Showing 138001 words to 141000 words out of 155423 words
Chapter 47 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
sun zo da niyyar tozarta gwamnan, sai gashi sun samu nagartaccen d'an shi ya musu bayani, da nasiha mai ratsa zuciya.
Haka suka tafi jiki ba kwari.
Masu karbar makullan gidajen da Sultan din ya bayar sun sallama sun karba sun yi godiya sosai, sannan su ka tafi.
Har qarfe biyar ba malam ba bayanin malam, Sultan da sultana su ne suka yi alwala, suka ce wa Hajiya ma ta yi alwala, suka dauki qur'anan su suka yi ta karantawa, Gwamna ne ya farka da wani irin ihu, mai cike da razananniyar qara, wanda ya sanya Hajiya Ikee da Sultana miqewa suka buya a bayan Sultan a guje, sai makyarkyata suke, shi kan shi ba dan qarfin imani ba da ba zai iya zama a wajen ba, guduwa zai yi.
Jijjiga jikin Gwamna ya dinga yi, Sultan kuwa na ci gaba da karanto ayoyin da ya san ana ruqya da su, bai daina jijjigar ba har sai da ya fado qasa, duk jikin shi ya nannade, musamman qafafun shi, idanun shi sun qara fitowa kamar wanda ake turo su ake musu hayaqin barkono tsabar ja da suka yi.
Sultana da Hajiya Ikee ba abinda suke Banda kuka, dan ko addu'ar ma sun kasa.
Yau ace mutum mai cike da isa da izza kamar gwamna Halliru ne a nannade kamar wata igiya, su na cikin haka, Gwamna ya fara motsa baki ya na so ya yi magana, Sultan bai tsaya ba, karatu kawai yake ya na kumawa, Hajiya Ikee ko qiftawa ba ta yi saboda kallon shi, a ina ya iya wanan karatun? Da yaushe ya iya wannan karatu mai dad'in sauraro haka?
"Za mu sha jiniiii ! A bamu jinii ! Mu na so mu sha jinin d'an tayi !"
Abinda Gwamna Halliru ke ta nanatawa kenan, kamar karatu, duk wani yunkuri na Sultan akan ya ga lamarin ya lafa, ya zo da sauqi inaaa ba wani sauqi, sai ma qara tunzura su da yake, suna jin zafi da qonewar da suke amma ba za su fita ba saboda taurin kai.
A hankali tsoron da Sultana take ji ya fara tafiya, matsawa ta yi dan ta zauna, ta taimaka wa Sultan su ci gaba da karatun tare, ta ga Daddyn su na bin ta da wani irin kallo, ya na murmushi, sai dad'i ya kama ta, a zaton ta lafiya ce ta samu, a nannad'en da yake ya fara matsawa kusa da ita, hannu ta kai zata kama nashi hannun, kamar daga sama ta ji an ce,
"Kar ki taba shi, tashi daga wajen, Hajiya ku shiga daga ciki, ku bar mu, da izinin Allah, Allah zai bashi lafiya"
Sultana ta so yin gardama, amma ta tashi ba dan ta so ba, wani ihu gwamna ya saki, ya na fadin,
"Za mu sha jiniii, za mu sha jiniii jinin d'an tayii ! Za mu sha jiniiin d'an tayin can !"
Kallon su gaba daya ya koma kan Sultana da ke kallon hannun gwamna Halliru, wanda ya daga yatsan shi manuni, ya na nuna cikin ta, da sauri ta kama cikin ta ta na shafawa, cike da tsoro Hajiya Ikee ta ja ta jikin ta ta rungume, nan da nan kuwa suka bar wajen, Malamin da ya yi alqawarin zuwa ne, ya kunce jakar da ya zo da ita, ya daukko wani ruwan da ya yi wa addu'a, ya dauko wasu mayuka na korar shaidanun aljanu, shafawa Gwamna su ya yi, sannan ya fara karatu shima ya na watsa masa wannan ruwan.
Azaba ta yi azaba, gumurzu ya yi gumurzu, Gwamna ya gaji da tumurmusa shi da suke yi, amma ba shi da ikon hanawa, a can cikin ran shi ya yi dana sanin fara siyasa, ya yi dana sanin sanyawa zuciyar shi son abun duniya, amma ba shi da damar hana duk abinda ke faruwa, a can qasan ran nashi ya ke addu'a, Allah ya dau ran shi ya huta, hawaye ne ke gangare masa, ya na bin Sultan da kallo, malamin ne ya ke magana, dan yanda ya ga jikin shi ya saki, da alama sun jigata kwarai,sun qoqqone, shi ya sa jikin su ya saki.
"Ran ka shi dade, Ranka shi dade Halliru,"
"Ba za mu tab'a rabuwa da shi ba, sai dai ku kashe mu tare da shi,"
"Haka kun ka ce? To kuwa za mu yi addu'a Allah ya dauki rayuwar ku, ku ku mace ku bar shi"
"Allah ma ba zai bar mutum kamar Halliru ya ci gaba da rayuwa a doron qasa ba, ka kuwa san wane ne Halliru? Ka san me ya aikata a doron qasa? Ka na da la...."
"Ba na son sanin wane ne shi, ina roqon ku ta girma da azziqi, ku rabu da shi, kahin Allah ya ci gaba da qona ku,ta sanadin ayoyin shi da muke karantawa, don kuwa duk mun ka fara ba mu bari sai kun mace, maqiya Allah"
"Sai dai ka kashe mu, amma ba inda za mu, kuma sai mun sha jini, dan lokacin da yake bamu jini ya gota"
Sultan ne ya miqe cikin tashin hankali ya ce,
"Malam jinin shi suke zuqa, in suka sha jinin shi yanzu ba wanda za a qara masa zai iya rasa ran shi"
Kallon shi sosai Malam Ya yi, ya kalli gwamna da ya fara shure shure, qafafun shi na miqewa daga nannadewar da ya yi.
Sultan ne ya ta fi da gudu ya na qoqarin rungume gwamna Halliru, Malam kuwa na ci gaba da karatun Alqur'ani, tare da yarfa masa ruwan da aka yi wa ayoyin ruqya, jikin gwamna Halliru sai makyarkyata yake, ya na jijjiga da qarfi, jini ne ya fara fita ta hancin shi, idanun shi sun kada sun yi jawur.
Hankalin Sultan ya gama kaiwa qololuwa wajen tashi,
"Daddyyy, Daddy, kalle ni, Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, ya Allah ka kawo mana agaji, Daddyyy ! Daddyy Please open ur eyes, Dad.."
A hankali jikin gwamna ya sake, kan shi ya fad'a qirjin Sultan, wani irin kuka mai cin rai Sultan ya sake,ya jima ya na kukan kamar zai shide Malam kuwa samun waje ya yi ya zauna ya na ta tasbihi ga Allah, duk abinda Allah ya yi shi ne daidai.
Kukan Sultan ya yi yawa, ta yanda har sama su Hajiya Ikee na jiyowa, a tare suka sauka qasa ita da Sultana, ganin abinda ke faruwa ne ya sanya Hajiya yanke jiki za ta fadi, Sultana ta taro ta, tare da cewa,
"Hajiya mu godewa Allah, tunda ya samu kwana, (bacci) mu isa, sannun ku Malam, Allah shi bada lada, mun gode,Yah Sultan ba kuka za ka yi ba, mu godewa Allah, tunda ya samu bacci , yanzu Mom ke fad'an ba su kwana, mu tai mu yi sallah mangariba ta yi"
Da qarfi Sultan ya ce,
"Wai ke ba ki da idanu ne? Daddy is gone, he is dead, ya mutu, ya rasu,"
Idanun ta ne suka cika da hawaye, ta fara kada kai, ta na so ta yi dariya, ta na kuma so ta yi kuka,
"Wasa ka ke yi ko? Daddy ba zai mutu ba, daddy bai mutu ba"
Da gudu ta sake Hajiya Ikee ta qarasa faduwa hannun kujera ta yi kan mahaifin nasu, da ya sake jiki, a jikin Sultan, jijjiga shi ta fara ta na kiran sunan shi, cike da kidimewa, gaba daya yau ilimin su, da tunanin su ya gushe (Allah kar ka gusar mana da hankalin mu, a lokacin da muke da tsananin buqatar shi, Allah kar ka sa mu
aikata abu da jahilci a lokacin da muke tsananin buqatar aiki da ilimi) wani irin kuka Sultana take mai tsananin ban tausayi, tare da surutan da basu kamata ba ace musulmi na gari ya na furta su, a lokacin da ya yi rashin wani nashi .
Mutuwar ta gigita kowa, Malam dai tun da ya zauna ya ke kallon kowannen su, tausayin su ya cika masa zuciya, ya san a wannan yanayin da suke ciki, wa'azi ko nasihar ma ba za su ji ba, a hankali ya fara furta
"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,"
Tun ya na yi a hankali har ya fara da qarfi, sai a wannan lokacin ne hankalin su ya fara dawowa jikin su, suka fara furtawa su ma, su na kuka su na maimaita wa.
Cikin qanqanin lokaci Sultan ya fara waya, ya na sanar da dangin mahaifin nashi na nesa da na kusa, har da dangin Hajiya Ikee, hankalin shi bai kawo ba ya kira Lawwali ya sanar da shi.
Har sai da aka wanke Gwamna Halliru, aka kai shi makwancin shi na gaskiya a wannan lokacin, sai bayan sun dawo ne ya tuna ya kira Lawwali, wanda ya ke ta gyaran gidan su dake nan unguwar.
Lawwali ya shiga rudani, da tashin hankali jin mutuwar uban gidan nashi, tunawa ya yi da cewar, kafin magariba ya wuce ta qofar gidan kafin ya isa nasu, bai ga kowa a gate ba, har ya ke tunanin yanda rayuwa ta koma, ace gidan Gwamna Halliru ne shiru a bushe ba mutane.
Bayan ya katse wayar cikin sauri ya sanya kayan shi, ya yi alwala ya yi sallahr Isha'i, ya na idarwa ya fita dan zuwa gidan, mota ya dauka dan ya na so ya yi saurin isa.
Tafe yake ya na ta tunanin rayuwa, ya na kukan baqin cikin irin rayuwar da ya kasance ya na aikatawa a baya........
*Yau ba appetite ɗin rubutu,amma a haka na cije na daure na ci gaba, sai gobe inshaa Allah kuma*
💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻
BY HAERMEEBRAERH
PAGE 61:
Ya na daf da isa gidan, ya ga wata mata zaune a jikin ginin da aka saka street light, da dan qunshin buhu a gaban ta, sai sandar ta da ta jingine a jikin jakar ta, ta rufu da mayafi, da alama anan take da shirin kwana,duk yanda akai ba ta san a wace unguwa take ba, domin a iya sanin shi, wannan unguwar tuni wani zai ciki da ita, a yi wani sihirin da ita, dan neman abun duniya.
Yi ya yi kamar zai tsaya, ya taimaka mata, kawai ya yi gaba, dan ya san yanayin yanda rayuwar ta koma, su kan su, sun sha haɗawa mutane trap da mabarata.
Bai tsaya a ko ina ba sai a bakin gate din gidan su Sultan,mutane ne danqam a wajen gidan, kamar da rana, da kyar ya samu shiga ciki, har da 'yan jarida, da sabon gwamna mai ci,da muqrraban shi.
Lawwali gaisuwa ya dinga miqawa mutanen da ya tarar, tare da ta'aziyya, wasu na yi mishi ta'aziyyar shi ma, kasancewar shi surukin gidan.
Sai da wajen ya d'an lafa ne, Sultan ya raka Lawwali ciki, nan ya samu Sultana a yanayin da ya kasa jurewa sai da kwalla ta taru masa a idanun shi, matan wajen na ganin haka suka firfita, aka basu waje, a hankali ya isa gefen ta ya zauna,cikin murya mai sanyi ya ce,
"Sultyna, ki yi hakuri, mu yi hakuri gaba daya, mu yi ta yi wa Daddy addu'a, dan ko ita ce kad'ai ya ke bid'a wajen mu, kuka ba zai dawo da shi ba, ki yi hankuri kin ji, jarumar mata ta"
A hankali ta ja jikin ta, ta kwantar a nashi, cikin kuka ta ce,
"Ba ina kukan rabuwa da shi bane, dan na san komai daren dad'ewa sai mun rabu,ina kuka ne akan tunanin Daddy bai samu ya furta kowacce kalma da ake saka ran Allah zai yahe masa ba,na tabbata sai ya sha azaba a lahira, saboda abinda ya kasance ya na aikatawa"
Da sauri ya sanya dogon yatsan shi a labban ta, ya ce,
"Kar ki ce haka, kin mance da me kike fadi min kullum, ba a shiga tsakanin bawa da ubangijin shi, in mutum ya yi shisshigi tsakanin bawa da ubangijin shi, shi sai Allah ya hana mishi rahamar sa, ya yi wa wanda ya ke wa zaton Allah ba zai duba da idon rahama ba rahamar "
A hankali ta fara jin wani sanyi a ran ta,
"Haka ne, yanzu ba abinda ya mana saura da ya wuce mu yi ta masa addu'a"
"Allah ya jiqan shi, ya gafarta mishi, na yahe mishi duk abinda ya yi min a rayuwa ta, ni ma ina fata ALLAH shi yahe min"
Wani irin dad'i ne ya kama Sultana, ta qara kwantawa a jikin shi ta na murmushi,
"Na gode miji na, na gode, Allah ya amsa addu'ar ka,....ina Mubaraka?"
"Dazu da mun ka hito gaba daya, mun yi wa daji bankwana, bankwana na har abada da yardar Allah, sai nace zan kawo ta nan wajen mu ta zauna ta ce ah ah, na kai ta gida, to ban san an yi rasuwa ba sai d'azu"
"Allah Sarki, ai da ta zo mun zauna, gidan ai da girma ba laihi, "
"Ke San ta da son su Lamishi,ba ta tahowa wajen mu yanzu, ban qi ba in ta gaji da zama wajen su,amma ke san mi ya faru?"
"Sai ka hwadi,"
"Da na je gida, na ga sauyi sosai wajen Baban mu,na tarar ya na yin rumfa, ban san mi ya ka son yi ba, mun gaisa cikin wani irin yanayi da ban san ya zan kira shi ba,ba wannan rawar kan kamar zai min kwacen kuddi, ita kan ta Lamishi haka, duk sun yi wani iri, har da yi wa Barakana oyoyo"
"Alhamdu lilLAAH, Allah ya qara kawo mana zaman lafiya, da shiriya,"
"Ameen Allah ya jiqan Daddy,"
Ta ji dad'in yanda Lawwalin ke ta masa addu'a ko ba komai, hakan ya nuna ba wani riqo a tsakanin su.
"Kin ci abinci kuwa?"
"Ahh ahh, gashi can, an kawo mana ni da Hajiya, mun kasa ci,amma yanzu da ka yi magana, na ji ina jin yunwa, ba zan iya ci bane kawai, baki na ba dad'i"
"Ayyaa dear, haka zaki daure ki ci, kin jiya?"
Tashi ya yi, da kan shi ya haɗa mata tea, ya bata, ta shanye tass,ya bata abinci kadan, ta ci, ta masa godiya, sannan ya mata sallama,ya leqa dakin da Hajiya Ikee da qawayen ta ke zaune, ya musu ta'aziyya.
Abun da ya gani ya bashi takaici, ba dan ace ya shiryu ba, da in ya buga wa wata mata da ta kafe shi da ido tsawa, sai ta rasa ina zata ta buya dan tsoro.
Tsaki ya yi a daidai saitin matar da zai fita, ta na zaune kamar wadda ta zo biki, ko ina gwala-gwalai ne,ga wata arniyar shadda ta zuba sai maiqo take.
Ta kunna snap chat kamar wata yarinya, ta na zaro harshe, ta na mayarwa, ya na shiga ta kafe shi da Mayun idanun ta, inda yake a tsugunne ta miqar da qafar ta sai da ta taɓa tashi,kallon da ya mata ne ya sanya ta janye wa da sauri ta na yaqe,ita a dole ba da niyya ta yi ba.
An zo gidan rasuwa amma wasu rasuwar bata dame su ba ma, wasu kuwa sun sanya hijabi,an riqe carbi, amma ba abinda suke sai hira.
A haka ya fita ya na takaicin yanda gidan rasuwa ya ke komawa kamar na biki, a wannan zamani.
Bai sake komawa wajen Sultana ba, gaisawa suka sake yi da su Sultan, ya tafi gida.
Sai sha d'aya na dare wasu mutanen suka dinga tafiya.
Sai da Hajiya Ikee ta zo bacci hankalin ta ya sake tashi, ita kuka Sultana kuka, ba mai lallashin wani,tabbas ba su taba zaton sun shaqu da shi har haka ba sai yanzu, ko ba komai shi din uba ne mai kulawa, ko sun ci, ko basu ci ba, ko suna da wata damuwa, ko basu da ita, shin farin cikin fuskar su ya ishe shi? Ko ya na so su fi haka farin ciki?
Har safiya Sultana bata rintsa ba, ta na kan sallaya, ga yunwa ta na ji, ta kasa cin komai.
Hajiya kuwa ba zata iya tuna sanda ta saka ko da ruwa bane a bakin ta.
Tausayin Hajiyar ne ya sa ta miqe da kyar, marar ta na murdawa, ta nufi hanyar parlour, za ta hado mata tea, wani irin jiri ne ya ɗebe ta, ta kusan faduwa, daddafe jikin bango ta yi, Hajiya Ikee da sauri ta isa wajen ta,cikin kuka ta ce,
"Dan Allah samu waje ki zauna, ko me ki ke so za a miki,dan Allah kar ki sa wa kan ki damuwa ke ma na rasa ki, ba zan iya daukan rashin ku ba,"
Kuka Hajiya Ikee ke yi sosai, Sultana kasa bata hakuri ta yi, sai da wasu 'yan uwan Hajiyan suka sa baki, sannan ta rage kukan.
Zama suka koma suka yi,tace a hadowa Hajiya Tea, da kyar aka tursasa ta ta sha, jin shi ta yi kamar mad'aci, amma haka ta daure ta sha.
A haka, a haka dai har sai da akai sadakar bakwai,sannan mutane suka tattafi gidajen su, dan yanda suka saba in sun zo a ci a sha a raqashe da kaji babu, duk da ana kawo na sadaka, amma ba kamar da gwamna na da rai ba.
*******************
A kwana na goma sha biyu, Lawwali ya je gidan Gwamna,dan gaishe da Hajiya, yanzu ya na bata girma sosai, saboda tausayi take bashi.
Ya na nan duqe gaban ta, ta na ta bashi labaran yanda tsohon gwamnan yake kyautatawa iyalan shi, da yanda ya ke matuqar son su, su Lamishi suka yi sallama, amsawa Hajiya Ikee ta yi, cikin d'an sakin fuska .
Zama su Lamishi za su yi a qasa, da sauri Hajiya Ikee ta ce,
"Dan Allah ku tashi daga qasa, rayuwar ga duk labari ce watarana, dan Allah mu yahe wa juna, abubuwan da sun ka hwaru a baya,"
"Allah Sarki Hajiya komi ya wuce, ya hankuri?"
"Alhamdu lilLAAHi,"
"Allah shi jiqan gwauna, shi mai rahama, Allah shi gafarta mai"
"Ameen Allah shi bada lada"
Mai Buruji, Mubaraka, duk sai da suma su ka bada gaisuwar su wajen Hajiya,da Sultana.
Sultana ce da ta fito daga ciki, ta je yin alwala, ta ga su Lamishi, da sauri ta je ta durqusa gaban su, suka