Showing 9001 words to 12000 words out of 48692 words
Chapter 4 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
tsuntsaye, da fatun namun
daji babu kyan gani sai doyi suke,
korayen cike da wasu bakaken abubuwa
56
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
marassa kyawun gani a cikin kowacce
kwarya suna motsi, wanda hakan ya
baiwa bukkar smell mara dadi mai
hamami da wari, daga saman bukkar
kuma an sakale konannen kan Damisa,
abun dai zallah kyankyami. Saida ta
hadiye numfashinta.
Wani dukunkunannen mutum ne
zaune a kan fatar Akuya, dan tsurut
dashi kamar (Dwarf) wato (Wada).
“Ku koma ku shigo da kafar hagu,
kuma kada ki kara yi mana sallama.
Tuni ai Tsimbirbira ta san da
isowarki Safiyah ‘yar Usmanu da
Hafsatu matar Zayyanu”. Bokan yace
da Safiyyah cikin fushi.
Saura kadan Sophie ta saki fitsari a
wando, ko ta taka da gudu ta koma.
Ammara ta gane hakan, sai ta rike
hannunta cikin karfafawa ta jata suka
koma suka yi yadda yace din.
57
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Maraba – lale da uwargidan
Zayyanu. Magajin Bello Rafindadi masu
kashin arziki na gidaje har ‘ya’ya da
jikokinsu.
‘Ya’ya tsakaninki da Zayyanu
akwai su, saura taki kadan su riskeku.
‘Ya’Ya fal! Har sai kince sun
isheki”.
Safiyyah ta kara tsurewa, jin ya
ambato sunan wadanda suka haifeta da
Zayyan, kuma har sana’ar gadon
gidansu Zayyan din ya sani, zuwa yanzu
ta fara gayawa kanta gaskiyar lamari
gidan BOKA ta kawo kanta, bama na
malaman Tsubbu ba, irin masu aiki da
aljanu da rauhanai don gani har hanji,
wadanda kullum Malam yake gaya
musu ziyartarsu don neman biyan
bukata halakace babba. Domin
mu’amala dasu “shirka ne”.
Suka yi zaman Rakuma a gaban sa,
kamar masu neman gafara. Ammara
58
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
tace da shi “itama dai ba sai na fada ba
na sani, tazo neman haihuwa ne itama.
Allah ya taimaki Tsimbirbira a taimaka
mata, saboda yadda naji dadin
taimakon da aka yi min na cika
alkawarina na kawo duk mai bukata. Itama gata na kawo ta Tsimbirbira
ta share mata hawaye (wa’iyazu billah).
Haihuwa kawai take so, walau mace
walau namiji, da gaggawa”.
Tsimbirbira ya fashe da dariya yace
“tuni ai labarinta ya iso garemu da
bukatarta tun kafin isowarta.
Abu daya zuwa biyu muke bukata
daga gareta; jan zakara da jar kaza
(fingi-fingi) da za’a hada kwanciya, sai
kuma kwan haihuwarta da maniyyin
mijinta. Za’a yanka bunsuru a baiwa
Tsimbirbira jinin, mu zamu dauki kwan
haihuwarta da kanmu, bayan kwana
biyu kuma zata dawo ta kawo mana na
mijinta, wanda shine mahadin da za’a
hada maganin da zan bata.
59
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Shekara bazata zagayo ba sai ta
haifi ‘yan biyu maza biyu zar”.
Safiyyah was shocked and frightened
yanzu kam, don ta gama amanna ta
kusa fita daga addinin musuluncima
gabadaya, saboda rashin tawakkalin ta
da Zayyan ya jaddada mata karba da
muhimmancin yinsa ga musulmi. Kamar yaya ta bada kwan
haihuwarta ta ina za’a dauke shi? Da
sperm din Zayyan kuma, ko ta wace
hanya hakan zata yiwu?
Don haka ta juya a firgice ta dubi
Ammara da fuskar tsoro da firgici mai
yawa.
Nan Ammara ta kashe kunya tayi
mata bayanin da a baya bata yi mata ba
dalla-dalla. Ta yi mata ‘yar rada
(whisper) a kunnenta.
“Ai dama na gaya miki sai an dan
kauce hanya, sannan za’a samu biyan
bukata, ke zaki san yadda zakiyi ki
60
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kawo masa duk abinda ya bukata, na
jikinki kuwa zaku shiga daga cikin
shigifar can ne ya dauka, ta hanyar
saduwa dake! Mijinki ba ganewa zaiyi
ba”. Safiyyah ido ya raina fata. Boka ya
mike ya shige dan dakin wai yana
jiranta, ta bishi da kallon razana da
firgici mai yawa cikin kyawawan
idanunta. Ammara ta shiga convincing dinta
cikin kyakkyawan lafazi cewa “is just a
simple thing, bai fi ya tara dake na ‘yan
mintunan da basu gaza biyar ba, kokari
zaki yi kawai ki jure ki daure warin
jikinsa, don kin ganshi dan tsurut
dinnan amma ba karamin fitinanne
bane, and you will enjoy him morethan
your husband…..”.
A wannan lokacin ne Safiyyah ta
samu kalmar “Innalillahi wa’inna Ilaihi
Rajioun” ta fado cikin kwakwalwarta,
61
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
bakinta kuma yayi maza ya kama, ya
furtata a fili.
A hankali ta runtse idanunta.
Nutsuwarta da tsoron Allahnta suka
dawo jikinta. Taji ta tsani haihuwar ma
bakidaya in dai son ta ne yau ya kawo ta
ga wannan halakar. Ta tuno tarbiyyar da dattijan
iyayenta suka kare rayuwarsu a dorata
a kai. Sun kuma sha gaya mata akan
damuwarta na rashin haihuwa cewa
babu mai baka abinda Allah bai ga
damar baka ba. A yau a bayan idon Ammi, Malam
da Zayyan gashi rashin hakurinta ya
kawo ta ga halaka har guda biyu; shirka
da zina, zinar ma da aurenta….. yau ga
inda rashin tawakkalinta, da rashin jin
lallashin mijinta ya kawo ta, wai za’a yi
zina da ita da aurenta…. kuma da
wannan kazamin mushrikin.
62
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Kafin Ammara ta ankara Safiyyah
tayi wuf! Ta mike ta kama hanyar fita
bukkar. Tana fitowa kuma sai ta taka da
mugun gudu. Gudu take da gaske tun
karfinta kamar mai gudu akan iska, ita
kanta bata san ta iya gudu ba sai yau,
domin gani take kamar Bokan zai biyota
ko yasa rauhanansa sau daukota su
maida masa ita kota wane hali.
Gudu take babu waiwaye har ta
samu ta fita daga gonar, ta shiga ainahin
cikin kauyen Daka-tsalle.
Jama’ar kauyen na kallonta sai
gudu take kamar wani ya biyota, ba
tareda ta san inda take jefa kafarta ba,
ba kuma ta waiwaye, tana rokon Allah
in mafarki ne take yi saboda damuwar
rashin haihuwa yayi gaggawar farkar da
ita haka daga wannan mummunan
mafarkin.
Gudun neman tsira, nadama da
ceton Imani Safiyyah ke yi, wanda yafi
kama da gudun famfalaki, har ta hau
63
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kan babban titin kauyen, ba tare data
sani ba. Bata lura ba wata mota kirar
Honda ta taho da gudun gaske duk
kokarinta na kaucema Safiyyah hakan
bai samu ba. Direban kawai ganin
Sophie yayi ta fado gabansa, yayi
kokarin cin birki ya hango trailer a
bayan sa, dole ya zabi bige Safiyyah don
ceton kansa da motocin dake bayansa,
wadanda cin birkinsa a lokacin zaisa
trailer din ta danne su gabadaya.
Haka ya kwashe Safiyyah ya jefar a
gefen titi, sannan shima ya gangara
gefen titin ya tsaya yana ambaton
“innalillahi wainna ilaihi rajioun”.
***** ***** *****
Motocin da ke tahowa daga bayansu duk
suka yi wucewarsu babu wanda ya tsaya,
yamma tayi sosai, burin kowa ya kai gida
ko gari mafi kusa kafin shigowar dare.
Sai tsirarun mutanen da abin ya
faru akan idon su ne suka kawo agaji,
64
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
suka rufu akan Safiyyah da aka
wancakalar a gefen titi, suka taimaka
masa aka saka ta a motar wanda ya bigeta
din. Wani dattijo ya shiga gaban motar
don nuna musu asibiti mafi kusa.
Safiyyah kwance a bayan motar, aka
doshi babban asibitin garin Kura da ita.
Da kyar likitocin suka yarda suka
amsheta saboda babu report din
‘yansanda, wanda ya buge tan yace basu
hadu da police ko daya ba daga
Daka-Tsalle har suka iso Kura, don haka
asibitin ne suka kira police aka rubuta
report, shikuma ya biya kudin duk
treatment din da ya kama za’a yi mata.
An yi sa’a Sophie bata samu karaya
ba amma dai akwai gocewar kashin kafa
dana hannu, sai kananun raunika da
kukkujewa, abinda ya daukesu har bayan
isha’I ana mata treatment kafin Safiyyah
ta fara dawowa hayyacinta. **** **** ****
65
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A can kuma Tudun wadar Zaria, wato
gidan Anti Dije, hidimar biki data jama’a
bata sa Antin ta gane Safiyyah bata nan
tun sassafe ba. Sai bayan azahar da
Rayyah kanwarta ta gane rashin
dawowarta gidan, ta tuno tun safe data
ganta tana shiryawa lokacin su Sabah
suna barci ita kuma ta farka tace mata
zata dan fita ne, amma yanzu zata dawo,
to bata dawo din ba.
Kuma har la’asar ta kawo kai
Safiyyah bata dawo ba wanda hakan yasa
kannenta da suke tare a daki daya duk
suka damu, suka soma kiran wayarta ana
cewa “not reacheable”. Daga bisani Sabah ce taje ta samu
Anti Dije cikin kawayenta cike da
damuwa, a lokacin ana shirin tafiya
Mother’s Eve. Tace.
“Anti Dije, ko Yaya Safiyyah ta
gaya miki inda zata je ne? Tun safe fa
data fita bata dawo ba, kuma bata gaya
mana ina zata je ba”.
66
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Anti Dije ma sai a lokacin ta ankara
tun safen itama bata ganta ba, jama’a ne
suka sa hankalinta bai kai wurin ba, tace
“to ina Safifi zata je haka tun safe
bata gayawa kowa cikinmu ba? Amma
kira Zayyan ki tambayeshi, bazai kasa
sanin ina taje ba, babu inda zata je bada
saninsa ba, in kin bibiya ma suna tare”. Sabah ta kira Zayyan, bugu daya ya
dauka suka gaisa yana ta tsokanarta da
amaryar robarsa, yadda ya saba
tsokanarta don ita ke bin Safiyyah a
haihuwa, amma bata biye shi a wasan ba
yau, cikin damuwa tace, “Yaya Zayyan, aunty Safiyyah ta
gaya maka inda zata je ne in bi bayanta?”
Yace “kamar yaya? Ba kuna gidan
Anti Dije ba?” Sabah ta kara shiga cikin
rudu, ta ce “eh, duk muna can, kuma tare
muka kwana da ita a daki daya, amma da
safennan tace ma Rayyah zata dan fita
bazata jima ba, amma har zuwa yanzu
67
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
karfe hudu bamu ganta ta dawo ba, kuma
wayarta bata shiga, Anti Dije tace
watakila kuna tare a kiraka a ji”.
Shima ya tuna da safe wajen karfe
goma sun yi waya da ita, lokacin isarta
Standard Hospital kenan, tace masa “she
will call him back” bata jinsa sosai,
saboda tana cikin mutane, sai ya dauka
‘yan bikin gidan Anti Dije take nufi. Nan
kuwa a lokacin tana magana da kawarta
ta kan layin asibiti Ammara ne. Tun daga
lokacin kuma bata kira shi din ba, shima
kuma yaje Batsari gidan Yayarsa Zubaida
ta tsare shi da zance irin nata na kullum,
wato na kushe rashin haihuwar Safiyyah
har yau. Don ma har yau basu san
wanene mara haihuwar tsakanin shi da
ita ba, da bai san ya zai kare dasu ba.
Zubaidah tace “sun lura Safiyyah ta
tsare gabansa da bayansa, ta hana shi
auren diyar kowa, ta shiga rigar arziki
tana wadaka son ranta, tana bakin cikin
kada wata tazo ta ci, ta hanashi auren da
68
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
zai karu dashi sai tatse shi suke itada
iyayenta kamar hanji.
Ita kuma Safiyyar ta kasa tsinana
masa komai tunda har yau ta kasa mayar
da shi Uba, cikakken namiji mai iyali
kamar kowa.
Tace “kwarai zan so sanin me
Safiyyar nan ta taka da take juyaka har
haka Baffa, ita ba wani shahararren kyau
ba, ita ba aji ba (class) ita kuma ba iya
kwalliya ba, kullum ka ganta cikin ragga,
wai ita me addini, ko sabida sun saka
sunanka a minjaye sun wanke sun baka
ka shanye ta bakin Mama?”.
Tsaki yayi “mtssw!”. Ya mike yayi
bakin kofa ya hau saka takalmansa. A
karshe dai basu yi rabuwar dadi ba shi da
Yaya Zubaida, don har yace mata ba zai
kara tako kafarsa gidanta ba, shi
zumuncin Allah ne ya kawo shi baizo don
ta aibata masa mata ba.
69
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ire-iren yadda yake kare martabar
Safiyyah dinnan a wajen danginsa, yana
matukar kara mata bakin jini a wurin
ahalinsa bakidaya, ba tun yau ba.
Bacin ran Yaya Zubaida ne yasa bai
kara kiran kowa a waya ba ranar, har
itama Sophien, ya juyo zuwa gida
Katsina, inda cikin rashin sa’a kafin ya
kai ga isowa Rafindadi Yaya Zubaida ta
kira Mama Fatu ta mata korafin ya yi
mata rashin kunya akan bakarariyar
matarsa, don kawai tace yazo Batsari ya
ga ‘yammata gasu nan fululu, ya auri mai
haihuwa. Shine ya zageta tatas (a
cewarta).
Don haka yana dawowa Mama ma
ta dira a kansa, tace matsayin Zubaidah
agareshi yafi na duk wani
kwashe-kwashensa da zai zageta sabida
mace, Mama ta kara masa zafi bisa zafi,
bai samu sararin sake kiran Safiyyah ba
saboda kuncin ran da suka hadu suka
saka shi.
70
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Da faduwar gaba a ransa kadan
yace da Sabah “yana zuwa”. Sai ya kashe
nata kiran, ya soma kokarin gwada kiran
layin Safiyyah.
Abinda dai ake gayawa su Rayyah
din shima shi aka shiga gaya masa wato
“not reacheable” wanda hakan yayi
matukar tada hankalinsa, domin ba
abinda ya zo ransa a lokacin sai
kidnapping. Dama dai yau tun safe yake fama da
faduwar gaba, don haka jikinsa ya gama
bashi ba lafiya ba, jikinsa har tsuma yake
a lokacin, yace Sabah ta hada shi da Anti
Dije. Sun dade suna magana na cankar ina zata
je, don itama Anti Dije duk da tana cikin
sabga yanzu hankalinta yafi daukuwa ga
ina Safiyyah ta shiga, ta tabbatar masa
bata san ina Safiyyah taje ba, kuma bata
da kawaye a nan Zaria. Cikin fara shiga
damuwa Zayyan yace, to gashinan tahowa
Zariyan yanzu, su hadu su san abin yi, in
71
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
cigiya zasu bada su bada cigiyarta, da
report ga ‘yan sanda.
Kwarai hankalinsa ya soma tashi.
Don haka akan hanyarsa ta zuwa Zaria
daga Katsina, tuki kawai yake amma
hankalinsa baya jikinsa. Da tunanin ina
Sophie zata je babu sanin sa, ba izninsa? Yaushe suka fara ‘yar haka shida
Safiyyah?
Me take boye musu shi da ‘yan
uwanta da Antinta?
Babu irin tunanin da bai yi ba akan
ina Safiyyah zata je haka ba tareda ta
gaya masa ko kannenta ko Antinta ba, a
dai wannnan rayuwar da muke ciki ta
kasarmu Nijeriya, ta insecurity da
insurgency (rashin tsaro da ta’addanci)? Amma ko kusa bai kawowa ransa
cewa Safiyyah zata iya zuwa wani wuri ba
tareda izninsa ba, yardar da yayi mata da
amincin dake cikin aurensu masu yawa
ne, don haka ko kusa Zayyan bai kawo a
72
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ransa bata ji nasiharsa ba, da yace su
dauki tawakkali akan maganar haihuwa,
cewa da yayi sun rufe batun haihuwa da
gaske yana nufin hakan baka da zuci, bai
zaci ta saka kafa ta wofantar da zancensa
ba. Ko yaya Zayyan zai ji a ransa, in
yaji cewa Safiyyah ta yi kunnen uwar
shegu dashi ne ta kama hanyarta ta fita
duniya neman haihuwa ta kowacce
hanya??? **** **** ****
Sanda Safiyyah ta dawo hayyacinta
ta kuma fahimci a inda take kwance
asibiti ne, tana kuma jin ciwo ko’ina a
jikin ta, ba karamin firgici ta shiga ba.
Likita da Nas din dake duba ta suka dinga
kwantar mata da hankali, har suka ce ta
godewa Allah da babu karaya, shi kuma
wanda ya buge ta ya dinga bata hakuri,
da kyar suka samu ta nutsu, tace dashi
babu komai ai tsautsayi ne. Nan suka
tabbatar mata an gyara gocewar kashinta
73
KAWAR ZUCIYA 2