Showing 135001 words to 138000 words out of 155423 words

Chapter 46 - A GARIN MU HAUSA NOVELS BY HAERMEEBRAERH.docx

26 Oct 2025

451

inyamuri ya ce ya sanya koken cikin kayan Isah kamar yanda mun ka tsara, kuma an kama Isah, an kulle shekara goma zai yi a kurkuku,"

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'una, kaiii wanga yaro kwai baqin mugu, wato abokin naka ka ci wa amana haka? Shi na can daure ga hukumar da bata san sassauci ba, ka mayar min da d'iya ita da zaura (bazawara) ba su da banbanci, Allah ka isar min, Allah ka isar mana abinda yaran nan su ka yi muna"

Kuka sosai Hajiya take faman yi, a haka suka koma gida, Laminu na nan ana shirye shiryen miqa shi ga kotu, asirin shi ya gama tonuwa.

Tun a hanya Hajiya ta kira Hansatu ta ce ta samu abun hawa ta taho,ta wa driver waya ya kawo su Ameenatu gidan ta, cike da damuwa Hansatu ta ce to, bata so ta tsaya tambayar Hajiyan meke faruwa ta waya.

Rurrufe ko ina ta yi, sannan ta leqa gidan 'Yabbuga ta gaishe ta, ta sanar da ita zata gidan su,a hanyar ta ta zuwa bakin titi, ta wuce ta qofar gidan su Lamishi ta ga ana ta shiga da kayan gado.

Ga wata rumfa nan Dan Talo na ta bugawa a qofar gidan da kan shi.

A bakin gate din gidan su aka ajiye ta, ta shiga, bayan ta gaida mai gadi ta wuce cikin gidan.

A parlour ta tadda Yaya Musa da Yaya Abdullahi (Yayan matar Musa) su na zaune cikin jimami, su na ganin ta kowannen su fuskar shi ta sake danyancewa da tausayin ta.

Hajiya kuwa kuka ta sanya, ta dinga yafitar Hansatu da hannu, wajen ta ta nufa ta zauna daf da ita, ta na so ta yi kuka, dan ta san duk abinda ya sanya Hajiya kuka ba qarami bane.

"Hajiya mi ya faru? Mutuwa an kai? Me ya samu Aunty Azizah?"

Ta na fada ta na kallon Abdullahi, da sauri ya kada mata kai, alamar Ah ah,

"Lafiyar ta qlou, ta na Spain ma yanzu haka,"

"To me ya faru?"

Yaya Musa ne ya daure ya labarta mata komai, Hansatu kuka ta sanya, tare da fadin

"Ba zan taba yafe maka ba Isah, soyayyar ka ba ta amfanar da ni komi ba,ka cutar dani, ba iyaka, na hakura, amma sai da ka haɗa da mahaifiya ta, Isah me ta yi maka? In ni ce baka so sai ka sawwaqe min, me mahaifiya ta ta maka?......Hajiya, Hajiya, kin tuna sanda an ka sace su Ameenatu? Tabbas Isah na da hannu a wannan satar"

"Ahh ahh Hansatu, babu kyau zargi, dan kuwa wannan zargi ne, ba ki tabbatar ba"

"Hajiya ina da yaqinin da sa hannun Isah a wannan lamarin saboda tun sannan suke abota shi da Laminu, Hajiya akwai abubuwan da ban sanar da ke ba saboda bana so hankalin ki ya tashi, na dauki alqawarin tunda ni na bijire muku na zabe shi, komi ze yi min zan shanye ba zan fada wa kowa ba, Hajiya Isah na min......"

Nan dai Hansatu ta dage ta sanar ma da mahaifiyar ta komai da Isah yake mata, Hajiya da kowa da ke wajen ya tausaya mata,sannan sun mata faɗa sosai, musamman akan qin sanar da Hajiya tunda ya tafi wancan karon bai neme ta ba, ai da ta sanar tun a sannan da an dau mataki.

"Tau shi kenan yawuce ,Musa ai ka ga da rabon Allah shi hannunta shi can ga hukumar da sun ka fi mu iya hukunci, yanzu yanda za a yi, kai da Abdullahi,ku shirya ku je can wajen shi, ya sakar min d'iya ta, walle ta gama auren shi, ya qarasa shekarar shi goma ya bid'i wata ya aura, ina dalili.

In ya tsaya muku taurin kai, ku faɗa masa za ku yi qarar shi akan abinda ya yi wa hansatu a can, ku tsoratar da d'an nema, ya sake ta dolen shi, yarinya ta da kyawun ta ba zata rasa mashinshini ba"

Abdullahi ne ya kalli Hansatu da sauri, a zuciyar shi ya na ayyana abubuwa da dama, babban abinda ya sani shi ne, wannan karon ba me auren ta sai shi, ba zai bari ta sake kufce masa ba.

An tsaida magana a cikin sati na sama za su tafi zuwa saudiya, Hansatu kuwa ta ce ba za ta koma unguwar su ba, unguwar gulma, dan ta san yanzu magana ta karade unguwar, za a yi ta nuna ta da baki da ido ne.

Hajiya ma cewa ta yi ta yi zaman ta, ai kuwa ita da yara nan suka samu wajen zama abun su, tun daga ranar Hansatu ta samu abokiyar hira, haka zata zauna ta yi ta bawa Hajiya labarin abubuwan da Isah ke mata, Hajiya kuwa ta ce,

"Ke ko gama zama da baqin mugu,dan neman sallamamme kawai"

****************************

Da isar su asibiti, Hajiya Ikee ta ɗora idon ta akan yaran nata, sai ta fashe da kukan murna, fess ta gan su, wanda ba haka suka zata ba gaba dayan su, wani haske da sheqi ma taga su nayi, musamman Sultana.

Bayan sun gaisa ne, ta ja su har gaban gadon da gwamna yake kai, duk ya fada ya rame,sai gulu gulun idanuwa, bakin shi ya karkace hannu da qafar shi kamar wanda Inna ta taba,asibiti sun tabbatar da cewa ba shi da wani ciwo da ya danganci asibiti a yanzu,sai qarancin jini da yake fama da shi,kullum ana qara masa jini leda biyu zuwa uku, hawan jinin da ya kama shi ma ya sauka, tun da jimawa, sun yi gwaje gwaje sun rasa dalilin da ya sa yake a shanye haka, kuma jinin shi ke yawan qarewa.

Hajiya Ikee na gama basu labarin rashin lafiyar mahaifin nasu Sultan ya ce,

"Hajiya ai da wahala Daddy ya warke,ko da zai warke din ma, domin kuwa mutane irin shi na fama da cututtukan da ake rasa gane kan su ne sakamakon Allah ya isa da mutane ke yi musu, da za a ce za a tara duk mutanen da ya zalunta, su yahe masa, na miki alqawalin sai ya miqe, amma in basu yahe masa ba, zai wahala ya tashi "

"Innalillahi, na shiga uku ni Ikilima, ina zan saka rayuwa ta? Yanzu fissbillahi haka ka ke ganin ba zai tashi ba sai mutane sun yahe masa? To mu yanzu ina mun ka san adadin wanda ya zalunta?"

"Ba lallai bane kuma, ta yu Allah shi bashi lafiya, amma fa zai karbi hukuncin da ya aikata a ranar gobe, in dai be tuba ba"

"Yau na shiga uku na lalace ni ikilima"

Kuka sosai Hajiya Ikee ke yi, shawara Sultana ta kawo, akan su maida Gwamna gida a na maganin Islamic, saboda yanzu kusan watan shi biyu a kwance, komai sai an masa, Hajiya duk ta rame,

"Ai dole gida zamu kai shi, in kunka ji kuddin da asibitin ga ke karba duk kwana guda sai tsoron Allah ya kama mutum, gwamnan da an ka mayar yanzu so guda ya taho da tawagar shi sun ka duba Daddyn ku, da 'yan jarida, akai ta hotuna da video, ko sisi basu bamu ba, amma sun ce sun basuwa kuddin jinya har ya  ji sauqi, kuma ga shi asibiti kullum ni ka biyan kuddi"

"Hummm Mum kenan, a bar tone tone, mu samu yanzu a kama muna shi mu tai gida"

Bayan komawar su gida ne suka sha kallon ikon Allah, gwamna banda ihu da shure shure ba abinda yake, abun ya yi matuqar basu mamaki,Sultan ne ya ce su fitar da shi waje, ai kuwa ana fita waje ya dena ihun, sai zare ido kawai yake, da jin tsoron kar a maida shi ciki.

"Sultan mu tai gidan mu na can titin zanna, wataqilan nan ne bashi so"

"Bamu da wani gida da ya yi saura sai wanga, dan kuwa duk na bayar, anjima ma za a taho amsar makullai,nan din dai zamu koma, dole ya yi hankuri,"

"Yau na shiga uku na lalace ni Ikillma, kai wa Allah ku bamu makullin guda, wanda ka bawa wancan su amshi wanga"

"Muka san menene acikin gidan da za mu ba wa wasu shi? Mu din dai mu za mu shiga,koma menene ku ne kun ka jawo muna, dole a haka zamu shiga mu zauna da koma me ne ne a ciki"

Sultana ta kula da cewa ran Sultan ya fara ɓaci, abinda bai taba yi da iyayen su ba kenan, bayyanar da bacin ran shi irin haka, su kafe ya kafe, dan haka shiga maganar ta yi,

"Hajiya mu shiga sai a nemo mallammai masu ruqiyya su taho su taimaka muna, ko ya ka ce Yah Sultan"

Dauke kan shi ya yi, sannan ya ce,

"Ku shiga ciki, bari na shiga gari na samo malamin da zai zo a hwara tun yanzu, makullan gidan su na cikin safe din Daddy, ki bude ki basuwa in an zo amsa"

"Toh sai ka dawo"

*Ku taimakawa  gwamna Halliru da malami me ruqyaaa*

💅🏻 *A GARIN MU* 💅🏻

BY HAERMEEBRAERH

PAGE 60:

Sultan ya yi yawo, iya yawo amma bai samu dacewa da malami ko guda d'aya da zai taimake su ya je ya yi wa Gwamna Halliru ruqiyya ba, wanda suka amince za su je kuma bai gamsu da kalar tasu ruqiyyar ba, dan kuwa cewa suke aljanun yanka suke so a musu su sha jini, za su rabu da shi, (da damar masu cewa su na cire aljanu da yanka, ko kuma aljani ya fadi buqatar shi a masa sanan ya fita, ba rugiyya suke ba, domin ba haka ake ruqiyya ba a sunnar Annabi Muhammad ,bai bamu umarnin yi wa aljani hidima ba, kar fa mu manta Allah ya daukaka mu sama da su, kuma cutar da mu suke saboda ba ma ganin su, amma kuma a dinga musu hidima? Ko a je wajen su neman taimako? Duk wanda yake haka ya sabawa Allah, in bai tuba ba Allah zai kama shi, ko ya azabtar da shi kamar yanda gwamna halliru ke shan wahala a hannun su, ya nemi taimakon su ba na Allah ba, su kuma a yanzu suna azabtar da shi, saboda abinda ya kasance ya na aikatawa).

Da kyar ya samu wani malami guda ɗaya da ya amince zai je ya ga Gwamnan, amma sai da yamma, bayan ya sallami d'aliban shi da ke d'aukan karatu a wajen shi.

Sultan ya koma gida a gajiye, tun daga gate ya ke jiyo kururuwa da ihun gwamnan, gidan shiru, ba wata hayaniya, dan kuwa duk ma'aikatan sun gudu, mai gadi ne guda d'aya kawai ya rage, shi ma dan bashi da wajen zuwa ne, ya sa ya ke zaune a nan din.

Da shigar Sultan gidan, Sultana ta tunkare shi, idanun ta sun yi luhu luhu, saboda kukan da ta sha ta qoshi, ganin mahaifin nasu a cikin mawuyacin halin nan ba qaramin tashin hankali bane a gare ta, ko ba komai, ya gwada masu soyayyar da bata da misali.

"Yah Sultan ya na gan ka kai d'ai? Suman Daddy uku bayan tahiyar ka, na rasa me zan masa ya samu sauqin abinda yake ji"

Kuka ta fashe da shi, saboda tsananin tausayin mahaifin nasu, sultan ne ya kama hannun ta, idanun shi sun yi jajawur, ya ce,

"Mu je ciki, ki dena kukan haka nan, kukan ki ba shi zai bashi lahiya ba,daddy addu'a shi ke buqata, mu tai a samu a kunna karatun Alkur'ani kahin mallam ya taho, dan ba yanzu ne zai taho ba, sai yamma"

Cikin ikon Allah kuwa ana kunna masa karatun Alkur'ani bacci mai dadi ya dauke shi, zama suka yi jingum jingum su na kallon shi, kowannen su da abinda yake saqawa a zuciyar shi.

Hayaniya suka jiyo sosai, daga wajen gate din gidan, a tare suka tashi suka nufi waje, Hajiya babu ko mayafi, daga ita sai leshin jikin ta da d'ankwali, Sultana kuwa tun da suka je bata cire mayafin ta ba, haka suka fita.

'Yan jarida ne sun kai su takwas a qofar gidan, sai roqon mai gadin suke ya bar su su shiga daukan rahoto.

Su na ganin iyalin gwamnan kuwa suka hau daukan su hoto, tare da qoqarin yi musu tambayoyi, tambayoyin kuwa sun matuqar sanya Sultan da Sultana jin nauyi da kunyar amsa su, tambayoyi ne wanda  da suke tattare da  gaskiya, amma kuma ba za su iya amsa su ba kai tsaye.

Dan haka Sultan ya musu izinin shiga,kamar jira suke, cikin turereniya da rige rige suka shige gidan.

Zama Sultan ya yi a saman kujera da ke a farfajiyar gidan, sannan ya ce,

"Tambayoyin duk da kun ka yi muna, sun nuna cewa wasu daga cikin 'yan jarida musulmai ba su san amfanin aikin jarida ba ga rayuwar su, ta duniya da lahira, domin kuwa da damar su su yad'a labarin da zai jawo su yi suna, ko su samu wata daukaka ta duniya, ko arziqi shi d'ai suke bid'a, ba labaran da za su gyara, kuma su taimaki al'umma ba,misali, yanzu kun taho ku na so ku ji mi na na ya sami tsohon Gwamna, kun taho da list din zargin da mutane ka yi akan shi, me ya sa sanda shi na kan mulki, ba ku zuwa dan taimaka masa wajen yi mishi tambayoyin da za su sa ya yi aiki dole? Ko ku na nufin ba ku da wadannan tambayoyin tun gabanin ciwon shi?

To Bari na baku amsa, amsar da na ke so ku yad'a ta a duniya kowa ya ji, da farko dai dole ne mu san cewa duk abinda ya ke faruwa gare mu a wannan qasa, da wannan yanki,na harikar kidnapping, da kashe kashen rayuka, da sace dukiyoyin al'umma, ba komai ya jawo mana ba, sai sab'awa Allah, daga mu har shugabannin mu, domin kuwa Allah ya ce,

"Wancan ne, haka abin yake, lallai Allah bai kasance yana canza wata ni’ima da ya ni’imta akan wasu mutane ba face har sai sun canza abin da yake cikin rayukansu, kuma lallai Allah mai ji ne, kuma masani.”

(Suratul Anfal: 53)

Kenan mu na da laifi wajen barin tafarkin gaskiya, da annabin mu ya dora mu akai, mun qirqiri sab'on Allah kala kala, a jihar nan ne matasa da basu da ilimi, ba su da aikin yi ke sata, suke shaye shaye, su ke kisan kan mutane, su ke garkuwa da 'yan uwan su mutane, su ke tsafi, suke zina, suke luwadi, suke mad'igo, ba kalar zunubin da ba a aikatawa, to ku na tsammanin Allah ya kauda kai akan abinda ake yi? Ba daban Allah me rahama bane ba ma ku na tunanin yanzu da akwai wata halitta da ta yi saura a duniya?

Allah ya na cewa a cikin qur'ani mai girma

"Ka ce, Shi mai iko ne akan ya aiko da wata azaba a kanku, daga samanku, ko kuma daga karkashin kafafunku, ko kuma ya rarraba ku qungiya-qungiya, kuma ya dandana wa sashen ku masifar sashe (ma’ana: wasun ku su addabi wasu). Ka duba yadda muke sarrafa ayoyi, tsammaninsu suna fahimta.”

(Suratul An’am: 65)

Sannan Allah ya ce,

"Barna (musibu da fitintinu) sun bayyana a cikin qasa da teku (a ko’ina), saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah (yana nufin) ya d'and'ana masu sashin abin da suka aikata, tsammaninsu za su dawo kan hanya (su daina laifin da suke yi, su tuba).”

(Suratur Rum: 41)

Da Allah ya so da ya halakar da mu gaba daya kamar yanda ya yi wa wanda suka gabace mu, amma ya jinkirta mana ya na nufin Mu tuba, shin baku da labarin al'ummar da ta gabace mu ne? Wadan da Allah ya halaka saboda sun saba masa?Allah ya ce a cikin alqur'ani mai girma.

"Kuma da Allah yana kama mutane saboda dukkan abin da suka aikata (na zunubi, kuma ya zamanto baya yafe wani), da bai bar wata dabba ba a bayan kasa. Amma yana jinkirta masu zuwa wani ajalin da aka ambata. Sannan idan ajalinsu yazo, to, lallai Allah ya kasance mai gani ga bayinsa.”

(Suratu Fadir: 45)

Amma sai Allah ya ke hankuri da mu, ya ke yahe muna da mun roqe shi gafara, sannan Allah ya ke jinkirtawa wanda suka qi roqon gafara, dan in sun je gare shi ya musu azaba kwatankwacin abinda suka kasance su na aikatawa, ba dan ba zai iya kama mu ya azabtar da mu a duniya din ba ne.

Da mu da shuwagabannin mu sai mun koma ga Allah za mu ga dadai, an riga an kashe matasan mu, ba ilimi, ba sana'a, ba kasuwanci, zaman banza ya yi yawa, mutum naso ya saka sutura ko ya ci abinci, ko ya samu abun hawa ba shi da ikon yin hakan, in ba shi da cikakken imani sai ya je zuwa neman kuddi ta kowacce hanya, me kyau da mara kyau.

Ina mana nasiha mu ji tsoron Allah a duk abinda muke aikatawa, akan duk wani muqami komai qanqantar shi da Allah ya bamu, saboda wasun mu daidai da muqamin kwasar tutu mutum ya samu, buri nai shi cutawa na qasa da shi,ba tausayi, a tsakanin mu, ba soyayya a tsakanin mu, balle jin qai.

Ina fatan na amsa dukkan tambayoyin ku a wannan jawabi nawa, mu ahalin Gwamna Halliru Murtala Gusau, mu na roqar mishi yafiya daga wajen mutanen da ya yi wa mulki ba daidai ba, mu na roqon ku da ku yafe masa, domin Allah, kar ku diba abinda ya shiga tsakanin ku da shi na rashin adalci ko kyautatawa, ku dubi Allah ku yafe masa"

Duk dauriya irin ta Sultan a daidai wannan gabar sai da ya fashe da kuka, saboda ya sani, ba lallai ne mutane su yafe wa mahaifin nasu ba, sannan in masu redio da talabijin sun saurara ko kuma sun kalla, to wanda suke a qarqashin mulkin shi da ba su da kafar sadarwar fa? Wanda suka mutu fa? Wanda shi ya kashe su da hannun shi fa? Ta yaya za su yafe masa bayan ba su da rayuwa.

Kukan shi ne ya tsananta, har ya sanya 'yan jaridan da kan su suka janye abun maganar daga gare shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login