Showing 39001 words to 42000 words out of 48692 words
Chapter 14 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf
tsakaninmu nida kai
Baba. Uba ne da tilon Dan sa”. Kawai sai ya ga Baba Murtala ya
daddage ya fashe da kuka.
Jikin Zayyan ya yi sanyi, don ya
dauka zafin maganarsa Baba Murtala ya
ji, amma sai Baba ya kama hannunsa ya
rike yana kallonsa da kauna ido fal
hawaye. Ya ce, “Bar ganin ina zubda
hawaye, Bello na tuno. Ya taba cewa, ba
don ka yi aure da wuri ba da zai fi so ka
auri daya daga cikin ‘ya'yana mata don
kara dankon zumuncinmu. A lokacin sai na ce masa, kada ya
kara irin wannan maganar kada mu taba
tunanin yi muku auren hadi, wanda a
karshe bata zumunci yake zama.
Yau da ka furta da bakinka cewa,
kana son Azeezah, duk da yadda nake ta
232
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kushe ta a idanunka, tun zuwanka
Zayyan ban yabi halin Azeezah ko daya a
kunnenka ba, ko sau daya ban fadi
alkhairi akanta ba, sai hakan ya tuna min
da abinda Bello ya taba ce min a kanka. Ya taba ce min, yana son
baudaddiyar halayyarka, abin da kowa
bai so ko ake ganin disadvantage dinsa,
sau tari kai shi kake so. Abinda baya
burge kowa kai shi yake burgeka. Ya ce auren da ka yi shi kadai ya
mara maka baya saboda daga Hajiya
Fatu har ‘yan uwanka mata babu mai son
auren saboda diyar Alaramma ce kuma
stammerer. Da wannan nake cewa, ni kuma na
baka Azeezah, ka nemi yardarta, in Allah
ya sa ta amince da zarar mun gama
wannan project din, sai mu durfafi daurin
aurenku”. Shayin da basu sha ba kenan a yau,
haka suka fita suka barshi a wurin ya
huce.
233
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Baba Murtala farin ciki ya hana shi
sukuni, suna tafe a hanya direban Baban
na sharara gudu da su a bayan Hyundai
din Alhaji Murtala, sai ya ji Baba na
waya da Azeezah din. “Azeezah kina gida ne?”
“Mun fita ni da Mama Agege,
amma muna hanyar komawa gida yanzu
haka”.
Ya ce, “To ki shirya tarbar bako yau
da daddare, wajen karfe takwas in na
dawo gida”.
A dukunkune da fuska ta ajiye
wayar don ta yi tsammanin ya dauko
mata malamin da ya ce zai dauko ya
dinga koya mata karatun addini a gida ne.
Ita a wurinta ta wuce zama gaban
Malamin islamiyya yanzu. Baba Murtala
kuma ya ce, ko izfi goma ya san bata hada
ba.
Don haka ko da suka dawo gida ita
da Mama, bata yi wani kyakkyawan minti
234
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
goma a falo ba, ta gudu dakinta tasa
sakata.
Zayyan sai goshin magriba suka
dawo gidan shi da Baba, don haka
masallaci suka wuce kai tsaye, wanda ke
like da gidan Alhaji Murtala.
Can suka zauna suka bi jam'i har
bayan da aka idar da sallar isha. Ko a
masallacin Addu’a yake cikin ransa, idan
nemansa da Azeezah alkhairi ne a gare su,
shi da Safiyyah, Allah ya bashi kwarin
gwiwar iya tsayawa a gaban wata macen
da sunan neman soyayya ba Safiyyah
Dandume ba.
Da suka fito daga masallaci Baba ya
ce su wuce cikin gida su yi dinner, sai ya
ce ma Baba yana zuwa.
Ya koma masaukinsa ya sake
wanka, yau Zayyan kananun kaya ya
saka, shirt da wandon jeans baki Tommy
Hilfiger. Zai fesa turare kawai idanun
Sophie suka fado cikin nashi idanun, sai
ya fasa.
235
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Don ji ya yi tamkar hakan ya zama
cin fuska a gare ta.
“To na nawa kuma Malam Zayyan?
Tunda gaka ka dauki wankan zuwa zance
gun budurwa?”
Wata zuciyar ta tambaya ta kuma
kara masa da ce masa, “You are no longer
a trusted husband to Sophie, you are now a
“man” like other men, who are guided by
their heart desires and emotions”. Ma'ana; kai yanzu ba dan amanar
Safiyyah bane. Ba mijin da zata bugi kirji
ta yarda dashi bane. A yanzun daya kake
da sauran maza babu banbanci, wadanda
ke tafiya akan muradin zuciyarsu da
shaukin dake zukatansu". Wannan tunanin ne ya sa jikinsa
yin sanyi kalau, ya maida turaren
muhallinsa ya ajiye. Ya fasa fesawa.
Amma sai wata zuciyar ta tabbatar
masa da cewa, kara aure ba cin amana
bane ga maza, ba kuma cin fuska ne ga
Sophie ba. Karewa ma, yana ganin zai
236
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
nemi wannan auren ne don ya samar
mata maslaha a zama da shi, sannan ya
nemo mata nutsuwa da kwanciyar
hankalin data rasa a cikin rayuwarsu.
Muhimmi shine zai yi auren nan ne
ma don ta samu Da daga gareshi. Wanda
ya yi alkawarin nata ne da duk macen da
ya haifa, kuma hakan maslahar ta ce a
rayuwa da Mama, duk wata tsangwama,
duk wani zargi na ta mallake shi zai kau
daga idanun Mama yanzu.
Da wannan tunanin ya dan samu
karsashin nufar cikin gida. Wai shi
Zayyan ne yau zai je zance gun budurwa
ba Safiyyah ba. Yana taku a hankali
kamar ya fasa zuwa zancen, musamman
da yake jin tamkar idanun Safiyyah na
kallonsa.
Amma da ya tuno surar Azeezah
da iya kwalliyarta sai nan da nan wata
zuciyar ta ce,
"Zayyan kada ka bada maza mana,
polygamy ba kanka farau ba".
237
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya samu Baba yana waya, tuni an shirya
musu abincin dare. Ya yafito shi da
hannun damansa don ya zauna gefensa as
usual.
Sai da ya gama wayar sannan suka
fara cin abincin Baba na masa hira. Duk
da Baba Murtala ya fahimci yau ya kasa
sakin jikinsa da shi, shi ya sa ma yake
kara jan hirar tasu don ba ya so surukuta
ta shiga tsakaninsa da Dan nasa Zayyan
tun yanzu. Yafiso su ci gabada gudanar da
rayuwarsu normal ta uba da Da yadda
suke yinta.
Sai da suka kammala Baba Murtala
ya ce, ya shiga daga falon Hajiya Nana za
ta turo masa Azeezah.
Bai jima da zama ba Hajiya Nana ta
turo ta falon. Azeezah ta shigo fuska a
turbune don ta dauka ko Malamin
islamiyyar ne ya fara zuwa, don daga
Mama har Alhajinsu ba wanda ya gaya
mata cewa Zayyan ne. Don haka da ta
ganshi a falon ta kusan sakin fitsari daga
tsaye. Duk ta rude, domin kwarai Zayyan
238
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
mijin Safiyyah ke da kwarjini a idanun
‘yammata.
Rasa me za ta ce ta yi, tunda dai ai
ta san babu wata manufa da Baba zai turo
mata shi in ba ta neman aure ko dalili
makamancinsa ba.
“Zauna mana Azeezah”.
Zayyan ya fadi cikin tsare ta da idanunsa
da suka kara ruda ta.
Haka ta dosana ta zauna a nesa da
shi akan hannun kujera.
Ya gyara zama ya ce,
“Kun dawo kenan?”
Ta amsa da “Eh”. Tana wasa da ‘yan
yatsunta.
Sai ya yi gyaran murya ya ce, “toh
dai Azeezah, ba sai mun ja ta da nisa ba,
tunda dukkanmu ba yau muka san juna
ba. Kuma diyan Baba ne mu duka ba
bakin juna bane.
239
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sannan ni ba yaro bane kamarki,
na kusa shiga shekaru arba’in, kin ga
kenan babu bukatar yin kwane-kwane ko
bata wa junanmu lokaci.
Azeezah na ganki a gidanku, gaban
iyayenki kuma na yaba, in short I admire
you, zan so kara ki cikin iyalina idan kin
amince.
Sunana Zayyan Bello, kamar yadda
kika riga kika sani, ni dan marigayi
aminin Baba ne. Ina da mace daya mai
suna Safiyya, wadda tunda muka yi aure
sama da shekaru goma ba mu taba samun
matsalar da muka kasa warwarewa a
tsakaninmu ba”.
Ya dan nisa kafin ya sassauta
murya ya cigaba da cewa.
“Azeezah ni da matata muna da
fahimtar juna, ina son kara aure ba don
ta rage ni da komai ba, ina kuma barar
shigowarki cikinmu, don kara dankon
zumuncin gidanmu da gidanku. Idan har
kin amince bana so abin ya dauki lokaci,
240
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
don ni da ke babu bukatar sanin asalin
juna, sai amincewarki kadai nake nema”.
Duk wata kalma guda daya da yake
yi a kan matarshi kular da Azeezah ta ke
yi, har ta ce a ranta, wai shi wannan a
wurinsa haka ake zuwa neman soyayyar
budurwa? Da alama farin shiga ne gun
zuwa zance wajen budurwa ‘yar zamani
kamarta.
Ba zai maida hankali wajen gaya
mata irin kamun da soyayyarta ta yi masa
ba, sai wani yan-yan-yan akan tsakaninsa
da matarsa?
Kamar ta yi kuka saboda ba
wannan take son ji ba, ta ce cikin gatse.
“Kuna da irin wannan fahimtar
juna da soyayyar kai da matarka, to meye
naka na son kara aure, kuma me ka zo
nema a gare ni tunda ba so ba ne ya
kawoka? In zumunci ne ai da abinku na
ganku kaida Baba, so ko dani ko babu ni
zaku cigaba da abinku yadda na
riskeshi”.
241
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Tana fadin hakan ta sha mur sosai,
ta dora kafa daya kan daya, don ta tsani
rainin hankali irinna maza.
Kwarai tambayar tata ta shammace
shi, har ya rasa amsar da zai bata, hakan
yasa ya baiwa kansa assignment na ‘yan
sakanni. Don ya samu amsa kwakkwara
da zai bata. Yana ganinta yarinya, mai tarin
wauta, ashe-ashe tasan abinda take yi?
Meye dalilin son kara aurensa? In har
yanada komai da yake bukata a gidansa?
Shine assignment dinda shima ya baiwa
kansa a yanzu. Dalilai da yawa masu muhimmanci
sun yi mujazar wannan son karin auren,
domin yana ganin shine kadai maslaha a
gare su shida Safiyyah, don yana
sha’awar mace irin Azeezah a gidansa da
rayuwarsa, yana son mace ‘yar gayu, mai
wayewar kai, domin likely mace mai body
shape dinta da irin dirarrun dugadugan
kafar Azeezah itace daidai shi.
Ustazancin Sophie yayi masa yawa, tsayin
242
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
shekarun da sukayi tare da zata canza da
tuni canza to ba’a sakewa mutum nature
dinsa, wanda shi yake hana ta sakin jiki
su yi irin soyayyar da shi yake so, for over
a decade da aurenshi da Sophie yana
ganin bai samu sakewarta da shi a gadon
aurensu irin yadda yake so ya kai sau
goma ba, saboda kunyarta da kawaicinta
akan hakan, amma ba don bata sonshi ba.
Azeezah za ta yi bridging wannan
gap din, ga dukkan alamu, duk da tarin
negativities dinta da mahaifinta ke kuka
dasu, shi ba zai zame masa matsala ba in
dai zai samu yadda yake so da ita, yake
kuma kwadayin samu a gidan aurensa, ko
da kuwa Safiyyah ta haihu, hakan ba zai
hana shi wannan auren ba.
Sannan idan Allah ya nufa ya samu
haihuwa da Azeezah kafin Safiyyah dan
ko ‘yar na farko da yardar ubangiji zai
zamanto tukwicin kauna ta gaskiya ne da
zai yiwa Safiyyah.
243
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A takaice sexual dysfunction din Safiyyah
da neman mata yaro daga gareshi, su ne
dalili kuma silar son kara aurensa.
Azeezah ta kafe shi da idanunta
tana jiran amsa, tana kuma ankare da
yadda tambayarta ta jefa shi a gumi da
tunani. Zayyan ya dago a hankali suka
hada ido, sai ya yi mata murmushin da ya
kara narka zuciyarta a kansa. Ya ce, “kisa a ranki babu namijin
da zai zo neman aure a inda babu
burbushin soyayya a ransa. I like you
Azeezah, amma don Allah kalmar SO
dinnan ki yimin jinkirinta, har sai na
tantance ta a raina, kada in fade ta a
lokacin da bai dace ba.
Na yi miki alkawarin adalci da farin
ciki a gidana, don ke kanwata ce da ba
zan iya cutarwa ba, ina son aurenki bisa
yarda da amincewarki”.
Maganganun nasa sun ki zauna
mata daidai a kwanyarta, don jinsu ta ke
tamkar rainin wayo. Amma me?
244
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zayyan din ya zo da karfin
chemistry din da ya fizge zuciyarta nan da
nan zuwa gare shi, har ta ke jin ba za ta
iya ce masa dole sai ya takura kansa ya
furta mata abin da ta ke son ji ba, tunda
dai ya ce babu namijin da zai zo neman
aure a inda babu burbushin soyayyar
mace a ransa.
Zayyan ya katse mata tunanin da ya
jefa ta da cewa,
“Can I go ahead Azeezah? Kin
yarda iyaye su shigo cikin lamarinmu, in
sanya ki cikin iyalina?”
Azeezah ta juyar da kai gefe,
zuciyarta na bugawa da shigar SO farat
daya, babu bata lokaci zuciyar tace itafa
ta yi na’am da dan mutanen Rafindadi.
Ko ma dai me yake nufi da cewa ta yi
masa uzurin jinkirin kalmar soyayya
zuwa wani lokaci za ta yi wannan uzurin,
domin ta tabbata wuyarta a yi auren,
tunda har ya kawo kansa ya yi confessing
na neman amincewarta da bakinsa.
245
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Tana wannan tunanin, ya sake
maimaita tambayarsa na neman yardarta
har ya ce,
“Kamar yadda ki ka gani ni ba yaro
ba ne Azeezah, ba zan iya long dating
dake ba, I truly admire you, ki ba ni
yardarki”.
Sai ta samu kanta da gyada kai
kawai, ta kuma tambaye shi ko yaransu
nawa shi da maidakinsa Safiyyah?
Zayyan ya dan ciza lebensa cikin
‘yar damuwa kafin ya ce.
“Muna fatan Allah ya kawo su nan
gaba. In kuma daga wajenki Allah ya
bamu, ina neman alfarmar ki baiwa
Safiyyah ko me ki ka haifa na farko. Na
tabbatar miki za ta yi masa rikon da ko
ke ba za ki yi masa ba tunda Da na ne. Za
ta yi masa tarbiyyah irin wadda ko ke ba
za ki yi masa ba. Za ki yi mana wannan
alfarmar Azeezah?”
Wani abu a halin Azeezah shi ne, ba
ta boye abin da ke ranta. Ita ma bata so a
246
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
boye mata. Ko kuma tarin kuruciya ne ya
debe ta a wancan lokacin? Har ta yi masa
alkawarin yi masa wannan alfarmar.
Ta ce, “Allah da Ya halicce ni bai yi ni da
son hidima da hayaniyar yara ba. Amma
zan so in san kai da ita din waye mai
matsalar haihuwa, don ka ce min kun yi
kusan sama da shekaru goma tare?” Wani abu da ba zai iya ba shi ne,
yin zancen nan da wani, wanda ya
kasance sirrinsu shi da Safiyyah, don
haka ya ce da Azeezah, “We are all fit and
healthy Azeezah, muna jiran hukuncin
Ubangiji a kai. Now, tell me about your
samari? Su nawa ne?”
Azeezah ta yi wata ‘yar shashashar
dariya ta ce, “To me ye ruwanka da su
"Dan Daddy?" (sunan da ta sa masa
kenan, wato dan Babanta Alhaji Murtala,
don Baban ma ce masa yake Dan wajena,
tun ba su hadu ba ta sha jin yana ma
mamansu Hajiya Nana zancensa), tunda
dai kai Allah ya kashe ya baiwa
Azeezar?”
247
KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sai bayan ta fadi hakan cikin
subutar baki sai ta ji kunya sosai, shi
kuma Zayyan sai kansa ya kumbura.
Abinka da namiji a hannun wayayyar
yarinya, tuni Azeezah ta sa ya sake da ita,
ta bashi labarin ita cikin masu sonta
mutum daya ne soyayyarsu ta yi nisa a
makaranta, wato wani mai suna Faris.
Sun hadu ne a Cyprus.
Bayan dawowarsu daga karatu ya
zo nan gidansu zance, Baba ya ganshi da
wani (haircut), wanda bai masa ba. Tun
daga ranar Baba ya saka masa
karan-tsana, wai askin ‘yan iska ne
akansa kada ya kara zuwar masa gida”. Dariya sosai Zayyan ke yi, Azeezah
ta dauki hankalinsa sosai da salon
maganarta ta 'yan gayu, ga iya Hira,
musamman yanayin yadda ta ke magana
cikin rangwada da karya kai, har da yada
hannuwa cikin salo mai daukar hankalin
da namiji.
Ya ce, “What I want to know now
(abinda nakeson sani yanzu?), ke kina son
248
KAWAR ZUCIYA 2