Showing 24001 words to 27000 words out of 48692 words
Chapter 9 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
inganta ba, ko Allah ya
sauki Safiyyah lafiya, a lokacin da take
goyon cikin. Ance ba’a fushi da iyaye, amma
hakika Zayyan ransa ya sosu sosai da
attitude din mahaifiyarsa, abunda Mama
Fatu tayi ga iyalinsa bai taba zaton uwa
zata yi shi ga dan data haifa ba. Har
hakan yasa ya dan dauke kafa daga
Katsina, na dan wani lokaci.
Ya maida hankali ga taya su Sabah
kula da lafiyar Sophie, su su kula da ita
daga safe zuwa dare, shikuma ya yi nasa
jegon daga dare zuwa safe.
143
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A lokacin da Sophie take jegonnan
ne kuma ya fahimci wani abu a halittarsa,
wato jikinsa baida jimirin hakuri da
rashin matarsa na lokaci mai tsaho.
Kusan kullum Safiyyah na barci
irinna masu jego, shi kuma yana fama da
shan ruwan kanwa, domin kwantar da
sha’awarsa ta da namiji, kwarai ya kan
gaza hakuri da ita cikin dare, baya kuma
son ketare iyakar Ubangiji don har
lokacin jinin biki Safiyyah take yi.
Ga Safiyyah da kunya, ire-iren
hanyoyin nan na kwantar da hankalin
miji a yayin biki ko al’ada nauyinsu take
ji, wani irin nauyi abun yake yi mata,
sosai take jin kunya in ya nuna mata irin
abubuwan da yake so tayi masa wadanda
su kadai zasu iya kwantar da hankalinsa,
duk kokarinsa na fahimtar da ita shida ita
babu sauran kunya ta wannan fannin,
shekara goma ba wasa ba, ta bude idonta
suyi irin rayuwar data dace dasu amma
Safiyyah kunya da nauyi da gidadanci
144
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
basa barinta, irin dai upbringing na gidan
manya data riga samu da kuma rashin
good socialization da zai bata damar
samun exposure akan kula da miji, ko irin
‘yan karance-karancennan na zamani da
ake daukar ilmin rayuwar aure a cikinsu
Safiyyah bata yi. Kaidai barta a
karance-karancen da zai zurfafa ilmin ta
na Architecture.
Ganin karatun hikayoyin soyayyah
take a matsayin bata lokaci ko rashin
tarbiyyah. Not because she doesn’t love
him. Amma ta gaza sanin hanyoyin kula
da bukatunshi na aure yadda ya kamata,
alhalin karshen duk wani so da
soyayyarta ta diya mace a duniya tasan na
mijinta Zayyan Rafindadi ne.
A’ah ita dabi’arta na kunya,
russunar da ido, da kana’a, nature dinta
ne da Allah ya halicceta dasu tun fil azal,
kunya da kawaici da rashin zaqewa akan
sexual relationship dinsu. Komai shi yake
yi a gadon aurensu. Ita saidai ya barta
145
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
dasu rufe ido da ji masa kunya, da kiran
sunansa. Wannan ba zai zamo abun
mamaki ba, in aka yi la’akari da irin
(decent upbringing) din da Safiyyah ta
samu a gida. Har Sophie ta yada wanka Zayyan
bai je Katsina ba, ya kuma gama shirya
surprising dinta da tarewarsu a sabon
gidansu dake cikin shahararren Estate
dinsa da ya kammala, wanda sai yanzu
Allah yayi kammaluwarshi, watau
SUNSET ESTATE, Estate dinsu shida
Safiyyah dake GUZAPE. A ranar data
yada wanka wato ranar da ta kwana 40
da haihuwa ya shirya komawarsu gidan.
Cikin ikon Allah a ranar sai ga
mahaifinta Malam Usman da kansa a
gidansu ranar da suke shirye-shiryen
tashi. Haroun ya kawo shi har Abuja tun
daga Dandume, a motar Haroun din. Nan suka shiga hidima da bakuntar
babban bakonsu Malam, Zayyan da
Safiyyah da su Sabah kowa hidima yake
146
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
da zuwan Malam, su dora wannan
tukunya su sauke wannan, ana wadata
malam da cimaka ta alfarma. Ya wuni sur
tare dasu cikin kauna da soyayyahr Uba
mai girma, ya yi musu nasiha da wa’azi
sosai akan muhimmancin karbar
jarrabawar Ubangiji kowacce iri ce,
komai dacin ta, da ribar dake cikin hakan
watarana.
Ya tunasar dasu tanadin da
Ubangiji yayiwa iyayen da suka haifi da
ya koma. Tare dashi aka tare ranar da
yamma SUNSET ESTATE. Ya kwana tare
dasu a sabon gidan a ‘guest wing’ Haroun
kuma a hotel ya kwana, kusan kwanan
zaune sukayi ranar suka raba dare a falon
Safiyyah shida Zayyan da Safiyyah, yana
mai basu sirrin addu’oin neman biyan
bukata, abinda ya tadowa Zayyan kewar
Baba Bello. Suka kasa tafiya suje su
kwanta har asubah suna like da Mallam.
Zayyan ya kara jin kansa maraya
sosai da soyayyar da Malam kema
147
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah, sai yanzu yafi jin kewar Baba
Bello, ya san da Baba yana raye da
abubwan dake faruwa da yawa basu faru
ba, da tuni shi da Safiyyah sun ga gata a
wannan haihuwar tasu, da kauna da
tattali, a wannan lokacin da ba abunda
suka fi bukata fiyeda kaunar iyaye da
support dinsu.
Tabbas da Baba Bello na raye, ba
zai watsar masa da iyali yadda Mama tayi
ba, alhalin tana ikirarin tana sonsa tana
kuma kaunarsa, a matsayin tilon dan data
haifa namiji ta kasa taya shi son iyalinsa.
Sai yaji idanunsa sun kawo ruwa da
hamma a lokaci guda, har Malam ya lura
yace su tashi su je su kwanta haka.
Da malam zai koma a washegari
yace tunda Safiyyah ta yada wanka, ta
kuma samu lafiya zai wuce da Sabah da
Rayyah Dandume.
Karon ta na farko da sake haduwa
da Haroun kenan, tun bayan aurenta da
yazo washegari daukar Malam zasu wuce.
148
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Gabadaya Haroun din Malam ya canza
mata, ya zama babban mutum, Haroun
ya samu cigaba sosai ta kowanne fanni na
rayuwarsa, harkar danyen man fetur
yake yi yanzu da ‘Dangote Refinery’,
saboda abinda ya karanta kenan a
jami’ar Maiduguri wato (Petro-chemical
Engineering).
Bayan gaisuwarta da Haroun ya
amsa ya kuma yi mata ta’aziyyah bai bar
wata kalma ta kara shiga tsakaninsu ba.
Bai ko kalleta ba, abin ya tsaye mata don
kuwa Haroun a can baya yafi kowa shiga
sha’aninta ita ke basar dashi. Sanda akayi
aurenta kuma ya koma Nsukka yana hada
kwalin karatunsa na biyu kuma tun
bayan aurenta in zata iya tunawa Haroun
bai taba kiranta a waya ko sau daya ba.
Al’amarinta da Yayanta Ridhwan
(Yaya Shaikh) shi yafi komai bata
mamaki akan na Haroun din Ammi, don
in Haroun kishi yake tayi aure ta barshi,
alhalin an san yana sonta tun tana
149
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
karama, itama kuma ta san yana sonata
koda bai taba furta mata ba. To Yaya
Shaikh kuma fa?
Kalmar so ko kwalli daya bata taba
gittawa a tsakaninta dashi ba. Gara
Haroun zata ce hatta Ammi ta sha gaya
mata son ta yake yi, tun tana karama,
amma yana kallon kansa a wanda bai isa
ya aureta din ba, kasancewasa almajiri ga
Mallam.
A wannan zuwan da Malam yayi ne
yake gaya mata cewa anyi auren Yaya
Sheikh a Doha (Qatar), ya auri wata
Shuwa Arab haifaffiyar Maiduguri da
suka hadu a karatu mai suna Assafe. Da Malam yace zasu tafi tare dasu
Sabah Zayyan ki yayi, don yaga yadda
zaman nasu ya zamewa Safiyyah abin
debe kewa, bata shiga damuwa da tunani
saboda kullum suna gefenta suna
kwasarta da hirar Ammi, sai ya shigo
falon suke musu sallama su shiga dakinsu
data basu. Don haka zamansu tare da ita
150
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ya taimaka ainun wajen dawowar
walwalarta.
Sai ya roki Malam alfarmar ya bar
su Sabah su cigaba da zama tare dasu
zuwa bayan sallah, don a lokacin an kusa
shiga watan Ramadan saura sati guda
wata mai alfarma ya kama. Da kyar Malam ya yarda ya barsu,
amma yace sallah da kwana uku
lallai-lallai ya gansu sun dawo Dandume.
Malam da Haroun suka kama
hanyar komawa Dandume washegari.
Kulawar mijin kwarai irin Arch. Zayyan
Bello Rafindadi, da addu’ar caring iyaye
masu riko da addini irin nata, sun
taimaka matuka gaya wajen dawowar
nutsuwar Safiyyah, bayan rashin IVF
babyn da suka yi. A kullum yana
karfafata da cewa “data haihu, da bata
haihu ba shifa yana sonta a haka, she will
forever remain his ALTER EGO,
151
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sa’annan the only partner da yake son ya
rayu da ita a duniyarsa da lahirarsa.
Ba wani abu wai shi rashin
haihuwa da zaisa ya juya mata baya. Yana
rokon Allah ya taya shi akan hakan. Shi
ita ya aura ba abinda zata haifa masa ba
da baima sanshi ba. Cikin kalaman sa na koyaushe
Zayyan ya kan ce mata “koda zasu mutu
basu haihu ba, bazai taba amfani da
hakan ya wulakantata ko ya goranta mata
ba, ko ya juya mata baya ba wai dalilin
rashin haihuwa. Ire-iren kalamansa masu dadi
kenan da suka taru suka farfado da
Safiyyah, ta soma komawa harkokin ta na
yau da kullum, bayan rasa dan da suka
haifa ta hanyar Dashe (IVF). A wannan gabar ne kuma bayan
dawowarsu SUNSET ESTATE Zayyan ya
bata gwaggawaban jari, yace ta soma
business din duk da take so, duk don ta
152
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kwantar da hankalinta, da kokarinsa na
faranta mata, a bisa wuyar data sha
wajen samun ciki da haihuwar In Vitro
Fertilized Baby dinsu, wanda ya kira da
suna a cikin zuciyarsa “Areef”. ***** ***** ****
Kudin project din wani Estate da
yayiwa gwamnati ne ya fito a goman
karshe na watan Ramadhan, ya samu
kudi masu kauri a hannunsa, aljihunsa
yayi nauyi sosai. Abinki da Da nagari, ba
wanda ya fara tunawa as usual idan ya
samu kudi masu kauri a lokacin sai
mahaifiyarsa, Mama Fatu.
Tuni ya manta da bacin ran da
Mama ta saka shi a ciki watanni kadan
baya da suka gabata, don shi duk wata
nasararsa a rayuwa, yana fara dangantata
ne da iyayensa. Don haka sune na farko da yake
tunawa idan alkhairi irin wannan ya same
153
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
shi. Yayi ma Baba Bello Sadaqah sannan
yayiwa Mama Fatu hidima. Gashi ya jima
bai je Katsina ba yayi kewar Mama. Don
haka ya samu Safiyyah har daki yake
gaya mata cikin farin ciki. “Sophie kina ina ne? Zo daga kusa
ki ji?”
Ta fito daga daki tana daura kallabinta,
“gani nan Habiby, wani abu?”
Suka game a karamin falonta, da
rabi-rabin runguma, saboda ya taho da
sassarfa ne itama ta fito da sauri, ya riko
kugunta ya zagayeta da hannayensa biyu
yana murmushi irin na namijin da
aljihunsa ya cika da albarka a gaban
iyalinsa. Yace ma Safiyyah.
“Wannan sallahr so nake zan
gwangwaje Mama da wani abu mai
daraja, wane kaya ne na kwalliyar mata
suka fi kowanne daraja?”
Safiyyah na murmushi ta sakalo
hannayenta a wuyansa itama, tace “Gold!
154
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
(Zinare). Shine karshen kwalliyar mata
mai daraja”.
Yace “to Alhamdulillah. Zan
sayama Mama sarka da dan kunne da
zobe da warwaro na zinare don in
gwangwajeta ba zatonta. Na san Mama da
son kwalliya. Kudinnan dana gaya miki
inata jira su fito na project din Bwari, yau
sun fito cikin ikon Allah.
Yace “bana taba manta wata sallah
ina dan shekara goma. Baba yazo bashi
da kudi isasshe a hannunsa, yace iyalinshi
mu hakura da kayan sallah, saboda ya
samu yayi wasu abubuwan muhimmai da
‘yan kudin hannunsa. Mama sai tace “ai ba komai
Babansu, Allah ya dada rufa mana asiri
Baban Baffa.
Sai ta dauki sarkarta ta zinare ta
siyar, tayi mana kayan sallah, ta baiwa
Baba ragowar kudin tace,
155
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“kayi duk hidimarka da sauran
kudinnan Babansu Baffa”.
Tun lokacin abun ya tsaya min a
rai. Don naga wani irin feeling na godiya
da bazan taba mantawa ba a fuskar Baba
ga Mama. Na kudurce nikuma sai na biya
Mama ‘gold’ dinta duk sanda Allah ya
bani gwaggwabar dama. Ya rubuta cheque na kudi masu
yawa ya baiwa Safiyyah wadanda har
saida suka bata tsoro, yace “Sophie, so
nake Mama na tayi gayu da babban
Zinare, ta fito kamar tauraruwa Zahra a
cikin mata a wannan sallahr”. Safiyyah ta karba tana jinjinawa
halarcin Zayyan akan son iyayensa, tace
“amma Habiby, tare da kai zamuje mu
zabo ko? Yace “a’ah ni mace ne? Ina
nasan design mai kyau? Kawai kije ki
zabo, sannan ki sayawa su Zahra suma
duka kanana da bai kai na Mama girma
156
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ba. Da kuma amaryata Sabah da kanwata
ta kaina, Rayyah”.
Nan suka zauna bisa doguwar
kujera three seater, yayi mata bayanin
yadda yakeson na kowa ya kasance, da
sauran mutanen da zasu yiwa kayan
sallah a cikin kudin bayan sakon Mama,
dama duk shekara ya saba hakan, ‘yan
uwanshi kaf da nata, da iyayenta da nashi
babu wanda baya yima kayan sallah na
gani na fada. Kai hatta dan almajirin
gidansu Safiyyah wani yaron dake zama
gidansu yana zuwarma Ammi aike mai
suna Saminu, ya shaida soyayyar Zayyan
ga ahalin Safiyyah, don duk shekara
bandirin shaddah baya wuceshi shima,
duk sallah karama Zayyan bai mantawa
dashi. Balle kuma kannenta uku, wato
Sabah da Rayyah da Rayha, koda ba’a
hannunsu zasu yi sallah ba ya maida yi
musu kayan sallah cikin obligations dinsa
(hakkinsa), tun bayan dawowarsu Abuja.
157
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sosai Safiyyah ta yi masa addu’ar
karin budi da nasara cikin al’amuransa,
tayi godiya yadda ya dace macen kwarai
ta godema mijinta in yayi hidima ta
bajinta irin wannan, ta kuma kara
alfahari da Habiby dinta domin ya cika
dan halas din da kowacce Uwa zata yi
fatan haifar mai kaunarta da yi mata
halarci kamarshi.
Baya taba iya yin dogon fushi da
Mama Fatu (no matter how) yadda zata
bakanta masa da halinta.
A kullum fatanta shine na samun
‘ya’yan da zasu yo gadon wadannan
nagartattun halayen nasa, Zayyan Bello
ya cika dan halas, uwa da ubanshi babu
sama dasu a komai, tana addu’ar Allah ya
bata ‘ya’ya daga gareshi su gado komai
nasa, itama su ji kanta a tsufanta, ko ba
don bata da shi ba.
158
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A washegarin ranar suka je wani
dankareren shagon zinare suka zabi latest
design na set din wani white gold saukar
jiya-jiya daga Dubai. Ya lashe miliyoyin
kudin da Zayyan ya warewa Mama har
da dori. Ta kuma sayawa sauran
kannensa dan kunne kowacce yadda yace
tayi. Sannan suka zarce kasuwar Wuse
market tayi siyayyar komai da ya lissafa
mata na kayan sallar jama’arsu,
karkashin rakiyar kannenta su Rayyah,
kaya ta zabowa su Zaitoon na gani na
fada, masu tsada da quality, ta hada ma
Mama da saitin turarukan (Aventus for
Her) da ya taba gaya mata cewa dashi
kadai Mama Fatu take amfani a matsayin
nata neman albarkar, ta sayi wani
tsadaddden akwati dan karami mai kyau,
ta zauna ta jera turarukan nan da saitin
(white gold) din a cikin akwatin gwanin
ban sha’awa sukayi kyau a cikinsa. Kai
159
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kace wata yarinya budurwa za’a kaiwa
toshin sallah.
Sannan ta siyowa dukkan
kannenshi da kannenta kaya kamar
yadda ya tsara.
Da Zayyan ya dawo gida ta nuna
masa sayayyar duka tayi masa bayanin na
kowa, yayi murna sosai da ganin sakon
Mama da kannenshi, ya jinjina ma
fasaharta da iya zaben design din zinare.
Amma yana bude na su Sabah ya dauki
atamfar yana juyawa a hannun shi, ko
daga kalarta da rashin nauyinta ya san
bata fi atamfar dubu takwas ba, ya dubi
Sophie sama da kasa ya hade rai yace.
“Safiyya menene haka? Me kike
nufi da hakan?”
Hankalinta ya tashi, ta dauka wani
abu ne tayi masa ba daidai ba, sai taji
yace yanzu don me zaki siyowa su Sabah
160
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kaya masu