Showing 12001 words to 15000 words out of 48692 words

Chapter 5 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

TAKORI 2025
na kafa dana hannu. Kuma mutumin yayi
settling bill din gabadaya, aka ce ta bada
lambar wani nata a kira su a gaya musu
halin data ke ciki suzo su kula da ita, don
bazata iya tafiya gida a yau, kuma cikin
wannan halin ba. Sai a lokacin Safiyyah ta tafi ga
tunanin ainahin abinda ya faru, da kuma
sanadin afkuwar hakan, tabbas
gagarumin laifi ta yiwa Zayyan. In fact, ta
ci amanar aure, bayan ta fita babu iznin
mijinta yanzu da bokannan ya samu
nasara akanta fa, itada Zayyan shikenan
ko! Aurensu ya lalace kenan! Yanzu gashi
alhakin Zayyan da Allah yasan bashi da
hakkinta, yasa mota tayi awon gaba da
ita, don Allah ya nunawa Zayyan bata ji
wa’azinsa da ban bakinsa ba, har gashi
yanzu bata san ranar warkewarta ba,
babu kafar yawon asibiti neman haihuwa
data zuwa gidan Malaman tsubbu, balle
ayi maganar kafar komawa gida.
74

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Kawai sai Safiyyah tasa kuka, ta
soma yinsa kadan kadan da sheshsheka.
Sannan with a heavy heart ta fado/rattabo
musu lambar wayar Zayyan, wadda ke
kwance a kokon kanta tamkar karatun
sallah. ‘Guilt’ ne dai gashinan duk ya
lullubeta, don hakika taci amanarsa (tayi
satar fita) abinda bata taba yi ba tun
aurensu, har anyi kokarin yi mata fyade
da aurenta. Tunda sai da yace mata tayi
tawakkali ta hakura da batun haihuwa in
dai don shi take nemanta, amma kafiya da
ci da zuci irinnata yasa taki ji.
Wani ikon Allah Zayyan yana shiga
garin Kano inda daga nan zai dauki titin
da zai kai shi Zaria, wajejen karfe takwas
na dare wata bakuwar lamba ta kira shi.
Zayyan bai ko kalli wayar ba
saboda halin da yake ciki, yana tuki yana
azkar, da fari kamar bazai amsa kiran ba
75

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
don baya cikin yanayi na iya amsar wayar
mutane, amma ganin nacin mai kiran a
karo na uku yasa ya daure ya dauka,
murya a dashe.
Nan aka yi masa sallama, aka ce
daga Asibitin gwabnati na garin Kura ne,
suna tareda mai dakinsa wadda tace
sunanta Safiyyah, mota ce ta bigeta akan
titin garin Daka-Tsalle, taji raunuka
amma da sauki. Zayyan saura kadan sityarinsa ya
kwace masa ya shiga fadin…..
“Innalillahi…”. Allah ya taimake shi ya
rike sityarin sosai. Yace musu yanzu ya
shigo Kano, nan da ‘yan mintuna zai iso
asibitin Kuran ya dauketa. Cikin mintunan da basu gaza
talatin ba, da taimakon kwatancen
mutumin da ya buge Safiyyah ya isa
asibitin kauyen.
Safiyyah kasa hada ido da Zayyan
tayi, ta runtse ido tana hawaye lokacin da
76

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
taji sallamarsa a dakin, cikin muryarsa
mai ratsa zuciyarta yace “AsSalamu
alaykum” sannan ya murdo kofar dakin
ya shigo cikin nutsuwarsa, a nitsensa yake
tsaf bai bari rudewar tasa ya gigice ba
yanzun daya ganta kwance hajaran
majaran a kan gadon asibiti, makale da
allurar karin ruwa a hannunta, gadon da
take kwance ya nufo kai tsaye gabadaya
hankalinsa ya dauku gareta. A hakan
kuma yake gaisawa da jama’ar dakin.
Tana ji suna gaisawa suna kuma
jajantawa shida mutumin daya bugeta da
kuma likitan da ya kula da ita da kuma
Nas din.
Ya nemi alfarmarsu kan cewa a
darennan zai wuce da ita Zaria bazasu
kwana ba, tunda alhamdulillah ba karaya
a jikinta. Amma Safiyyah taki yarda su
hada ido sam. Da taimakon ma’aikatan jinya mata
aka sa Safiyyah a gaban motarsa. Zayyan
yayiwa ma’aikatan da suka kula da ita
77

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
alkhairi na kudi sosai. A daren wajejen
karfe tara na dare suka kamo hanyar
Zaria.
Tsakanin Kura da Zaria, bai fi
tafiyar awa daya da rabi ba, tun basu yi
nisa ba ya kira Anti Dije ya gaya mata ga
inda ya tsinto Safiyyah.
Anti Dije ta dinga salati da
sallallami, kannenta kuwa sai kuka, jin
wai ta samu accident a wani kauye, ita
kuwa tun hawansu titi ma tayi barcin
gajiya da wahala a seat dint ana gefen
damansa, sakamakon allurar barcin da
aka yi mata.
Kai tsaye ABUTH ya nufa da
Safiyyah don a kara bincikar lafiyarta da
kyau, bai yarda da kwarewar asibitin
kauyen ba, ta kuma samu kyakkyawar
kulawar data dace, kai shi yana tantama
ma yanzu akan lafiyar kwakwalwarta, in
ba haka ba me ya kaita wani kauye
Daka-Tsalle, wa ta sani a can? Ko dai son
78

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
haihuwa ya soma motsa masa
kwakwalwar Sophie ne?
Don a cikin handbag dinta da aka
bashi wadda duk uban gudun da taci bata
yarda ta yasar da ita ba, yaga takardun
tasa-tasai (test-test) na wani asibiti a cikin
jakar. Sannan tun isowarsa Kura da suka
hada ido uffan bata ce masa ba, bata ma
kara yarda ta hada ido dashi ba, ignoring
haduwar idonsu take, don gani take daya
kalli idonta zai ga tamkar Tsimbirbira ya
aikata abinda ya ambata da ita. Daman dai iyalin Baba Zayyan in
har ba asibitin koyarwa na Ahmadu Bello
ba, basa gane kowanne asibiti, hatta daga
Abuja suna tahowa suzo ABUTH idan
lalura bata gaggawa bace, tun bayan
rasuwar Baba Bello ya zama addicted da
asibitin ABUTH.
79

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A can asibitin Anti Dije ta samesu,
tare dasu Sabah su duka ukun har ita
hudu gabadayansu a rude suke.
Duk da ransa a mummunan bace
yake da Safiyyah amma haka ya daure
yayi ta hidimar lafiyarta, ya shiga nan ya
fita can tare da likitocin dake dubata a
A&E ko a fuskarsa bazaka ga fushin sa ko
bacin ransa da Sophie ba. Har saida ya tabbatar an bincike
lafiyarta sosai ba wani mummunan rauni
bayan gocewar kashin da kukkujewa da
buguwa. Aka bata magungunan rage
zogin ciwo ta sha. Tsakanin Anti Dije dasu
Rayyah kadai ake tattauna wannan abu
da ya daure musu kai, ko ina Safiyyah
taje a Kura da Daka-Tsalle ba tareda ta
bari dayansu ya sani ba? Don Zayyan ya
tabbatar musu acan ya daukota. Har
lokacin Safiyyah barcinta take sadidan,
an bata maganin barci don ta huta daga
azabar ciwon kashi, kuma alhamdulillah
iyaka abinda likitan Kura ya fada suma 80

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
shi kawai suka gani. Iyaka tsinkayensu
sun kasa cankar inda taje, da kuma
abinda ya fitar da ita ana tsaka da bikin
‘yar Antinta wato Ni’ima.
Da daddare bayan Anti ta kawo
musu abincin dare tace “Zayyan kaje
dakin bakin Babansu Ni’ima ka kwana ka
huta mana, mu sai mu kwana da ita,
akwai gajiya a tare da kai sosai”. Amma
Zayyan yaki, yace da Anti Dije shi zai
kwana su su tafi. Anti bata tafi ba saida ta
tabbatar ta zuba mishi abincin data kawo
da kanta ya ci, tuwon semo da miyar
egusi, har lokacin Sophie bata farka ba,
ya kai su Anti Dije gida ita dasu Rayha ya
dawo asibitin, sai ya biya ya taho ma
patient din tasa da Rufaidah Youghurt,
don ya san tana sonta sosai, kuma ya
samo mata wanda tafiso (thick and
creamy) da fresh milk din Hollandia. Da
duk abinda zasu dan bukata na kwana
biyu a asibitin harda su brush da maclean
da sabulun wanka, don an bata (bed rest)
na kwana biyu.
81

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Yana tafe yana waya da Anti Dike.
Inda ya hana su Anti Dije gayawa Malam
da Ammi komai akan fitar Safiyyah, yace
shi zai iya tackling koma menene, tunda
dai bata taba yin hakan ba. Kuma tunda
alhamdulillah ba mummunan rauni sosai
a jikin ta, to ba sai sun ji ba, don kada a
daga musu hankali.
Daga shagon Rufaidah masallacin
asibitin ya nufa yayi sallar magriba da
isha da suka subuce masa, ya rokawa
Safiyyah lafiya, a ransa yana addu’ar
Allah yasa alkhairi ne ya fidda Safiyyah
daga gida. Wanda ya bigeta ya tabbatar
masa a Daka-Tsalle ya buge ta kuma da
ganin ta ba cikin hayyacinta take ba, da
gudun gaske ya ganta tsakiyar titi a
gabansa. Sai ya soma karfafa tunaninsa
na anya kwakwalwarta lau take? Hakan
kuma bai danne fushinsa ba, amma ya
danne fargabarsa.
Sanda ya dawo dakin wajejen karfe
goma sha daya na dare ne Safiyyah ta
82

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
farka. Yana shigowa suka hada ido, ba
yadda zata yi tayi ignoring ya riga ya ga
idonta biyu. Sai ta tsayar da idanunta
suna kallon nasa cike fal da hawaye.
Ya dauke kai kamar bai kula ta
farka din ba shima, kwarai yaga razana
da rashin gaskiya a tattare cikin idanunta,
sai ya ja kujerar dake gabanta can daga
saitin kanta ya zauna, ya bude lemun da
ya shigo dashi na gongoni na ‘Schweppes’
ya soma sha.
Sosai Zayyan ya share Safiyyah, a
ransa yana kissima irin ‘silent
punishment’ din da zai yi mata, har sai ta
fallasa abinda take boye musu da bakinta,
yayi kamar bai ankara da cewa ta soma
sakin sassanyar kukanta cikin in’inarta
na nuna nadama ba, ga firgicin tuno
Tsimbirbira. Data rufe ido shi take
hangowa ya biyota. Jikinta ya hau rawa
da kyarma. Rashin ganin fuska daga
Zayyan yau, da yadda yayi murtuk da ita
ya hade giran sama da na kasa shi yafi
83

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
komai tsoratata da kara sakata a
damuwa.
​Ga mamakinsa shi kansa, yau
kukan Safiyyah ko kadan bai sosa ransa
ba, don ya san na rashin gaskiya ne, duk
da babu abinda ya tsana irin kukan
Sophie, balle kuma bacin ranta akan
komai, amma yau kwarai ta yi abinda bai
taba zato ba, (satar fita) zai kira abun ko
cin amanar yardar da yayi mata? Har
shaidan na kimsa masa ko tun yaushe
Sophie take yin hakan gareshi bai sani
ba?
Kuma ina da ina Sophie take zuwa
in tace masa zata je Zaria gun Anti Dije?
Har sai yau da Allah yayi niyyar nuna
masa, shine yasa mota ta kadeta, yadda
bata da damar komawa gida bai ganewa
idanunsa inda taje ba? Da yake shi
Ubangiji ya san bashi da hakkinta, duk
wata kyautatawa da trust dinsa ya
mallaka mata su. Ransa ne kawai bai cire
84

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ya baima Sophie don soyayyah, kauna da
yarda ba.
A irin yardar da yayiwa Sophie, da
nagartattun halayenta daya riga ya
shaida, da tarbiyyar da yake da tabbacin
ta taso a cikin ta, baiyi zaton abinda
zuciyarsa ke zargi yanzu a kanta ba
gaskiya bane, amma fisabilillah bai taba
kawowa a ransa Sophie zata iya ketare
iyaka a cikin aurensu ko ta ha’ince shi ba.
Tunda ta san ko me take so in ta nemi
izninsa bazai hanata ba, gashi yanzu taje
tana neman salwantar da rayuwarta a
banza.
A zahiri Sophie bata taba bata masa
rai ta bakanta masa, ta kuma sa masa
zato da shakku akanta irin yau ba. Wani
matsanancin kishi da bai san yana dashi a
kan matar tashi ba sai yau yake fiddo
kansa sarari, cikin fushin da yayi da
Sophie.
Tun Safiyyah na kuka kadan kadan
har kukan nata ya fito fili. Ta soma rera
85

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
masa shi kamar ana busa sarewa ko yaji
tausayinta ya saki fuskarsa. Sau tari ta
san Zayyan baya bata bakinsa wajen cewa
kayi masa ba dai-dai ba. Kuma baya son
kayi masa laifi kayi ta bashi hakuri. Shiru
yake yi ya dafa mutum da manyan
idanunsa da shirunsa har sai ka
gwammace ya bude baki yayi maka
balbalin fada, ko ya zane ka da bulala
fiyedawannan long silence din da zaiyi
maka. Don zafin kallon data ke gani cikin
idanunsa yafi na bulala radadi a jikinta
da zuciyarta.
To irin abunda yayi mata yau ma
kenan. Da kukan nata ya fara damunsa
sai ya mike ya shiga toilet yana daura
alwala don dare ya nausa yanaso yayi
nafila, kasancewar a (amenity room) suke
su biyu kacal, ya gama alwala ya wanko
bakinsa da brush da maclean dinda ya
sayo musu na ‘Longrich’ sannan ya fito
ya fice daga dakin. Ya bar mata kamshin
ultraviolet dinsa kadai a dakin asibitin.
86

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Can anjima sai gashi ya dawo tare
da nurse mace guda daya. A lokacin tana
tsane hawayen idanunta tana harhada
kalaman da zata yi masa bayani dasu a
ranta, don kawar da zargi data lura ya
samu muhalli a zuciyarsa da wanke
laifinta. Suka shigo shi da nurse din,
ganin ta farka kuma ruwan da aka saka
mata ya kare sai Nurse din ta cire mata
ruwan da allurar dake hannunta don ta
huta.
Tace “to kukan na menene kuma
Mrs. Safiyyah Rafindadi? Bayan gaki ga
Oga a gefenki, tunda ya kawo ki ko sau
daya bai zauna ba, yanata dawainiya
dake. Likita yace ki maida hankalinki
wajen shan magani cikin lokaci, in sha
Allah sati daya yayi yawa za kiji dadin
jikinki”.
Safiyyah ta gyada kai. Sai nurse din
ta bata maganinta na dare. Sannan tayi
musu sallama ta fita, bayan tace inda
wani abu shi Zayyan ya kirata.
87

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Dakin sai ya koma wani irin tsit,
bayan fitar nurse din. Zayyan ya yada
kansa bisa kafadarsa akan kujera yana
zaune bisa kujera kwaya daya dake
dakin, wadda ke fuskantar Safiyyah dake
kwance. Ko ya tambayeta ya akayi ya
tsintota a Kura? Ko ina kika je a Daka
tsalle? Kawai yaja bakinsa yayi shiru. Ita
kadai ta gane cewa ‘silent anger’ ne a
kwance kan fuskarsa ma’abociyar
kwantaccen saje da gargasa, kuma ‘silent
punishment’ dinsa na shiru dinnan da yafi
komai kidimata yauma yake son yi mata.
Daga baya Zayyan sai ya lumshe
idanunsa yana sauraron kukanta, har
barci yayi awon gaba da ita.
A washegari ma haka ta wuni kuka,
sikuma ya wuni zaune gabanta silently.
Sallah kadai ke fiddashi masallacin
asibitin. Su Anti Dije sai yamma suka zo
musu ranar za’a kai amarya Ni’ima
88

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
gidanta kenan, washegari su Sabah kuma
zasu koma Dandume.
Har magriba suna tare dasu sai
bayan isha suka tafi. Bayan sun tafi again
zata cigaba da kuka ya bar mata dakin,
bai dawo ba sai da ya tabbatar tayi barci.
Washegari aka sallamesu suka
tattaro suka kamo hanyar Abuja, ko
gidan Anti Dije basu koma ba, sai a waya
ya gaya mata sun wuce. Tayi addu’ar su
sauka lafiya. Sun wuce Kaduna sosai amma ba
umh ba umh umh tsakaninsu. Sai ta
kukan a fili tana so ya kulata, at least ya
tambayeta daga ina kike Sophie mana?
Yadda zata samu gangara tayi masa
bayani. Amma mutumin saima ya hade
giran sama dana kasa yana tukinsa
hankalinsa kwance, ransa a bace,
hankalinsa ya dauku sosai ga tukin da
yakeyi.
89

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Data tabbatar Zayyan bazai kulata
ba kuma bashi da niyyar hakan, sai ta
soma magana cikin rishin kuka.
“Kayi hakuri, kayi hakuri Habiby,
ka dubi halin da nake ciki ka gafarta min.
Wanda ba komai ya janyomin ba sai
rashin jin maganarka, da rashin daukar
nasiharka, kace inyi tawakkali amma na
kasa. Ka yarda koma ina naje, kuma
kowanne irin hadari na sanya kaina ciki,
sannan na hadu da wannan tsautsayin
duk ya faru dani a dalilin son mu rayu
tare ne, da son samun ‘ya’ya daga gareka,
da son cigaba da rayuwa da kai cikin
kwanciyar hankali da soyayyar
mahaifiyarka data ‘yan uwanka dana
rasa, kwadayina kullum yana ga samun
tsatso daga gareka Habiby!”.
Tayi shiru kadan tana kallon yadda
yake sake hade girar sama data kasa, tana
son gane ko bayaninta yayi wani tasiri?
Sai bata gane komai ba.
90

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sophie ta gyara kwanciyarta a gefen
damansa, jikinta duk ya mata tsami, ta
fuskanceshi sosai cikin damuwa da zafin
ciwo, fuskarta kan tafukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login