Showing 18001 words to 21000 words out of 48692 words
Chapter 7 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
da fitinar Mama Fatu?
A daren suna waya shida Mama,
yake yi ma Mama maganar cikin
damuwa,
“Mama yanzu saboda Allah kinji
dadin hakan? Mama uzzurawarki ga son
Sophie ta haihu kota halin kaka, yasa
Safiyyah fara tunanin muyi IVF kawai”.
Mama ta tambayeshi cikin halin
ka’in kula ko meye IVF din?
Nan ya yi mata bayanin cewa
“Dashen Da a mahaifa”.
108
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Mama ta zabura, tace “to ba dai
cikin zuri’ata ba, amma in kun ga shi zai
fishsheku to kuje ku yi tayi.
Indai mutum yace ra’ayin Bature
zai biyewa shi ya jiwo, shi dama kowa
yasan halakakke ne, ku zai halakar ba ni
Fatima ba”.
Mama bata hana ba, amma ta nuna
matsalarsu ce yin IVF ba tata ba. Don
haka shi da kansa ya yarda suje Kaduna a
yi musu Dashen, don itace kadai last hope
din su. Basu kara bi ta kan Mama akan
zancen ba, suka shirya suka tafi Kaduna
da niyyar ayi musu dashen haihuwa.
A wani babban asibitin kudi a
Kaduna wai shi (Nisa Fertility and Gynae
Center Kaduna) akayi ma Safiyyah da
Zayyan dashen Da (IVF), sosai suka tsaya
suka naqalci ilmin abun, ta yadda suka
gane komai akansa, kafin su yarda aka yi
mata.
109
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
**** ****
****
RANAR DASHEN
110
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
S
111
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
afiyyah ta sha ‘yar wuya wajen yi mata
dashen IVF, amma ta dade tana gayawa
kanta babu wani dadi a duniya da ya
wuce (samun Dan kanka).
Shikuma uban gayyar ba kananan
kudi ya kashe akai ba, amma ya gayawa
kansa shima gara su haihun, wato su
samu Dan ko daya ne a rayuwarsu, in ba
haka ba bazai taba samun kan Safiyyah
ba. Haka Mama bazata barsu su huta ba. Na farko idan har ba haihuwa
tasamu ba bazata taba dawowa ‘Hijabhie’
dinsa ta baya ba, bazata dawo musu da
farin cikin su irinna baya ba, da kulawar
soyayyarta da yake ta kewa yazu dare da
rana. Shima kuma ba zai huta da
kwarzabar Mama data su Yaya Zubaida
ba, duk dai akan rashin haihuwar matar
tasa, itama Sophie bazata taba hutawa da
gorinsu da wulakancinsu da habaicinsu
ba wanda basa ko gajiya, kuma shi yafi
komai saka mata inferiority complex. Kai
sai ka rantse haihuwar nan kudi ake
112
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sakawa a sayota da arha a bakin titi, ko
iyawar mutum ke bashi ita.
Abin farin ciki a garesu kuma shine
kamar almara, daga attempt na farko,
cikin ikon Allah watanni uku da yin
dashennan aka tabbatar da zaunawar ciki
na wata uku a jikin Safiyyah Usman (Mrs
Zayyan Rafindadi). Duk da cewa a mafi yawan lokuta
kashi 25-30 cikin 100 na masu yin IVF a
karon farko ne kawai ake yin nasara.
Amma yiwuwar nasarar na karuwa
bayan an sake gwadawa sau da dama. Dole Likitocin suka rike Safiyyah a
asibitin har tsayin watanni hudu don a
samu cikin ya zauna da kyau, hutu zallah
Safiyyah keyi a gadon asibiti, ta wanke
goma ta tsoma biyar. Zayyan ya dauki
nauyin komai na kulawarta da hutunta
wato ya tsaya ma Safiyyah.
Samun miji tsayyaye akan
damuwarka da bukatunka ma kadai irin
113
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Arch. Zayyan Bello Rafindadi, ba
karamar sa’a bace ga diya mace. Ta
wannan fannin kam Safiyyah tayi sa’a, ta
kuma ta yi sa’a, ta yi wa mata ‘yan
uwanta da yawa kwalele, na sa’ar samun
mijin da ya tara wadannan qualities din.
Shi Zayyan a halayyarsa da babi’unsa
akwai kyautatawa iyali, he’s a caring
husband, baida son kansa, baida mugunta,
abin hannunsa kakaf! Na iyalinsa da ‘yan
uwansa ne, mutum ne mai kulawa, mai
tattalin farin cikin iyali, sannan mai sonta
da tausayinta da son kwanciyar
hankalinta, in ka dauke matsalar
mahaifiyarsa Mama mace marar kawaici
da rashin maida surukin da baiyi mata ba
nata, da ‘yan uwansa mararsa kara da
zumunci ga Safiyyarsa, da kiyayya da
raini gareta maras dalili, to da sai ace
Safiyyah tafi matar gwamna sa’ar
rayuwar gidan miji kam, saidai kawai
matar gwamna ta nuna mata firda-firdan
motoci da kantamemen gida da rashin
hutu da rashin kwanciyar hankali.
114
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Yo kiyayyarsu maras dalili mana?
Don ta ko’ina ta duba ta hanga dalilin
kiyayyar Mama da ‘yan uwan Zayyan a
gareta, bata iya ta hango ta ina ta kuskuro
su kota ragesu ba, bata ga hujjarsu mai
ma’ana na kinta ba, iyaka kokarinta
kullum tana yi wajen kyautata musu, duk
wani abu da ya zama hakkinsu ne a
wuyanta Safiyyah babu jinkiri tana
kokarin saukeshi ba sai Zayyan ya fada
ko ya sani ba, ba kuma sai ya saka ta ba,
hannunta a mike yake kullum ga kowa
nasa, wajen kyauta da yawan alkhairi,
balle ga su dangin mijinta da haihuwarsu
barkar haihuwarsu ko bikinsu baya wuce
alkhairinta, kuma sai tayi babbar bajinta
take jin dadi, kai har da wanda ba
hakkinta ba, Safiyyah yi musu take,
saboda kaunar data ke yi ma Zayyan.
Amma Mama Fatu da ‘ya’yanta babu
ragayya ko kankani a tsakaninsu, babu
godi bare an gode kawai don bata haihu
ba, ko tace Allah bai bata haihuwa dasu
ba, babu mai yaba kokarinta, bata da
115
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wani farin jini a idonsu saboda ubanta ba
mai kudi bane, ba mai Mulki ba, kuma ba
mai irin tsarin rayuwarsu ta ‘yan boko
ba, babban dalilinsu kuma na yanzu an
doshi decade bata haihu da dansu ba
(shekara goma). Sosai cikin jikin Safiyyah ya
bayyana kansa a watanni na biyar da yin
dashensa, Safiyyah abin nema ya samu
wai matar Dansanda ta haifi barawo, tafi
Zayyan So da dokin isowar IVF Baby
dinsu. Zancen nasarar IVF da suka samu
ya kai kunnen Mama Fatu daga bakin
Yaya Zubaina, kasancewar komai Zayyan
zaiyi sai yayi shawara da Zubaina.
Yanzunma ya damka mata alhakin fara
hada musu kayan haihuwar Baby ne inda
yace, ta hada komai (unisex) don yaki
yarda ma ayi scan a gano musu jinsin
jaririn, yace shi kome Allah ya basu abin
so ne da kauna da tattali a gareshi, walau
mace walau namiji.
116
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah tun samun cikin ta bata je
Katsina ba, kuma basu hadu da Mama
ba, don Zayyan ya hanata tafiye-tafiye
tun fitowarsu asibiti, wato tun zaunawar
cikin. Ta kan dai kirata a waya tayi
gaisuwar da bata wani tasiri wajen canza
matsayinta a gun Mama Fatu.
Don haka Mama bata san cikin IVF
ya kankama ba.
Har saida Zubaina tazo ta sameta
kan wane shiri ya kamata suyi na
haihuwar matar Baffa, kuma ince ko ta
bada dakan yajin haihuwa da sauransu,
don dole suyi gagarumin shiri, su yi duk
abinda ya kamata a haihuwar Baffan
Mama ta farko, bayan kwashe shekaru
goma ba’a samu cikin ba.
Ta cigaba da gayawa Mama cikin
farin ciki da taya dan uwanta murna,
“yanzu kinga Mama cikin
taimakon Allah IVF din da sukayi
117
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
(dashen haihuwa) kamar da wasa ya
zauna”.
Ina wuta Mama Fatu ta jefasu shi
da Safiyyah? Don babban ashar Mama ta
saki, tana cewa “Safiyyah ta ja mata Da
ga halaka, saboda bakin cikin ta kasa
haihuwa ta hanyar da Allah ya tsara,
saboda tana bakin cikin kada ya auro
wata ita ta haifa masa naturally.
Mama bata taba zaton maganar da
Zayyan yayi mata watannin baya cewa
wai ta tunzura Safiyyah ga son yin IVF
zasu aikata din ba, ta dauka magana ce
kawai ta fatar bakinsu. Shiyasa bata wani
hana su sosai tun a lokacin ba. Mama tace ita ko a zamanin
jahiliyyah bata taba jin inda aka haihu
haihuwar dan halak ta hanyar Dashe ba.
Tace dan Dashe ba cikin zuri’arta
ba, duk da Zayyan ya gaya mata tun kafin
ayi bata taba daukar zancen wani serious
ba, sai bayan data ji sun aikata din kuma
118
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ya zauna. Ta fitini kanta da zage-zage.
Zubaina ta rasa yadda zata yi ta ganar da
Mama IVF ba haramun bane a
addinance.
Tace a ranta Mama kamar wadda
bata yi ilmin zamani ba? Koko ace ta take
sanin, saboda son ranta.
Mama ta kafe akan ra’ayin ta na
cewa ba dai cikin zuri’arta za’a ajiye dan
Dashe ba. Har ita Zubainar Mama ta
hadasu ta zage tas, tace itace babbar
munafuka da ita kadai ake kulle-kulle a
gidan Baffa, ita dashi duk an saka
sunansu a minjaye su duka an shanye, to
su kam wato itada sauran ‘yan uwansa
sunfi karfin gidan Alaramma.
Nan da nan kuma Mama ta figi
wayarta ta kira Safiyyah. Don ta kasa
hakura da zancen IVF.
Safiyyah na zaune a falonta, ta saka
tirtsetsen cikinta a gaba, wanda kullum
taji motsi a cikinsa sai tayi tazbihi ta
119
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
tsarkake kudura da iradar Ubangiji.
Kunun gargajiya na “Tamba” take sha a
kofin Mug, wayarta tayi ruri.
Koda ganin yau Mama da kanta ta
kirata, Safiyyah farin ciki taji mai yawa,
ta dauka a dokance cikin matukar
girmamawa har da russunawarta, ta
dauka sannu da jiki Mama zata yi mata,
don tun fitowarta daga asibiti basu yi
waya da Mama ba. Don ko kiran Mama
tayi don ta gaidata Mama bata amsa
kiranta sai taga dama. Kuma gashi yau ta
kira ta da kanta ba sako ba. Don haka yau
Safiyyah da taga kiran Mama cikin
wayarta ba karamin farin ciki taji a ranta
ba.
Amma tana dagawa da sallama jin
gurnanin Mama kadai ta cikin wayar yasa
taji gabanta ya fadi, mummunar faduwa.
Ta hadiyi miyau da kyar tana amsa
wayar Mama cikin ladabi mai girma,
Mama ta basar da gaisuwarta da
ladabinta tace,
120
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Sannu Hakimar Baffa! Babbar
mace Hakima a gidan Baffa! Ko ince
sannu Hakimar Dandume ‘yar Mallam
jikar Alaramma. Ni ba kira nayi don mu
gaisa ba, kira nayi inji dalilin kawomin
Dan dashe cikin zuri’ata mai tsafta. Ashe karyar Malanta kuke babu
sanin Allah cikin lamarinku, ki gayamin
Ayar da ta ce in ka kasa haihuwa kayi
dashen ciki, ko wadda tace dashen ciki ya
halatta, zan so kwarai sanin dalilinki na
baiwa kanki abinda Allah bai ga damar
baki ba, saboda tsoron kada Baffa ya sake
ki ne ko don kada ya kara aure da wadda
zata haihu?
Da zai yi dayan biyun wadannan
din da tuni bai yi ba? Yau kuke tare
dashi? Ko yau aka fara jiran haihuwar
taki?
Shin ana aure dole ne Safiyyah, ko
Baffana shine autan maza da kika bi kika
laqe masa haka? Alhalin bazaki amfanar
dashi komai ba?
121
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
In kina nufin ‘ya’yan dashe zaki ke
kawomin cikin jikokina kuma in amsa kin
yi kuskure, don bazan amsa ba, ba dai ni
Fatuma ce zan goya dan Dashe a bayana
da sunan jika ba. Don haka tun wuri ki nemi Kakar
diyanki in kin haifa a can Dandume, bani
Fatun Bello Rafindadi ba, don ban yarda
da halaccin haihuwarsu a addinin
musulunci ba…...”. Safiyyah kasa karasa sauraron
Mama tayi, ta saki wayar a kan kujera
tana fidda hawaye masu zafi.
Ba cin mutuncin Mama gareta ne ya
sata kuka ba. Face jin a fakaice Mama na
son tabo mutuncin iyayenta, cewa basu
san Allah ba. Alhalin su ko sanin anyi
dashen ma basu yi ba. Zayyan bai san da wannan wayar
da Mama ta bugowa Sophie ba, itama
kuma bata gaya masa ba, ita kadai ta bar
122
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
abun a ranta yayi ta cinta wanda ya
sabbaba mata sabuwar damuwa kuma.
A rashin saninta shima Mama ta
kira shi har gabanta, tayi masa nasa
wankin babban bargon akan Dashe da
suka yi kwatankwacin nata, tace “ya bata
kunya ya rasa mazantaka, ya bari
Safiyyah ta mayar da shi waina a tanda,
sai yadda taga dama take juyashi, tunda
har ta ja shi suyi dashen Da da ilminsa da
komai babu iznin ita data haife shi.
A karshe ta gaya masa cewa
“wannan dan ko an haife shi ba jikanta
bane, na Alaramma ne shikadai”.
Maganar nan tayi masa zafi kwarai,
Mama na son sheganta masa Da ne tun
ba’a haifeshi ba ko yaya? Wannan cikin
da yadda yake son sa tun bai zo duniya
ba? Ya kidima ya shiga rudu, ya shiga
tashin hankali mai yawa akan kalaman
Mama.
123
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A iya saninsa ya gayawa Mama
zancen zasu yi IVF, kuma bata yi wani
mummunan umarni a kai ba. Cewa tayi
kawai in sun ga shi zai fishshesu to suje su
yi. Don haka tunda ya dawo gida a
ranar Safiyyah ta kasa gane kansa, amma
koda wasa bai gaya mata komai ba akan
zuwansa Katsina, itama kuma ta ja
bakinta tayi shiru bata gaya masa wayar
da suka yi da Mama akan cikin ta ba. Haka kowannesu ya bar abun a
ransa yana damunsa, har zuwa sanda
suka manta da shi suka cigaba da shirin
taryar Baby dinsu, cike da wata irin
soyayya ta daban ga yaron, ko yarinyar,
tun bai zo duniya ba. **** ****
****
Cikin Safiyyah ya shiga watanni na
bakwai, karkashin kyakkyawar kulawar
124
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
likitocin ta, kulawarsu, tattalinsu da
burinsu duka ya koma kan cikin. Wani
abun mamaki Zayyan din da a baya yake
cewa bai damu da haihuwa ba blah blah
blah… sai gashi da akayi wa Sophie
dashen Dan, sai yazo yafi kowa son shi, da
dokin a haifa masa shi ya dauka.
Har dakin da Babyn zai rayu bayan
an yaye shi daga nono Zayyan ya ware a
kusa da nasu shi da Safiyyah.
Ya zuba komai na bukatar yara
‘toddlers’. Mama Fatu dai ko me yasa?
Daga baya bakinta ya mutu akan batun
cikin, bata kara aibatawa ba, bayan
wancan wankin babban bargon data yi
musu. Ganin dukkansu sun dauke mata
kafa.
Wannan ya biyo bayan ranar da
tayi arba da Safiyyah da tirtsetsen cikinta
a gabanta, aka ce Uwa-Uwa ce ba’a sake
ki saidai uwardaki, shi da kansa ya
hakura da abinda Mama tayi masa ya
dauko Safiyyah da tsohon cikinta
125
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
musamman ya kawo ta don ta gaida
Mama, daga ranar bakin Mama dana
‘ya’yanta yayi la’asar daga gorin Sophie
ta kasa haihuwa, sun yarda ko yaya ne dai
ashe akwai kwan haihuwa irinna kowacce
‘ya mace a jikinta, suka gasgata jita-jitan
da suke ji din, na cewa tabbas ta samu
ciki daga bakin Zubaina, wanda a da suka
kasa yarda da gangan.
Saboda a ranar ta same su bakidaya
a gidan mahaifan nasu (banda Zubaina),
suna tsaka da family meeting kamar
yadda suka saba tare da Baba Murtala
akan habakar Estates dinsu na nan
Katsina, da