Showing 42001 words to 45000 words out of 48692 words

Chapter 15 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

TAKORI 2025
Faris din, ko kuwa Babana yayi miki
kancal ne daya koreshi?”
Ta yi masa wata hararar love, ta ce,
“In ma na so shi, to kafin in dora ido a
kan Dan mutanen Rafindadi ne, shi kam
sharp shooter ne, tuni ya sa na manta da
kowa har ni da kaina ina mamaki”. Zayyan ya mike ya iso inda ta ke
zaune, ya dan tsugunna kadan saman
kanta, ya dafa hannun kujerar da ta ke
zaune yana murmushi.
Azeezah ta shaki ultraviolet dinsa
sosai, wanda ya riga ya kama jikinsa da
ya fesa ko bai fesa ba, har ta kusa shidewa
a wurin don wata soyayyarsa mai dadi
data kara kamata. Ya ce, “Insha Allah ni kuma na yi
miki alkawarin ba za ki yi nadamar zaben
Dan Rafindadi a matsayin abokin
rayuwarki ba. In dai za ki girmama min
Sophie, za ki taya ni lallabata da martaba
ta to in sha Allah zamu zauna lafiya.
249

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
​Ina tabbatar miki za ki same ni fiye
da yadda kike so, ko kike burin samun
abokin rayuwarki”.
Tun daga ranar soyayyar shi da
Azeezah ta kullu a gidan mahaifinta,
kullum suka dawo aiki shi da Baba, to a
falon da aka ware musu yake yada zango
can Azeezah za ta kai mishi abincin ranar
shi dana dare. Tuni Hajiya Nana ta daina hada
mishi kwano da Baba, har ranar Baba
Murtala ke masa tsiya da cewa, Azeezah
mai yankan kauna, haka kawai ta raba
mishi kwano da dan wajensa. Baba Murtala da Mama Fatu sun fi
kowa farin cikin wannan al’amari, don
kafin ya gama kwanakin aikinsa a Lagos
Mama da Azeezah sun gaisa a waya a
gabansa ya kai sau uku. Hajiya Nana kam bata so ba,
musamman jin Zayyan yana da mata,
amma ganin yadda ‘yar da uban duk suka
mika wuya, sai ta sallama musu. Amma
250

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kwarai ba ta son Azeezah da auren mai
mata, don ita kadai ta rayu a gidan Alhaji
Murtala tun daga kuruciya har girma.
Kuma Azeezar nan ita kadai ta rage musu
mace a gabansu. Sai dai ta san Hajiya Fatu irin farin
sani, a matsayinsu na matan abokan juna
tun kuruciya, ta san Mama Fatu tun
Architect Bello na raye, kuma a saninta
ba ta da wata matsala da mijinta da
al’umma, wannan ne ya yi convincing
amincewar Hajiya Nana Aisha, don
Mama ta kira ta officially ta ce ba jimawa
za su kawo lefe.
Namiji kenan, duk inda yake
sunansa namiji in dai a kan mace ne, ko
idan ya so kara aure. Shi kansa yana
mamakin wannan al’amari domin bai
taba planning dinsa a kamus din
rayuwarsa ba. ​Rabonsa da ya kira Safiyya, ko ya
saurari kiranta da sakonninta tun
saukarsa a Lagos, da tozalinsa da ‘yar
Babansa Alhaji Murtala.
251

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Kullum da dare kusan kwana yake
yana questioning kansa, yana mai
kalubalantar kansa a kan wannan
hukuncin da ya yanke. Amma ba ya bari
tuhumar ta yi nisa yake kare kansa ta
hanyar gaya wa kansa hakan shi ne kadai
solution ga dukkan matsalolinsa da
Sophie.
Allah sarki Safiyyah, tana can
Abuja amma ruhinta yana Lagos, cikin
damuwar canjin farat daya data samu
daga Habiby dinta, wai yau Habiby ne ko
wayarta ya daina dagawa kuma bai kara
nemanta ba har kwana takwas da
tafiyarshi, a kan laifin da a ganinta bai
kai ya kawo ba.
Shin me ta yi masa haka ma da zafi
ne? Ba yau ta soma rejecting dinsa a
auratayya ba, amma bai taba daukar abin
da zafi irin wannan karon ba.
Ba ta da masaniyar yana can Lagos
yana banzar soyayya da diyar
ubangidansa, wadda cikin dan kankanin
252

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
lokaci ta kunce masa lissafi, ta sauke masa
hadda.
Ba ya ko tunawa sosai da Sophie sai
ya zo kwanciya bacci, to yanzun ma
saboda wayar tsakar dare (midnight call)
da suka tsiri yi shi da Azeezah ba ya ko
samun lokacin da zai yi missing dinta
cikin dare. Abun da ya sani shi ne, son
Safiyyah a zuciyarsa daga Allah ne, babu
mai maye gurbinta. Babu mai tumbuke
matsayinta, amma ya rigada yazama
attracted and highly infatuated ga son
auren Azeezah.

Yadda Mama Fatu ta dauki zancen
auren Azeezah da matukar muhimmanci
kamar dama a jirace take bai kamata ya
bashi mamaki ba, amma hakika ya
bashin. Don kafin ma ya baro Lagos
Mama da Zubaidah sun gama hada lefe
na gani a bada labari kamar diyar
gwamna za a kaiwa, akwatuna dozen,
masu matukar matsayi, babu ce kurum
babu a cikin lefen da Zubaidah ta hada.
253

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ana i-gobe zai baro Lagos, shida Azeezah
ido ya raina fata, sukayi wata irin sallama
ta soyayya saura kadan suyi runguma
yayi maza ya fice, zuciyar sa na balli balli.
Da kyar ya kwanci kansa daga zarce
iyaka. Mama ta gayawa Hajiya Nana
cewa suna so su kawo lefe washegarin
dawowarsa gida.
Abin dai tamkar tatsuniya ko kuwa
almara. Komai da komai ya faru tamkar
kiftawar ido, neman auren da bayarwa da
saka rana duk sun faru ne cikin abin da
bai gaza sati uku ba. Ranar da ya koma Abuja bai ko
gayawa Sophie yana hanya ba, bai tashi
jin kunyar kansa da kansa ba, sai da ya yi
tozali da Safiyyah.
Damuwar da ya jefa ta a ciki ashe
har kwantar da ita zazzabin sati guda ta
yi, ta rame ta yi fiyat, kamar da ka bushe
ta zata fadi, amma kyawun nan na
Safiyya yana nan daram, duk da
muguwar ramar da ta yi.
254

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya ji kunya in ya ce kunya, yana nufin
kunya ta karshe da bai taba ji a
rayuwarsa ba, don Sophie ba ta ma san da
dawowarsa a ranar ba.
Tana kitchen tana dafa ruwan ‘tea’
da za ta saka a hantar cikinta dake
raurawa, ta ji motsin shigowarsa falon, ta
hanyar amfani da nashi safayan makullin
gidan. Safiyya ta juyo da sauri jin motsin
shigowarsa da kamshin turarensa. Suka
hada ido, sai ya ji kunyar da bai taba ji ta
diya mace ba ta lullube shi, hade da wani
irin 'guilt'. Fuskar Sophie kadaran-kadahan,
wato ba yabo ba fallasa ta ce, “Sannu da
zuwa”. Sannan ta juya tana ci gaba da
juye ruwan zafin da ta kammala tafasawa
a karamin ‘tea flask’. Tana kokarin
hadiye hawayen da ke son gangaro mata. Zayyan ya canza gabadaya har
wata kuruciya da fresh fatar jikinsa ta
kara, alamu ne na yana cikin mabayyanin
255

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kwanciyar hankali, hutu da jin dadin
zamansa a Lagos, bai ma san halin da ya
jefa ta ba. Ta sa dan yatsanta ta dauke
hawayen da ya gangaro ta karshen
idanunta. Zayyan ya tako har inda take cikin
shanye kunyar tasa, ya sanya hannayensa
ya sakalo kugunta ya dora habarshi
saman kafadunta yana sakale da waist
dinta, ya ce cikin muryar rarrashi. “Sophie I’m back, me ya faru da ke
haka, irin wannan rama haka my Dear
Safiyyah?”
Safiyyah ba ta taba hararar Zayyan
bisa saninta ba sai yau, ta zabga masa
harara ta zare hannayensa daga kugunta
ta dau tea dinta da kofin mug ta bar
wajen. Haka ya biyo ta falon cikin karfin
hali irin na Da namiji, ya ce.
“Laifuffukana ba za su lissafu ba
gare ki Safiyyah, na sani. Amma ki
gafarce ni yanzun ki fara ba ni abinci ba
256

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
don halina ba, I terribly miss your
cooking”.
Hawaye suka sulmiyo daga idon
Safiyyah, wani weak point dinta kenan
guda daya shima ya sani, ba ta iya barin
Zayyan da yunwa, don haka shayin da
bata sha ba kenan duk da itama yunwar
take ji. Sai ta koma kitchen ta shiga
hidimar girka masa abinci.
Shi kuma ya bi ta kitchen din ya
zauna a kan granite yana ta baibaye ta da
kalaman ban-hakuri da amsar laifi. Shi
kansa ya rasa hujjarsa ta kin neman
Safiyyah ko amsa wayarta har ya je Lagos
ya dawo. Gani ya rika yi yana daga wayarta
ko tana jin muryarsa za ta gane ya fada
komar wata macen ba ita ba, amma ba
don laifin da ta yi masa a ranar da zai tafi
ba. Ta kammala dafa masa jallof din
cous-cous da ya ji veggies da hanta sosai,
257

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ta zubo a faffadan tray ta kai masa kan
dining din dake cikin kitchen din.
A nan ya zauna yana ci, yana yima
girkin Sophie cin yaushe gamo da kewa
mai yawa.
Ya yi- ya yi ta zauna su ci tare ta ki
tsayawa don in ta ci gaba da tsayuwa a
wurin rauninta bakidaya da take boyewa
zai bayyana kansa. Ta ji ciwon abin da ya
yi mata, domin ya zarta hukunci a kan
laifinta, a ganinta ya koma zalunci kuma
ya dauki hakkinta.
Tunda ta bar kitchen din shima ya ji
ba zai iya ci gaba da cin abincin ba, tashi
ya yi ya biyo bayanta zuwa dakinta.
Tana canza kayan jikinta, tana
kokarin daura towell don shiga wanka
Zayyan ya zagaye ta cikin hannayensa, ya
kai mata sumba a wuya, ta goce da zafin
nama. Ya sake kai mata a bakinta, nan ma
ta kwace, amma Zayyan bai bata damar
hakan ba domin tuni ya samo bakinta ya
soma yi mishi tsotson yaushe gamo. As
258

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
usual duk yadda ta so bijire ma Zayyan a
wannan fannin da wuya ta ke samun
nasara. Wuyarta ya soma kissing bakinta
da nasa
Kuka ta saka masa, shi kuma ya
soma lallashinta har da roko. Bai sakaya
mata yadda bijirewarta gare shi ya saka
shi sha’awar kara aure ba. Duk da bai fito
fili ya fada mata har auren ya nema ba,
an kuma bashi, amma kuma Safiyyah duk
ta sha jinin jikinta.
Wanda hakan ya sa ta kara jin
bacin ranta ya ninka na baya. Wani abu
da Zayyan bai taba yi ba shi ne, tursasata
kan ta yarda da shi, amma yau? Yadda
yake so haka ya sarrafa Sophie, alhalin
taki amincewa, yace saidai duk su mutu
amma bazai iya hakurin ba, tana kuka
tana gaya masa ta tsaneshi ta kuma tsani
auren bakidaya. Ko a jikinsa, nemawa
kansa nutsuwa kawai yake. Duk sha’awar
Azeezah da ya kwaso a Lagos a nan ya
sauke ta tas.
259

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sai da ya samarwa kansa nutsuwa yadda
ya kamata sannan ya sassauta mata. Ya
koma gefe hannunsa cikin tarin lallausar
sumar kansa, ya rasa abinda ke masa dadi
kuma. Yau shine da marital rape ga
Sophie, amma ai ita ta jawo! Sama da sati
uku kenan rabonsa da ita.
A kasalance ya dube ta tana
kokarin suturta kanta da towel dinta da
ya jefar gefe don ta shiga wanka ya ce,
​“Safiyyah, ashe soyayya na komawa
kiyayya saboda rashin haihuwa?”
Saura kadan Safiyyah ta zagi
Zayyan yau, to kuma durawa soyayyar
ashariya, amma ‘Yan gidansu basa zagi
sam. Ta galla masa harara idanun sun yi
jazur da danshin hawaye, ta shige toilet. Ya sanya shorts dinsa ya bita har
toilet din, tana wanka a shower tana
kuka, nan ma sake nanikarta yayi, suka yi
wankan tare, ya nado ta a tawul ya dauko
ta suka fito, ya shiga goge mata jiki da
karamin towel, sannan ya dauki lotion
260

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
dinta na Nivea ya soma wani irin shafa
mata a dukkan jikinta, tana ki tana komai
sai da ya shirya ta tsaf, ya sanya mata
bakar jallabiyyarsa, ya tarairayo ta ya
aza bisa cinyoyinsa, sannan ya ce. “Now tell me, me ye matsalarki
Sophie? Ko kin daina sona ne Safiyyah?”
Ya dago habarta ya dube ta cikin
ido, sai ta rufe idanun nata da ke zubar da
hawaye har a lokacin. Ba zai gane irin
ciwon da ta ke ji a ranta ba a kan rashin
haihuwa da shi, haka ba zai gane yadda
biris din da yayi da ita har tsayin sati biyu
ya kassara zuciyarta ba.
Duk ma ba wannan ba, Zayyan bai
taba iya wuni guda bai kirata a waya ba,
amma yau kwana dai-dai har goma sha
hudu! Zayyan ya kwashe ba ta ko ji
muryarsa ba. Alhalin yana lafiya sumul
kalau. Jikinta ya gama ba ta (something is
fishy) don wannan ya zarce punishment
kan duk wani laifi da yake ganin ta yi
masa.
261

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya yi rarrashin duniya yana
rokonta ta yafe masa, wani abu ne ya
kutso cikin rayuwarsa a wannan tafiyar
da yayi, da ya hana shi kiranta.
Yayi ta zagaye-zagaye, ya kasa gaya
mata komai, har dai ya samu ta ce masa
ta hakura ta kuma yafe, amma don Allah
tana rokon alfarmar su kara yin IVF ko
ta samu sanyi a zuciyarta kamar kowacce
mace. Ya tuno da gargadin Mama a kan
sake yin IVF, in ya gaya mata Mama ta
hana kuma zai zama tamkar ya kara hada
gaba tsakaninta da Mama, dama Ya Allah
cika. Don haka ya samu gangara ya ce. “Safiyyah tuni na samo mana solution a
kan wannan matsalar, IVF mun yi shi a
baya, wannan karon na canza shawara,
na ce me zai hana in kara aure?
Mu yi fatan Allah ya kawo rabo na
gaggawa?
Safiyyah na miki alkawarin ko me
matar ta haifa na farko danki ne halak
262

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
malak dinki, ko shayarwa in kin so ke za
ki shayar da shi”.
Safiyyah ta yi yunkurin mikewa
daga cinyoyinsa ya sake maida ita ta
zauna, don ta fara tunanin ko Zayyan ya
fara shaye-shaye ne? Kalmar zai kara
aure a wannan lokacin ita tafi komai bata
mamaki, ba almararsa ta wata ta haifi Da
ya kyautar mata ba.
Ta yarda da aka ce duk wadda ta ce
namiji uba ne za ta kwana marainiya!
Haka kuma duk inda mijinki ya kai
da sonki, kada ki dauka akwai bambanci
tsakaninsa da sauran maza, duk sunansu
MAZA!
Ta tsaya ma tana asarar hawayenta
ya zama asara ko faduwar da babu tashi.
Don haka Sophie ta share hawayenta, ta
dube shi da idanun rahma ta ce.
"In kana ganin wannan shi ne
mafita, kuma zai samar min sa’idah a
wurin Mama da ‘yan uwanka, sannan zai
sayo min soyayyar Mama ta yarda ban
263

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
mallake ka ba, kamar yadda kullum suke
cewa, sannan hakan zai ba ka farin ciki
Zayyan, sannan baza'a kara yimin gorin
haihuwa ba, to (you have my full support)
ka kara aurenka”. Ya yi sak da zuciya da idanu, yana
kallonta kamar mai son karantar
gaskiyar da ke cikin zuciyarta. Don bai
taba zaton al’amarin zai zo masa haka
cikin sauki daga Safiyyah ba. Ita ma ta
dube shi cikin ido, yau babu kallon
soyayya, ta ce,
“Yes, I mean it”.
Ya ce, “Amma na ji wani suna daga
bakinki wanda bada shi kika saba
ambatar sunan mijinki ba, anya Safiyyah
har zuciyarki kin amince in kara auren?”
Safiyyah ta buda hannuwa irinna
matsalar taka ce ba tawa ba tace,
“Habiby, na fada na kara Habiby,
Habibiy, shikenan ko?
Ka yi hakuri tuntuben harshe ne
nayi nace Zayyan!”.
264

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Amma ita a kasan zuciyarta ta san
soyayyar ce ta ragu, ta yi flat a kasa daga
wannan lokacin.
​ **** **** ****

Washegari ya shirya yayi mata
sallama ya tafi Katsina, ita kuma ta yi
amfani da wannan damar wajen yin
azumi, ta wuni da azumin tadauwi’i a
bakinta, tana tunani irin mai cin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login