Showing 18001 words to 21000 words out of 46889 words

Chapter 7 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

wani tunda ya auri ‘yar Alaramma,
bayan already na iso menopause, ba nida
wani Da namijin sai kai kadai kuma Baffa.
Hatoon tace a ranta (don ta san bata
isa ta fada a fili yaji ba) musamman ganin
yadda yake mazari da kumburin nan, in ta
sake ta fada a fili ko Mama tayi kadan ta
kwaceta a hannun Yaya Baffa yau. “Kai amma su Yaya Baffa an sha kasa!
Aji (class) ya fado kasa warwas! Duk
kwalisar nan tashi da kwarewa a daukar
wanka, ya kare a ‘yar gidan alaramman
kauye, ‘yar kauyen Dandume, shi dama ya
cika kwashe-kwashe, ko abokansa in an

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

duba za’a ga ‘ya’yan talakawa ne mafi
yawansu, duk a wurinsa suke nema, kai
cikin abokansa na shiyyar Rafindadi har da
na Allah ya baku mu samu.
​Mama ta tsefe shi ta taje tas, akan
matan duniya ‘ya’yan masu hannu da shuni
dana ‘yan boko dana ‘yan kasuwa dana
‘yan siyasa sun kare ne a cikin jihar
Katsina? Da zai tsallaka ya dauko mata
diyar alaramman kauye? Tace kuma ita bama rashin wadatar
gidansu yarinyar ne damuwarta ba, kamar
yadda za’a mallake mata shi da maluntar
da bata san kowacce iri bace, haka kawai.
Yo ai ita ko wacece zata auri Baffa sai
wadda iyayenta suka ci suka tada kai, saidai
taci riba da ita, ba dai ta zama ‘yar kallo a
gun matarsa ba. Ko tna ji tana gani a mayar
mata dashi saniyar tatsa ba.
Tace to idan matan Katsina sun kare
ne Baffa, ita zata nemo masa, in kuma kyau
ya hango, to ya bari ta samo masa
Barumiya. Diyar asalin ‘yan boko kamar

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

nashi iyayen, ko wadanda suka fisu naira da
boko.
Tace ita sam! Bata son kwashe-kwashe
da jogane-jogane irinna zubar da aji da
barar mata da class cikin kawayenta. Idan
kuma kyau ne ya debo shi a Dandumen,
kowa ya san babu mai kyawun kabilar
fulanin Rumawa a fadin jihar Katsina. ​Suna tsaka da haka Baffa yaki cewa
komai akan fadace fadacen Mama, sai ga
Bello ya dawo gidan, daga wata tafiya da
yayi ta aikin ginin titina a jihar Jigawa.
​Duk da a gajiye yake kamata yayi ya
haye samansa kai tsaye ya samu hutu,
amma kumfar bakin Mama yaja hankalinsa
sosai don har kofar gida ana jiyo tashin
fadanta, ya san Mama ta saba fada akan
abinda bai kai ya kawo ba amma ganin
yadda Zayyan yayi durkushe tsumumu
gaban Mama, yayi tsugunno kamar na mai
neman gafara yanata zufa, ita kuma Mama
tana sake surfeshi, kamar zata hada da kai
masa duka, Zayyan ya dukar da kai kawai,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ko dagowa bai yi ba, sai digar gumi yake
daga goshinsa zuwa kan yatsar kafarsa,
lallausar fatar bakinshi dake zagaye da
gashin bakinnan da ake kira (quarter
million) tana raurawa tana hardewa sabida
tashin hankalin da kalaman Mama suka
saka shi, wadanda a takaice suke nufin
Mama bata amince masa ya nemi auren
Safiyyah ba, tayi watsin Allah tsine da
zancen sabida Safiyyah bata yi daidai da
ra’ayin matar data ke so ya aura ba.
A lokacin da shikuma bakidaya
zuciyarsa ta gama matowa a kan Safiyyah.
Dukkan burinsa na yanzu ya dora shi
ne kacokam akan mallakarta ta hanyar
auren sunnah, Mama tana ta fada da mita
kamar ta kara da arar wani bakin, ta inda
take shiga bata nan take fita ba, ta kara da
cewa “yaushe ka isa auren ne ma Baffa? Ko
aikin yi baka da shi? Kuma baka karbi
kwalin masters dinka a hannunka ba har
yanzu? Uban waye zai ciyar maka da
matar?

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

​Haka kawai zaka je ka wani rakito aure
gidan Alarammomi da jira suke kaima ka
basu, to shekarun naka har guda nawa suke
da suka isa daukar dawainiyar mata da
danginta?” ​ “Shege ne shi da bashi da Uba?”
Baba Bello ya karbe zancen yana
shigowa. Tun kafin ya nemi jin ba’asin
zancen abinda yace da Mama kenan cikin
fushi, wanda da wuya ka ganshi cikinsa
indai akan Mama Fatu ne. Mama ta shiga
koro masa bayani cikin takaicin da har a
furucinta zaka ji shi, tace.
“yanzu saboda Allah Baba! Zayyan ya
rasa inda zai je ya nemo aure sai gidan
Alarammomi, irin masu bada karatun buzu
a zaure, a kauye kuma fa!”.
​Budar bakin Baba Bello sai cewa yayi
“kai masha Allahu amma, da wannan
kyakkyawan zabi na Zayyan, tsatso nagari
irin albarka kenan, tsatson malamai
magada Annabawa”.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

​Mama sai ta saki Baba galala! Tana
kallon Baba cikin haushi. Don da wuya ta
nuna bata son abu Baba ya so shi. Baba
Bello ya dauko gangar wa’azi ya soma
bugawa Mama Fatu, bayan ya sallami
Zayyan kan ya tashi ya basu wuri, cewa
hakan data yi ba hanyar da zata yi
confronting al’amarin bane, idan ‘ya’yanta
sun kawo zabin da bai yi mata daidai ba.
Yace ko ganin yarinyar nan baki yi
ba, baki yi bincike akan dabi’u da halayenta
ba, balle su iyayen nata da kika rainawa
matsayi, kawai daga ance diyar malamai sai
ki ari wani abu daban ki yafa! Ya
Subhanallah Malamai fa aka ce! Masana
ilmin Allah da Manzonsa masu hani da
mummuna da umarni da kyakkyawa,
wallahi Fatima kiji tsoron Allah bansan
yaushe kika koma haka ba.
​To so kike kenan ya dauko miki diyar
makada da mawaka in bai dauko diyar
masu karantar da Al’qur’ani da Sunnahr
Ma’aiki ba?

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

​Ina laifin Zayyan anan Hajiya Fatima?
Maimakon ki godewa Allah da ya nutsar
miki dashi, wannan yaron duk rawar kan
samarin zamaninnan bazaki sameshi a ciki
ba. At 27, kina cewa bai isa aure ba, alhalin
yana so yayi auren, idan ‘ya’yanku suna so
su yi aure kuma kuna da halin yi musu
Allah da Manzonsa sunyi umarni da muyi
musu, hakan ya nuna yana so ya kame
kansa ne, ya tara iyali karkashin sunnah
baida ra’ayin sharholiya, kuma da diya ta
mutunci ‘yar masu albarka.
Don wauta da son zuciya sai kice a’ah!
Sabida wani ra’ayi naki na daban marar
muhimmanci?
​Wani lokacin Hajiya Fatimah kina bani
mamaki, don wani sa’in in kika yi wani
abun na rashin kan gado, akan son duniya
da girmama abin duniya sama da nagarta,
wallahi sai in ga kamar bake ba, wani abun
in kikayi sai inga ko Hatoon da bata son
zuwa islamiyyah saida duka, bazata iya yin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kamarsa ba, don rashin tsinkaye da rashin
waiwayen dake cikinsa”.
“Baba!”
Yadda ‘ya’yansa ke kiransa, bashida
zafi ko kadan amma yau ya sille Mama tas
da soso da sabulu, sannan yace tasa a ranta
auren diyar Alaramma an yi an gama ma,
sai idan su suka ce bazasu baiwa dan sa
Zayyan ‘yar su ba, ko yarinya tace bata
sonsa.
Yace “kuma auren ma na gata zan yi
masa, ba sai na jira samun aikinsa ba, zan
masa komai a matsayinsa na Da namiji
daya tilo da na mallaka a rayuwata”.
Baba bai bata lokaci ba, sati daya da
wancan zuwan na Zayyan gidansu Safiyyah
yasa Zayyan din a gaban mota ya raka shi
har gidan Malam Usman a Dandume.
Kuma koda suka je ma a lokacin
daukar karatu magidanta suke yi a gaban
Mallam. Saida suka zauna aka kammala
aka yi addu’a tare dasu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Malam yana ganin Zayyan ya shaida
shi, kuma kamanninsa da dattijon da suke
tare yasa nan da nan ya gane mahaifinsa ne.
Da girmamawa da mutumtawa da far’a
irin ta Malam ya baiwa Baban Zayyan
hannu suka yi gaisuwa irinta manya,
sannan Baba yace ya zo da kansa ne
nemawa Zayyan iznin auren yarinyar
wajensa, don kamar yadda Zayyan ya gaya
masa, ta san da shi, makarantarsu daya,
kuma ita ta bashi iznin ya zo ya gabatar da
kansa ga mahaifinta. Ya kara da cewa “kayi
hakuri Malam ban turo wakili ba nayi
rashin kawaici na zo da kaina. Saboda
Zayyan na musamman ne a wuri na saboda
biyayyar da yake yi mun, kuma shikenan
mini Da namiji”.
Malam yaji dadi kwarai da gaske, ya
kuma yaba da saukin kan Baba, don ko da
ganinsa ka san ba karamin mutum bane.
Hira suka barke da ita daga bisani, da hira
tayi hira tsakaninsu har tarihin iyaye ya
shigo ciki, nan Malam ya gane ainahin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

iyayen Arch. Bello ya sansu, don sunyi
makwabtaka da kakansa a Rafindadi tun
farkon kafuwarta.
​Malam Usman da Arch. Bello basu
rabu a ranar ba, sai da suka kulla
kyakkyawar alaqa da abota a tsakaninsu.
Kuma daga satin daya biyo baya ya
fara zuwa zance gun Safiyyah Usman
Dandume, da yardar iyayensu duka
bangarorin, komai na soyayyarsu bisa
tsarin da Malam ya kafa mai tsauri da
wuyar bi Zayyan ke bi, yana kokarin
kiyayewa, don akwai shi da biyayya ga na
gaba da gudun zuciyar babba, bai taba
karya dokar Malam ba, misali baya tsare
Safiyyah da zance a makaranta kuma baya
zuwa sai sati-satin da malam yayi izni
kadai, har gidan Antinta a Zaria baya zuwa
a renakun da aka masa iyaka da ita.
Baba Bello kuma bai bata lokaci ba,
watanni uku a tsakani da fara neman sa da
Safiyyah bai ko yi shawara da Mama Fatu

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ba yasa aka kai kudin aure mai tsoka
Dandume.
Daga Zayyan har Safiyyah kallon
komai suke kamar a mafarki ko kuwa
almara sanda aka kai kudin aurensu,
saboda basu taba zaton al’amarin zai zo
musu da wuri kuma da sauki haka ba.
Duka-duka haduwarsu da kankamar
maganar auren ba’a fi watanni tara ba.
Safiyyah da mai binta Sabah, Rayyah
da autarsu Rayhah, dukkasu har ita
Hafizan Alqur’ani ne, tun tana shekaru
goma sha hudu tayi hadda da sauka.
Kannenta wadanda kwanikar haihuwarsu
Ammi Hafsatu tayi, shiyasa zaka dauka ko
‘yan uku ne, suka biyo bayanta akan
wannan tsarin na gidansu. Ba’a kaiwa
shekaru sha biyar a duniya yaran gidan
basu yi sauka da haddar Alqur’ani ba.
Gidansu Safiyyah gidane da aka yiwa
tubalin tarbiyyar Islam, da riko da
Alqur’ani da hadisin Manzo, babba da yaro
kowa mahaddaci ne kuma masanin hadisi.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Duk hujjar da ‘yammatan Ammi zasu baka
cikin maganarsu zasu hada maka da Aya ko
Hadisin da ya dace da ita.
Malam Usman a kasar Mali yayi
karatun addinin musulunci mai matukar
zurfi wanda al’ummar Dandume da
wajenta suke amfana dashi a halin yanzu.
Akwai manyan dalibansa da a yanzu
ake damawa dasu a gwamnatin Katsina da
kuma wadanda manyan ‘yan siyasa ne, don
haka kullum baka raba gidansu Safiyyah da
bakin motoci na manyan mutane masu
zuwa ganin Mallam, ko neman taimako
akan wani al’amari da ya shafi addini ko
fatawar ilmi daga gareshi.
Bayan masu zuwa daukar karatu,
kullum kuma zaka tadda gidansu cikin
kabakin alheri na kayayyakin abinci da
sutturah da dabbobin yankawa ayi sadaqa
daga almajiran Malam. Don haka gidansu
Safiyya kullum cikin kyakkyawar cima
yake.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Mahaifiyarsu Haj. Hafsatu da suke
kira “Ammi” haifaffiyar garin Dandume ce
itama kuma auren zumunci ne irin na hadin
iyaye da kakanni tsakaninta da Malam
Usman. Ammi da Malam, tamkar Lailah da
Majnun suke tun daga kuruciya har girma,
Malam bai ko kara attempting na kara aure
ba, don yakan ce “bai iya adalci akan
Hafsatu”, ya rike ‘yar uwarsa kuma
uwargidansa Hafsatu da kyau da amana,
suka hada kai da junansu wajen
tarbiyyarsu da rufa asirin ‘ya’yansu.
Yau da hantsi Ammi da Malam na
tattaunawa akan auren Safiyyah da ya
gabato musu, Ammi tace.
“Malam na fa saka fili na a kasuwa zan
maka gudunmuwa, inaso in baka ka hada
da abinda ya samu, don ayi kayan dakin
Safiyyah, dama saboda auren nan nake ta
ajiye da filinnan ban taba shi ba duk da
tarin bukatoci na.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

To amma naga kai baka fara shirin
komai ba har yanzu, gashi wata uku kamar
yau ne zaka ga sun zo”.
Malam ya dubi matarsa Ammi
(Hafsatu) yace “ai ko da suka kawo kudin
aure na karba, in kin lura ban zura jiki
gabadaya ga al’amarin ba, saboda inaso na
yi addu’a ta akalla sati biyu tsakaninsa da
wanda zuciyata ta kwadaitamin a kanta
kafin zuwansa, sannan in yi wasu sati biyun
ina istikharar neman zabin Allah, kafin ma
na saka musu lokacin daurin aure.
​Ni bana yin abu da ka, ban gayawa
Allah yayimin zabinsa ba, itama Safiyyah
kirawomin ita, in bata addu’ar da zata yi,
da tata istikharar, duk mu dukufa gayawa
Allah nida ita, kafin musa kai a cikin
al’amarin gaba-gadi. Ko don yawan maneman Safiyyah dake
zuwa wajena da bana ko amsa musu, sai shi
wannan Zayyan din kadai da hankalinsa da
karamcin mahaifinsa ya ribaci zuciyata ya
farauto soyayyata gareshi.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

To kinga akwai bukatar a tsaya a yi
addu’a ta musamman a kai, yadda ya
kamata, akan Allah yayi zabin alkhairi ba
son zuciyarmu ba”.
​Ammi tace “gaskiyar ka Malam! Don
nidai ban san meyasa ba, har yanzu ko
kadan maganar auren Safiyyah da Zayyan
dinnan taki kwantamin dari bisa dari a rai,
sai nake ganin kamar gidan da ya fito yafi
karfin shigar Safiyyah. Koko ince bai yi
daidai da tsarin gidajen da ya kamata mu
kai ‘ya’yanmu aure ba.
Bana son shigar da ‘ya’yana gidan da
aka ginu akan rayuwar duniya da akidar
boko zallah. Magana ta domin Allah
Malam, ban taba kawowa ba Haroun zaka
baiwa auren Safiyyah ba (babban
hadiminsa kuma babban almajirinsa)”. ​Malam yayi murmushin manya yace
“ko? Ni kuma wallahi na dauka zaki ce ne
“Sheikh” Yana nufin Yayanta Ridhwan
(Yaya Sheikh) wanda Malam ya kai karatun
degree akan Shari’ar musulunci a kasar

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Misra shekaru biyar da suka wuce, wanda
tare suka taso da Safiyyah a gaban Malam
da Ammi din.
Sai da Ridhwan ya samu tafiya
Al-azhar ne ya bar gaban Malam da Ammi.
Kuma ko bayan kammalawarsa bai dawo
ba ya samu aiki a Doha (Qatar) yayi
zamansa. “Yaya Sheikh”. Sunan da Safiyyah ke
kiran Yayanta Ridhwan dashi kenan,
saboda rikon addininsa da malantarsa
kamar Malam ne ya haife shi ba Yayansa
marigayi Malam Abubakar Dandume ba. Kafin ya tafi Misra shima yana bada
karatu a madadin Malam, musamman idan
malam baya gari ko yanada uzuri. Yaya
Shaikh dan gaban goshin Malam ne.
Ammi tace “ai ni nasan ba soyayya
tsakaninta da Ridhwan, amma Malam?!
Haroun, shi yafi dacewa ka baiwa auren
Safiyyah.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Duba da irin yawan hidimar da yake
maka da zurfin ilmin addinin sa, sannan tun
tana karama yake nuna alamun yana sonta.
Mutanen nan na Rafindadi daga
zuwansu ban ga ka tsananta bincike a kan
gidansu ba, ka aminta ka kuma basu damar
kawo kudin aure, kamar wadanda suka ja
maka ‘Yaasin’ kafin su iso maka". Dariya Ammi ta baiwa Malam sosai,
saida yayi murmushi yace "Amma Hafsatu
kinsan Prof. Bello Rafindadi kuwa? To ai
shi din baya bukatar dogon bincike saboda
sanannen mutum ne a Rafindadi, sannan
tsohon shugaban jami’ar Katsina ne, kowa
ya san shi, ya kuma shaideshi, duk wani
bincike da nayi akansu kyakkyawar shaida
ce take fitowa, ta cewa;
“Prof. Bello ya isa da gidansa!".
Ammi tace "amma dai Malam ka sake
tunani da kyau akai, ni a ganina Haroun
zaifi rike mana Safiyyah da mutunci da
martaba”.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Malam ya gyara zama ya fuskanci
Ammi sosai, halinta ba bako bane a gareshi
bata ko son harka da wanda ya fita kumbar
susa a duniya, ta tsaya iya matsayin da
Allah ya bata na matar aure a kauye, ita
bata wuce gona da iri. To amma shi kansa bai san meyasa ya
zabi Zayyan akan Haroun ba, Haroun din
da ya sani fiyeda kowanne yaro tun
Safiyyah na yarinya sonta yake yi, ita kuma
jininta yafi haduwa dana dan uwanta “Yaya
Sheikh”, bata ma san me Haroun yake yi
ba.
Lokacin da Yaya Shaykh ya tafi karatu
Misra Safiyyah da yake kira “Safifi” ta sha
kuka, kodayake Haroun da bakinsa bai taba
zuwa yace masa yana kamun auren
Safiyyah ba sai hidima da yake da ita tun
tana yarinya kan jiki kan karfi kan
aljihunsa. Komai ya samo sai ya kawowa
Ammi yace a baiwa Safiyyah. Shikuma
Malam, zuciyarsa tafi karkata ga sha’awar
watarana Yaya Sheikh ya dawo gida ya auri

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kanwarsa Safiyyah. Wannan kafin bullowar
Zayyan ne.
Yace “Hafsatu ki cigaba da yimin
shaidar da kinka riga kinka yimin kin ji?
Bazan taba yima ‘ya’yana aure don
abun duniya ko wani mukami na mutane
ba, amma kuma bazan baiwa Safiyya
Haroun ba, sabida abinda baki sani ba har
gobe bansan asalinsa ba, na bude ido kawai
na ganshi cikin almajirai na ne yana
gararramba ba iyaye ne suka kawo min shi
ba, haka na kama shi na rike gam, saboda
naga alamun nagarta da rashin koshin
lafiya a tare dashi tun a lokacin.
Bama wannan ne muhimmin abinda zai
hanani bashi aurenta ba a’ah, halinsa yayi
sanyi kwarai, da wuya ya iya tanqwara
Safiyyah idan ta butsare wallahi sai
jajirtaccen namiji kin san ta dai ba
bakuwarki bace, raggon namiji bai iyawa
da halin Safiyyah idan tana son abu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

To Haroun kam in baki a bude, bayan
rashin sanin iyayensa da ban yi ba har gobe,
wanda ba shine kadai ya hanani bashi
aurenta ba, idan ya auri Safiyya ita zata
koma mijin shi ya koma mijin tace, saboda
kullum dani zai dinga kallonta, wato ya
kalli kanshi a matsayin
hadiminta/almajirinta, duk girman da yake
bani ita zai koma baiwa. Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login