Showing 3001 words to 6000 words out of 48692 words
Chapter 2 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
har ya zamar mata tamkar
‘desperation’ ba tareda sanin Zayyan
ba, don ba kowanne lokaci damuwar
20
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
take zuwar mata ba, musamman in suna
tare, sai idan ta kadaice ko tana tare da
danginsa. Na yau ne kadai Allah yasa ya
ritsa da dawowarsa.
Don haka Zayyan yau ya sha
mamaki don bai taba ganin Safiyyah
cikin wannan yanayin ba, jage jage da
hawaye gashin kai a hargitse zaune
dirshan a tayal din toilet. A saninsa
matarsa Safiyyah macece jaruma, mai
tawakkali kuma, da iya shanye damuwa
komai girmanta.
Da kyar ya samu ya lallabi Safiyyah
ta daina kukan amma ta bullo da
sabuwar rigimar cewa dole suje asibiti a
binciki lafiyarsu. Tace duka tsararrakin
aurenta daga mai ‘ya’ya uku sai mai
biyu. Hatta Zaitoon da Zahra da aka
aurar a bayan bayanta sun haihu
wannan shekarar.
Zayyan sai ya fara harzuka, ya dago
da mamaki ya dubeta, yace.
21
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Safiyyah ban fahimce ki ba,
haihuwar abin competition ta koma? Ko
kuwa don ace kema kin haihu kikeson
haihuwar?
Ban sanki da haka ba sam. Kada
shaidan ya samu gurbi kuma. Don idan
don dayan biyun wannan ne kike son
zuwa asibitin, to ni ba inda zanje, sai
kije su rakaki inda aka basu nasu
maganin haihuwar ki karbo naki”. Haka suka kwana a ranar
baram-baram kowa zuciya a kusa, a
ganin Safiyyah Zayyan bai damu bane
sam da rashin haihuwarsu, saboda bashi
ake yiwa habaicin yana cika masai da
kashi ba. Rashin nuna damuwar tasa akai ya
kara ninka tata damuwar, don a ganinta
damuwar ba tata bace ita kadai, tasu ce
su duka, inda alkawari.
Haka ya jefa filo akan center carpet
na dakin barcinsu yayi kwanciyarsa ya
22
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
rabu da ita. Yanata sake-sake a ransa.
Ko dai wani yayi musu labe ne yaji
kalaman Mama Fatu shine yazo ya
tseguntawa Safiyyah ta waya ya daga
mata hankali? Kalmar Mama ta ‘bakarariya’ ko
shi tayi masa babu dadi.
Yana wannan tunanin ya ganta ta
cikin dan hasken dim light din dakin, ta
mike a hankali ta shige toilet, ta dauro
alwallah ta fito, ta canza sutturar jikinta
daga rigar barci zuwa hijabin sallahrta,
ta shafa turaren ‘musk’ a hannayenta. Safiyyah ta fuskanci gabas ta tada
sallah.
Yana daga cikin manyan dabi’un
Sophie dake burgeshi. Suke kuma kara
mata matsayi a ransa. Cikin halin farin
ciki ko akasinsa, bata bari shaidan ya
jagoranceta ko ya rinjayeta tayi wani
abu ba daidai ba. Tafi gane tayi sujjadah
ta gayawa Allah kukanta.
23
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Haka yaga ta raba dare a kan abin
sallarta, shima kasa barcin yayi, yana
jin tsigar jikinsa na tashi da kukanta,
tana kuka tana yiwa Allah kirari, tana
kambama shi cikin sujjadarta ta hanyar
kururuta girman izzarsa da buwayarsa,
cikin rokonsa itama ya bata haihuwa,
kamar yadda yake baiwa daukacin
bayinsa. Ta san ba wai ya manta da ita
bane”.
Daga kwancen da yake Zayyan ya
tayata amsawa a ransa da;
“Ameen, idan alkhairi ce a garemu
da addininmu Safiyyah Allah ya
bamu!”.
Ganin yau bata da alamar sanya
hakarkarinta a katifa har goshin
asubahi, balle kuma yasa ran zata bi ta
kansa, yanzu tafi son samun ‘ya’ya
akansa ma kenan, humm. Mata
iyayenmu!
24
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Hakan yasa ya ji kishi a ransa na
ko ta haihu ‘ya’yansu zatafi so a kansa.
Duk kulawar da take masa kansu zata
koma. Shi kuma ta rage kulawar da take
bashi, haka ya hakura yayi barcinsa ya
kyaleta yana tunani mara hujja. Ya
manta ko inji ne yana son hutu
musamman idan bashi da service.
Washegari suna karya kumallo ya
daga kai daga kurbar tea kadan ya
dubeta da kulawa, sai yaga duk ta zabge
a dare daya, saboda daurawa kanta
damuwar da ya kira ta babu gaira babu
dalili. Yaga cewa shi dai a karan-kansa da
bakinsa bai taba cewa “Sophie, meyasa
baki haihu ba har yanzu? Ko sai yaushe
zaki haihu min? Ko me ya hanaki
haihuwa, ko ni Zayyan ina son haihuwa”
ko ire-iren accusations dinnan marasa
dadi makamancin wadannan da ake
yiwa wadda ta samu jinkinrin haihuwa
koda wasa bai taba hadashi da ita ba, to
25
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
na menene zata bi ta damu kanta shima
ta saka shi a damuwa rana daya?
Domin sanin kanta ne rashin
walwalarta tabbas ta san dole zaiyi tasiri
akan tashi walwalar.
Tana ta faman juya cokali a cikin
tea ta dan dago, jin yayi clearing voice
dinsa, sai suka hada ido, kuma duk sai
ta bashi tausayi. Ganin ta ko kasa
kurbar ruwan shayin da ya hada mata,
sai juya cokali take a cikinsa. Zayyan ba
tareda dogon tunani ba yace.
“Na yarda, muje asibitin a duba
mu Sophie. In dai shine abinda zai baki
kwanciyar hankali, na lura dake jiya ko
runtsawa bakiyi ba.
Don haka on one condition zamu je
gaban likita; duk abinda sakamako ya
nuna, inma nine da matsala ko kece da
matsala kada ki daga min hankalinki ki
yi tawakkali ki karbi kaddara”.
26
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ai kuwa ga mamakinsa nan da nan
Sophie ta ware. Ta kurbe shayin da
gaggawa har tana kone bakinta. Ta
furzar da ruwan zafin a gefe da sauri,
yayi mata sannu. Tace “Habiby nagode,
tashi mu tafi”. Yace “dole ki gode min
mana Sophie, tunda kin ci ni da yaki.
Ni Zayyan ban taba fatan zuwa
teburin likita wai da sunan neman
haihuwa ba, because I believed time ne
bai zo ba. Kuma nasan dukkunmu
lafiyarmu kalau tunda kina regular
period”. Safiyyah bata saurareshi ba tuni
tayi daki ta hau shiryawa.
**** **** ****
Zayyan da Safiyyah ne zaune a
gaban teburin Dr. Muwadda a ABUTH.
Duk wata babbar lalura ta rashin lafiya
kota ‘medical check-up’ iyalin Baba
Bello sun fi ganewa zuwa ABUTH, sun fi
yarda da kwarewarsu. Da wuya ka ga
27
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sun canza asibiti sai ‘on emergency
case’. Don haka takanas Zaria suka taho
daga Abuja, bayan samun appointment
na ganin kwararriyar likitar mata Dr.
Muwadda Abdullahi Shinkafi. Likitar ta yi ma Safiyyah duk wani
bincike da bature ya tanada ta hanyar
tasatasai (test-test), sannan ta koma kan
Zayyan shima ta bincike lafiyarsa tsaf.
Kwana uku a jere suna zarya a asibitin
ana gwaje-gwaje da aune-aune, inda
sukayi masauki a Zaria Guest Inn, kafin
fitowar sakamakonsu.
Ranar da aka tattaro sakamakon
suna waiting room na ganin likitar, kafin
a kirasu ofishin likita Safiyyah saida ta
zaga bayi ya kai sau uku, saboda
fargabar abinda likiciyar zata ce mata. Shikuwa Zayyan ko a jikinsa, don
ya riga ya sakawa ransa haihuwa ba ita
kadai ce farin ciki tsakanin shi da
Sophie ba.
28
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Akwai tsantsar soyayya mai
haddasa farin cikin da walwala, wadda
ta riga ta haifar da fahimtar juna mai
girma a rayuwar aurensu.
To na meye zai damu kansa kan
abinda Allah bai ga damar basu ba???
Sakamako dai ya nuna cewa
Safiyyah ce mai matsala bashi ba,
tanada lalurar PCOS (polycystic ovary
syndrome). Likita Shinkafi, ta kira
matsalar Safiyyah da suna ‘unexplained
infertility’ na sanadin matsalar PCOS. Ta dorata kan treatments masu kyau
na masu lalurar pcos, da magunguna
masu tsada wadanda zasu iya taimaka
mata tayi conceiving idan tanada rabo.
Tun a hanyarsu ta dawowa Abuja
Safiyyah ke fakar idonsa tana dauke
kananan hawaye a idonta, alhalin yana
tuki. Ya saka musu karatun Al’qurani a
cikin motar cikin qira’ar Salah
Bukhatir, a cikin karatun ne Sheikh
29
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Bukhatir yazo ayar da take addu’ar
samun zuri’a dayyibah cikin Suratul
Furqan. Ya karanto ayar nan cikin
qira’arsa ta hafsu mai dadin sauraro;
“Wallazeena yaquluna Rabbana
hablana min azwajina wa zurriyyatana
qurrata a’ayunin wa ja’alna lil
muttaqeena imaama…”.
Sai kukan Sophie ya kasa boyuwa a
wannan gabar, domin ta kasa cotrolling
dinsa, ta soma sheshshekarsa a fili tana
bin Ayar tana maimaitawa cikin kuka.
Kuka sosai Safiyyah ke yiwa
Zayyan a cikin motar har saida
kukannata ya soma rikitashi, yace cikin
rawar murya.
“Safiyyah kina so in zubar damu a
motar nan ko?”
Ta girgiza kai, ita tafi kowa sanin
yadda Zayyan baya son kukanta don
fitar dashi yake a hayyacinsa. Amma
yau dole tayi kuka a gabansa. Ashe-ashe
30
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
itace mai matsalar! Kukan nata ya karu,
fiyeda na baya. Ba shiri Zayyan ya faka
motar a gefen titi.
“Sophie, so kike ki daga min
hankali akan abinda banida ikon baki
shi ko? So kike in dorawa kaina
damuwar gazawata da kasawata ga baki
farin cikin da kike so?” Safiyyah ta girgiza kai tana share
wasu hawayen da suka kawo mata caffa
da gefen gyalenta, tace “ba haka bane
Habiby, inaso ne ko yaya ne nima in ga
dan kaina, wanda zai zama fruit to our
love. Nima in zama UWA inyi
experiencing abinda ake ji a motherhood.
Shekaruna kullum gaba suke yi,
har gashi ina neman dosar shekaru
talatin banida Da ko daya.
Kuruciyarmu kullum karewa take yi, ba
baya take komawa ba. In ban haihu yanzu ba sai yaushe
Habiby? Sai na kai menopause? Banida
31
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sanyin idaniyar da kowa ke alfahari
dashi wato DA. Banida bakin da zan
kira kaina Maman wane ko Maman
wance.
Kaima da kanka Zayyan watarana
zaka tsaneni, tunda na kasa maida kai
UBA. Ta hanyar ajiye maka abinda
kowanne uba ke fatan samu”.
Karo na farko da yaji Safiyyah ta
kirashi da suna ZAYYAN wanda ya
nuna tashin hankalinta a fili yake, bata
ma san ta fada ba, a kwanakinnan ya
fahimci Safiyyah ta zama desperate ga
son haihuwa kadai. Zayyan ya rungumo Safiyyah sosai
a jikinsa, ya ma manta a kan hanya
suke, ya sumbaci saman goshinta zuwa
karan hancinta, ya ja birki yayi togaciya
a lips dinta, inda yayi mata kykkyawar
sumba mai zurfi. Yace “Sophie ni ba
abinda zaisa na tsaneki, haba Safiyyah,
haba Sophie na, nifa Safiyyah na aura
32
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ita kadai bada tunanin zata haihu min
ko bazata haihumin ba.
Ta yaya kuma don baki haihu ba sai
in tsaneki akan lalura, bayan daidai
gwargwado nasan cewa Allah ke bada
haihuwar nan?
Kada ki kara wannan shirmen
tunanin bana so, abinda ni Zayyan na
yarda dashi shine haihuwa ta Allah ce,
da ya bamu da bai bamu ba you will
forever remain my alter ego!” Da haka yayi ta lallashinta har ya
samu tayi shiru tana ajiyar zuciya a kan
kirjinsa. Can kuma tace “Habiby,
babbar damuwata itace PCOS dinnan
yanada magani ne ko a’ah, ni da ace ma
tace unexplained infertility kadai ne, sai
inga kamar zan fi samun sauki a raina
fiye da ace mun PCOS gareni. Ni ban
gamsu da binciken wannan likiciyar ba,
don a tarihin zuri’ar gidanmu kaf! Babu
mai PCOS”.
33
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zayyan yace da karfafawa “to hell
with PCOS and whatever! Ni Zayyan
Sophie kawai nake so, haihuwa in Allah
ya kawo ina maraba da ita, haka in bai
bamu ba, muna cikin godiyarsa as well. Ya hada hannuwansa biyu yana
rokonta. “Chapter closed, don Allah
Sophie. Bana son kara jin zancen
haihuwa a bakinki daga yau. Kuma
kada ki kara kai mu gaban Likita”. Amma ina! Safiyyah bata hakura
ba saida tayi bincike ta hanyar tuntubar
wadanda ta sani akan kwararriyar
likiciyar matan da tafi kowa kwarewa a
Arewa, nan aka bata labarin Dr. Hadiza
Shehu Galadanci, ta jihar Kano. Ta samu labarin Dr. Galadanci ne ta
hanyar Anti Dije, ta kudire in ta samu
Zayyan ya kaita Zaria bikin Ni’iman
Anti Dije sai ta biya Kano ta ga Dr.
Galadanci tunda kwana uku zata yi a
Zaria. Watakila Dr. Shinkafi bata san
aikinta ba, ita a zuri’ar su Ammi ba mai
34
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
PCOS, kuma ance shi mostly gado
akeyi.
Hakan ce ta faru. Lokacin bikin
diyar Anti Dije Safiyyah ta samu
Zayyan ya kaita har Zaria, daga nan
sukayi sallama shikuma ya wuce
Katsina gun su Mama, a can zaiyi hutun
karshen mako, ita kuma ta ci biki a
cikin ‘yan uwanta, duk da bata da
walwala, ga kannenta duka sun zo suma
daga Dandume.
Biki yayi biki gida ya cika da dangi
da abokan arzikin su Anti Dije, ita da su
Sabah daki daya suka kwana,
washegarin saukarta a Zaria Safiyyah
sai ta zare jiki ta tafi Kano ita kadai ba
tareda Zayyan ko wani nata ya sani ba,
ta hau motar Kanoline daga Zaria, daga
nan ta nufi asibitin Standard da Anti
Dije ta bata labarin a can aka yi mata
maganin barin ciki data yi ta yi
shekarun baya .
35
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Da tambaya da taimakon wayewar
kanta sai ga Safiyyah akan layin mata
masu son ganin Dr. Galadanci.
Bata sha wahalar samun asibitin
Standard ba, saboda babban asibitin
kudine da yayi kaurin suna ga matan
Kano.
Duk da Sophie bata taba zuwa
Kano ba sai wannan karon. Hakan bai
sa ta rikice ba. Mai Keke Napep ta
dauka drop tace ya kaita Standard na
Tarauni. Shikuma da yake ya riga yasan
asibitin nan da nan ya kaita ya zabga
mata kudi.
Safiyyah ta bude file ta biya duk
abinda aka cajeta na ganin Prof. Dr.
Galadanchi, kasancewar Safiyyah
sammako tayi bana wasa ba, daga Zaria
zuwa Kano, yasa karfe goma na safe ma
tana cikin garin Kano. Aka dorata akan
layin da mata uku ne kacal a gabanta.
36
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ta samu kujera ta zauna a waiting
lounge na ganin likiciyar, bata dade da
zama ba wata farar mata da ba zata fice
tsararta ba itama tazo ta zauna a kusa
da ita, bayan tayi wa Safiyyah sallama.
Sai zuba kamshin Humra matar take. Suna nan zaune matar na amsa
waya lokaci-lokaci, can kuma ta jefa
wayar a kyakkyawar Jakarta, cike da
shishshigi ta dubi Sophie, don taga kalar
hutu sosai a jikinta itama, ita kuma
dama da irin kalar wadanda take
kawance kenan, sai ta hau jan Sophie da
hira kadan-kadan babu alamu na
bakunta, ko irin yau ta fara ganinta
dinnan.
“Baiwar Allah sannu fah. Na ce
sannu fah. Halan kema matsalar rashin
haihuwa ce ta kawo ki ganin Dr.
Galadanchi?”
Safiyyah sai da taji gabanta ya fadi,
matar tayi murmushi ganin irin kallon
da Sophie tayi mata na mamaki, sai tace,
37
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“yo meye abin mamaki don na
canki matsalarki? Ai daidakun mata ne
ne da sukazo Standard da ba matsalar
data kawo su kenan ba, musamman
masu fama da lalurar (PCOS)”. Sophie ta bita da kallo kawai, don
bata ma san menene ‘PCOS’ din ba ita
har yau, bata taba jinsa ba, sai a bakin
Dr. Muwadda Shinkafi. Ta ce a ranta,
“wasu matan dai Allah ya zuba
musu surutu da shiga sharo ba shanu!”.
Matar bata san tunanin da Sophie
ke yi a kanta ba, ta cigaba da cewa.
“Alhalin basu san cewa wahalar da
kansu kawai suke yi a banza ba. Ni
dinnan da kike gani wane kalar asibitine
banje neman haihuwa ba, kasashen
duniya manya da kanana babu inda
bamu taka don neman haihuwa ba nida
maigida na.
Mun zubar da dukiya da lokacinmu
kamar me a yawon asibiti, duk a banza.
38
KAWAR ZUCIYA 2