Showing 15001 words to 18000 words out of 155423 words
kamar a gidan kurkuku
"In haka kike tunani ran ki shi dade ki bari, domin zaman ki anan shi ne ruhin asirin ki da kariyar ki, kinga duniyar da ke a wajen gidan nan? Duniya ce ta azzalumai, duniya ce ta daukan rai ,duniya ce ta shan jini, da kwace muhalli, duniya ce azzaluma,duniya ce cike da miyagu masu raba Mata da maza da mutuncin su, zaman ki a inda iyayen ki sun ka killace ki shi kad'ai ne kwanciyar hankalin ki da kariya a gare ki"
Cikin kuka Sultana ta ce,
"Su kuma bayin Allah da ake kashewa fa? Haka za su ci gaba da rayuwa?"
Tashi ta yi da gudu ta fita daga dakin,
Lamishi kuwa komawa ta yi wajen Mai Buruji, ta ce su tafi kawai, dan bata ga alamar Sultana za ta ci wani abu ba.
Dakin mahaifan ta ta nufa ta dinga buga qofar da qarfi, Hajiya Ikee ce ta fito ita da Sultan ,Sultan na ganin yanayin Sultana ya san ba lafiya, cikin hanzari ya nufe ta, tare da qoqarin kama ta ta kwace ta yi gefe,
"Ina daddy? "
"Yanzun Nan ya fita, za su fita government house me ne ne sulty na?"
Da gudu ta fita, ba ko takalmi a qafar ta,
Gwamna ya shiga motar da zata kai shi gidan gwamnati kenan, bayan shi da gaban shi kuwa motoci ne masu bashi kariya, duk sun yi shirin tafiya, ganin Sultana ta fito a birkice cikin kuka, da hargowar kiran sunan shi ne ya sa ya dakatar da su, ya fita,
"Sulty baby me ke faruwa? Ina za ki haka?"
"Daddy, Ina zaka je? Za ka je wajen mutanen can ne da aka qonawa garin su? Daddy pls help them, they really need ur help, daddy su ma fa mutane ne, Kuma a qarqashin kulawar ka suke, me ya sa haka take faruwa da su ne?"
Dan kallon gefe da gefen shi ya yi, ya ga kan mutanen da ke wajen a dan duqe, wasu kuma sun qura musu ido, dan jin amsar da zai bayar, dan kama kafadun ta ya yi, ya goge mata hawayen idan ta, wanda ba su daina zuba ba duk da gogewar da yake ta yi,
"Sulty baby, yanzu haka can zani,ki koma ciki, guards ku tsananta tsaro, kar a bar kowa ya shiga ko ya fita,"
Ya kalli idanun Sultana a lokacin da yake fadin hakan, saboda ba yau ta saba satar jiki ta fice ba,sai dai ya ji labarin ta kai taimako wajen Wanda ibtila'i ya fadawa.
".....ina nufin kar a bar kowa ya fita, a tsananta tsaro"
Ture hannun shi ta yi daga kafadun ta, cikin hawaye ta ce,
"Me ya sa ba za a ba wa mutanen can tsaro ba kamar yanda ake ba wa wannan gidan? Shin masu gadin mu a gidannan nawa ne? Yawan su bai isa ya kare wani qaramin garin ba? Me ya sa ba za a kai taimako wajen da ya dace ba?.."
"Keep quiet sultana and go inside kafin na saba maki,"
Mota ya bude cikin fushi ya shige, nan da nan kuwa aka kunna jiniya, motocin da ke bashi kariya na biye da ta shi.
Qoqarin durqusawa take a wajen ta na kuka, Sultan ya tallabe ta, sai wutsil wutsil take tana son kwacewa, motar su Lawwali ce ta shiga gidan , Lawwali ne a gaba gefen mai zaman banza, yau ce rana ta farko da ya fara dora idanun shi a kan Sultana, yau ce rana ta farko da ya taba jin wani abu mai nauyin gaske, wanda bai taba jin kalar shi ba a gaba daya rayuwar shi ya soki zuciyar shi, wani irin yanayi ne mai dad'i cike da shauki, da wani dandano wanda bai san yanda zai fassara shi ba, har motar ta tsaya,yaran shi suka fara fitar da wasu buhuna da aka nannade aka ma wani irin dauri, wanda komai kwakkwafin ka ba ka Isa gane me ye a cikin daurin ba, Lawwali na zaune a mota, har Sultan ya yi nasarar dauke Sultana wajen Lawwali bai ma sani ba, ganin ta kawai yake a cikin kwayar idon shi, kamar a mafarki ta na zuwa gaban shi,shi kuwa sai zabga murmushi yake.
"Oga an gama,"
A dan daburce ya kalli No 1,
"Tau tau, ya Yi, shiga mu tahi, kun aje dai inda Excellency yacce ko?"
"Eh oga,"
"Tau ya yi, muje"
Kallon inda ya ga Sultana a duqe ana fama da ita ya sake yi, ya dan saki murmushi,
'shege Excellency, dole ya dinga kaffa kaffa da zuwan mu, ashe ya aje kadara mai tsada a gidan shi,'
Cikin zuciyar shi ya ke wannan tunani, har suka fita daga gidan suka dauki hanyar dajin su bai magana ba, No 1 na Masa magana gaba daya hankalin shi ya tafi wajen tunanin sultana.
*********************
"Ki na nufin har yanzu ba su dawo ba? Kuma ki ke zaune a gida ki ke kukan banza ba ki tafi Nemo su ba? In wani abu ya samu yara na Hansatu sai na maki abinda ya fi qarfin mutuwa azaba, ..ba Zaki tashi ki tafi makarantar tasu ba?"
A tsawace ya Yi maganar, cikin rashin kwarin jiki, da ciwon da qirjin ta ke Mata ta miqe ta nabin bango, duhu ya fara, ko yar touch light dinnan ba ta da shi, ga shi ba wuta a unguwar, cikin duhun da ya fara Shiga, ta nemi takalmin ta, ta dauki mayafin ta, ta fita.
Ko Bai Mata fada ba, ta na da niyyar in ta idar da sallah ta fita Neman su, amma me ya sa ba zai Taya ta ba, zai aika ta? Ko su tafi tare, yaran ai Shima na shi ne, zuciyar ta ce ta sanar da ita cewar,
'Hansatu yau ne kike tare da Isa ? Yau ko ke Kika Bata ai ba zai je Nemo ki ba, ballantana yaran da ya tsana, ya ke ganin su na daga cikin silar talaucin ku'
Hawaye ne masu tsananin zafi ke sauka a fuskar ta, a zuciyar ta kuwa wani irin quna ta ke ji, qirjin ta ne ya sake Yi Mata suka, sai da ta damqi saitin zuciyar ta, ta durqusa a tsakiyar hanyar, da mazajen kirki na unguwar na ta fitowa daga masallaci Dan komawa gidajen su.
A hanyar Isa ya same ta,
"Tsayuwar me kike anan?"
Daga Kai ta Yi a wahale ta ce
"Gaba (qirji)na ka Yi min ciyo, Amma yanzu zan tafi"
"Hummmm"
Shi ne kawai abinda ya fadi ya wuce ta ya na kwafa, da kyar take tafiya, ko da ta Isa makarantar sai ta gan ta a rufe, tun daga gate din ma alamu sun nuna ba kowa ciki, Mai gadin wajen ta tambaya, ta Masa kwatancen yaran, ya ce Bai gan su ba yau, ya gane su, yara ne nutsattsu masu hankali, ga qoqari, malaman kan su na yaba qoqarin su.
"Hajiya jiya dai sun taho, Amma yau ban gane su ba,mu na gaisawa da abokina Amadu ai kullum, Amma yau ban gane su ba"
Idanun ta sun fara bushewa, Ina yaran ta Suka tafi to? Su ba masu yawo bane,
"To ko gidan mu Suka tafi?....kaii inaa, tun da suka je sau uku na Hana su ba su sake zuwa ba, yau shekara biyu, to Ina suka tafi?"
Yawo Hansatu ta fara, lungu da saqo na unguwar nan, Bata ga ko ji Wanda ya ga yaran ba.
Hankalin ta ya tashi ya Kai qololuwa, yara har uku, ace sun Yi batan dabo? Ina Suka shiga? A wanne hali suke? A hannun wa suke? Wa ya sace su?
Tunani ne ya Mata yawa, ta yanke jiki ta fadi a qofar gidan Asshibi.........
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAEH
PAGE 11:
Ta jima kwance a wajen, mutane ba su kula da ita ba, saboda duhun dare da ya shiga , da misalin takwas da wasu 'yan mintinan mijin Asshibi ya dawo, hasken fitilar motar shi ne ya haska ta, dan haka a tsorace ya fito daga motar, ya na gudun mugayen mutane, masu kwanciya da niyyar neman taimako, daga nan su cutar da mutum.
A hankali ya fita daga motar, sannan ya tsaya daga nesa,inda da an ce kyat ya zura a guje, ko da ya yi ta magana ya ji shiru, wayar shi ya dakko ya haska Hansatu ,ganin alamar gajiya, da wahala a tare da ita, ya tabbata wannan ta na buqatar taimako, da wayar shi ya yi amfani ya kira Asshibi, amsawa ta yi tare da sanya babban hijabi, saman qananan kayan ta, bata fi mintuna biyar ba ta fito.
Bayani ya mata, suka isa gaban Hansatu a tare, Asshibi ta ce,
"Boyar Allah, boyar Allah ko ni tashi dannan, ba ki ganin wajen akwai datti,"
A wahalce murya can qasa, Hansatu ta ce,
"'ya'ya na,....ban gan su ba...tun da suka tafi makaranta ban gan su ba....."
Mijin Asshibi na jin haka ya miqe da ga tsugunon da ya yi, gefe can ya koma ya lalubi wayar shi, ya danna kira, cikin qasa qasa da murya ya ce,
"Kai taho garka ta(qofar gida na) ka dauki matar ka, ga ta nan ta hwadi,"
Komawa ya yi wajen su Hansatu ya na jimami, cikin tausaya wa Asshibi ta tallafe ta suka shiga ciki, kamar kar ta bi Asshibi , amma ba ta da kwarin yin musu da ita.
Ko da suka shiga, kunun da ta dama take sirki da shi, shi ta sakawa Hansatu a babban cup, ta saka sigar da madara ta juya sosai, ta kafa mata a baki, Hansatu na jin abu da sigar, ga qamshin kayan yaji, sai yunwar ta ta murda, cikin ta ya bada wani irin sauti da qara.
Ba bata lokaci ta kurba sau biyu, za tai na ukun ta tuno da yaran ta, shin a wanne hali suke ciki, sun ci abinci kuwa, a wanne muhalli suke, su na raye kuwa?
Wani irin kuka ne da tunda aka haife ta bata taɓa yin irin shi ba, ya kwace mata, Asshibi kuwa hawaye ne kawai na tausayi ke saukar mata,ganin hawayen ta kuwa tashin hankalin mijin tane, dan haka dakin shi ya shiga, wayar Isa ya sake kira, cikin fada ya ce ya je ya dauke matar shi, ko ya sanar da ita ina yaran suke.
"To dan tonanniya, gani nan garkar ka, ku turo ta mu tafi,"
Komawa parlour ya Yi, ya ya na Basu hakuri, sai suka ji ana buga qofar,da sauri mijin Asshibi ya fita dan ganin wane.
Sun dan jima da Isa suna tattaunawa kafin ya koma,
"Wani mutum na ya taho, ya na neman Mata tai, yanda ya yi min bayani, ina kyautata zaton ita ce wagga, raka ta can garka"
Da kyar Hansatu ta miqe, cikin dan saka ran wataqila yaran sun koma gida.
Ko da ta ga isa, ta ga yanda ya bata rai, ta san ba nasara, wani malolon baqin ciki ne ya tokare mata maqoshin ta, cikin murya mai rauni ta ce,
"An gane su?"
"Ba ke ce ki ka tafi nemo su ba? Ke zan tambaya an gan su ko ba a gan su ba"
Kafe shi ta yi da jajayen idanun ta, sannan ta ce,
"Yanzu tsakanin ka da Allah Baban Amina ba ka tafi neman diyan ga ba? Ni kad'ai zan ta neman su? Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibatee wa aklifnee khairan min ha, ya Allah ka bayyana min yara na cikin qoshin lafiya da aminci da salama"
Ta na taka qafarta wajen gate din ana kawo wutar lantarki, ihun yara har da wasu manyan ne ya karade kunnuwan su, hasken da ya bayyana ne ya sanya Hansatu jin kwarin guiwar ci gaba da neman su.
Gida gida haka ta dinga shiga neman su, wasu su tausaya mata, wasu su dinga ganin sakacin ta.
Har sha dayan dare Hansatu na yawo, ita da wasu daga matan unguwar da suke da mutunci, wanda ta zaci sun san ta za su taimaka mata wajen neman yaran ko leqe zuwa qofar gida ba su yi ba.
Hankalin ta ya tashi ainun, isa kuwa wajen mazajen unguwar ya tafi ya na cigiya, duk wani lungu da saqo na unguwar an duba ba yaran,shawara aka tsayar akan washegari a je akai cigiya gidan talabijin da rediyo, masu wayar cikin su tun a daren suka bi ta gida, ta na da wasu hotunan yaran da aka taba daukan su a Makarantar boko,nan akai zooming fuskar su aka dauka, aka watsa social network.
Hansatu ji take me za ta zauna a gida ta yi? Bata san a wanne hali yaran ta suke ba?
Tashi ta yi, ta yi alwala ta yi ta nafila, ga yunwa na cin ta, cikin ta se qara yake, qarshe da tsayuwar ta gagare ta, a zaune ta qarasa sallar ta.
Isa kuwa banda minshari ba abinda ya ke ja, daga farkon gado, ya koma qarshe, daga qarshe ya koma tsakiyar gadon har asuba ya na baccin asara.
Asshibi kuwa tunani da tausayin Hansatu ya gama nuqurqusar ta, ta sha kuka ta gode Allah, wannan tausayi nata ne ya jawo masu barin unguwar da suke a baya, da an rasa yara ko kuma ta ji an sace Wani ta dinga damuwa kenan, wasu sun danganta hakan da rashin haihuwar ta, wasu sun danganta hakan da ganin ido, duba da cewar bata da halin kirki itama, amma mutane na manta cewa dan Adam tara yake, bai cika goma ba, dik yanda ka kai da mugun hali, ba za a rasa mai kyau ba a tare da kai, haka duk yanda ka kai da kyakkyawan hali, ba za a rasa mummuna ba ko yaya yake a tare da kai.
***********************
Abu kamar wasa qaramar magana na neman zama babba, yau sati Daya da kwana uku, ba labarin su Amina ba motsin su, Hansatu ta fita daga hayyacin ta, mutane ko ta ina zuwa ake masu jaje, labari ya kai har wajen Hajiyan Hansatu, abin d'a da mahaifi, sai ga ta ita da yayan ta sun je, cikin wata rantsattsiyar mota mai numfashi, duk wanda ya ga Hajiyan Hansatu zai mamakin ta na da diya amma ta bar ta take a wulaqance haka, dukiya sai kuka take a jikin ta, duk da ba ta wani ci ado ba, a ganin ta, amma a ganin idon talaka ta ci ado ne sosai .
Hansatu ta dake, ko kuka bata yi, sai tasbihi a zuciyar ta, ganin Hajiyan ta ne ya sanya bakin ta rawa, a hankali kwallar da ta cika ta tumbatsa a idon ta ta fara kwaranya, zama Hajiya ta yi a kusa da ita, ta kama hannun ta, itama kwantar da kan ta tayi a cinyar Hajiyan nata, jaje Hajiya ta mata,ta amsa da kyar, cikin kuka ta ce,
"Hajiya yara na duka fa aka ɗebe man, ba guda ba, ba biyu ba, dika ukun, Hajiya ina ji a jiki na, mutuwa zan yi, hankali na ya fara barin gangar jiki na, zuciya ta tafi ciwon da aka sanyawa gishiri zafi, tafi gulandon da aka fama ciwo Hajiya, na rasa inda zan saka raina Hajiya ,"
Kwalla Hajiya ta mayar, domin ba wanda bai tausaya wa Hansatu ba a wajen, hatta da su Lamishi da suka shiga yi mata jaje sai da zuqatan su suka raunana.
"........dan girman Allah kar ku cutar da yaran nan, ku taimake Ni ku dawo mana da su, mahaifiyar su ba ta da isasshiyar lafiya, shin wai ku ba ku da imani ne?"
A guje Hansatu ta qarasa waje, dan jin me mijin ta ke fadi, ta zaqu ta ji me ke faruwa, a handsfree Isa ya Sanya wayar, kowa da ke wajen ya kasa kunne, Hajiyan Hansatu kuwa kamar ta amshe wayar take ji.
Daga wayar ne mai magana ya ce,
'Taurin kan ka ne zai sa na kashe daya daga yaran yanzun nan, tun shekaran jiya na ce ka aiko milliyon goma, ka tsaya neman ragi, Ina ruwana da talaucin ka da ka ke fada? Bani da lokacin jiran ka, in baka kawon milliyon goma ba nan da kwana uku, gawar yaran ka za ka gani a titi'
'Dil Dil Dil Dil'
Shi ne qarar da wayar ta yi, sai a sannan ne mutanen wajen suka kula Hansatu ta suma.
Ruwa aka yayyafa mata sannan aka kaita daki,ta na tashi ta dinga kuka,
"Yanzu baban Amina tun da jimawa aka ce akai kudi ba ka fadan ba? Me gadon nan yake ko gidan nan da muke ciki suke? Da ba za mu siyar ba? Yara na sun fi min komai na duniyar nan, ka nemo mai saida gidan a siyar dan Allah ka amso min yara na"
Kuka take sosai, isa na share hawayen qarya.
"Hansatu kaina ya kulle ne, kwata kwata na manta a gidan kan mu muke ma, bari na je na siyar da gidan na aika musu kudin"
Miqewa ya yi zai fita, Yayan Hansatu ya ce,
"Dakata, in kun saida gidan yaran sun dawo ku zauna a ina? Muje na rubuta maka cheque ka karba ka fidda kudin ka basu"
Isa zubewa ya yi gaban qanin bayan shi ya na godiya, kamar wani soko, Hansatu kuwa kukan farin ciki take tayi, ko ba komai yaran ta za su dawo gida lafiya da yardar Allah, kuma gashi ta shirya da iyayen ta.
Ana bama isa cheque ya wuce banki ya cire kudin , ya nufi maboyar su shi da mijin Asshibi, tun a hanya ya sanar da shi ya na tafe.
Kamar yanda suka tsara kuwa Isa ya bashi kaso daya cikin kaso uku na dukiyar nan, sannan ya tafi ya boye nashi kason a banki.
Sai da ya gama komai sannan ya koma ya debi yara suka nufi gida.
Yara fess da su, Ahmad har dan kumatu ya yi, saboda kullum sau uku suke cin abinci a rana, Amina kuwa dake ita ta na da wayo, ta rame ta yi duhu, saboda kewar Umman su.
Ko da suka isa gida ranar ba wanda bai kukan farin ciki ba, yanda Hansatu ta kidime