Showing 30001 words to 33000 words out of 48692 words

Chapter 11 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

ya san zai jima bai zo
Katsina ba.
179

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
***** *****
****
Tunda suka dawo Abuja yake
tattalin Safiyyah da farin cikinta. Duk
abinda ya san yana faranta mata shi yake
yi, duk abinda ya san yana bata mata rai
ya nesantata da shi. Har wani dan outing ya tsirar musu
fita yanzu kullum da daddare suje eateries
ko shawarma joint daban-daban, girki
kuwa Safiyyah iya cikinsu take yi su biyu
ma’aikatan gidan su suke yin nasu. Ni dai
mai rubutu! Nan kusa ban ga mace ‘yar
gatan miji wadda miji ya gatanta ya ke
tattali don ya mantar da ita matsalar
rashin haihuwa, sannan ya girmama
matsayinta a zuciyarshi duk da haka,
wato duk da rashin haihuwar, irin Mrs.
Safiyyah Rafindadi ba.
​Yammacin wata Lahadi ya dawo
gidansa bayan motarsa shaqare da cefane
180

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
da provision dinsu yadda ya saba duk
karshen wata, Safiyyah ya samu tayi
daidai da takardun zanenshi akan gado
wai tana zane, ko sallamarshi kanta a
duke ta amsa ba tareda ta dago ba, wai
kada tayi kuskure cikin zanen da take yi,
don a lokacin idea din zanen ke tuttudowa
a cikin kanta.
Ya cire bakar babbar rigarshi ta
bakin yadin voile din filtex ya ajiye a
gefenta, yayi mata duban rahma yace.
“Lallai ma Sophie, wato zane kike
shiyasa ko kallo ban isheki ba, balle in
saka ran zaki mike kiyi welcoming dina?”
Still bata dago ba sai ‘yar dariya
data yi, ta cigaba da Zanenta bilhaqqi,
don IDEA da hikimar zane sun cika
kwakwalwarta a daidai wannan lokacin,
so kawai take ta juyesu akan takarda don
kada su gudu.
181

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
​“Afuwan Habiby, Afuwan kaji?
Amma don Allah kada ka katseni”.
Zayyan ya rasa me take zanawa
haka da har ta kasa bashi attention dinta
ko yaya, ya karaso gabanta ya tsugunna
yana leka zanen, ya dora hannu saman
bayanta cikin wata irin siga ta kulawar
miji zuwa ga matar da yake matukar so. ​“To ko zan iya sanin me kike
zanawa haka? Arch. Safiyyah Rafindadi?
Na ga kamar ba gida ba, ba kuma Estate
ba”.
Sa a lokacin ta dago da murmushi
tana kallon sassanyar fuskarshi, da
kwantaccen sajensa ya kara ma fuskar
kwarjini, fuskar da bata taba gajiya da
kalla da sajenda bata gajiya da shafowa
da hannunta koyaushe. Yanzunma haka
ta kai hannu ta shafi sajen nasa with so
much love, tace.
​“Habiby yau tsegumi kakeso? To ba
wani abu bane nake zanawa irin naka ba,
182

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ko irin wanda ka sani, ni yau
“Ultra-Modern Market” ce nake zanawa
irin ta turawa.
Ka tuna sanda muka yi tafiyar nan
zuwa conference din “Ranar Masu Zane
ta Duniya (World Architecture Day) da
aka gayyace ka a birnin Berlin?” Muka
ga kasuwar nan ta zamani harka ce min
ta burge ka? Da zaka iya da ka zana ta? To tun lokacin abun na raina, ina
jiran ranar da zan samu nutsuwa in
kwaikwayeta in zana.
To tsarin ta na dauka yanzu nake
nawa zanen a kansa”.
Da admiration sosai yake kallon
zanen nata yana mamaki, kodayake in dai
Sophiensa ce ai bai kamata yayi mamaki
ba, in dai akan hikimar zane ne, in bata
fishi ba, to zasu yi kunnen Doki, duk da
yana gaba da ita a kwalin karatu. Ya shiga tattara takardun wuri
guda yana turesu gefe yana fadin.
183

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
“Ko kina sane da cewa kuma yau ce
ranar cin abincin Zayyan ta duniya? It’s
my lunch time! Yanzu dai ayi hakuri da
zanennan a kawomin abinci, yunwa sosai
nake ji a duniya, in na gama kuma a
dumama min shimfida irin dumamawar
da aka dade ba’a yi min ba.
Baby, na rasa gane kan ki tun last
week kike avoiding dina cikin dabara”.
Murmushi tayi, don ta gane me
yake nufi, ta dauki kayan zanen da
takardun ta kai daya dakin ta adana su ta
dawo. Kuma daga lokacin ta manta da
zancen sabgar zanen kasuwa ta shiga
hidimar hadawa Habibinta abinci, mai rai
da lafiya wanda ta tabbatar zai gamsar da
shi.
Lafiya kalau suka ci abincin dare
tare, tana shiga toilet da zummar tayi
wanka, sai taga isowar bakon watanta.
Tsaki tayi, daga haka ta soma
kuncin rai ita kadai, sau tari hakan ce
184

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
take kasancewa da ita duk sanda taga
isowar period dinta, ta shiga kunci kenan,
tunda alama ce ta cewa ciki dai bai samu
ba har yanzu.
Haka tayi wankan cikin dacin rai
da bacin rai mai tsanani, domin ta saka
rai, dama kuma in period dinta ya kusa,
sau da dama behaviour dinta ya kan dan
canza, ta zama ‘moody’. Shi bai san dalili
ba amma a satinnan ya lura ta rage shige
masa, kuma tana kakkauce ma
haduwarsu a shimfida. Ashe dalilin duk
wannan ne, period ne ya kusa yin sallama.
Ta fito daga wankan kenan ta
ganshi kwance a gadonsu daga shi sai
shorts, yayi dai-dai a tsakiyar gado irinna
jiran isowar uwargida yana waya, sai
kawai taji ranta n abaci, aikin Habiby
kenan soyayya da iya romance amma bai
damu da haihuwa ba, Safiyyah ta fada a
ranta. Daga yadda yake wayar (with
respect) ta fahimci shi da Baba Murtala
ne.
185

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sai ta zauna akan stool din mudubi
tana shafa lotion a jikinta a hankali, cikin
son bata masa lokaci da rashin kuzari a
tare da ita. Me ke damun Sophie ne?
Idonsa ya kai ga saman kirjinta
wanda ya ciko sosai saboda haihuwar
data yi duk jikinta ya zama danye (fresh)
dashi.
Sha’awar matar tashi da baya taba
gundura da ita (duk da baya samun
yadda yakeso daga gareta saboda
alkunyarta) nan take tazo mashi. Gashi
yanada tafiya Lagos a washegari, kan
wani muhimmin project na ginin flyover
da Baba Murtala ya samo masa kwangilar
yinsa.
Hasali Baba Murtala aka baiwa
kwangilar, amma ya barwa dan nasa, yace
shi yayi madadinsa, don yana son ya
shigar dashi harkar ginin bridges da
flyovers bayan harkarsu da yafi sabawa
da ita ta ‘Real Estate’.
186

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya gama wayar ya ajiyeta a gefensa,
a lokacin ita kuma Safiyyah ta gama
laqailaqan shafa man nata, ta sanya
kayan barcinta masu dan kauri, tazo ta
haye can kuryar gado ta kwanta, ta ja
lallausar duvet ta rufe rabin jikinta. Zayyan ba haka yaken son ganinta
ba, don alamu ne na bazata marabceshi
ba, shikuma gaskiya yau din wata
sabuwar samartaka ce ta bakunceshi, jin
kansa yake at the zenith of his thirties. Ga
tafiyar da zaiyi a washegari wadda zata
daukeshi kusan sati biyu babu dumin
Safiyyah a gefe.
Yayi maza ya daga duvet din nata
shima ya shige, ya mika hannu yayi musu
light up. Amma da ya kai hannunshi
gareta janyewa tayi kamar yasaka mata
shocking, ta koma can karshen gado ta
lafe abinta, tana faman kuncin rai. Da matukar lallashi a cikin sautinsa
da taushin muryar da ba koyaushe yake
mata amfani dashi ba, Zayyan yace “kada
187

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ki mun haka Sophie. I’m thirsty. Na lura
fa tun shekaranjiya kike avoiding
haduwarmu a gadon nan, kike min
wannan ciccijewar dana kasa gane ta
mecece. Ko meye dalilin wannan kuncin
ran da kikeyi yanzu?” Murya can kasa Safiyyah tace,
“Nifa babu komai”.
Zayyan ya mirgina ya shige cikin
jikin Safiyyah da azama, sosai yabi ya
kanainayeta ta ko’ina ya like mata, ya
ninketa bakidaya a cikin kirjinsa, yana
gaya mata cikin radar jan hankalin
masoyi da iya lallashin mace. “Idan kika juya min baya a daren
yau, komai zai iya faruwa dani Sophie,
kin san ke ce kadai maganin damuwar
nan tawa, daga ke banida wata.
Babu wani uzurinki da zan iya
karba yau, sati guda kenan kina doje min,
alhalin ban yi miki laifin komai ba”.
188

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya kai bakinsa saitin kunnenta yana
cewa da ita cikin rada “hakurina ya kare
Safiyyah, ki dubi girman Allah ki dubi
darajar aure ki karbeni ko one round ne,
haba Sophie me kike so inyi ne?” Maganarsa ta karshen nan har
kunya ta bata. Amma Safiyyah ko gezau,
don yau wani miskilanci ne ya sameta
babu gaira babu dalili, tayi kememe tayi
kemadagas ta ki yarda da shi da
lallashinsa. Ta kuma kasa bude baki tayi
masa bayanin cewa period dinta ya zo, ya
canza mood dinta, don ta san kota fada
din, in dai Zayyan ne ba hakura zai yi ba,
bazai fasa cewa (she should try and find
another way to comfort him) ba, ita kam
ta fara gajiya da nacin Zayyan, tun bayan
data haihu abin nasa karuwa yake,
mutum ne very romantic sosai.
Ita bata san cewa yanzu ne ta zama
mace sosai a wurinsa ba, yafi samun
nutsuwa da gamsuwa da ita a yanzu,
fiyeda kafin ta haihu, tunda ta yada jego
189

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ya koma sabon ango shikuma, ya laqe
mata kamar kaska, don tafi masa gardi da
zaqi yanzun.
​Wannan ya biyo bayan kayan
gyaran da Yaya Zubaina ta aiko mata na
“Manzil Alwafir” dake Kaduna.
(Duk wasu matsaloli na aphrodisiac
ko gyaran aure “Manzil Alwafir” sunada
maganinsu, including treatment na cutar
PCOS da sauran matsalolin da suka shafi
mata don gyara matantaka da inganta
rayuwar aure. Manzil na aika kayansu ko’ina
cikin Najeriya, za’a iya tuntubarsu ta
wannan layin waya 09045065562).
Safiyyah kam ta karba ne gun
karamar uwarta Anti Dije bayan
haihuwarta tayi amfani da kayan Manzil
yadda ya kamata, bata ko san amfaninsu
ba, bata kuma san abinda zasu jawo mata
kenan ba.
190

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Yayi lallashin, yayi ban bakin, yayi
ban hakurin in ma laifi yayi mata bai sani
ba, amma Safiyyah ko a jikinta, ta ki
bashi access din komai, koda kuwa na ya
samu damar da zai sumbaceta ne. A
karshe ma da ya fitineta da lallashin sai ta
bara baki ta abinda ke cin ranta.
“Ni kam wai don Allah Habiby, na
dauka don samun haihuwa ake wahalar
yin abinnan?
To ni gara a daina kwata-kwata,
tunda ba haihuwa zai ke sa in yi ba…..”.
Ta fada masa hakan cikin kuncin
rai, tareda kankame jikinta waje daya,
har da kyallin hawaye cikin idonta da
yake iya gani ta dan hasken fitilar dim
light. Wannan maganar data fada ne tasa
ya fusata, ransa ya baci, komai ya fita
kansa, saiya janye jikinsa ya juya mata
baya, yayi rub da ciki bisa cikinsa ya
rungume hannuwansa a kirjinsa, domin
191

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sophie ta gama kular dashi. Zayyan ya
rufe idanunsa yana yaki da zuciyarsa mai
cewa ya saka karfinsa na da namiji yau a
kan Sophie kawai, ta haka ne zai goge
rainin da ya fahimci ya fara samun
muhalli a tsakaninsu, wato ya kwaci
hakkinsa kota wane hali jikin Safiyyah
tunda dai Allah shaida ne kan bashi da
wata matar sai ita, baida inda zai je ya
sauke wannan bukatan sai gurinta. Ga
tafiya ta sati har biyu a gabansa.
Wata zuciyar na tankwarashi da
cewa “Sophie ce, His alter ego!
Matsayinta ya wuce (marital rape) a
gareshi, kada Allah ya nuna masa ranar
da zai sakama Safiyyah karfi, don biyan
bukatar ransa ko saboda hutun gangar
jikinsa, yace a ransa wato lamarin mace
babu abinda ya kaishi ban takaici da ban
haushi wani lokacin, musamman idan
kayi saken da ta san karfin soyayyarta a
ranka.
192

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
To daga sannan ka gama shiga uku,
ka gama yawo a hannunta.
Yace a ransa to ita Safiyyah bayan
sanin weak point dinsa data riga tayi, cikin
lamarinta na yanzu harda rashin godiya,
tunda ta ina ya rage ta ko ya kuskure ma
nata bukatun data kasa haihuwar, har da
zata gaya masa bakar magana haka, wai
tarayyar su ta auratayya kullum bata
sakawa ta haihu?
Wannan maganar ce tasa ya
hakura, ya juya mata baya shima amma
ya kasa ko runtsawa a daren har goshin
asubahi.
A takaice Zayyan shi kadai yasan
irin azabar da ya dandana shi da
zuciyarsa a daren yau.
Amma Safiyyah ko a jikinta, tace
banda sawa da yake tayi tana jika
gashinta yana kakkaryewa kullum saboda
yawan wanka, ita wahala abin yake bata
yanzu, saboda bata yin komai cikin dadin
193

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
rai kamar can baya. Hankalin ta ya bar
kan soyayyar miji, kacokam ya koma na
soyayyar samun Dan kanta.
Abin ya fita kanta kwatakwata
tunda bai sawa ta samu cikin haihuwa.
Kamar akan dole take bashi hakkin nasa
yanzu, tun bayan haihuwarta.
Wanda hakan ya jefa shi a damuwa
da rashin samun satisfaction da ita yanzu,
idan ma ta kyale shi din kenan, baya
samun yadda yake so daga gareta, don ta
dauke zuciyarta daga kan sexual life
dinsu, ta mayar kacokam kan son
haihuwa.
Da safe ta hada masa breakfast
amma ko kallonta bai yi ba itada tebirin
breakfast din nata, ya dau wanka da
karin guga, ya murza hadaddiyar hular
‘Tonak’ a saman goshinsa, kai sai ka
rantse da Allah ba shine ya kwana
begging matarshi yana matse ciki tana
jansa a kasa ba sabida yadda yabi ya
daure fuskar nan tam. Ta gaisheshi, karo
194

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
na farko da yaki amsa gaisuwar Sophie ta
safe, a tsayin shekarunsu goma da aure.
Bata damu ba, ta hau gyaran dakin
da suka kwana tana fadi a ranta Zayyan
sai da haka, in ba haka ba tsofeta zaiyi da
kwarzaba irin tasa don baya gajiya, tun
bata ajiye masu yi mata addu’a ba. Ya dauki ‘brief case’ din shi ya fice,
sai ta ‘text messege’ ya gaya mata ya
kama hanyar Lagos, a takaice ya gaya
mata zasu fara project din da ya gaya
mata shi da Baba Murtala. Bata ga text din nasa ba sai bayan
ya jima da barin gidan, har ya shiga jirgi
lokacin, jikinta kuma sai yayi sanyi
lokacin data karanta, bata san tafiya ce
dashi ba, ta kuma ga rashin kyautawarta
ga Habiby dinta koda ace ba tafiya zaiyi
ba, wannan ne karo na farko daya taba yi
mata sallamar tafiya wani gari a waya.
​Ta ji babu dadi har ranta, anya
Zayyan ya cancanci unfavourable
195

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
treatment din da take masa a satinnan,
don kawai bata jin dadin zuciyarta kan
rashin haihuwa sai ta huce komai a
kansa?
​Kada dai ya kasance shaidan ne
yake yi mata ingiza mai kantu, don ta
zama butulu, ungrateful ga ni’imomin
Ubangiji a gareta, ta zama mara godiyar
Allah da rashin gode masa bias alfarmar
mijin kwarai daya bata? ​A take jikinta ya kara yin la’asar, ta
yi maza ta shiga kiran layukan wayarsa,
amma cikin rashin sa’a a lokacin Zayyan
ya shigar da wayarsa ‘flight mode’ don ya
shiga jirgi ha ra zarga belt, ya kashe
dukkan wayoyinsa. Bai kunna ba har saida ya sauka a
filin jirgin Murtala Mohammed, inda ya
tarar da “Seyi”, direban gidan Baba
Murtala kenan ya na jiran saukarshi.
Seyi ya dauke shi da trolly dinsa
zuwa gidan Arch. Murtala Babangida
196

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
dake Ikoyi, da bacin ran Safiyyah fal
ransa.
****

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login