Showing 48001 words to 48692 words out of 48692 words

Chapter 17 - KAWAR ZUCIYA 2 BY SUMAYYA TAKORI KABARA .pdf

shugaban kasa ba, a'a
ita diyar magada Annabawa ce, wadanda
duniya bata gabansu”.
Zaitoon ta shaka sosai sai ta bar
dakin.
Aunty Dije ta ce, “Marasa kunyar
yara kawai, Allah ya hada ku da dangin
miji masu irin halinku”.

Sannan ta kara ja ma Sophie kunne
a kan kada ta sake ta tanka su ko me za
su ce mata, giyar farin ciki ke dibarsu. To
Allah na kowa ne, kuma zai iya mata abin
da ta kasa.
282

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Sai da ‘yan kawo amarya suka ware
Aunty Dije ta kada kan su Sabah su ma
suka wuce guest house din da aka yi musu
masauki a nan cikin Sunset Estate. Suka yi
sallama da ita a kan cewa da safe ba za su
shigo ba, sammako za su yi su juya gida
abinsu.
To shi ne fa Zayyan bai shigo
gidansa ba sai can dare kamar yadda ya
faru a farkon littafin, fatansa shi ne Allah
ya sa wannan auren da yayi bai zamo
(biggest mistake of his life) ba, wato bai
zamo babban kuskuren sa a rayuwa ba,
maimakon nemo mafita ga matsalarsu shi
da Safiyyah.

Kiran sallar asubahi ne ya dawo da
shi daga 'down memory lane' din da ya
tafi, wanda ya kunshi gwagwarmayar
kuruciyarsu data soyayyarsu data rayuwar
aurensu shi da Safiyyah. Da kuma ranar
yau, wato ranar da "Azeezah Murtala" ta
tare a gidansa.
283

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Azeezah ta iso cikin rayuwarsu da
fatansa na zata zamo maslaha ga
matsalolinsu.
Da ya dawo kuma ya dade zaune cikin
motarsa saida ya tabbatar 'yan kawo
amarya sun watse, kuma maimakon ya
tafi dakin uwargida yayi mata sallama ya
wuce gun amarya sai ya zabi ya wuce
masterbedroom dinsa, yayi tunanin
rayuwar sa da Safiyyah tun farkon fari,
because he lacked all the courage na dosar
inda Safiyyah take a wannan daren.
Zayyan ya kwanta ne kawai
rigingine a gadonsa yake wannan dogon
tunanin. Don yanzu da Azeezah ta zama
mallakinsa, bakin alkalami ya riga ya
bushe sai yake jin kamar yayi kuskure,
kuma kamar bai kyautawa Safiyyah ba.
Kamar wannan shine kuskure mafi girma
daya aikatawa rayuwarsa, maimakon
kawo maslaha.

284

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
Mu duka ni da ku masu karatu dai
mun san cewa "not all that glitters is gold".
Azeezah nada duk abinda yake so a diya
mace, while soyayyarsa naga Safiyyah
diyar Malamai, amma kuma muna sane da
cewa Zayyan ya manta cewa babu yadda
za’a yi ka samu rayuwa dari bisa dari
daidai da ra’ayinka da burinka, dole kowa
yana da irin nasa nakasun a wurin abokin
rayuwarsa.
A rayuwa, sau tari idan Allah ya
baka wannan zai iya hana maka wancan
kamar yadda Safiyyah ta kasance, duk dan
Adam tara yake bai cika goma ba, ba duk
abinda mukeso daga abokan rayuwarmu
muke samu dari bisa dari daga garesu ba. Duk da haka Zayyan yana da
kyakkyawan fatan cewa ‘Azeezah Murtala',
will meet all his dreams in a woman, his
expectations and beyond.

Mu biyo Arch. Zayyan da matansa
Safiyyah da Azeezah a littafi na uku. Yanzu
285

KAWAR ZUCIYA 2 TAKORI 2025
ne zamu fara labarin Zayyan da Safiyyah.
1&2 shimfida ne.
SUMAYYAH ABDULKADIR -Takori
07030137870
(WHTSP only)
01/04/2025
(Wannan littafi na sayarwa ne,
GUNDARIN LABARIN ZAIZO A
MANHAJAR TELEGRAM KADAI)





286

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login