Showing 21001 words to 24000 words out of 46889 words

Chapter 8 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

kuwa rayuwar
aure zata yiwu da haka?”.
​Haka malam yayi ta kawowa Ammi
hujjojinsa, da misalai na dalilinsa na zabar
Zayyan akan Haroun, ya gaya mata ya yaba
da hankalin Zayyan, yaga alamun jarunta
da mazantakar kwarai a tare dashi. Sannan kuma ya kuma yaba da
dattakon mahaifinsa, domin mutum ne na
kwarai da kowa ya shaida a jihar Katsina
bakidaya, sannan akan ilmi aka sanshi ba
wai akan tarin dukiya ba. Ya kuma ce “duk da haka Hafsatu kin
sanni sarai, bazan shigar da Safiyyah gidan
Rafindadi da ka ba, sai na russuna akan

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

goshina na lankwasa gwuiwoyina a gaban
Ubangijin daya halicceni, wato sai na
gayawa Allah cikin talatainin dare akan ya
zaba min abin duk da fi alkhairi a gareta,
kome Allah ya zaba mana dashi zan yi
amfani, itama sai in ranta ya kwanta da
auren Zayyan din bayan istikharar da zan
bata, sannan za’ayi daurin auren”.
Malam yasa murya ya kira Safiyyah, ta
zo ta tsugunna gwiwa bibbiyu a gabansa
tace “gani Allah gafarta Mallam!”. Yace “zo
nan mu raba dare nida ke akan sha’anin
aurenki”. Nan ya bata istikhara yace tayi a
daren yau, tayi addu’a sosai, shima zai yi
duk su nemi zabin Allah akan aurenta.
Washegari Lahadi Zayyan yazo
Dandume zance wajen Safiyyah, a yau ne
suka taba tattaunawa extensively akan
rayuwar kowannensu, Zayyan ya baima
Safiyyah tarihinshi dana iyayenshi kaf,
itama ta bashi nasu in detail, basu taba yin
hira mai zurfi da tsayi akan junansu irin
yau ba, yanayin neman auren Zayyan da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Safiyyah cikin dattaku kamar na mutanen
da, sabida koyarwar gidansu Safiyyah da
suka dora soyayyar tasu akai, har sunan su
Hatoon yau ya gaya mata, da su Yaya
Zubaida, sai yau Safiyyah ta san adadin
‘yan gidansu, da hotunansu cikin wayarsa,
ita kuma ta kira kyawawan kannenta uku
mata duk yau tayi introducing dinsu ga
Zayyan wato Sabah, Rayha da Rayyah suka
zo suka gaida Zayyan daya bayan daya.
Daga shi har Safiyyah farin shiga ne a
sha’anin soyayya, they are all novice. Don
haka soyayyarsu a lokacin mai sanyi ce
kuma mai tsabta, ba irin ta zamanin nan ba
dake cike da sabon Allah, Zayyan bai taba
son wata yarinya ba, bai kuma taba
sha’awar yin aure nan kusa ba, kai shi bai
san ma shi namiji bane mai bukatar mace
sai bayan haduwarsa da Safiyyah Usman
Dandume.
**** **** ****
A DISTANT BROTHER

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Safiyyah ta wayi gari yau da farin ciki, da
tsayuwar zuciyarta wuri guda akan aurenta
da Zayyan Bello, bayan kammala istikharar
da Malam ya bata, ta jinan duniya ba
wanda take so sai Zayyan. Da hantsi ya dubi
ludayi, Yaya Sheikh ya fado mata a rai,
kawai sai ta kira wayarsa. A kokarinta na
son shaqa masa takaici irin wandayake
shaqa mata duk sanda yace bata iya gayu
ba babu saurayin da zai kwasheta. Kwana
biyu tayi kewar Yaya Sheikh don ya dade
bai kirata a waya ba, ana I gobe daurin
aurenta da Zayyan tana ciki wani irin
madaukakin farin ciki, tayi mamaki da ko
Allah ya sanya alkhairi Yaya Sheikh bai
bugo ya ce mata ba, sai ta yi kundumbala
ita ta kira shi.
Ridhwan Abubakar Dandume (Sheikh)
yad aga wayara Safiyyah, ko gaisawa bata
bari sun yi ba cikin tsokana take gaya masa;
“Yaya Sheikh ko kasan? I have finally
found my Soulmate, a cikin HIJABI! (A
karshe dai gashi ta samu abokin rayuwa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

cikin sutturarta ta hijabi), da yake Yaya
Sheikh kullum baya rabo da yi mata gorin
bata da mashinshini ne saboda bata gayu
irin na ‘yammatan yanzu, sai fama da
Hijabi, shi ko a kafa aka daura masa ita zai
kwance ya yar, ya zura da gudu saboda
rashin iya gayunta.
Ya kan yawan ce mata, shi in ya tashi
aures ai mace sai mai kyalli da daukar ido
da iya daukar jambaki, gazal da jagira da
iya saka suttura kadai zai aura. Wadda I ta
shigo wuri sai an san ta bayyana. Wadda in ya ganta zai ji sanyi daga duk
wani bacin rai saboda haduwarta da iya
gayunta.
Kullum abinda yake fada mata kenan
in yaso tsokana da son kular da ita. Kai
kace ‘yar mace da dan namiji suke ba ‘yan
maza zar ba.
Don haka da dariya sosai yau itama
take ramawa inda, take gaya masa Zayyan
dinta ya fishi komai, ya fishi kyau

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Ba-Rumeh ne, kuma Uwa Uba yana
matukar sonta a hakan da take cikin
Hijabin, gashi ya fishi iya gayu da iya
daukar wankan da yake mata
gori…..ya-yan-yan”. Safiyyah sai ji tayi shuuuu! Kamar an
katse wayar, kuma daga ranar bata kara
samun Yayan nata Ridhwan a waya ba,
sannan bai kara kiranta ba ko da wasa.
Wannan abu ya bata mamaki, don ita wasa
take masa, at least yaji inda dadi irin gori
da cin fuskar da yake mata kullum.
Koyaushe ta kira wayarshi bata shiga,
but to her utmost surprise (ga babban
mamakinta) sai taji yana hira dasu Ammi
lokaci-lokaci akan shirin auren nata.
Har Ammi ta gaya mata cewa ya aiko
da gudunmuwar kudi mau kauri yace a
hada ayi mata kayan daki. Abin ya sosa
mata rai, me Yaya Shaikh ke nufi da yanke
alaqarsu kuma bazai mata ko fatan alkhairi
tsakaninta da shi ba?

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Kenan ita blocking dinta yayi daga
wasa ko me?
Itama daga ranar sai kawai tayi zuciya
ta rabu dashi, bata kara gwada kiran Yaya
Sheikh a waya ba.
**** **** ****

​​ AURENSU

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

A

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

hankali Zayyan ya kara lumshe idanunsa,
ya cigaba da tariyo abubuwan da suka faru
dasu bayan nan shi da Safiyyah. To cut it
short, yayi nasarar samun auren Safiyyah
(at a very tender age) daga shi har ita suna
tsakiyar shekarun kuruciya, in her teens
shikuma in his twenties.
Irin auren nan na mutanen da ga
‘ya’yansu, da ake kira AUREN GATA shi
mahaifinsa Baba Bello yayi masa da
Safiyyah kamar yadda ya alkawartawa
Mama, cewa zai masa auren gata, to ya cika
wannan alqawarin, domin Baba shi yayi
masa komai na hidimar auren nan including
lefe, wanda Malam yaki yarda a kawo yace
can in sun hadu a gidan auren su ya bata
amma ba a gidansa ba.
A kullum sanda Baba yake raye, yana
kara jaddada masa da ya rike Safiyyah da
amana, 'yar masu dattaku ce itace asalin
'yar manyan mutane, kuma matar rufin
asirinshi ce. Baba Bello ya kan ce “na saka
himma na aura maka itane bisa ganin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

dacewarta da kai da nagartar gidan data
fito, da kuma uwa-uba karfin sonta dana
gani a tattare da kai, ba tareda na jira
lokacin da ya dace ace kayi aure yayi ba”.
Baba ya kara ce dashi "ya aura masa
ita da wuri ne don kada ta kubuce masa.
Domin mata irin Safiyyah da suka fito
daga tsatson kwarai tamkar allura cikin
ruwa ne wato na mai tsananin rabo ne”.
Bazai taba mantawa da ire-iren
wadannan kalaman na mahaifinsa akan
Safiyyah ba, masu sawa kullum yake kara
ganin darajarta da kimarta a bayan ran
Baba. Yake kuma girmama kowanne
kankanin al’amarinta. Da amincewar mahaifin Safiyyah da
nasa dari bisa dari aka daura aurensa da
Safiyyah... aure mai dimbin tarihi. A
wannan lokacin da tunaninsa ya zo nan,
murmushi ne ya kubce masa daga kwancen
da yake, sakamakon tuno wani abun da ya
faru bayan daurin aure.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Wato tun daga lokacin da aka daura
musu aure sai Safiyyah ta canza masa, ya
rasa gane kanta, duk ta damu, ta shiga
kunci marar dalili.
Har ta kai da cewa ta rokeshi kan bata
shirya tarewa ba, tana so ya roki Malam da
Baba a bata lokaci, saboda gabadaya auren
da yuwuwarsa yazo mata ne bagatatan, bata
yarda da yiwuwar komai ba sai data
tabbatar ya tabbata din. Wato an daura shi,
tunda gashi har Malam da Limamin garin
Dandume da ya zama Alwalinta sun kirata
sitting room din Malam na soro a ranar
bayan an watse, sun damka mata sadaqinta
na aure a hannunta.
A baya Safiyyah kallon komai take
kamar wasan film, wato daga haduwar ta
da Zayyan har zuwa gajeruwar soyayyarsu
sun faru kamar kiftawar ido, zuwa
daidaitawar iyayensu, zuwa maganar auren
data bullo duk bata yarda dasu ba sai bayan
ta tabbatar an daura mata auren shaidu sun
shaida, tun daga nan ta shiga damuwa, ta

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

fitini kanta ta fitineshi shima da rokon
alfarma na rashin son tarewa yanzu.
Da farko tace masa ya roki a barta sai
ta gama jarrabawar karshen zangon da zata
fara, ta huta ta nutsu bayannan, duk ta
dauka Zayyan zai ce a’ah, ganin yadda yake
ta dokin tarewar tata, tunda Malam yace
biki ba’a gidansa ba saidai in ta tare suyi
can a gidansu, amma sai taji kawai ya amsa
inda ya ce mata cikin lallashi da tausasa
kalami.
“sophie, kinsan burina kawai in
mallake ki mu rayu tare ko, daga wannan
banida wani sauran buri a duniya sai na
fatan gamawa da iyayena lafiya.
Kuma gashi Allah ya cika min wannan
burin, alas! Ya mallaka min ke Safiyyah,
bada tsumi ko dabara ta ba.
To gaggawar me zan yi kuma a kan
tarewarki, ai anyi mai wuyar, don haka ki
kwantar da hankalinki ni ta fannina “no

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

haste”, na baki damar tarewa a gidana a
duk lokacin da kika shiryama hakan.
Zayyan will be patiently waiting for you
to come (Zayyan zai jira isowarki cike da
hakuri)”.
Daga ranar da aka daura auren su ne
ya soma kiran ta da suna “Sophie”, ya cire
mata suna “Hijabie”, don a cewarsa yanzu
babu sauran Hijabi a tsakaninsu!.
Wasa-wasa har ta gama jarrabawarta
Safiyyah tana dojewa tarewarta, Malam da
Ammi ma basu matsa mata ba, don wani
zazzabi zazzabi ta soma a tsaitsaye, irin na
sabon aure. Kannenta da Ammi kadai ke zuwa saye
sayensu a kasuwa na 'yan kayan dakinta da
kayan kitchen, da suka tsara za’a yi mata
daidai karfinsu.
**** **** ****

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Yau Zayyan ya zo ya samu Mama a
falonta, ya zauna gefenta yana sosa kai, ta
harareshi ta ce “Baffana, tunda aka daura
maka aure ka daina zama muyi hira ko? Ka
daina samun lokacin hira dani da
kannenka, bini-bini kullum kana hanyar
Dandume, Dandume dai, ina ka fito
Dandume, Ina zaka, Dandume.
Ni ko dana ga Safiyyar nan a hoto,
yadda ta gigitaka ta tafi da imaninka haka
na dauka zata fi haka cika ido da daukar
ido don kwalisa, sai naga abu ‘yar firit,
fuska salalam ido ba ko tozali, sai dogon
hanci da manyan idanu kwala-kwala kamar
na mage, in ce ko sune kadai suka burgeka?
Gaka Baffana masha Allah katoto da
kai (giant), amma sai ka dauko mace ‘yar
firit, siririya kamar karan raken takanda.
Ai da ka nemo mai dan kumari kamarka da
yafi”. Shi abinma sai ya bashi tsoro, don dai
shi, Lillahi wa Rasulihi bai ga makusa
tattare da halittar Safiyyah ba in ka cire

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

rashin kwalliyarta kuma wannan ra’ayi ne,
shima yanason kwalliya amma yasa a ransa
a matsayinsa na namiji, shi zaiyi shaping
mace a gidansa yadda yakeso ta mike amma
hakan sai a hankali in akayi la’akari da irin
background dinda ta fito, ya kan rasa gane
ina Mama ta dosa kullum akan maganar
Safiyyah, bata taba yabawa ba!
Kullum sai ta samu abun kushewa a
aurenta take barinsa ya bar dakinta, bata
taba godewa halarcin Safiyyah gareshi ba
na yarda da tayi ta aureshi yana dalibi,
itama daliba, ba ko tunanin aikin me zaiyi
ya ciyar da ita, shi ko da wannan aka barshi
Safiyyah ta gama masa komai, tunda ta
aureshi bisa yarda da soyayya tun bai zama
abinda ya zama yau ba. Safiyyah matar
sirri ce, abokiyar rufin asirinsa.
Yadda take tashen kyawunnan da
kuruciyar nan da kokari a karatu a ABU,
da irin maneman da ya kasa a kanta,
manyan mutane masu zuwa wurin
mahaifinta, shi ya san mutum ko shine

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

hasidin iza hasad, ba zai ce Safiyyah bata da
kyau ba sai Mama Gwanin na Iya, wai 'yar
firit ba kumari, to dambe zasu ke yi da zai
dauko dirkekiya? Don haka ya kan rasa
gane ta ina Mama zata yabi wani abu akan
auro Safiyyah da yayi, wanda shi yasan
daga shi har mahaifinsa basu saka son
zuciya cikin al’marin ba sai kwadayinsu da
asalinta (nasaba) da training dinda ta samu.
Yace “amma Mama kinsan ba kullum
nake zuwa Dandumennan ba, ko bayan
daurin aure sau biyu kawai naje, mahaifinta
mai ka'idane, baya son zaryar maza a
gidansa, ni kuma ina kiyayewa. Ban daina zama hira daku ba Mama.
Na maida hankalina wajen hattama (project
work) dina don na samu na yi submitting a
sallameni, shiyasa bana iya zaman hirar
yanzu, kullum ina library fa Mama, itama
Sophie ba son tarewar take yi ba”. Ya
karasa maganar cikin damuwa da jin
tausayin kansa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Mama ta yarda, don ta san Zayyan a
dabi’arsa baya karya, baya munafurci ko
nunkufurci, in yanason abu yana so kawai,
sannan rawar kafarshi akan Safiyyah ita ta
san gaskiya da sauki akan ta mazan da suka
yi sabon aure, ko don bai san me auren ya
kunsa bane at all sabon shiga ne? Tunda har
ya bar matarsa sama da sati biyu da daurin
aure a gidan iyayenta ba zancen tarewa wai
tana jarrabawa, itama jan magana ne kawai
don taji dadin bakinta, amma ta san ba
Dandume yake zuwa ba.
Yana Zaria can cikin makaranta
kodayaushe, ya hada hankalinsa wuri guda
ya kammala rubutunsa a wannan dan
tsukin, don Baba Bello ma ya gaya mata
kwatankwacin abinda Zayyan din ya gama
fada mata yanzu, cewa Baban Safiyyah dan
ka’ida ne, baya barin Zayyan zuwa zance
barkatai. Ya kuma hana suyi mata lefe ko
bikin bidi’o’in ‘yan boko. Koda aka daura
auren ma yace shi in ba Safiyyah tarewa
zata yi yanzun ba, to Zayyan kada ya dinga

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

yi masa zarya ya cigaba da zuwa sati-sati
bisa ka’idarsu yadda suka saba.
Mama tace a ranta tabdijam! Baffa an
debo aure gidan Alarammomi fiyeda haka
ma za’a gani ne.
Malam ya baiwa Ammi kudi masu
yawa kasancewar yana noma yana fidda
amfanin gona duk shekara, sannan yana
kiwo, ga gudunmuwar da Sheikh ya aiko
musamman don auren kanwarsa Safifi. To
kacokam abinda Malam ya fidda wannan
shekarar a kan kayan dakin Safiyya ya
karar dashi.
Ya hana Ammi sayar da filinta, yace ta
ajiyewa kannenta suma ba jimawa zasu yi
ba a gaban su, tunda duk suna sakandire
yanzu.
Ammi ta cigaba da shirye shiryen
tarewar Safiyyah a hankali, ta sayi wannan
ta sayi wancan ta adana, yayinda Safiyyah
nata dokin ga tarewar kullum raguwa yake

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

yi. Bata san meyasa ba, kawai taji bata son
tarewar (not because she doesn’t love him).
In da namiji daya data fara ji a ranta
duk duniya to Zayyan Rafindadi ne, amma
sam taji bata so ta tare a gidansa bayan an
daura musu aure.
Wasa-wasa saida aka share watanni
biyu da daurin aure amma Safiyya taki ko
zancen tarewar nan ayi mata.
Duk wani uzuri na duniya Zayyan yayi
mata a matsayinsa na sabon ango mai
hakuri da iya controlling eager dinsa.
Already Baba Bello ya kama musu dan
gidan da zasu zauna a Zaria, kusa da
makaranta, har su kammala, amma
Safiyyah ta ki.
Malam da Ammi tun basu damu ba,
don suna ganin makon gida ne ke damunta
da sabo da ‘yan uwanta, har abin ya fara
damunsu suka sakawa Safiyyah ayar
tambaya.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Malam yace addu’a ya kamata suyi
mata, watakila shaidan ya shiga lamarinta
Ita kuma Safiyyah a karan-kanta ta san
ba wani shadani akanta, ba komai ya
hanata son tarewar ba face maganganun
Anti Dije da suka tsoratata.
Tun bayan da aka daura aure in suka
zauna itada Antin a gidanta, ba abinda Anti
Dije ke mata sai fadakarwa irin ta Aunties
mata kawayen ‘ya’yansu, kuma shaqiyyan
iyaye. Fadakarwar Antin akan daren farko
ne, tace dare ne na musamman ga kowacce
amarya, bla bla bla......ga ire-iren abubuwan
da suke faruwa cikinsa.
Anti Dije tace “akwai abubuwa masu
ban tsoro da Sanya razani ga diya mace a
cikinsa”.
Tun bayan da aka daura aure Antin
marikiyarta ta Zaria bata da aiki sai yi
mata irin wannan hudubar akan shiga
gidan aure, da koya mata abubuwan da ya
kamata ta sani, a matsayinta na farin shiga,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kuma sabuwar matar aure a halin yanzu,
wadda ba jimawa zata bi sahun sauran
iyaye mata, har Anti Dije tayi kuskuren
fada mata yadda ake shan wahala a wannan
daren ga budurwar da ta kai mutunci, wasu
har sai an musu dinki ko ruwan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login