Showing 45001 words to 48000 words out of 48692 words
Chapter 16 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
zuciya.
Wai Zayyan ne ya gaya mata da bakinsa
yau zai kara aure, don ya samo mata Ds
daga gareshi, in ba ta yi da gaske ta
yakice al’amarin daga ranta ba zai iya
zauta kwakwalwarta.
Ko bayan da aka sha ruwa addu’a
ta yi ta musamman a kan in tana da
rabon haihuwa da Zayyan Allah ya kawo
wannan rabon cikin gaggawa. Don ta
tabbata bada wasa yake yi ba, da ya ce
yana so zai kara aure. Dansa ko ‘yarsa ne
kadai za su maye mata gurbinsa a yanzu
265
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
da ya fara tunanin kawo wata macen
cikin rayuwarsu.
Ta san tabbas daga wannan lokacin
ta rasa previous Habiby dinta. Bazai kara
dawowa irinna baya ba.
Ko da dai dama daga tafiyarsa
Lagos zuwa yanzu ta san wannan ba
Zayyan dinta data sani a baya bane, duk
da yana kokarin wanke mata zuciya da
kalamai na fatar baki, a banza man kare
a wurinta. Bayan ta yi sallar magriba ta sha
ruwa, ta samu wayar Aunty Zubaina,
tana dauka ko gaisawa Antin ba ta bari
sun yi ba, tace,
“Safiyyah kina da masaniyar abin
da ke faruwa kuwa, kuma da yardarki da
amincewarki ake nema wa Zayyan auren
diyar Baba Murtala?”
Sai da ta ji kirjinta ya bada dam!
Bana jin maganar karin auren ba a’ah, na
jin ko wa Zayyan zai aura. Amma tuni ta
266
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sa ma ranta salama don haka ta ce wa
Anti Zubaina cikin kasalalliyar murya.
“Ya dai gaya min ko na amince ya
kara aure? Kuma jiya-jiya ne muka yi
zancen Anti”.
Anti Zubaina ta ce, “To ai an gama
komai, gobe za a kai lefe da kudin aure
duka. Ya dace yayi miki cikakken bayani,
ni banason munafurcin maza in sun tashi
fitinar karin aure. Amma ki bar ni da shi, zan gamu da
shi wallahi, ba haka ake fada wa
uwargida neman aure ba”.
Kasa cewa komai Safiyyah ta yi,
don yanzu ta gama gano dalilin Zayyan
na share ta a tafiyarsa Lagos, wato ya yi
gam da katar da ‘yar masu kudi burin
mahaifiyarsa. Baba Murtala ya damesu ya shanye
Baba Bello a kudi da tarin dukiya balle
Zayyan. Ko me suke dashi yau a dalilin
taimakon Baba Murtala ne. Safiyyah ta
kara jin tausayin kanta, me zata yi yanzu?
267
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Kuma me za ta ce a kai, banda yi musu
fatan alkhairi?
Ammi kawai ta iya kira jikinta
babu lakka, kuma ta kasa hawaye ko taji
dama dama. Tana ajiyar zuciya ta labarta
ma Ammi komai. A karshe ta ce,
"ki yi min addu’a Ammi, zuciyata
tana tafarfasa, Zayyan ya shammaceni,
abu ne da ban taba zato daga gareshi ba,
saboda na tabbata wannan auren Zayyan
zai yi shi ne don radin kansa, babu wanda
ya tursasa shi ga yinsa. Amma Ammi da a ce na haihu ko
sau daya ne, ba zan taba damuwa don
Zayyan ya kara aure ba”.
Tausayin ‘yar tata ya kama Ammi
Hafsatu, ba tun yau ba tana sunsuno
ranar faruwar hakan ga Safiyyah, duba
da matsalar rashin haihuwarta da
yanayin yadda mahaifiyarsa ke
alakantarta, harda ita kanta Ammin. Babu wata mu’amala ta surukuta
ko girmamawa ko kulawa da ta ke samu
268
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
daga Hajiya Fatu a matsayinta na wadda
ta wanke ‘ya sukutum ta basu. Babu ko
gaisuwar mutunci ta zuwa gida kota
waya, rabonta da su hadu ma da Haj.
Fatu har ta manta, amma wace ita da za
ta hana su aure don su samu haihuwar da
Safiyya ta kasa yi musu?
Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta
shiga lallashin diyarta. Lallashi da
karfafawa irin wanda ya dace kowacce
uwa ta gari ta yi wa ‘yarta.
Ta ce, “Ki kwantar da hankalinki
Nana Safiyya, kishiya ba kanki farau ba,
haka rashin haihuwa. Kedai ki yi zaman
aure domin bautar Allah ki kyalesu, in ya
so tazo ta haifi ‘ya’ya dozen. Ubangiji Subhanahu wata’ala da
kanSa, ya ce Yana jin kunyarku (matan
da bai baiwa haihuwa a duniya ba).
Ki dauki karin auren nasa a
matsayin kaddararsa da taki, ba a
matsayin gazawarki ko kasawarki ba.
269
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah na yarda da tarbiyyar da
muka baki, kada kiyi amfani da hakan ki
muzguna wa mijinki. Ki masa uzuri sau
saba’in da Allah ya ce ki yi masa.
Albarkarmu na tare dake in Sha Allah ba
za ki taba wulakanta a dalilin rashin
haihuwa ba”.
Nasihar Ammi ta karfafe ta, ta zuba
mata wani kwarin guiwa. Tun daga ranar
sai ta maida komai ba komai ba, ta shiga
harkokinta.
Koda Zayyan ya dawo daga Katsina
bayan an gama komai na aurenshi da
Azeezah sosai ya ga canji daga gare ta, ta
shiga hidima da shi yadda ta saba.
Ganin haka shi kuma ya saki
jikinsa ya ba ta labarin Azeezah kakaf!
Da yadda al’amura suka wakana a Lagos,
kai har irin hirarrakin da suka gudana
tsakaninsa da Azeezah sai da ya kwashe
gaya mata. Kullum yana kwantar mata da
hankali, yana kara jaddada mata
270
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
alkawarin adalci da na girman matsayinta
in Sha Allah bai taba canzawa a gareshi.
Kowa zai auro zai auro ta ne don ta haifi
Da ta bata, shi ba wata soyayya a
zuciyarsa bayan tata. Don haka Safiyyah ta kwantar da
hankalinta suka ci gaba da tsare-tsaren
auren shi da ita. Maimakon kayan fadar
kishiya tsabar kudi ya bata masu yawa, ya
ce ta yi duk abin da ta ke so da su, don ya
san bata da matsalar sutura. Ya gaya mata ko sisinsa bai yi ciwon
kai ba wajen hada wa Azeezah lefe, duk
Mama da Zubaidah ne suka yi masa.
Wannan ya kara tabbatarwa da
Sophie yanzu Mama ta yi surukar So.
Baffa ya auro mata classy suruka irin
wadda ta dade tana masa buri.
**** **** ****
An saka ranar daurin auren Zayyan da
Azeezah sati biyu masu zuwa, wata daya
da zuwan shi Lagos. Baya kiran Azeezah
271
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
a gaban Safiyyah, haka ko ita ta kira shi
in Safiyyah na wuri bai amsawa.
Ranar daurin auren na matsowa
fargabar Zayyan na karuwa saboda silent
treatment din Safiyyah gare shi. Ko da
can Safiyyah mai biyayya da yakanah ce,
da kula da shi, kai dai barta da kunya da
nuku-nuku a gado da kin yi masa yadda
yake so, da dressing irin yadda yake son
ta yi masa. Kullum Safiyyah kara samun
nutsuwa take saboda nasihohin Ammi,
kullum sai Ammi ta kira ta a waya ta
karfafe ta, ta kuma gaya mata wani sirri
cewa.
"Babban abinda ke kama miji, yasa
'guilt' ya baibaye shi in ya tsiri kara aure
shi ne biyayya ba fandare masa ba.
Saboda the more ta yi creating
distance a tsakaninsu, saboda kara
aurensa, the more amaryar za ta samu
damar kara shiga ransa da nesanta shi da
soyayyarta, ta kuma samarwa kanta
matsuguni a zuciyarsa".
272
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Har gobe Safiyyah tana matukar
son Zayyan dinta, in ma ta ce son ya ragu
ko ya tafi to ta fada ne don ta ji dadin
bakinta (out of frustration). Don haka
Safiyyah ta tattara kishi ta ajiye a gefe, ta
kuma barwa ranta cewa ko matar Zayyan
ta tare ba dai ta tsaya rigimar kishi da ita
ba.
In ma an karfafe shi ya yi auren ne
don a muzguna mata, ko a nuna mata
iyakarta ta rashin haihuwa, insha Allah
za ta rungume ‘ya’yan Zayyan kamar ita
ta haife su. Soyayyar nan tata da Zayyan
natural ce, ba abinda zai sameta da
yardar ubangiji saboda wani dalili na
karin aure da ba kansa farau ba.
Zayyan bai taba yi mata alkawarin
ba zai kara aure ba, ya dai yi mata
alkawari na soyayya da amana. Don haka
yanzu da auren ya zo masa bagatatan
tsakaninta da shi sai fatan alkhairi, da
addu’ar ya zamo mai adalci a gare su,
kamar yadda shima kullum yake fata.
273
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah ba ta tashi susucewa ba sai
ranar da ya ce ta hada mishi kaya a jakar
matafiya zai je wajen kanwarta a Lagos.
Daurin aure saura kwana uku lokacin.
Ganin ya dau sabon aski ya shigo da
sababbin dinkuna na alfarma, ya ce ta
zuba masa a jaka. Cikin dauriya duk ta
ke yin yadda ya ce, da ta zo daukar masa
turaren ‘Ultraviolet’ ne sai zuciyarta ta
idasa tsinkewa. Zayyan bai lura da cewa jikinta ya
hau rawa sannan idanunta sun cicciko da
kwalla ba, domin ta bashi baya tana zuge
jakar, bayan ta cusa turaren, ya ce.
"Am, Sophie kinga na manta in
gaya miki gobe Mama ta ce za'a zo a yi
kafin Azeezah don bayan daurin aure da
kwana uku Azeezah za ta tare".
To dama gidan tun sanda aka gina
shi tagwayen gidaje ya yi wa kansa a
matsayin (semi-detached bungalow) tun
sanda aka gina Sunset Estate.
274
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Don haka barin hagu ya bai wa
iyayen Azeezah su yi mata kafi.
Ai kuwa washegari an ga barin dukiya a
gidan Arch. Zayyan Bello Rafindadi.
Wasu ubansu-ubansu royal furnitures
kawai ake saukewa daga company a
gidan. Su Yaya Zubaida an kasa tsaye an
kasa zaune abin nema ya samu wai matar
dan sanda ta haifi barawo, kai ka ce diyar
gwamna Zayyan Bello ya auro, saboda
dukiyar da aka tamfatsa a sassan
Azeezah.
A can Lagos an fara biki na
alfarma, haka a Katsina Mama ta yi
gayya ta fita tsara an soma biki na
bugawa a "Ovasion", za a daura auren
Arch. Zayyan da Azeezah Murtala
washegari asabar a gidan kakanninta da
ke Masari a Katsina.
Bayan ya dawo daga Lagos duk
jikinsa ba lakka, saboda sabon nauyin
iyalin da ya tabbata zai dada hawa kansa.
Washegarin ranar ne daurin aure a
Masari zai je Katsina ne inda daga can
275
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
zasu dunguma zuwa main house dinsu
Azeezah. Inda acan za'a daura auren.
Safiyyah tun asubah tana kitchen sabida
shi yana barcin gajiya tun dawowarsa,
kafin ya tashi barci ta shirya musu karin
kumallo mai rai da motsi data san yanaso;
sinasir da waina da miyar ganyen
alayyahu, Ugu leaf da hanta.
Suka karya kumallo a dining kafin
ya shiga wanka tana ta faman tsokanarsa
wai ya fara kyallin goshi, tun ba'a je
dakin amarya ba. Harararta Zayyan yayi
ya shige toilet. Wajen wankan ma ita ta surka
masa ruwan wankan, ta zuba turaren
wanka mai dadin kamshi na desire dunhill
a cikin ruwan, sannan ta ajiye masa bath
gel dinsa na Cien a gefe da farin tawul, ta
juya za ta ja masa kofar, sai ya riko
hannunta cikin marairata da karaya.
“Sophie, karasa ladanki mana ki
cuda min baya… na rantse ba ni da karfi
yau”.
276
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Dariya ta yi ta ce a ranta, za ka ji
karfin sai zuwa dare inta iso”.
Wani abu kamar daci-daci a
makogaronta ya taso mata, wani tukuki
ya turnuke zuciyarta, don haka ta yi
saurin janye hannunta daga cikin nasa ta
fice ta rufo masa kofar, tana neman
hadiye abin nan da ya yi mata tsaye a
makogaro, amma ta kasa.
Tana bude baki don yin magana
kuma ta san fashewa za ta yi da kuka, ko
harshenta ya lankwashe ko ya karye
gabadaya, don haka yi masa shirun ta fice
da gudu-gudu shi ne mafi alkhairi a
gareta. Ya yi wankansa tsaf, ba karsashi ko
na kwabo a jikinsa, musamman saboda
shirun da Safiyyah ta yi masa. Ta kuma yi
tafiyarta daga toilet din ko kallonsa bata
kara yi ba. Yana shiryawa a dakinsa cikin wata
sabuwar bugaggiyar shadda ‘yar ubansu
277
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wadda Baba Murtala ya dinka masa don
fitar daurin aure.
Yana so ya kira Sophie ta daura
masa links na hannun rigarshi da
maballin wuyansa yadda ta saba, ya ji
nauyin hakan ya kyale ta. Ko ba komai ta
yi masa kokarin da ‘psyche’ dinsa bai
taba bashi ba. Da ya kammala shiryawa ya same
ta a dakinta tana faman fiddo kaya daga
wardrove tana shiryawa duk don ta
maida kanta busy, ta hana kanta zama
shiru balle wani mugun tunanin ya sarke
ta. Daga bakin kofa ya tsaya hannayensa
biyu zube cikin aljihu, ya yi kokarin su
hada ido, amma Safiyya ta ki. Ta cigaba da
ninke kaya.
Ba ya son ya taba jikinta kada ya
jangwalo rauninta, don haka ya yi
magana daga inda yake tsaye.
“Mun wuce Masari daurin aure sai
wajen dare kuma in taron mata ya watse
zan dawo Sophie”.
278
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Safiyyah ta hadiye miyon bakinta ta
ce.
“Ällah ya sa a daura a sa’a, Allah
ya sa abokiyar arzikinmu ce, Allah ya
bada zuri’a mai albarka da ake
nema..…”
Wadannan kalaman na karshe ta
karasa su ne cikin rawar muryar da ba ta
so rauni ya fito a cikinta ba.
Shi kansa ji ya yi ya kasa daurewa,
don haka ya shigo cikin dakin sosai ya
karasa ya rungume ta, ya ce.
“Ina rokon Allah ya sa zuri’ar nan
ta fara samuwa daga gare ki Sophie, ina
kara rokonSa ya fidda ni kunyarki wajen
adalci.
Ina jaddada rokona gare shi da Ya
ba ni zuri’ar nan tare da ke komai rashin
yawanta.
Kada Allah ya nuna min ranar da
zan fifita wata a kanki, a dalilin
haihuwa…”
279
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Su duka jikinsu da muryoyinsu
rawa suke yi, Safiyyah na amsawa da
"ameen".
“Allah ya fara kwantar da babyna a
nan..." (ya sanya hannu kasan mararta)
kafin kowacce mace ta samu wannan
babbar alfarmar…...”
Fatar bakin Safiyyah na rawa ta
kara amsawa da "ameen".
Da tsakanin mutuwar jiki Zayyan
ya bar dakin Sophie, yayin da Safiyyah ta
yi zaune dirshan a gefen gadonta ta sanya
fuskarta cikin tafukanta rike da singlet
dinshi da ya cire, ta cukuikuiye fuskarta a
cikin singiletin, amma ba kuka ta ke yi ba. Karfe hudu na yammacin ranar
waliyyai suka daura auren Arch. Zayyan
Bello Rafindadi da Azeezah Murtala
Babangida, bisa sadaki na burga, wanda
Mama ta bayar na wara-waran zinare
manya guda uku.
280
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Daga nan aka wuce reception na
maza, already amarya tana Abuja tun jiya
gidan mahaifinta da ke Katampe.
Sai yamma lis ya dawo Abuja,
kuma ko da ya sauka a Abuja bai shiga
gidansa ba Park din cikin Estate din ya
nufa ya tsaya a jikin ‘railer’ yana tunani,
daga baya ya wuce gidan amininsa
Habibu Nahuce, daidai lokacin da aka
kawo amarya Azizah dakinta.
Abin kunya har da Yaya Zubaida
aka yi shimfidar gadon amarya, su
Zaitoon kuwa sai yada ma Safiyyah
habaici ake ana cewa, uwargida sai kin yi
hakuri fah, ah toh Azeezah ‘yar babban
gida ce shi ya sa za ki ga komai nata
daban.
Kada ki ga furnitures ubansu ‘yan
Dubai ki dauka Yaya Baffa ne ya saya
mata. Kin san da uba ake ado ba da miji
ba”.
Kasancewar Aunty Dije ta zo ma
Safiyyah dannar kirji a ranar, ta kuma ji
281
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
me suka ce, sai ta tashi zaune daga
kishingidarta, a ranta tace lallai Zahra da
Zaitoon basu da kunya, sai ta ce musu,
“Kun manta kuma wani lokacin
abin an ce abin fini uba in fiki miji ne?
Allah na tuba Safiyyah tun asalinta ba ta
son tarkace ita, dan English parlon nan
nata ya ishe ta, tunda ba ‘yar sarki ba ce,
ba 'yar gwamna ko