Showing 6001 words to 9000 words out of 48692 words
Chapter 3 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
TAKORI 2025
A karshe dole nabi hanyar da ta
bulle dani, yanzu haka yara na biyu.
Wannan zuwan kuwa na zo ne likita ta
rufe min bakin mahaifa in samu in huta
da haihuwar haka ko na shekara biyu
ne, yarana kuma su kara girma”. Safiyyah sakin baki tayi tana kallon
matar, wadda ta laqawa suna “fadi ba’a
tambayeki ba”. Hankalinta ya dan fara
daukuwa ga abinda matar take labarta
mata, amma bata gane zaurancen
hanyar da take nufi ta bi, wadda ta bulle
da ita din ba.
Zata so taji wannan kowacce irin
hanya ce, da har haihuwar tazo ta isheta
tana neman dakatarwa, ko itama ta
gwada, ko Allah zai sa ta dace.
Safiyyah sai ta saki jiki da matar
nan wadda tace sunanta Ammara, nan
suka shiga hirar haihuwa, kamar sun
dade da sanin juna, abinki da irin ka
gamu da mai irin ciwonka, wanda ya
rigaka samun waraka.
39
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ammara tace “shekaruna ashirin
da aure kafin na samu haihuwar yaran
da nake dasu yanzu. Kema kinsan mun
sha damuwa nida maigidan”.
Safiyyah kuma tace “ita kuma
shekara takwas kenan da aure, ko bari
bata taba yi ba”. Sai hira ta kara
mikawa tsakaninsu akan hakan.
Ammara tace “haka kawai naji kin
kwanta min a rai, gaki kyakkyawa ga
kuruciya ga hankali, ga hutu, banda
haka banida sakewa da bakin fuska
sam. Naga damuwa baro-baro a tare
dake, haka kawai yarinyar ki dake zaki
bar ciwon damuwa ya kamaki a banza
saboda haihuwar da samunta ruwan sha
yafi ta saukin sha. ‘Yar uwa ki rabu da wani yawon
asibiti ana cin kudinki a banza, kibi
hanyar da zata bulle dake kawai.
40
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Rayuwar nan saida dan kaucewa
sannan ake ganin daidai”.
Ta kara saka Safiyyah a duhu, har
ta kai da tambayarta “dan kaucewa
kamar yaya shin? In ji dai ba kauce
hanya ta addini ba?”
Ammara tace “kusan hakane,
amma ba sosai ba, zauna nan ‘yar uwa
kiyita walagigin bin likitoci suna
jagwalgwala miki mahaifa suna cika ki
da surutan wofi, kuma basu da maganin
da zasu baki ki haihun”. Nan ta bude wayarta ta nuna mata
hotonta tare da maigidanta da
kyawawan yaransu maza biyu kanana
kamar haihuwar kwanika, nan ta kara
brainwashing Safiyyah wadda a lokacin
nan ba abinda ta dauka a matsayin farin
ciki da kwanciyar hankalin dan adam
sama da ‘ya’ya.
Haka Ammara tayi ta kwance kan
Sophie, tana kara zurmata ga bin irin
41
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
hanyar data bi ta samu haihuwa. Wadda
har zuwa lokacin ta ki fitowa fili ta
fadeta sai indirectly take maganar.
Allah sarki Sophie, ita da kanta
bata san ta zama desperate ga son
haihuwa ba sai yau. Ta yadda har ta dan
rasa kyakkyawan tunaninta ta kuma
kasa zurfafashi, tarbiyyar shekaru
kusan 28 da ilmin addini da mahaifinta
Malam ya bata basu sa ta yi tunanin
meye ita wannan hanyar da ake ta
muku-muku da ita ba’a fito da ita fili an
gaya mata ba?
Haka ilmin bokonta duk bai yi
amfani a wannan lokacin ba. Biyan
bukata kawai take nema.
Ammara tayi nasarar yiwa Sophie
famfo mai yawa a wannan danzaman
nasu, har take ce mata ta rabu da
zancen kawai na mijinta (Zayyan) da
yake cewa shi bai damu ba, tace zance
ne kawai na mazan da ke son kwanciyar
hankalin matansu, karya yake yi yace
42
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wai bai damu da haihuwa ba karya ne,
maza sun fi mata son ‘ya’ya.
Ta kara jefa Sophie a tagumi da
damuwa mai tsanani. Tace “da yawan
alfarmomin da take samu yanzu a wurin
mijinta (wanda babban dan siyasa ne a
jihar Kano) a baya data kasa haihuwa
bata samesu ko guda ba”. Tace mata “saboda matsalar rashin
haihuwa taga bala’in dangin miji
kala-kala, dana uban miji, don
mahaifiyarsa ta jima da rasuwa.
Tace bata samu daidaito da
martaba a idon su ba sai bayan data yi
musu haihuwar fari, Da namiji, tace
uban mijinta ya kafa mata karan tsana,
har ya taba yin umarnin da aka saketa
saki daya, tace da Safiyyah “a karshe
dana ga ba sarki sai Allah sai na
bazama, na hada da (dan kaucewa)
sannan na samu biyan bukata.
43
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Wadda a halin yanzu ta sayomin
kwanciyar hankali a gidana, da zama
lafiya da miji na da ubansa da ‘yan
uwansa.
Nice tauraruwarsu, tunda na aje
masu ‘ya’ya kuma maza”.
Safiyyah wadda a cikin kowanne
harafi na labarin da Ammara ke bata
soyayyarta da da burinta da haihuwa na
karuwa (to an extent), haka tsoron ta da
rashin samunta shima yana ta kara
ninkuwa. Har taji a ranta ko dai itama
ta bi hanyar data bulle da Ammaran,
komai tsananinta?
Wadda har yanzu dai bata kai ga yi
mata bayaninta baro-baro ba, aka kira
Safiyyah ganin likita, Ammara tace zata
jirata ta fito itama ta shiga ta fito, sai su
karasa maganar. **** **** ****
Safiyyah a teburin Dr. Galadanci.
Bayan ta gaya mata matsalarta na cewa
44
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
shekarun ta 8 da aure babu haihuwa
babu alamarta, likitar tayi mata ‘yan
tambayoyi na cewa ko ta taba ganin
likita akan matsalar? Ta ce eh, sun je
ABUTH da mijinta ba jimawa sun ga
gynaecologist, sai Dr Galadanci ta nemi
ganin result din ABUTH din.
Sakamakon Safiyyah na ABUTH
shi likitar ta karba ta fara budewa, sai
taga cewa ba wani banbanci da duka
gwajegwajen da itama zatayi mata. Duk
da haka Dr. Galadanchi tayi nata
binciken yadda ya kamata ta kuma ce
Safiyyah ta koma reception ta dan jira
fitowar sakamako.
Wannan gap din na jiran
sakamako ya baiwa Ammara da
Safiyyah damar sake hadewa a waiting
lounge suka dora daga inda suka tsaya
kafin sakamakon Safiyyah ya kammala. Safiyyah ta kasa maida kwadayinta
kan haihuwa da labarin Ammara, har
tace da ita don Allah ta gaya mata
45
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kowacce irin hanya ce hanyar data bi ta
samu haihuwa, Ammara tace “da dan
wuya fa, amma in har kin yarda yafi
komai sauki, tunda dai ba a garinnan na
Kano kike ba zuwa kikayi kuma a yau
zaki koma inda kike, mafi kyau shine a
yau muje na raka ki, da zafi-zafi akan
bugi karfe ‘yar uwa, daga can zaki samu
motar Zaria tunda kan titin Zaria ne
kauyen yake dama, ba sai kin dawo ta
Kano ba zaki samu mota daga can har
Zaria. Tafiyar mintuna talatin ce kacal
daga Kano zuwa kauyen na Daka-Tsalle.
“Kauye kuma?” Safiyyah ta
tambayi Ammara, ta ce “Eh a can ne
malamin yake. Koyaushe aka je kuma
ana samun shi saidai layi”. A can kasan
ran Sophie taji dan tsoro, ta ji fargaba
da darsuwar wani abu, saboda dai ta
fahimci komai yanzu, wato ta hanyar
bin malamai ake samun haihuwa.
Amma data tuno gore-goren Mama
Fatu da ‘ya’yanta, ta kuma tuna cewa
46
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
‘ya’ya fa zata samu itama kamar kowa,
sannan wadanda su kadai ne zasu dorar
da soyayyarta da Zayyan dinta, da kara
mata matsayi a zuciyarsa data
mahaifiyarsa ta daina kyararta, kuma
sune kadai (‘ya’yan) zasu tsaya tare tare
da ita a ranar da kowa ya gujeta ko ya
juya mata baya ko ranar da bata da
karfi ko ta tsufa, amfanin haihuwa da
‘ya’ya yanada yawan da bazai kidayu
ba, sune zasu kula da ita idan bata da
lafiya, sune….sune…sune komai na
uwarsu kamar yadda suka zama sanyin
idaniya ga Ammi, aminanta abokan
shawararta, itada Sabah, Rayyah da
Rayha.
Amfanin haihuwa yanada yawan da
bazai lissafu ba, kuma damuwar rashin
ta yana da girman da zaisa ka gane
dalilin halin yanayin dokantuwa da
desperation din da ita Safiyyah ta samu
kanta a ciki.
47
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Har sai ranar daya faru gareka,
wato ranar daka budi ido shekarunka
kusan goma da aure babu ko barin ciki
balle batan wata a tare da kai sannan
zaka gane irin yanayin data ke ciki. Sakamakon binciken Dr.
Galadanchi dai ya nuna kusan abu daya
dai dana Dr. Muwadda Shinkafi ta
ABUTH. Bakinsu yazo daya cewa;
polycystic ovary syndrome (pcos) shi ya
hana Safiyya ovulating. Fasihiyar Likitar tace “amma ki
kwantar da hankalinki ke da mijinki
duk kuna da kwan haihuwa, nashi kwan
lafiya kalau yake. Amma naki kwan
baida kwaliti (inganci) a dalilin cutar
‘polycystic ovary syndrome’. PCOS cuta ce wadda ‘cyst’ wato
‘maruru’ yake fitowa a cikin ‘ovary’ din
mace (wajen kwan haihuwa) wanda
yake hana mace ‘ovulation’ har hakan
ya haifar da rashin haihuwa. Akwai
mata da yawa dake fama da lalurar pcos
48
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wadanda basu san sunada shi ba, haka
akwai da yawa da alamun pcos ko daya
baya nunawa a jikinsu, misali daga cikin
alamominsa akwai fitowar gashi a kirji
kona kasan fuska da sauransu. Kinada pcos wanda alamominsa
basu nuna a jikinki ba. Kuma babu
alamun cewa naki na gado ne. Pcos an fi
gadonsa, amma akwai wadanda keda shi
ba tareda sun gada ba. Ana kuma iya
maganceshi a hankali. Ta taimaka mata da shawarwarin
da suka kamata ta bata, ta rubuta mata
magunguna masu kyau da tsada da zasu
taimaka mata ta dauki ciki da taimakon
Ubangiji dana treatment data dorata
akai. Ta kuma bata lambar wayarta don
su dinga communicating kai tsaye ta
waya ba sai tazo ba, akan duk wani
cigaba da aka samu ko akasinsa, tace ta
yarje mata kiranta kai tsaye.
Dr. Galadanchi tace ita tana ganin
matsaloli na pcos iri-iri daga mata
49
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
wanda ke hana su haihuwa. Tace “a
yanzu dai babu likitan da zai ce miki ga
hakikanin lokacin da zaki iya samun
haihuwa sai dace, maigidanki na bibiyi
nashi results din daga binciken ABUTH
ya nuna lafiyarshi kalau, don haka kada
ki fidda rai, da taimakon Allah zaki iya
haihuwa a sanda Allah ya nufa with
treatment, ki dage da shan magungunan
nan dana rubuta miki”.
Wannan bayani ya kara jefa
Safiyyah cikin damuwa maimakon ya
sanyaya mata, har fiyeda damuwar da
result din ABUTH ya saka ta. Wannan
ya sa ta kara amanna da maganganun
kawarta ta Standard, wato Ammara,
tun kafin ta baro gaban teburin likitar.
Na cewa ba abinda likitoci zasu iya
kullawa wanda baya haihuwa, sai dai su
saka ka kayi ta asarar kudinka wajen
sayen kwayoyin banza, da surutun wofi
mara tabbas wadanda bazasu taimaka
maka da komai ba.
50
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A iya hange da tsinkayen Sophie na
lokacin sun amince ta yarda da
shawarar wannan matar kawai, in dai
hakanne kadai hanyar da zata samar da
haihuwa gareta da gaggawa, akwai
alamun gaskiya sosai a cikin
maganganunta, saboda babu alamun
karya ko damfara a tare da ita, ko wani
alfanu takeson samu daga gareta, face
taimako da haduwar jini, don da ganin
ta tafi karfin neman komai a wajen
wani.
Allah shaidarta ne akan cewa tayi
addu’a kuma tana kan yi, ta sha duk
wasu tsadaddun magungunan da Dr.
Shinkafi ta rubuta mata na tsayin
lokaci, wadanda ta duba ta ga duk
kusan irin wadanda Dr. Galadanci ta
rubuta mata yanzu ne ba wani banbanci
mai yawa. Amma Allah bai sa ta dace
ba. Watakila mafitar kadai itace
wannan da Ammara ta kawo.
51
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Watakila Allah ya nufeta da zuwa
Standard Hospital ne yau don ta samu
mai taimaka mata, don haka bari kawai
tayi kundumbala ta bi shawarar
Ammara, wannan dogon bayanin na
likitoci ya isheta, bata ko son sake jinsa. Tana wannan tunanin sai ga
Ammara dinma ta fito itama daga
ofishin likitar, take gayawa Safiyyah
cikin far’a,
“an daure min bakin mahaifa
(IUCD insertion), muna iya tafiya
yanzu”.
Suka fito tare, Ammara ta bude
motarta wata kankanuwar (Peageout
507). Ta bude ta shiga ta kuma mika
hannu ta budewa Safiyyah kofar gefenta
tace, “in har kin yarda da shawarata kin
kuma yarda bazan cuce ki ba, to kawai
ki shigo mu wuce in kaiki Daka-Tsalle.
Daga can zan saki a motar Zaria”.
52
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Without a second thought Safiyyah
ta amincewa ranta bin Ammara gidan
malami. Ta kama murfin mota ta bude
tashiga ta zauna ta rufe kofar.
Ammara ta fizgi motar da gudu
suka harba kan titi. Suka bullo ta
Tarauni suka hau kan Titin Naibawa
Zaria Road, wanda titi ne da zai kai ka
har garin Kura, ya kuma mike dakai
babu shan kwana har Daka-Tsalle. Suna tafe a hanya Ammara na tuki
tana kara yi mata famfo irin na matan
masu kudi da suka saba da harka da
malaman tsubbu. Take ce mata “ta saki
ranta, ta ganta kamar ace “kyat!” ta
zura da gudu. Tace ai da yawa yanzu
mata wayayyu sunfi ganewa zuwa wajen
malaman tsubbu akan duk wasu
matsaloli da suka sha musu kai ba
haihuwa kadai ba, ke har rashin lafiyar
da aka rasa gane kansa da gindinsa
malaman kauye sunada maganinsa,
hakan yafi musu sauki fiye da su
53
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
dauwama cikin bakin ciki da ciwon,
bacin rai da inferiority complex, irin na
rashin daukar ciki da haihuwa kamar
na kowacce mace, da kuma bibiyar
likitocin da bazasu kulla musu komai ba
sai karerayi da surutan banza. Tace Allah na tuba duk da ana cewa
zuwa wajen malaman tsubbu haramun
ne, to ai Allah mai afuwa ne mai gafara,
bayan bukatarka ta biya kawai sai kayi
sahihin tuba, da niyyar bazaka sake
aikatawa ba, ba shikenan ba?” Safiyyah sai ta soma shakkah, ta
soma tunanin anya ita a matsayinta na
Safiyyah diyar Malam Usman wanda ya
koyar dasu Tauheedin cewa ba’a yiwa
Allah wayo, kuma ba’a tursasashi,
saidai ayi ta rokonsa, anya wannan
hanyar ta dace da ita?
Idan ta bulle da Ammara, itama
zata bulle da ita ta samu haihuwa?
54
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ba duka abinda yayi wa ‘A’ ne yake
yiwa ‘B’ daidai ba.
Anya ma wannan hanya ta kaucewa
kamar yadda Ammara ta kirata ta
arziki da Alheri ce a gareta? In Ammi
da Malam da Zayyan suka ji ta taka
kafafunta wajen bokaye neman haihuwa
wane irin hukunci zasu yi mata? Tunda
dai taji ana daga baya sai ta tuba ta
shiga rudani.
Amma as a desperate and hopeful as
she is da haihuwa, sai tace bari dai ta
daure, in har zata samu haihuwa shi
Allah Gafurun Raheemu ne.
Daidai lokacin da suka isa dan
karamin kauyen, daga can nesa
Ammara ta faka motar tace gangarawa
zasu yi cikin gonar can dake gabansu,
har su tadda waccan bukkar da suke
hange daga nesa.
55
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Haka suka dage zannuwansu sabida
duwatsu suka soma taka tudu da
gangare suna shiga cikin gonar.
Cikin sa’arsu basu sha wahalar
samun dogon layi bama, mata biyu suka
tarar akan layin, don haka suka zauna
har suka gama suka fito kafin suma
suka saka kai a bukkar. Jikin Safiyyah ya soma sanyi da ta
yi arba da irin abubuwan dake cikin
bukkar, da babu kwana-kwana ko wani
shatale-tale sun fi kama da kayan tsafi.
Babu Ayar Alqur’ani ko daya ko
Gafakarsa, irin na shigifar mahaifinta,
wanda shima yake amsa sunan malami
kuma ake zuwa wajensa neman
taimako. Nan Qaho ne da kawunan matattun
dabbobi, can korrai ne da busassun
matattun