Showing 30001 words to 33000 words out of 155423 words
Chapter 11 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx
ki na fadin ta samu turmushe, ya yi tsanani ne sosai ?"
Dan bata rai Lawwali ya yi, dan ya qudirta da ya aje Sultana zai je gidan ya tada ma Lamishi da duk wani ragowar hankali da ya rage a jikin ta.
"Eh jiya ta fadi amma da sauqi an gyara mata, an dai ce ta bari har ya warke ne kar qafar ta samu matsala ,"
"Allah Sarki in kin je, ki ce ina diba ta, Allah shi bi da lahiya"
"Ameen, zan hwadi mata"
Burki ya ci a gaban makarantar su Mubaraka, goma har ta yi, ana qoqarin fita break, Mubaraka ta san me yake shirin yi, dan haka da sauri ta fita ta tare shi,
"Yah Auwal kar ka shiga dan Allah, in ma bulala ce za a min, na cancanta, kwana na biyu ban zo ba, yau na je late bai kamata ba, su nada 'yancin yi min komai, malamai na ne, ballantana ma ba zan shiga yanzu ba, saura yan mintuna a tashi break sai na hade da sauran ɗalibai kawai"
Kallon gate din ya yi, ya ga a bude yake, ya kalle ta ya ga ta na murmushi, bai san sanda shi ma murmushi ya kwace masa ba, sai ya nemi baqin cikin da yake ciki ya rasa,ya rasa kalar qaunar da yake ma qanwar shi, niyyar shi ya shiga ya buga masu warning akan kar a taba masa qanwa, amma ta hana.
Dafa kan ta ya yi, sannan ya rungume ta kadan, Sultana da ke kallon su cikin sha'awa da burgewa ce tai saurin daukan su a hoto ta na murmushi, hannu Lawwali ya zira aljihu ya bata dari biyar,sannan ya koma mota, ta na ta daga nasa hannu shi da Sultana ,sultana ma hannu ta daga mata, dauke da murmushi, zai tada motar kenan aka fita break, dan tsayawa ya so yi ya ga shigar Mubaraka, sai kuma ya fasa, ya bata ma Sultana lokaci matuqa ba tare da ya yi tunani Ba, sai a wannan lokacin ya ga tsaurin idon shi .
Hakuri ya dinga bawa Sultana, har sai da ta masa shiru, tunda ta ce ba komai, amma yaqi ya dena bata hakuri.
"Ran ki shi dade kin yi shiru, ko dai ba a yafe min laifi na bane?"
"Wa ya ce maka ka yi lehi? Ai kai lambar yabo ya kamata a baka, a matsayin ka na yayan da ya fi kowanne yaya so da qauna tare da kulawa ga qauna tai, ina ganin soyayya da kusanci na da Sultan amma naku, ya burge ni sosai"
"Koh Ran ki shi dade?ina godiya da yabawa, yabon ki ya fi duk wata lambar yabo ko girma da za a bani, "
Murmushi ta samu kan ta da yi, ba ta sake magana ba har suka isa, shi kuwa leqen ta ta madubi, shi ne ya zama aikin shi .
Bude mata qofar yayi, sannan ya take mata baya har office din ta, akwai mutanen da ta kula da su a jiya da ta ke bada taimakon nan, yau ma sun zo, su na ganin ta suka taso, fess da su,da alama mutane ne masu ilimi.
Har office suka je, Lawwali ne ya gabatar mata da su, domin ya san su, suma 'yan gwagwarmayar siyasar mahaifin ta ne, amma su mutane ne masu gaskiya da amana, gwamna na amfani da su in ya na son isar da saqon addini, ko kuma saqo wajen mutanen kirki, dan ya siye zuciyar mutane a ce shi din na Allah ne.
Ya rasa dama aikin da zai basu tun kafuwar gwamnatin shi, kullum suka je neman aiki hakuri yake basu, bude wannan NGO ya taimake shi sosai, dan haka ya ce su zo su taya sultana aikin.
Sultana ta ji dadin ganin su sosai , dan haka ba bata lokaci ta tattauna da su, ta kuma zabawa kowa bangaren da ya dace da shi .
Da taimakon su ta fara kasafin yanda zata gudanar da qungiyar, aiki ya sha kanta, da wannan damar Lawwali ya samu, ya tafi gida ba tare da sanin ta ba.
Ko da ya isa ya wuce Yabbuga a qofar gidan Asshibi, ta qurawa motar shi ido ta na son tai gulma dan bata gane motar waye ba,idon su karaf ya fada a na junan su, rakubewa ta yi a jikin ginin gidan Asshibi ta na salatin da ko iyawa ba ta gama yi ba,
Lawwali da ya san yanda Yabbuga ke mugun tsoron shi ne ya ci wani wawan burki dan nesa da su, ta na ganin haka, sai ta yi zaton baya ze yi ya je wajen su, bangaje Asshibi ta yi, ta afka gidan ta, ta na salati, ko ina na jikin ta rawa yake, Lawwali kuwa me zai banda dariya,qarasa wa ya yi gidan su,ya bude ya shige .
Lamishi na ta baccin ta hankali kwance.
A tsaye ya tsaya mata, ya ce
"Lamishi...Lamishi, shin kwana ki kai ko mi?"
Bude ido ta yi, tare da qanqance su, tsaki ta doka sannan ta ce,
"Sannu uba na, nicce sannu ubana, lalatacce tambadadde fado min a kai za ka yi? Ka tsaya min a ka kamar za ka hwado?"
"Ba wannan ya kawo ni ba, Barakana ba zata yi bautar gidan Gwauna ba,in ki na bari har ki ji sauqi tau, in baki bari ki hakura da aikin, ai dama kun tsufa barin ku kawai sun kai dan an saba, amma me kuke in kun tai?"
Kofin da ke gefen ta ta dauka ta maka masa a guiwa, ko gezau be ba, yo wace wahala ce shi be sha ba,
"Ka hwa rammin Lawwali, (ka fa raina ni Lawwali) in ce ga abinda za ai ka ce ah ah? Za ta dawo ta samen tunda ta kai qarata wajen ubana"
"Ni dai na fada maki, bata koma zuwa aiki wani gida, sai da son ran ta"
"Ka san bana jin magana, se ka buga zan gane me ka ke cewa ubana...kuma wane irin kaya ne na gani jikin ka? Jahili dai ka ke balle in ce ko aiki ka samu na taimakon qasa"
Ran shi ya yi mummunan baci da kalmar Jahili data jefe shi da ita, ba dan ya na musun shi din jahili bane, amma su waye silar zaman shi Jahilin?
Wani mugun kallo ya wurga mata, sannan ya sa kai ya bar gidan.
Zagin dai da ta saba, wanda shi ne ya dauki kaso saba'in na lalacewar shi, shi ta dinga qunduma masa, ta na maimaitawa, tare da fadin Mubaraka za ta same ta, su a dole qungiyar 'yan hadin kai, to duk abin su ita ta haife su, sai ta so kowa ya zauna lafiya, da sauran kalamai munana marasa dad'in saurara.
Da misalin qarfe uku na rana suka koma gida, Sultana ta so lokacin tashin su Mubaraka bai wuce ba su dauko ta, haka nan take jin son yarinyar, ta alaqanta hakan da ilimin da ta kula Mubaraka na da shi.
Sun isa gida sun tarar da Mubaraka ta kwaso wankin kayan sultana daga ɓangaren wanki na gidan, za ta mayar cikin gida.
Ko a fuska ran Lawwali bai ɓaci ba, tunda Mubaraka ma bata da damuwa akan hakan, shi dai ko ma mene zatai ya zama ta na son abun, da kuma dukkan alama ta na jin dadin aikin, ba bacin rai a fuskar ta, sai ma walwala.
Da hanzari ta aje kayan ta nufe shi, tare da yi musu sannu da zuwa baki dayan su, jakar Sultana ta amsa, sai sultana ta riqe, cikin murmushi ta ce,
"Na gode, na hutar da ke, kar gatan ya min yawa, ga wanki kin debo, a ina za ki riqe jaka? In yau kin kai min gobe wa zai kai min?"
"Ko Ni Kin kai wa izini har ciki sai in kai miki, ballantana Mubaraka,"
Kallon Lawwali Sultana ta yi, tare da sakin murmushi mai kyau, ta wuce ciki, ta na shiga suka tafa,
"Yah Auwal da alama Aunty Sultana na yin ka hwa, ka ga wani murmushi da tayyi maka?"
"Allah ya sa, wannan murmushi halayyar ta ne, kowa ma yi mishi ta kai, Allah shi nuna min ta yi min irin wanda ni kai mata,....ke ci abinci?"
"Ameeen Yah Auwal, eh na ci abinci ,kafin Mama(Mai Buruji) ta tafi gida ta ban abinci, nima na kusan gamawa, wankin sultana kawai zan je in isuwa"
"Tau ya yi, In ke qare ki yi min magana, zan jira ki can garka, mu tai gidana, da kai na zan maishe ki gida, dazu na tai gida ai"
Nan ya bata labarin me ya faru tsakanin shi da Lamishi, idanun ta ne suka kawo ruwa ta ce,
"Ni dai dama baka tai ba wallah, yanzu ta na iya gwada min bone kan haka da kai, ya kamata ka rage kulawa da ni, tunda bata son haka nan"
Wani kallon baki da hankali ya mata, sannan ya duqa ya dauki kwandon wankin, ya dora Mata akai, ya tallabe qeyar ta cikin wasa, yar qara ta saki, ya mata gwalo ya tafi, tare da sanar da ita yana jiran ta, sultana da ke tsaye jikin window'n dakin ta ne,ta saki labule, ta na murmushi, su na burge ta sosai.
Har dakin sultana Mubaraka ta shiga, bayan ta yi sallama, ta bata izinin shiga, ita ta jera mata kayan inda ya dace ,sannan ta tambaye ta ko da abinda zata mata?
"Babu komai, amma ina so na tambaye ki,"
"Allah ya sa na sani"
"Inshaa Allah, kin ma sani, Ni kuwa na ce, ke da Auwal maman ku daya Abban ku daya?"
Da kallo Mubaraka ta bi Sultana........
Kallon da ya gajiyar da ni burutu😂😂
A GARIN MU
WRITTEN BY HAERMEEBRAERH
PAGE 19:
"Yaya na ne, uwar mu guda uban mu guda da shi, amma ya girme ni sosai, mu na da wasu qannen maza ne su, guda biyu,"
Ajiyar zuciya sulatana ta sauke, sannan ta yi murmushin ta da ke qawata kyaun fuskar ta ta ce,
"Masha Allah, makarantar ku guda da qannen naki?"
"Ai su Jameelu ba su zuwa makaranta,yawon su kawai suke a unguwa, duk gidan mu ni kadai ta ka zuwa makaranta"
Gyara zama Sultana ta yi, cikin rashin fahimta ta ke kallon Mubaraka da ke mata bayani,
"Yah Auwal ya yi karatun allo, har ya kai ga sauke qur'ani, kamar yanda na ji labari, amma ban taba jin labarin ya yi boko ba, zama da masu ilimi na ya sanya shi koyon karatu da rubutu, sannan ya iya turanci kad'an, amma bai je makaranta ba, ni kuma kin ga wadda karatun nawa shi ke, yau in an bar ni na tai, gobe ba zani ba,su Jameelu kuwa ba su ko son zuwa makarantar Allah balle ta bature"
"Ikon Allah, zan so zuwa shiyyar ku niga wadda take, watarana"
"Kai ka kaiii, lallai ko da mun ji dad'i mara misali, ace ke da kan ki kin tai shiyyar mu,ko ba dan matsayin da ki ke da shi ba ma, domin kyawun halin ki da kullum Umman mu ke fad'a a shiyyar mu"
"Mubaraka kenan, to ni din wata ce daban? Ni ma mutum ce kamar kowa na duniya, a duniya babu wanda ya fi wani, sai wanda ya fi tsoron Allah, yawan dukiya, matsayi, muqami duk ba su na mutum ba, tsoron Allahn da bawa shike da shi, da kuma kyakkyawar mu'amala su ka yin mutum, ke gane?"
Daga kai Mubaraka ta yi, sannan ta ce,
"Aunty in tambaye ki? Dan Allah kar ran ki ya ɓaci da tambaya ta"
Kada kai Sultana ta yi, sannan ta bada hankalin ta ga kallon Mubaraka.
"Aunty yaushe na zaki aure?"
Dariya ce ta kwacewa sultana , ta ce,
"Mubaraka kenan, ni da ko saurayi ban da wa zan aura?"
Zaro ido Mubaraka ta yi cike da mamaki, sannan ta ce,
"Aunty ko dai ke ta baki kula su? Ko ni din nan, maza na cewa su na qauna ta, balle ke, aunty Sultana ke gane ki kuwa? Wa zai ce ba shi son mace kamar ki?"
Murmushi kawai sultana ta yi, domin ita maganar ma saurayi ko miji bata gaban ta tun da can, a kullum damuwar ta be wuce ta ga yanda zata fara aiki dan ta koyar da al'umma abinda Allah ya sanar da ita ba, sannan ta bude gidauniya ta na taimakon mutane, to yanzu ta samu buri d'aya ya cika, wataqila za ta duba maganar aure a nan gaba, domin maganar lecturing da take son yi da alama ba zai samu ba.
Lokaci Mubaraka ta kalla, ta ga ya tafi sosai, har hudu da rabi,da sauri ta miqe tsaye,
"Subhanallahi, na manta Yah Auwal na waje ya na jira na, na tsaya surutu"
"Jiran ki kuma? Yanzu ki na nufin sai mutum kamar Auwal ya tsaya jiran ki? Namiji ne fa, ba su son jira"
Murmushi mai dauke da tsantsar so da qauna Mubaraka ta yi, sannan ta ce,
"Aunty Sultana, ina so ki sa ido akan Yayana da kyau, a hankali za ki san wane ne wannan Auwal din, Yah Auwal daban shike cikin maza"
A bakin qofa Sultana ta tsaya, dan sauraron Mubaraka ba ta san ma ta na bin ta ba.
"Zan sa ido na biyu akan Yah Auwal din ki Mubaraka, sai gobe, ki gaishe da Lamishi da jiki"
"za ta ji"
A gurguje ta fita daga katafaren gidan, a zaune ta tadda shi a saman kujera ya na bacci, tsinke ta samu ta saka masa a hankali a qofar hanci, ai kuwa atishawa ya saki mai qarfi, miqewa ta yi ta na dariya, daga baya ta kama kunnen ta ta na bashi hakuri, kama ta ya yi, ya daga hannu kamar zai mare ta, cikin wasa ya san daki kuncin ta kadan, suka yi wa masu gadin qofar gidan da ke kallon su cikin sha'awa sallama, suka fita.
Sultana bata bar jikin window ba har sai da ta daina hango su, fuskar ta dauke da annuri ta fada wanka.
A hanya kuwa Mubaraka ta kwashe duk yanda sukai da Sultana ta sanar da Lawwali, murna a wajen shi kamar har ta ce masa ta na son shi.
Ko da suka isa gidan shi, sai da suka ci suka sha, ta yi wanka, ta maida kayan da ta cire, suka dauki yar qarama kuma tsadaddar motar shi da gwamna ya sai masa, tunda yanzu ba ya cikin tawagar su ta daji,ya na buqatar mota, ko da fitar gaggawa ta kama.
A motar suka isa gida, kafin su shiga Mubaraka ta lallaba shi ya sai balangu mutumin Lamishi, har da kaza da madara, suka isa.
Ko da suka shiga gidan shiruuu, ba kowa, ajiye ledojin hannun ta tayi, ta lelleqa, ba kowa da gaske, to ina suka je? Ina ita Lamishi me jinya?
Tsaki ya ja, sannan ya zauna su ka hau hira, ita kuma ta duba ko akwai abincin dare, ko se ta ɗora, gani ta yi akwai a flask, da zai ishe su, na gidan gwamna ne, dan haka ajiye naman ta yi, ta ce in sun dawo daga duk inda suka je an ci.
"Ke da kissani? Ta na can yawon gulma"
"Yah Auwal ina fada maka ka dinga tausasa harshen ka ga uwayen ka, umma ka ke fadin ta tai gulma"
Irin abun nan ya yi na 'yan mata masu yanga, ya murguda baki, ya yi fari, shi a dole an masa fada.
Dariya ta yi, ta ce,
"Dama Aunty sultana ta gan ka"
"Ki na ganin duk mun ka hadu in yi mata haka nan? Za ta so ni?",
"Walle ba ruwa na, in tayi shiri shiri kwancin kwana ta shere ka mari, ka gan ka kuwa? Awab-budurwa wallah"(ba ruwa na in ta yi kwance kwance ta kwad'a ma mari, ka ganka kuwa kamar budurwa)
Dariya sukai ta yi, har Dan Talo ya shiga gidan a gaggauce, buta ya dauka dan zagawa, Lawwali na ganin shi,ya miqe ya daure fuska,
"Lawwali, ai na hango motar ka ne, muna dawowa daga garkar Yahai, nicce bari na zo, ko zan samu wani abu, bari na hito daga yauce, (bayan gida)"
Ya na fadawa bayi, Lawwali ya zaro dubu biyar ya ba Mubaraka Ya ce,
"Amshi ki ba uban nan nawa me kwadayi, in ya hito daga tutun wahala, ban jira nai wallah, na tafi nemo yaki halal yaki haram din da suka so"
Magana ya ke kamar da wasa, amma cikin zuciyar shi zafi take, a ce iyayen ka basu damu da inda ka ke samo kudi ba, kuma da ganin Lawwali sun san dai ba aikin jima yake ba ko kafinta, ko dako, balle aikin office, Amma kullum nema suke a wajen shi, kuma basu yake, manyan kudi ma kuwa, se kace wani babban ma'aikaci, ko babban ma'aikaci watarana ya na zama bai da shi.
Mubaraka da ke tsaye cikin tausayin Yayan nata ne ta amshi kudin, ta na so ta bashi ko da hakuri ne, dan ta san ya yake ji, amma ya fice, tun kan ta ce komai.
Dan Talo da ya fito ya ga ba Lawwali, a zaton shi ya tafi ne, nan da nan kuwa ya hau ashar, ya na kiran lawwali da sunaye marasa dadin ji.
"Gashi hwa, ya bar maka kuddin, ya dai tafi ne an kira shi ga waya"
Baki Dan Talo ya washe, ya na kuma godiya, soke su ya yi, a sassan aljihun jikin shi, sannan ya fita.
Girgiza kai Mubaraka ta yi kawai, ta na nema ma ahalin ta shiriya.
***********************
Su Lamishi kuwa su na gidan Isah, Yabbuga nan ta tattare su suka fada, har da Asshibi, yau ta samu leqa gidajen shiyya, duk gidajen mutuncin unguwar ba d'aya da Yabbuga ta raka ta, sai nasu ya nasu.
Qarshe da suka shiga gidan Lamishi suka gaisa shi ne suka rankaya gidan Hansatu gaba dayan su.
Sun tadda Isah na gida, sun gaisa su na ta wani hira kamar sun samu abokin su, kafin daga baya ya fada daki, da fita zai amma ya fasa,Hansatu kuwa ta gama