Showing 33001 words to 36000 words out of 48692 words

Chapter 12 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

**** ****

Kasancewar gidan Arch. Murtala
babban gida ne na zamani ginin
(Bungalow) a shiyyar Ikoyi har da
tankasheshen sassan baki, anan Baba
Murtala yasa aka saukeshi. Saida yayi sallahr azuhur yayi
wanka ya huta, sannan Baba Murtala ya
turo Seyi, don yayi masa jagora zuwa
cikin gida wajensa.
Har falon da iyalin sa kadai ke
shiga Baba Murtala yayi umarni ga Seyi
ya kai shi.
Baba Murtala dai kamar ya hadiye
dan nasa saboda kulawa da maraba, ya
rasa ina yaka saka ina yaka aje da shi,
duk sanda yazo gidan haka yake nan-nan
da shi, Zayyan na shirin zama akan kilishi
197

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Baba Murtala yace “zo zauna nan a
gefena kaji Zayyan, Da na na kaina,
kullum na ganka ji nake kamar da Bello
nake tare.
Ka jima ba ka zo gidan naku ba,
yaushe rabon ma ka zo har na manta,
bana jin duk kannenka ka san su
gabadaya”.
Ya dauki waya ya kira maidakinsa
Haj. Nana Aisha, wadda ita kadai ce
matarsa tun ta lalle, yace da ita “Da na
Zayyan ya iso. Maza a Shiryo abincin
rana a kawo mana nida shi, muna
karamin falona”. Daga nan inda suke zaune Zayyan
na iya jin muryar Haj. Nana tana
kwalawa daya daga cikin ‘ya’yanta mata
kira.
“Azeezah! Azeezah!”
Daga can nesa ya jiyo amsawar
Azeezah din, da wata ‘yar gayun murya ta
yanga da lalaci, tace.
198

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Na’am, I am coming Mum”.
(Ma’ana ina zuwa Mama).
Ta fito daga dakinta ta iske Maman
nasu a kitchen, tana shiga Haj. Nana ta
hau fada “sai ki kule a daki da waya a
hannu, ki barni da aikin abinci nikadai
ko, na rasa mace irinki Azeezah, komai
naki kamar bana mace ba, sai kwalliyar
banza da iyayin wofi kika sani, amma
harkar kitchen data hankali ko oho, ni
Nana Aisha ina tausayawa mai tsautsayin
mijin duk da ya kwashe ki”.
Azeezah ta zumburo baki, kafin tayi
dariya, bata dai ce komai ba. In da sabo
ta saba da wannan gorin na Mum dinta.
Abin haushin har Daddy haduwa suke
suyi tayi mata gori. Cewa ita muna mata
ce. Duk abu na matan kwarai baza’a
sameta ciki ba sai chatting a waya da
midnight call. Mum din tace,
​“ki dauki abincin da na shirya daga
dining ki kaiwa Daddy da bakonsa a
199

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
falonsa, na kai dining yace a kai musu
falonsa”.
Azeezah ta ce “toh” sannan ta juya
don cika umarnin mahaifiyar tata tana
cewa a ranta ko waye wannan bakon da
Daddy ya kai har karamin falonsa wanda
su kadai ke da access din shiga wajen. Tana tafiya cikin rangaji tamkar
reshen bishiya ko hawainiyar da bata son
taka kasa don yanga da iya takun tafiya.
Tamkar budurwar Dawisu don class da
iya ado. Haj. Nana tace kiyi sauri mana,
kina wannan tafiyar taki kamar ta
hawainiya, yace a kai da sauri. Shi da dan
sa ne dan wajen marigayi Bello Rafindadi.
Kiyi maza kai musu, kizo ki rakani
saloon Agege”.
​A bakin kofar shiga falon ta tube
takalminta dauke da katon tray ta shiga
falon, saida ta shiga sannan ta tuna bata
yi sallama ba, tayi maza ta koma tayi
200

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sallamar ciki muryarta ta ‘yan gayu, don
tasan kadan da aikin Baba ya dizgata
gaban bakonsa, akan rashin sallama.
Ilai kuwa saida Baba Murtala ya ce
“da baki koma kinyi sallamar nan ba
Azeezah da tamu ce dani da ke”.
Zayyan ya dago kai daga kan
wayarsa yana kallon ‘yar gayun yarinyar
dake shigowa. Bata da tsayi can kamar
Safiyyah amma tafi Sophie kakkauran
jiki irinna ‘yan ajebo, ya sake kallon ta
karo na biyu yana tuna sanda ya santa
lokacin aurensa da Sophie da suka je
Rafindadi tareda Mamanta Haj. Nana
lokacin bata fi shekaru goma sha biyu ba,
lokacin ko kirgen dangi bata fara ba, yayi
mamaki da yaga itace yau tayi wannan
girman haka na farat daya?
Yanzu akalla zata yi shekaru
ashirin da biyu, komai na budurci da hutu
ya nuna a jikinta.
201

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ta shigo da tankareren tray din da
gidajen manyan masu kudi kawai zaka ga
irinsa, ta ajiye akan center table din dake
gabansu, ta gaida shi a gajarce ko amsawa
Zayyan bai iya yayi ba, sakamakon wani
tunani maras tushe da ya zo ya sarkeshi a
nan take.
Tunani ne yazo masa cewa. Ba don
ba don ba, ai da ya gwada cewa Baba
Murtala ya bashi auren ‘yarsa Azeezah ya
kara da ita, in yaso ta haifa masa Da, ya
dauka ya baima Sophie ta rike ta rainar
masa a matsayin nata, a huta matsalar
haihuwa dake damun Sophie.
​Abinki da namiji wanda ya fito
daga gida cikin kishirwar mace, a take
ransa ya kyasa masa Azeezah. Yayi ta
kawata masa suffofinta.
​Ba Azeezah ba da take zukekiyar
yarinya mai class, wanke hannu ka taba,
da iya gayu da takun tafiya mai jan
hankalin da namiji, a wannan lokacin ko
202

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wadda bata kaita komai bama Zayyan ya
gani kyasawa zaiyi a ransa.
Saboda wawakeken gibin da
Safiyyah ta bari a ransa daren jiya da yau
da safe kafin ya fito daga gida.
Sanye take da fitted gown ta wani
bakin lace mai adon ruwan gold, rigar ta
bi dirin jikinta ta kwanta sosai, ta fidda
duk wani tudu da kwari na jikinta, a
kanta kananun kalba ne na karin gashi
(attachment) wanda in ba gaya maka tayi
ba bazaka taba gane cewa sakawa tayi ba,
ta yi ado dashi ta dunkuleshi ta baya,
wani kuma ta zubo dashi gefen fuskarta.
Baba Murtala ya lura da kallon ‘yar
shi Azeezah da Zayyan yake tayi a sace,
har ta juya zata bar dakin, tana gaida shi
amma tsabar yayi nisa a tunani bai ma ji
gaisuwar tata ba. Tunani kawai yake yana sake cewa
a ransa “ba don ba don ba! Ai kawai da
ya gwada neman aurenta”.
203

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Baba Murtala yayi murmushi yace
“kanwarka kenan, marar kan gadon
gidan, “Azeezah!”.
Duk cikinsu itace sai a hankali,
komai sai an kwabeta na rasa mai yasa
bata taso da kan gado ba, ita ba ta fari ba
ita ba auta ba.
Ko don ita kadai ce mace a
cikinsu?”
Azeezah ta ciji lebe tasan mawuyaci ne
dama Baba bai dizgata ba shiyasa bata so
Mum ta saka ta kawo masa abinci falo
musamman idan yana tare da baki.
Baba Murtala yayi murmushi yace
“tana gaisheka” nan da nan ya shiga
nutsuwarsa ya yi maza ya canza fuska ya
mayar da ita ya dinke tsaf, ya amsa a
gajarce kuma ciki-ciki. Azeezah bata
damu ba, ta juya zuwa kofa, duk dakin ya
bade da kamshin wani sassanyan turaren
Humra na mata data shafa, mai sanyaya
rai. Zayyan ya bita da kallo, kugunta
204

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kamar zai karye don shape, sai kadawa
bom-boms keyi kamar da gayya take juya
jikinta.
“Yaa Subhanallah” inji Zayyan a
zuciyarsa. Baba Murtala ya lura dan nasa
ya tafi da yawa sai ya cetoshi da cewa,
“bisimillah Zayyan, mu ci abinci
ko?
Muna da wuraren zuwa da yawa a
yau, da abubuwan da zamu fara
gabatarwa fal. Don haka ka ci abinci ka
koshi ka ji ko.
Na gaya maka two weeks project ne,
so probably zaka zauna anan Lagos har
kwana goma sha hudu”.
Zayyan ya gyada kai, ya nutsu ya
maida hankalinsa ga Baban nasa, ya bude
warmers din alfarma da Azeezah ta ajiye
musu ya fara serving dinsu shi da Baba,
kowa a faranti daban.
205

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Baba Murtala ya kasa shiru da
canzawar yanayinsa. Don gabadaya
walwalarsa ta dauke.
​“Zayyan are you okay? Azeezah ce
fa, kanwarka ta gidannan naga kamar
baka gane kanwar taka ba, last week ta
kammala karatun digirinta a Cyprus ta
dawo gida”. ​Zayyan yaji kunya tunda Baba ya
gane kalar kallon da yakema diyarsa, a
fili yace “umh” kawai, don jikinsa yayi
sanyi kuma, a ransa yace “karewar hutu a
kasar waje tayi karatu. To akul! Dina”. Suna cin abinci Baban ya shiga
bashi labarin diyarsa Azeezah, a lokacin
da tana kankanuwa, yace hasali duk cikin
yaransa Azeezah daban ta zo, itace bata
da kwakwalwar karatu sai ta giggiwa,
kullum ta karshen aji take dauka a
makaranta.
​Ya samu ta gama sakandire da kyar
da sidin ludayi, sai tasa rigimar ya kaita
206

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
waje tayi karatu don sakamakonta bai yi
kyau ba, da kyar ya samu wata
makarantar kudi (private university) ta
dauketa a kasar Cyprus, shi yasa da ya
kaita makarantar ya barta ta karanci
abinda malaman jami’ar suka zaba mata
(Make up Artistry) sabida kanta bai jan
karatu sam.
Kuma da yake tana da interest akan
kwalliya din tun tana karama hobby dinta
ce, ta tsaya ta maida hankali ta kawo
masa dan shakwa-shakwan certificate na
zama professional Make-up Artist. Yace komai Azeezah tayi sai an yi
mata gyara, komai sai an saka ta a hanya,
kuma bazata rike na yau ba gobe sai an
maimaita, in ba haka ba sai an ga kuskure
da wauta a ciki, ya tambayi Zayyan, shin
ko ya taba ganin yarinya mai gurgun
bahagon personality irin na ‘yarsa
Azeezah?”
Sai kuma yagirgiza kai, cikin alhini
yace.
207

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ba don kamar ta daya da ni ba, da
tabbas nace canzawa Haj. Nana ita akayi
a asibiti, don dakikiya ce ta gaske
Azeezah”.
Abun ya baiwa Zayyan matukar
dariya, musamman ta sigar da Baba yake
bashi labarin kamar da sa’ansa yake hira,
har sai da Zayyan ya murmusa, ya ce
“haba dai Baba!” Yace “Allah Zayyan
Azeezah halinta sai ita, ni dai nan kusa
ban taba ji ko ganin yarinya mai son
rayuwar jin dadi na rashin kangado da
son kyale kyalen duniya irin Azeezah ba.
Itace ta biyun karshe a cikinsu,
amma kamar diyar fari sabida tsabar
wauta da rashin sanin ya kamata, duk
cikin ‘ya’yansa yace babu mai son
duniyarta, da son rayuwar hutu da jin
dadi zallah na wuce kima irin Azeezah. Can Baba Murtala yace “a kullum
in lamarinta ya dameni ina gaya mata
bamu zo duniya don mu huta ba, babu
wani jin dadi ga dan adam a wannan
208

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
rayuwar sama da ya bautawa Allah ya
nemi abin rufin asirinsa, hutu sai a
aljannah, jin dadi zai dauwama ne kadai
idan ka bautawa Ubangiji da lokacinka da
lafiyar daya baka. Ka tsare sallolinka. Kullum nayi gabas, ita sai tayi
yamma, in nayi kudu, sai tayi arewa.
Kamar bani na haifeta ba. Bata gado
halin kowa cikin mu ba tsakanin ni da
Haj. Nana wajen sanin abinda ya kamata
a rayuwa. Halinta na son kyale-kyalen
duniya sai ince a rariya Azeezah ta tsinci
abinta.
Yace daga Ashraf sai Aman sai ita.
sai kuma autansu Saifullahi, suke nan
yake dasu a gabansa yanzu. Babban
dansa Walid ya jima da rasuwa a dalilin
cutar koda, haka mai binsa mace
Taqiyyah ta rasu gun haihuwa. Zayyan ya muskuta cikin jinjina
labarin Azeezah da mahaifinta yake
bashi, a cikin yanayin sautin Baba
Murtala yana nuna matukar bakin
209

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
cikinsa da damuwarsa akan halayen diyar
tasa cikin karyewar murya irin ta
mahaifin kwarai da ya damu da tarbiyyar
‘ya’yansa, ya kuma tsaya ya karancesu
sosai, dukkan dabi’unta yace ko kadan
baya sonsu, kuma basa masa dadi a rai,
ba yadda zaiyi da ita ne, ya kasa canzata,
da ana sayarda halin kwarai da ko nawa
ne ya saka ya sayawa Azeezah ya canza
mata halayenta, sai Zayyan yace a ransa.
​“Allah daya gari bambam kenan!
Ita wannan komai nata ‘opposite’ din na
Nana Safiyyahrsa!
Sophie abinda bata so kenan wato
kwalliya, gayu da kyale-kyalen zamani,
Safiyyah bata damu taji dadi ba, ita dai
tayi ibadah, kuma ta kan ce duk wani abu
da zai janyo mata idon mutane kanta, ko
ya zame mata kyalkyalin da zai ja
hankalin maza a kanta, ko ya janyo idon
mutane gareta wanda har zaisa suyi mata
kallo na biyu, bata maraba dashi.
210

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Watau Safiyyah bata son ta burge
kowa don a wurinta ido guba ne.
Komai da Baba Murtala yace halin
Azeezah ne sai ya ganshi kishiyar na
Safiyyah in one way or the other. Duk
yadda ya so ya yakice tunanin Azeezah da
labarinta tun a wurin hakan bai samu
gareshi ba. Har karanta wasikar jaki yakeyi
shikadai. Yana comparing and contrasting
halayen nasu. Yace Safiyyah mai kokari
ce, kuma zaqaqura a harkar, karatu abin
mamaki ita kuma wannnan Babanta yace
dakikiya ce. Safiyyah mai gudun duniya wannan
mai matukar son duniya, da son jin dadin
dake cikinta. Yayinda Sophie ko kadan
bata damu da jin dadi ba.
Baudaddun halayenta da yaji daga
bakin Babanta yana mai kuka dasu, shi a
matsayinsa na namiji sai suka bashi
sha’awa, sabida wasu exceptional
211

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
characteristics ne da bai saba ji ba, akwai
abin so da sha’awa a cikinsu duk da haka,
is rare a samu irinta, shi sai yaga ba
matsala bane halayen nata face abin
sha’awa tunda mace ce. Karewa ma su
suka ja masa wani sabon attraction akan
Azeezah Murtala, wanda yasa ya shiga
damuwa da lamarinta, madadin yaji baya
sonta ko ya tsani halayen nata. Kwalliya
ai abar so ce ga Da namiji, haka yake so
Sophie ta koma, mace ‘yar zamani mai ji
da class da gayu, amma ita kullum sai
Hijabi.
​Yayi ta tunanin yadda yaga Azeezah
take twisting jikinta in tana tafiya kamar
tarwada a cikin ruwa, kai kamar da gayya
take juya lafiyayyun cikakkun
mazaunanta suna wani girgiza cikin
tafiyar da hankalin mai kallonsu. Tunanin halittar Azeezah da ya
samu kansa ciki ya kuma dinga yi masa
dadi ne yasa bayan ya koma masaukinsa,
sai kawai ya kwanta rigingine ya ki kunna
212

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wayoyinsa kwata-kwata, don ma kada a
katse masa tunanin da yake ciki a lokacin.
Yanata karfafa kansa kan me zai
hana ya gwada yiwa Baba Murtala
maganar ya bashi diyarshi Azeezah ya
aura? Shi yana son kwalliyar, yana son
kyale-kyalen nata, shine abinda ya rasa a
nasa iyalin, da kuma….. Azeezah kawai ta
burgeshi. Kuma ga dukkan alamu
AZEEZAH MURTALA ta hada duka
abubuwan da ya rasa a gidansa.
Safiyyah ta fado masa a rai, a
lokacin da yaji kwanyarsa ta lullube da
tunanin auren Azeezah, yana ta tuna
jerarrun hakoranta, kissable lips dinta.
Wani irin a jere ya hau sakin ajiyar
zuciya ba sassautawa, yana gayawa kansa
koma wane irin tunani ne ya samu damar
kutsowa cikin rayuwarsa akan wata diya
mace daban bayan Safiyyah a yau,
Safiyyah ce sila, ita ta bada kofa, ta bashi
dama, ita ta jawo masa koma menene.
213

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Data watsar dashi daren jiya ya
kwana da fushinta, ta barwa matan
duniya shi akan titi suke daukar
hankalinsa, taki alkinta masa sha’awarsa,
sabida rigimarta na son wata haihuwa da
bata isa ta baiwa kanta ba, karshe ta
barshi stranded (a ragaice) bisa titi yana
satar kallon ‘yammata.
Hausawa ma sunce “sai bango ya
tsage kadangare ke samun kafar shiga”.
Don haka kara aure da diyar Baba
Murtala gareshi yanzu ba zai zama laifi
ba, don kare kansa daga fadawa wani hali
na daban. Shi kadai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login