Showing 1 words to 3000 words out of 48692 words

Chapter 1 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025

KAWAR ZUCIYA



2



Sumayyah AbdulQadir
​ 07030137870 (whatsapp only)
​ babbangoro2015@yahoo.com
takorikabara@gmail.com


1

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025


Assalamu alaykum TAKORITES.
Kafin mu fara ina farin cikin tallata muku Hajiya
Aisha Umar Dauda mai A&A Incense &
Collections.
Dealers ne nadukkan kayan Oriflame
Products & GHT Products. Sanan suna da Room
Freshener, Toilet Cleaner, Tiles Cleaner, Glass
Cleaner, Dish Wash, Hand Wash, Shoes & Bags,
Hand Made Shoes, Atamfa, Shadda, Materials, Kid's
Wears, Electronics, Perfumes and many more. Domin sayen daya ko sari ana iya tuntubarsu
a;
No.1 Beside Lolo Dakare's Filling Station Hajj Camp,
Katsina State.
Suna aikawa ko'ina. Ko a tuntubesu kai tsaye
a wannan lambar waya don saka order.

08067303736
08054647489


2

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025





“Rabbana hablana min azwajina wa
dhuriyyatina qurratu a’ayunin wa ja’alna
lil muttaqina imaama”.

SADAUKARWA NE GA
“TAKORI’S LOUNGE”.
Ina alfahari da kasancewa tare daku har
tsayin wannan lokacin. Allah da ya
hadamu haka, a inuwar al’arshinsa ya
barmu tare cikin Alherinsa… har zuwa
ranar da muka daina numfashi. -Sumayyah
Abdulkadir
3

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
01/01/2025

KAWAR ZUCIYA ( Littafi na 2
W
4

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ani abu da ya ja hankalin Mama akan
Safiyyah shine har zuwa wannan lokacin
Safiyyah ba haihuwa, ba ko batan wata
balle a saka ran samuwar ciki. Duniya
kam daidai gwargwado suna cikinta
itada mijinta suna juya jin dadinta son
rai, itada Zayyan basu nemi komai sun
rasa ba, amma haihuwa shiru kake ji ko
sama ko kasa kamar an aiki bawa
garinsu, tuni anyi auren duka ‘ya’yan
Mama saura Hatoon, itama din da saka
ranarta a kanta.
Mama tana Katsina bata zuwa
Abuja, amma kullum Zayyan yazo
gabanta sai ta yada zance akan rashin
haihuwar Sophie, in kuwa suka hadu,
Mama sai ta fada mata baka koda ta
cikin ruwan sanyi ne akan rashin
haihuwa. Amma Zayyan bai taba
damuwa da korafin Mama ba. Hasalima
shi mantawa yake da wata haihuwa
saboda yawan hidimdimun dake kansa.
5

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Har ya zamana Safiyyah bata
marmarin abinda zai kawo ta Katsina,
Mama tayi nata, su Zubaidah suyi nasu
gorin, rannan Zubaidah take
tambayarta “wai sau nawa ake yi musu
kwasar masai a shekara?” Safiyyah ta dubeta cikin rashin
fahimta ta ce “kamar yaya?” Sai Yaya
Zubaidah ta gyara zama cikin izgili, da
shakiyanci, tayi dariyar rainin hankali
tace mata. “Yo dole in miki wannan tambayar.
Don na san a wata guda kike cika masai
da kashi, tunda kin gaza kasaye Da ko
‘ya ko guda daya, shine nake mamakin
ina kike kai buhunhunan abincin
gidanki da basa ko shekara sun kare in
ba masai ba?”.
Wannan magana ta yiwa Safiyyah
ciwo. Har ta kira mahaifinta a waya a
ranar tana kuka, tace “Malam kayi min
addu’a Allah ya bani haihuwa idan
inada rabo”. Kuma sune kalaman da
6

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
suka sa ta fara kwadayin son haihuwar
itama. Amma da fari bata ko damu ba.
Malam Usman kuma yace “Zan yi
miki addu’a Nana Safiyyah, Allah ya
baki mai albarka, daina kuka kinji baya
saka komai kuma baya hanawa. Komai
kika ga ya faru da rayuwar bawa haka
Allah ya riga ya rubuta masa. Idan
haihuwa alkhairi ce zan roka miki ya
baki, idan ba alkhairi bace a gareki ya
baki abinda ya fita alkhairi”.
Idan kuwa sune suka zo Abuja yin
wata hidimarsu suka sauka a gidanta to
har su tafi babu alkhairi a tsakaninta da
‘ya’yan Mama, sai gori da bakar
magana da habaici cikin lumana. Yanzu
sun bar kiranta diyar Alaramma sai
“Barren Lady”.
Ko su ce “‘Yar kauyen Dandume an
sha jar miya an yi bulbul. Amma har
yau babu Da ba jika a gidanmu balle
musa ran zamu samu mai sunan
Babanmu”.
7

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Cikin wasa da Dariya kadai zasu
gaggasa mata magana mai sosa rai akan
haihuwa, wanda sai ta yi wata yana
damunta a rai. Har ta soma tsangwamar
kanta da tunanin shin ita me ya hanata
haihuwa ne??? da gaske “Barren” din ce
ita???
Zayyan bai taba sanin wannan
sunan da Zubaidah ta kirata dashi ba,
don koda wasa shi bai taba damuwa ko
ankara da rashin haihuwarsu akan
lokaci ba, duk yawan korafin Mama a
wurin yake tashi ya barshi bai taba
sakawa a ransa ya dameshi ba. Sannan
yawan harkokin dake gabansa ma basu
barin shi ya tuna wai bashi da Da a
gabansa, haka korafin Mama bai taba
sawa yayi zancen haihuwa da Safiyyah
ba, sai wannan fateful ranar, da Mama
ta zaunar dashi tace.
“To Hatoon dai, an saka ranar
aurenta, nikuma bazan iya zama nikadai
a gidannan ba, babu Da ba jika, sai ka
8

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
san inda zaka samomin ‘yan
dugui-dugui da zasu dinga taya ni zama
da debe min kewarta”.
Zayyan bai gane me Mama ke nufi
ba yace “Au toh, sai na je na dauko miki
Baba Ladidi daga Rumah, ta cigaba da
zama anan bayan bikin ko?” (Kanwar
mahaifinta data riketa). Mama ta zabga masa harara tace
“Ladidin ce ‘yan dugui-dugui?”
Shi har lokacin Zayyan bai gane ba,
sai da Mama tayi masa fashin-baki, tace.
“Humm! Ita diyar Alaramma ashe
‘bakarariya’ ce ka auro? Sai uban
ladabi da uban sunkuyar da kai da bazai
amfaneni da komai ba? Shin ko kana
kirge da shekarun aurenku? Babu wata
albarkar aure kota bari a gidanka
Baffana?”
Dariya sosai yayi yace.
9

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Mama rigima, menene kuma
bakarariya?” Mama ta fassara masa
cikin gatse, “juya” mana (wadda bata
haihuwa). In maka da turanci;
BARREN! Da Larabci kuma ince
‘Aaqira’. Tunda kai hausa bata isheka
ba?”.
Sai yayi shiru. Kamar a lokacin ya
fara jin Safiyyah bata haihu ba har yau.
Jim kadan kuma ya daure yace,
“to Allah bai kawo mana ba Mama,
zamu baiwa kanmu abinda Allah bai
bamu bane?”
Mama ta katse shi tace “kada ka
dorawa Allah, saidai in tsarin iyali take
yi, don taci duniya da tsinke, ko kuma
bata da mahaifa sam a jikinta, ko bata
da kwan haihuwa. Ni kawai jika nake so, ba kuma na
kowa cikin ‘ya’yana ba sai naka Baffa”.
Yayi zugudiii yana kallon ta kafin yace
cikin shanye damuwa,
10

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“duk ‘ya’yan da su Yaya Zubaida
suka tara miki a gidannan Mama basu
isheki ba? Sai nawa kadai kike jira? Ko
jiya kince min Zahra ta haihu,
Zaitoonah ta kusa, in kawo akwatin
kayan barka…”. Mama tace “bazaka gane ba
Baffana, naka daban ne, ina son ganin
‘ya’yanka gabana. Allah shine shaida ko
dama can nikam Allah ya shaida diyar
Alaramma ba wani sonta nake ba, don
dai Allah ya jikan rai Baba ya daure
maka gindin aurenta ne, ba kuma wai
na sota daga baya bane, illa yadda naga
baka korafi akan ta, tana maka biyayya
daidai gwargwado kuma, ya tabbatar
min kana samun kwanciyar hankali a
tare da ita, shiyasa na zauna lafiya da ita
har wannan lokacin.
Amma akan matsalar rashin
haihuwa shekaru takwas da aure yanzu
Baffa?! Dole a ji mu a kan ‘drum’ nida
ita, da kai dake daure mata gindi, zamu
11

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
hau samu fado nida ku, na rantse da
Allah Baffa.
Duk cikin jikokina da kake ikirarin
an haifa min, ka gayamin in akwai
wanda zaiyi bearing sunan Bello
Rafindadi in ba naka ‘ya’yan ba???
‘Ya’yan wasu ne ba nawa ba, naka
sune nawa. Ko kuwa so kake daga
kanka ya zama cewa bayan Bello ya
yanke?”
Anan inda sukayi maganar nan da
Mama, anan wurin ya barta, don bai ji
Tauhidi da technology da ikhlasi a
cikinta ba shi, sai kace su zasu halicci
dan cikin jikinsu. Bai ko tashi da zancen
a ransa ba. Rigima da digimin Mama
wanne ne bai sani ba?
Ko wace irin kalar rigimar ta in
tanason wani abu ne bai sani ba? Babu!
Baba Bello ya sha fadi cikin raha cewa
Mama rigimammiya ce, bai kara yarda
da irin rigimar tata ba sai yau data
12

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
dawo kan rashin haihuwar Safiyyah ta
saki layin korafinta na baya na malunta
da mallakarsa a minjaye.
Tun kuma bayan rasuwar Baba
rigimarta a kansa shi Zayyan din ta
karu. Komai shi komai shi. Bata ko iya
sati biyu bata saka shi a idanunta ba
yanzu zata bashi query akan Safiyyah ta
rike mata shi. Kenan kuma yanzu rigimar tata ta
dawo kan haihuwarsu kenan ko?
Toh banda Allah wa zai bada
haihuwa a lokacin da aka kayyade
maka, in banda abin Mama?
Yana tafe akan hanyarsa ta komawa
Abuja daga Katsina yake wannan
tunanin, yau dai Mama ta saka shi a
damuwa dolen dole, bayan ya baro
Mama a safiyar yau ya kamo hanya.
Wasu gungun shanu ke tsallaka titi
saura kadan ya kwashe kafafunsu
sabida tsabar tunani, Allah ya
13

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
taimakeshi ya kauce musu, ya dafe
sityari sosai.
Wani ikon Allah kamar Safiyyah
tasan meke faruwa tsakaninsa da Mama
a Katsina jiya a kanta, kodayake kamar
hadin baki, a dan tsukin itama rashin
haihuwar damunta yake yi sosai. Ya shigo gidan yanata sallama bai ji
motsinta ba. Ya duba dakinsa da nata
duk bata nan, kuma bai ji alamar zubar
ruwa daga toilet ba.
Duk da haka yace bari ya duba
nata toilet din, sai ya murda kofar toilet
dinta, Ilai kuwa, a can ya sameta zaune
dirshan a dandaryar kasan tayal din
bandakin, ta hada kai da guiwa da wani
siririn abu rike a hannunta. “Sophie?”.
Zayyan ya kirata a tausashe, with
concern and love in his voice tone, kuma
cike da fargaba, don baya raba dayan
14

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
biyun kuka kashirban Safiyyah take yi
mai tsanani.
“Me kike yi anan haka? Meke
faruwa haka?”
Ya tambayeta yana takowa zuwa
cikin toilet din. Safiyyah bata amsa ba
sai ma jin zuwansa da tayi yasa kukanta
ya karu harda da gunji da jin
shigowarsa. A hankali kuma cikin faduwar gaba
Zayyan ya tako har zuwa gabanta, yasa
hannu ya zare abinda ke hannunta ya
duba, nan ya gane Pregnancy Test Strip
ne (PT Strip). Ya mikar da ita tsaye. “Hey! Is this
Pt strip? Me kikeyi dashi to? Tell me, are
you pregnant?”
Ya dago ta ya tallafota ya fito da ita
zuwa falo. Ya kwantar a jikinsa yana
tambaya.
15

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Safiyyah menene hakan? Na kasa
ganewa. Menene wannan abun, me kike
yi dashi a toilet kamar wata likitar
mata?”
Saida ya zage sosai da lallashi da
banbaki, ta tabbatar ya shiga damuwa
irin wadda take ciki, sannan ya samu ta
daina kukan. Ya rungumeta sosai a
kirjinsa, ya barta ta kwanta lamoo!
Kawai tana sauke ajiyar zuciya. Suka
baje a dandayar toilet. Kamshin
Ultraviolet (Paco Rabanne) dinsa yana
ratsasu tare, yace “Safiyyah kin
dagulamin lissafi, na kasa gane me ya
faru dake, kin tsoratani daga dawowata.
Ba ko sannu da zuwa? Please explain.
Kin sani a duhu!
Wani abu ya faru da bana nan? Me
ya sameki kike kuka? Me kuma kikeyi
da PT Strip? Wani ya zo ya gaya miki
wani abu ne daga Katsina?”
16

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Duk yabi ya sha jinin jikinsa akan
zancen da suka gama jiya a kanta da
Mama.
Da kyar ya samu motsin bakin
Safiyyah inda tace “ba wanda yazo nan.
Period dina ne yayi jinkiri, inata murna
ko bukatata a wurin Allah ta shekara da
shekaru ta biya, ko Allah ya amsa min
roko na, shine nayi pregnancy test, but it
shows “negative” yau ma kamar
kullum”.
Murmushi yayi ya tallabo habarta
saman tafin hannunsa, ya sumbaci
saman lips dinta lightly, yace,
“ke likita ce da zaki yiwa kanki PT
ko karambani da giggiwa na nemowa
kai damuwa irin naki Sophie? Haba
Nana Safiyyah! Da ilmiki na addini kike
damuwa akan abinda kinsan nufin Allah
ne? Ko na taba ce miki na damu ki
haihu yanzu?”
17

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ido fal hawaye Safiyyah ta dago
tana kallonsa da takaici, ba tun yau ba
ta san shi ba abinda ya dameshi da
rashin haihuwarta, most important
abinda yafi baima muhimmanci shine
‘soyayyah’ da kuma a inganta masa
shimfidar aurensa, tunda kullum yana
samun yadda yake so dinnan kuma a
shimfidarsu, batareda wani cikas din
ciki ko hayaniyar yara ko kailular dake
cikin shayarwa ba kuwa me zai
dameshi?
Ko kuma don ba shi ake cewa
“Barren Lady” ba.
Amma tana kirge da cewa aurensu
ya tasarma shiga shekaru takwas bata
taba ko batan wata ba, sai a wannan
lokacin da period dinta ya dan yi
delaying. Itama da farko ai bata damun ba,
amma banda yanzu da take neman
kaiwa shekaru talatin, don data
kokantawa Ammi damuwarta kan
18

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
matsalar rashin haihuwar nan a can
baya Ammi cewa tayi wai “lokaci ne”.
Ta kuma kara da cewa komai data
gani a duniyar nan yanada lokacinsa, in
Allah ya nufa. Ta cigaba da gayawa
Allah kawai, amma kada tasa damuwa a
ranta, ta kuma saka a ranta ba haihuwa
ce kadai farinciki ko alkhairin rayuwar
aure ba, zama lafiya ma cikin soyayyar
miji wani abu ne, ba kuma itace kadai
ke samar da zaman lafiyar aure a
duniya ba, sannan ba ita ce zata kaita
aljannah ba”.
Wadannan kalaman na Ammi suka
sa tun daga lokacin Safiyyah ta sanyawa
ranta salama, amma kwanan nan abun
ya zo yana barazana ga kwanciyar
hankalinta, musamman saboda gorin
‘yan uwan mijinta, da uwar mijin kanta,
duk sanda ta tuna shekara takwas ba
ribar aure tsakaninta da Zayyan, wanda
shi zai zama sanyin idaniya a garesu, ya
19

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kara dankon soyayyar tasu, sai taji wata
irin damuwa ta lullubeta.
Musamman saboda habaicin da
Mama da ‘ya’yanta suke sakar mata
directly and indirectly.
Ta jima tana sayen PT Strip a boye,
bada saninsa ba tana gwada kanta, in
taga babu komai haka zatayi kuka a
toilet ta gaji ta wanke fuskarta ta fito, ta
shiga harkokinta. Ya zamanto cewa Safiyyah ko dan
ciwon kai take yi ko zazzabi sai ta roki
Allah yasa laulayin ciki ne. Haka zata
shige toilet yin PT, amma kullum amsar
daya ce “negative”. Safiyyah ta fara tunanin ko bata
gamsar da mijinta ne shiyasa ta kasa
daukar ciki? Gashi ita bata yarda da
wani abu wai shi maganin mata ba. A
hankali abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login