Showing 15001 words to 18000 words out of 48692 words

Chapter 6 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

hannunta tace
“wallahi Habiby…..” sai tayi shiru, ta
kasa karasawa ta kuma saka kuka, ganin
yau Habiby ko alamun gezau ya ki yi da
damuwarta, balle yayi alamun zai karbi
rauninta da tubanta.
Sai a lokacin zuciyar Zayyan ta dan
fara russuna, yace “Umh? Ina jinki
Sophie, kin shirya magana yanzun? Ko na
kara miki lokaci ki kara deciding me zaki
gayamin? Bana son ki takurawa kanki sai
kin yimin wani bayani. Bana cikin
damuwa kuma banida matsala akan
hakan”.
Da sauri tace “na shirya zan gaya
maka gaskiya tsakanina da Allah, amma
don Allah kayi hakuri…” ai kawai sai
in’inar ta taho mata gabadaya ta sarqe ta,
dama in bata cikin nutsuwa sai ka nutsu
91

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
sosai zaka gane me take cewa in tana
magana in’inar bakidaya afkowa take yi.
​Amma da yake Zayyan da Safiyya
sai Allah duk abunda take fada ya gane
tsab, bashi da matsala ko kadan da
in’inarta, dadima take masa, nan ta fara
bashi labarin zuwanta gurin Dr. Hadizah,
da haduwarta da Ammara, da zuwansu
gurin Tsimbirbira la’ananne.
Haka kawai yaji zuciyarshi na
bugawa, gumi na karyo mishi, ya rasa ma
zafi yake ji ko sanyi, daga inda tace ance
sai ta kawo sperm dinsa.… baki daya
jikinshi kyarma ya shiga yi har tukin ya
soma kokarin gagararsa. Kafin ta kai aya
daidai inda tace ance sai Tsimbirbira ya
sadu da ita zata haihu, Zayyan bai tsaya
yaji karshen ba ya daka mata tsawa
jikinsa na zikiri, yace “bana son jin
labarin, bana son ji, please ya isheni
haka!!!”
​Ya fada cikin tsawar data kada ‘yan
hanjinta, kafin ya gangara motar gefen
92

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
titi a hankali ya kasheta gabadaya, don
tsoron kada ya kifar dasu.
Ya fara ambaton “Innalillahi wa
inna ilaihi rajioun”.
Ya kura mata ido cikin mamaki da
tsoro da tarin disappointment a cikin
kallon dake fitowa daga idonsa. Yace.
“Safiyyah!” (Sunanda tun suna
dating wato tun kafin aure rabon shi da
kiranta da shi), kafin ta farfado daga
wannan shock din na kiran asalin sunanta
yace. “Kinci amana Sophie, kinci
amanar aure, me ya kaiki binta in the first
place? Gaskiya kinci amanar tarbiyyar da
Malam da Ammi suka yi miki yau.
Ya buga sityarin da karfi yana fadin
“Ni Zayyan kika yiwa haka Safiyyah yau?
I can’t believe it!”.
Ya ma rasa me zai ce da ita, saboda
tsabar kaduwa. Sophien shi wani ya kusa
93

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ketawa rigar mutumci da aurensa saboda
son zuciyarta. Ya sake maimaita
“Innalillahi wa inna ilaihi rajiun”. Zayyan
ya dade bai shiga tashin hankali irin
wannan ba. Yace. “Safiyyah why? Don me kika je?
Ko saboda rashin godiyar Allah? In ba
haka ba ni Zayyan na taba nuna miki
wani abu da ya nuna na damu da haihuwa
ko rashinta? Ko na taba matsanta miki
akan inason haihuwa da har yasa kika
kusa jefa kanki a fushin Allah saboda son
wata haihuwa da ni bata gabana, wannan
rashin tawakkali har ina?”
Sai taji kaman saukar aradu
akanta. Tayi suman zaune ta kasa cewa
komai, domin ya dauki al’amarin da
girma har fiyeda yadda ta zaci zai dauka.
Shi gani yake ma kamar Tsimbirbirar ya
keta masa haddi sakayawa kawai tayi a
gaban idonsa.
94

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Wannan tashin hankalin da
Safiyyah ta gani a tare dashi yasa ta kasa
cigaba da kuka, don ta san duk abunda ya
gaya mata ta cancanci ya gaya mata ko
don ya huce bacin ransa. Sai ya koma magana cikin rauni.
Yace “Safiyyah Allah shaida na ne kan na
soki da zuciya daya, rashin haihuwa bai
taba sawa na rageki da komai ba, shi ne
zaki saka mun da wannan butulcin, ki kai
kanki ga wani zindiqi mushriki, kin
butulcemin, kin butulcewa Allah, kaicon
ki da rashin tawakkali Safiyyah”.
Ya ja motar a hankali kamar wanda
kwai ya fashewa a ciki suka cigaba da
tafiya. Har suka shiga Abuja bai kara ce
mata ko uffan ba. Kuka Safiyyah ta yi shi
har ta ji babu dadi. Kamar hawayenta
zasu kare.
95

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Taimakon Allah kadai yasa ya iya
karasa tukinnan, ya kuma kawo su gida
lafiya.
Yana fita daga motar ta biyoshi da
sauri tana bashi hakuri, zata rike
hannunsa yace “idan kika tabani wallahi
zan bata miki rai, sai kinyi dana sanin
zuwa kusa dani”. Ya shige ciki ya barta a
wurin. Nan Safiyyah ta zauna a kasa a
harabar gidansu a salube, don kafarta ta
kasa daukan nauyinta. Ba jimawa da
shigarsa ya sake turo kofa ya fito ya fice,
bata san ma inda ya nufa ba. Zayyan dai tun daga ranar ya
canzawa Safiyyah, wato ya dauke mata
wuta, suka koma zaman marina ko zaman
doya da manja shi da ita, baya shiga
harkarta, baya kulata a shimfida,
punishment sosai yake mata, amma in ta
gaishe shi zai amsa yana cigaba da tafiya.
96

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
A lokacin ya maida kanshi wani irin busy
machine saboda aiki, dare da rana zane
yakeyi, yana baiwa kanshi wahala yana ta
zane-zane ba gajiyawa, in ya fita harkar
neman kwangilarsa ma sai can dare yake
dawowa. Safiyya duk ta sha jinin jikinta
cewa Zayyan yana zargin Tsimbirbira ya
riga ya cika burinsa a kanta, ta dai boye
masa ne, don haka gabadaya Sophie ta
tsangwami kanta, ta tsani kanta, ta rame
ta zuge cikin kwana uku, ta tsani
haihuwar bakidaya ma.
Gashi ba halin ta kira kowa ta nemi
shawara, don tamkar ta yi kirari ta
dabawa kanta wuka ne a ciki. Musamman
Ammi da Malam, da tsine mata ne kadai
bazasu yi ba in suka ji abinda ta aikata
saboda son haihuwa. Ta yi istigfar ta nemi
gafarar Ubangiji yafi sau shurin masaki.
Tace koda wannan punishment din na
97

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
duniya Zayyan ya barta ya isheta
kankarar zunubinta.
Yau dai Safiyyah ta kasa jurewa,
Zayyan barin rayuwarta ne da bazata iya
rayuwa babu shi ba, duk ta rame ta
zaftare ta dawo rabi, dama jikinta ba
wani jiki bane na azo a gani, gainin zata
mutu a daki da damuwa sai ta tunkareshi
yau, ta same shi a master bedroom dinsu
yana changing zai shiga wanka.
Safiyyah ta tsugunna a gabansa
hawaye na tsiyaya a idonta, tace “wajenka
nazo Habiby, zan yi karin bayani, koda
bazaka yarda dani ba, na rantse maka da
Allah asibitin mata ne kawai naje a Kano
don a duba lafiyata, a ganomin me ya
hanani haihuwa. Don na kasa gamsuwa
da binciken wannan Dr. Muwadda din,
don ni dai ban taba jin wani abu wai shi
(pcos) a dangina na uwa ko na uba ba.
Nayi tunanin in nace maka daga
gidan Anti Dije zan je Kano asibiti again
bazaka barni ba, musamman da yake
98

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
kace kar na kara yi maka zancen komawa
asibiti, which I find it difficult to obey
(wanda na samu kaina da kasa bin
umarnin)”.
Nan ma shiru, Zayyan baice komai
ba, kokarin zagayeta yake ya wuce toilet
ta sake shan gabansa, ta rungume shi
tsamtsam tana hawaye “tace don Allah
kayi hakuri ka yafeni Habiby, I can’t
actually explain exactly what happened to
me that day… (bazan iya fassara
hakikanin abinda ya faru dani a ranar ba)
amma abun yafi kama da toshewar basira
….!”.
Ya dago manyan idanunsa da nan
da nan suka kada ya dubeta, saida hantar
cikin Sophie ta kada, har ‘yan hanjinta
saida suka hautsina da ganin bacin ran
dake kwance cikin idanunsa, yace. “Safiyyah kece kuwa? Is it really
my Sophie? Haihuwar da dole ake
samunta ne haka? Har da zanyi magana
ta karshe akai kice ta yi miki wahalar bi?
99

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Lallai shaidan yana son taka rawa a
tsakaninmu akan maganar haihuwa,
kuma sai akayi yaya bayan nan?
Sai Tsimbirbira din ya ja ki dakinsa
zai miki cikin haihuwa ki haihu, tunda ni
mijinki ban iya ba…, ko saboda ni na
kasa saka miki kwan haihuwa ko….?”
Safiyyah ta kusa samun dan karamin
hauka a lokacin, da wannan furucin nasa,
da hanzari ta kai yatsu ta toshe
kunnuwanta, kuka har da sheshsheka da
majina tace.
“Maganganunka sun yi min tsauri
Zayyan. Ni dai na rasa me ya sameni a
ranar, amma na yarda shaidan ne, na
rantse da wanda raina yake hannunsa bai
taba ni ba, ban shiga dakin da yace in
shigo ba na samu kaina da gudowa.
Habibi ko Ubangiji ana masa laifi a bashi
hakuri, ya yafe, (why not you Habiby?)
Ka yi hakuri ka yi min uzuri, koda
da uzrin bacewar basira ta wucin gadi ne
kadai”.
100

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Zayyan ya dago ya kalleta, Safiyyah
ta kara fashewa da kuka tace “ka yarda
wallahi komai nakeyi don mu haihu ne
Habiby. Ina son ‘ya’yanka, ina son samun
‘ya’ya daga gareka koda guda daya ne,
shiyasa na zama “desperate”, amma na
tuba daga yau na hakura, na bi Allah na
bi ka. Bazan kara zuwa ko’ina ba sai da
izninka.
Ta makalkaleshi kamar kyanwa,
tana yamutsa shi kamar Baby a jikin
uwarsa. Gabadaya Safiyyah ta jefa shi
cikin wani tunani hade da tausayinta. Ya
kuma gane da gasken gaske son haihuwar
kawai take a ranta, in kuma bai taimaka
mata ta samu ba, watarana zata jefa
kanta a halakar da ba zata iya fita ba
shima ta jefa shi, tunda an fara da bin
kawaye gidan boka.
​Tun daga lokacin ne, ya shiga
tunanin neman solution ga wannan
matsalar tasu, don hankalin Safiyyah ya
kwanta, shima ya huta da kwarzabar da
101

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
yake sha a wajen Mama Fatu, akan
zancen rashin haihuwarta. Ba don rashin
haihuwar Safiyyah ya dameshi ba, ko ya
zame masa matsala a cikin son da yake yi
mata, ko ya zama nakasu a cikin rayuwar
aurensu ba. Sai don kawai ya samo musu
kwanciyar hankali bakidayansu.
Dole ya sauka daga fushin nasa,
yasa hannu ya dagota ya tallafota zuwa
jikinsa, amma bakinsa da ya tafi yake
sumbatarta kusufa-kusufa, bai yi shiru da
yi mata nasiha ba, akan ta barwa Allah
maganar haihuwa. Don shima ta fara
saka shi a damuwa da son haihuwar tun
abin baya damunsa sam.

A wannan dan tsakanin Zayyan da
Safiyyah bakidaya suka fada wani hali na
soyayyar samun DA ta kowacce hanya,
duk iya tunaninsa ya rasa mafita akan
yadda zasu samu haihuwa, ga Mama Fatu
ta kara bude wuta da matsa mata lamba a
dan tsukinnan da ‘ya’yanta mata suke ta
102

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ajiye ‘ya’ya, don kuwa hatta su Zahra sun
haife mata jikoki saura shi, sun sake
haifewa kowacce karo na bibbiyu, su da
akayi aurensu bayan-bayan na Safiyyah.
Maganarta dashi yanzu babu hira mai
dadi irinta baya kullum sai korafi da
shagube akan rashin haihuwar Safiyyah
har fargabar zuwa gaida Mama yake yi.
Bata wata hirar arziki dashi kamar da sai
slogan dinta na gates cewa bakarariyar
matarsa har yanzu dai babu labari. Tace
bata ga riba cikin aurensu ba sai faduwa
da asarar ciyarwa da bautar da yake yiwa
mace.
​Wannan magana da Mama Fatu
tayi ta razana Zayyan da Safiyyah, wanda
shi ya kara rura dimautarta da dokinta ga
son haihuwa helter-skelter, abinda ya
kaisu ga yin bincike na ilmi akan yadda
ake samun haihuwa da gaggawa ga mai
matsalar lalurar PCOS.
A garin binciken nasu ne a teburin
likitoci daban-daban, kowanne likita
103

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
saidai ya kawo shawarar cewa suyi (IVF)
wato (In vitro Fertilization) da aka fi sani
(dashen haihuwa) da harshen Hausa.
Safiyyah duk da dokin abun ya
cikata wato IVF din, don wannan ne karo
na farko data ji ‘hope’ na zata haihu, in
dai Dan kanta ne da ya fito daga jikinta
kuma na Zayyan to ko ta wace hanya ce
tana maraba da samuwarshi, indai
addinin musulunci bai haramta ba, duk
da haka basu yi saurin amsawa likitocin
ba, sannan basu gayawa kowa ba, saida
sukayi nasu binciken na addini ta hanyar
neman fatawa daga daga malamai daban
daban, sannan sukayi bincike sosai a
yanar gizo suka tabbatar IVF baida illa
daga fuskar addini, da kuma tabbacin da
suka samu daga likitoci na cewa kashi
25-30% na attempt din farko ana samun
nasara.
Duk irin bayanin da yayiwa Mama
Fatu, na cewa sun je asibiti shida Sophie,
kuma suna kan zuwa har gobe, da
104

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
bayanan da likitoci suka yi akan matsalar
rashin haihuwar tasu, amma ya boye
sirrin matarsa inda yace ance matsalar su
(unexplained ifertility) ne shi da ita duk
lafiya suke, hakan bai sa Mama ta tausaya
ko ta tausasa kalamanta akan kaddarar
Safiyyah ba. Tace.
​“Fadi gaskiya kawai ka auro “juya”
Baffana, ba wani ‘unexplained infertility’,
tunda dai a shekaru kusan takwas da aure
ta gagara haifa maka Da ko guda daya, ai
JUYA ce kenan, musamman da babu bari
ba batan wata mai nuna alamar haihuwa. ​Wannan makauniyar soyayyar da
kake yiwa diyar Alarammannan tayi
yawa Baffa, na fadi na kara fadi meye
ribarta? Ribar kowanne aure ai haihuwa
ce, tunda bata da mahaifar haihuwa
kuwa, aurenta babu riba a cikinsa sai
asara”.
Ta kai ta kawo a yanzu Safiyyah ko
gidansu Zayyan ya gagareta zuwa, bata
iya shiga sha’aninsu na biki kona
105

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
haihuwa, bama sa gayyatarta, abun nasu
babu kawaici babu tausayi da alkunya,
kai sai ka rantse da Allah ita zata halicci
dan a mahaifarta. Idan kuwa tayi
kuskuren zuwa wani sha’ani na iyalin
Mama, kamar sunan haihuwar ‘ya’yanta
Zaitoon da Hatoon da akayi recently,
yadda kasan mujiya haka take komawa a
cikin su, saboda wulakanci da kaskancin
da suke mata, ga yada mata mummunar
magana cikin habaici a gaban kowa, akan
rashin haihuwa kai sai ka rantse a kasuwa
ake sayar da haihuwa.
A kodayaushe sukayi waya da
Ammi kuka take tana labarta mata irin
mawuyacin halin da take ciki da uwar
mijinta da ‘yan uwansa, Ammi ba abinda
zata iya a kai banda ta kwantar mata da
hankali, kullum tausarta kawai takeyi,
tace ta kara hakuri kan wanda take yi,
matsalar rashin haihuwa ba a kanta aka
fara ba, ba kuma kanta za’a kare ba,
kada kuma ta fidda rai. Saboda yadda
Safiyyah ke gaya ma Ammi Hafsatu halin
106

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
damuwar da take ciki da dangin mijinta,
har auren Safiyyah ya soma fita daga ran
Ammi, don ta kan ce a ranta sam Uwar
Zayyan uwar banza ce, bata da Ikhlasi.
Kamar bata haifi ‘ya’ya mata ba itama. Amma a matsayinta na uwa bata
nunama Safiyyah hakan ba, amma a
ranta ta fara tsanar auren yanzu, don
kwatakwata Safiyyah ta rasa nutsuwa da
farin ciki a cikinsa, tsakaninta da mijinta
lafiya kalau amma zuciyarta babu dadi,
duk da ganin zaman daular da take ciki
da kowa dake nesa da ita yake yi mata
baya sata zama cikin nnutsuwa. Yes, da
gaske Safiyyah tana cikin daular miji
domin Zayyan kullum kara buda masa
nasibi cikin harkokinsa Allah yake yi, har
wata ‘yar kiba ya aje ta musamman irin
ta kasaitattun mazan Abuja, masu murza
naira da jin dadinta son rai. Ita kuma
Safiyyah kullum ka ganta kamar marar
lafiya kamar kudin guzuri, bata da
karsashi da walwala a cikin tsararrakinta.
107

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Ya nutsa sosai ga tunanin mafita a
garesu. Har zuwa lokacin da Safiyyah ta
kara bijiro masa da zancen baya, wato
bukatarta na suje wani asibitin kudi a
Kaduna, bisa shawarar da likitoci suka
bata akan suyi (In vitro Fertilization). Sai ya shiga tunanin ko hakan za’a
yi kawai don Safiyyah ta samu kwanciyar
hankali ta rike Da a hannunta? Su kuma
huta da gori

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login