauka daga yar matattakalar benen ne ta tsaya cak, Lawwali ta gani tsaye da Daddyn ta su na magana qasa qasa.
Daddyn ta da alama ya shiga damuwa sosai .
Da dan hanzari ta isa gare su, takun takalmin ta, da qamshin turaren ta ne ya sanar da su zuwan ta, Lawwali na dora idon shi a kan ta, ya ji kamar an zare masa dukkan wata damuwar shi,da lakar jikin shi, har wani lumshe ido ya ke.
Shi abinda ka ke so, Indai ka gan shi, komai munin shi kyakkyawa ne a wajen ka, ballan tana kyakkyawa ji za ka yi kamar ba abinda ya kai shi kyau a duniya.
Sultana kallon Lawwali ta yi, ta ga yanda yake kallon ta, kunya ce ta ji ta kama ta, sai ta ɗan sunkuyar da kan ta qasa, ta na murmushi, bai san sanda na shi ya bayyana ba, gaishe da Dad din ta tayi, sannan ta gaishe da Lawwali, da hanzari cikin girmamawa Lawwali ya mayar mata da gaisuwar.
"Daddy lafiya? Na ga hankalin ka a tashe?"
A dan daburce ya kalle ta, ya hau yaqe, ya na dafa kafadar ta, tare da shafa kuncin ta ya ce,
"Sulty baby ba abinda ke damu na, dama ina tsaye ne ina jiran ki fito, kowa yunwa yake ji, amma ba ki fito ba, sai kuma gashi masha Allah, na ga yau kin yi wata iriyar kwalliyar da ban taba gani kin yi ba"
Dan kwabe fuska ta yi, cikin shagwaba, wanda ya sanya Lawwali dan jingina da jikin ginin da ya ke tsaye a jiki ,tare da hard'e hannun shi a qirji,ya lumshe idanun shi a hankali ya sauke su akan ta.
"Daddyyy ban yi kyau ba ko? Let me go and clean my face, yanzu zan dawo"
Da sauri Lawwali ya ce,
"Wacce baki kyawu ba? Ke gane ki kuwa? Tunda ni ke duniya ban taba ganin mace kyakkyawa awakke ba"
Wani irin farin ciki ne ya lullube Sultana, har gwamna Halliru zai fassara maganar Lawwali, sai suka ji Muryar Sultan na fadin.
"Ba ka yi qarya ba Lawwali,bayan budurwa ta ban taba ganin kyakkyawar macen da ta hiki kyau ba Sulty Baby"
Dan tura baki ta yi kadan sannan ta ce,
"Wace budurwa ka ke da? Bayan tsoron mata ka kai"
Dariya aka sa a wajen, suka nufi dinning table, aka bar Sultan da son kare kan shi, shi ba tsoron mata yake ba, kawai dai tausayin su yake ji.
Hajiya Ikee ma zama ta yi ta na dariya, tare da taya Sultan kare kan shi.
"Sultan ai jarumi na wallah ,matar shi sai diyar sarki ko shugaban qasa"
Lawwali na gaishe ta ta yi kamar bata ji ba, ita ta qi jinin talaka, masu aikin ta kaf ba dadin ta suke ji ba,
Lawwali da ya ga ta qi amsawa hanyar fita ya kama abin shi,dan ya basu waje, sai ya ji Muryar Sultana na fadin
"Auwal ka ci abinci kuwa?"
Cikin jin dadi, ya juya ya kalle ta, a ranshi ya na ayyana ta na bashi abinci a baki, da sauri ya kawar da tunanin ya amsa da .
"Eh na ci,in ke qare ki dai yi min magana mu tai"
"Tau ya yi"
Fita ya yi,ya nufi can baya inda suke shanya a gidan ,waya ya dauka ya kira No 2, bata wani jima ta na ringing ba ya dauka, cike da damuwa da tsoron Ogan nasu.
"Hello, No 2 garin ya kuka bari ya gudu? Wanne irin daqiqanci ka damun ku? Dazu 1 ya kire Ni yacce min wai tsohon gwamna ya gudu, ka sani, duk kun ka bari ya hita dajin nan baku nemo shi ba, da hannu na zan halbe ku, dukan ku, umarni na ne, ku hita har da su Sa'adatu a nemo shi duk inda ya shiga, bai isa hita wajen nan ba yanzu, ku bazama da motoci a nemo shi, da kun ganai ku halbe shi, kar ku jira komai, kuma ku sani, zan bincika, duk wanda nikkama shi na da hannu a taimaka masa ya hita,.....duk wanda ya taimaka masa.....hummm sai na zo dai kawai,"
'Oga....'
Kafin No 2 ya yi magana Lawwali ya kashe wayar, cikin fushi ya tafi, ko daya je ya tarar Sultana na ta neman shi, dan sake fuskar shi ya yi,sannan ya je da sauri ya bude mata qofa, wayar shi ce ta yi qara ya duba 'Excellency' shi ne a jikin wayar, daga wa ya yi, tare da yin qasa da Muryar shi,
"Kar ka damu ranka shi dade, na bada umarnin a nemo shi, da na aje ta za ni nima"
'Ah Ah kar ka kuskura ka bar min yarinya ita daya, ka tsaya a wajen ta, ban yarda ka matsa ko ina ba,'
"Amma ranka ya dade..."
'Umarni nake baka ba shawara ba Lawwali'
"To ran ka shi dade,"
Kashe wayar ya yi, ya shige motar ya ja su suka bar gidan,ya kasa sake fuskar shi saboda bacin ran da yake ciki, rashin zaman da ba ya yi sosai a wajen yanzu ya sa su na sakaci da abubuwan da ya kamata su na bawa mahimmanci.
Sultana ta dan damu da ba ta ga ya kalle taba, sai ta samu kan ta da jin ba dad'in rashin kallon ta da ba ya yi a yau.
"Tsayar da motar,"
Ta madubi ya kalle ta, cike da mamaki, kauda kai ta yi kamar ba ita ta yi magana ba,
"Ran ki shi dade mi kicce?"
Dora idanun ta tayi a nashi sannan ta ce,
"Dan koma baya kadan, ka tsayar da motar daidai waccan matar mai suya qosai"
Komawa baya ya yi, ya tsayar da motar, tunda ya dora idon shi akan ta ya manta da tunanin da ke a zuciyar shi ,fita ta yi, matar na ta soya qosai, ba mutane sosai a wajen, saboda hantsi ya fara.
"Assalamu alaikum, baba a bani qosai na nera dari,"
"Wa'alaikumussalam, to yarinya ki dan jira ke ga ni dai akwai wasu gaban ki"
"To Baba"
Lawwali ne cikin hade fuska ya nufi wajen zai magana, Sultana ta marairaice ido, ta masa alamar ya bari, yanayin yanda ta yi ya shige shi, amma sai ya koma ya tsaya a gefen ta, Ita kuwa kallon unguwar take, ta na kuma wa, da alamar su na buqatar taimako,yara baja baja ba masu zuwa makaranta, ita fa ta na son makaranta ,ta na bawa makaranta mahimmanci, ta na son ganin yara na zuwa makaranta, ba ta son ta ga yaran da ya kamata ace su na aji, ta gan su su na wasa a unguwannin su.
Wani yaro ne da zai kai shekara goma sha daya, ya keto a guje ya tada qura, saura kadan ya fadi, cikin qiftawar ido Lawwali ya tare shi, sultana kuwa har ta rufe ido, dan kuwa ta saddaqar zai fadin, shiru ta ji, dan haka sai ta bude ido a hankali,
"Ke gani bai fadi ba? Yara irin wannan sun hi ki son jikin su,"
Cikin murmushi ya fadi hakan, Itan ma murmushi ta mayar masa, tare da maida hankalin ta kan yaron da ke raba ido a tsakanin su.
"Me ya sa ka ke wargi ba ka tai makaranta ba?" (Wargi wasa kenan)
"Ba a biya min kuddin makaranta ba"
"Ina ne gidan ku?"
"Shi na can bayan shiyyar ga"
"Me ya kawo ka shiyyar nan?"
"Wargi nittaho wajen diyoyin innata (wasa na taho wajen yaran innata)"
"Ohh su ma ba su tai makaranta ba kenan"
"Uhm"
"Ok to mu tai na ga gidan ku, za ka kai ni?"
"Mi za ki yi gidan mu?"
Dariya ta yi sannan ta ce,
"Zan gaishe da maman ka ne, na ce ta na da yaro mai hankali"
Shiru yaron ya yi, tare da saurin amshe hannun shi zai gudu, Lawwali ya riqe shi, ya daga fuskar shi, ya na kallon dan baqi kyakkyawan yaron,
"Ina za ka tai,ka rake mu gidan ku mana,"
"Mama ta ta mutu masu halbi na sunka halbe ta, baba na shi na inda likita da Goggo ta, an halbe shi a qafar shi guda,likita ya ce za a yanke,ba kowa gidan mu"
Sultana na jin wannan labari sai hawaye ya fara gangarowa saman kuncin ta, Lawwali kuwa ji ya yi kamar an dora masa wani abu mai nauyi a qirjin shi,tun da ya ke bai taba jin haka ba, ko dan bai taba tsayawa ya yi magana da wanda suke illatawa bane?
Gani ya yi Sultana ta ja yaron ta rungume a jikin ta, ko kula da dattin jikin shi ba ta yi ba.
Mutanen da ke wajen kallon ta suke da mamaki, da kuma birgewa, hankalin mutane ya fara yawa kan su Dan haka mota ta ja yaron suka nufa, ta zauna ya na tsaye gaban ta, ta kira Lawwali, ta bude jakar ta ta debi dubu goma ta ce ya bawa mai qosai, ta qara jari.
Sai ga Mai qosai ta debo qosai me yawa ta kawo ma Sultana ta na ta godiya kamar za ta kwanta mata, ita kuma tana nuna ba komai.
Amsar qosan ta yi, itama ta yi godiya, matar ta tafi, ta na ma Sultana addu'a.
"Ina ne makarantar ku? "
"Makarantar mu na can shiyyar mu, yawancin yaran shiyyar mu da na nan shiyyar ita suka zuwa"
"Za ka raka ni a mota ne ko da qafa?"
"Mu dai tai da qafa,"
Ya na dan dariya ya fadi hakan, Sultana ta fahimta ya na tsoro ne, ba ta ga laifin shi ba, zamani ya sauya, jakarta ta dauka da wayar ta, Lawwali ya kulle mota, suka taka.
Har zuwa makarantar yaran, ana ta karatu, makarantar ga ta nan ne dai kawai, kuma a haka ta kudi ce, sallama ta yi, ta nemi ofishin shugaban makaranta aka kai ta, bata fito ba sai da aka lissafa mata adadin yaran da ba su biya