Showing 45001 words to 46889 words out of 46889 words

Chapter 16 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

sana’ar da Baba ya bari da
dukiyarsu.
Ya gayawa Baba Murtala shi bai taba
sha’awar wata sana’a bayan koyarwar da
yake yi ba. Kuma bashida ra’ayin tara
dukiya a rayuwarsa, don a ra’ayinsa ma
nashi kason da aka bashi ya yanke
shawarar Mama zai hadawa ta hada da
tumunin takabarta ta kara jarin
kasuwancinta.
Yace. “A komai yana so ya gaji
Babansa, amma banda a harkar irin neman
kudinsa na rashin hutu da tara dukiya,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

baya kuma son yayi disappointing Mama da
‘yan uwansa in bai zame musu abinda suke
hange a juya dukiyarsu ba”.
Baba Murtala sai yayi murmushi, ya
sake murmusawa, don ya lura rashin
mahaifinsa ya karya lagon jarumtar Zayyan
da yawa, ta wani fannin kamar mara
sauran ‘hope’, a rayuwa, wato ya maida
kansa (hopless) wanda bazai iya tabuka
komai ba, tunda ya rasa source of
inspiration dinsa Baba Bello.
Daga ranar Alhaji Murtala ya sha
alwashin zamewa dan amininsa Zayyan
UBA mahaifi. Uban da zai karfafa shi a
rayuwa har zuwa nasa karewar numfashin,
sannan ya zame masa ubangida na
kasuwanci. Ba abinda yake bukata a lokacin irin
soyayyar Uba da ya rasa, wanda ita kadai
zata karfafeshi a yanzu, ta dawo da
jaruntakarsa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Don haka Arch. Murtala Babangida
Masari, ya dafa kafadarsa ya ce dashi cikin
yin kasa da murya.
“Faduwar wani tashin wani ce my son
Zayyan, kada ka taba bari faduwar wani
naka ta zama faduwarka.
Dama wannan ranar nake jira, wato
rana irin wannan da zaka tako ka zo
gabana da kanka ba tareda Fatuma ta
turoka ba, ka nemi zama cikakken
‘Architect’ makwafin mahaifinka a gabana. Hajiya Fatu dasu Zubaina sunyi abinda
ya dace. Ka sani Bello ba raggo bane, na
kuma tabbata bai haifi raggo ba”.
Yayi murmushi ya cigaba “hakannan
Bello bai abota da ragwaye a sanina dashi
tun muna makaranta, in yaga baka da
kokarima baya kusantarka, kada rashinsa
ya maida kai ragon maza kaji ko Zayyan,
ka mike ka zama mai zafin nema irin
Babanka, duniya bata aure da ragwaye
yanzu, shi namiji rayuwarsa duka ‘yar

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

gwagwarmayar nema ce, in dai da dama
kuma da nasibi. Balle kai gashi kana da
damar, a gefe kana da ni, Babanka Murtala.
Allah kuma yace tashi in taimakeka, sai ka
shiga da kwarin guiwarka ka gani idan
akwai nasibi a ciki ko babu. Dama jira nake komai ya lafa ka kuma
kara samun nutsuwa, sannan in nemoka ko
baka zo ba. Duk da dai inada kyakkyawan
fata, na cewa zaka zo din watarana.
In ce da kai, ka zo mu cigaba daga inda
muka tsaya ni da mahaifinka. Ka mayemin
gurbin abokina Arch. Bello.
Nima cikin kewar rashinsa nake cigaba
da nawa harkokin. Mahaifi ko kwasar kashi
yake a matsayin sana’a yana so Dansa ya
gaji wannan sana’ar, in dai ta halal ce.
Da na Zayyan, ka zo a dama da kai a
harkar “Real Estate”, ka kutsa cikin
profession dinka da kyau ka yishi
practically, ka zama Professional Architect
dinda duniya zata san da zamansa, kamar

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

mahaifinka. Wato ka zama cikakken magaji
ga Bello Rafindadi, akan komai nasa.
Ina kara jaddada maka, “mutum ko
kwasar kashi ce sana’arsa, zai so ace dan sa
ya gajeshi a kanta”.
Ita wannan harkar ta gine-ginen gidaje
da zana su da bada hayarsu, wadda ta zame
mana silar alkhairi nida mahaifinka, ba
kamar aikin koyarwar daka saba da shi
bace, harka ce da babu hutu a cikinta kuma
wadda ke bukatar tsayuwar daka da cinye
lokaci, dole sai ka zage damtse ka kuma
jajirce sannan zaka ci ribarta.
Amma harkace ta ilmin zamani dake
kawo alkhairi sosai ga mamallakanta.
In da ka san irin wahalhalun da muka
sha ni da Bello, da fadi tashin da muka sha
akan harkokin nan kafin mu kawo wannan
matakin, zaka fi yarda kada abar sana’ar ta
bi ruwa a cinye jarinta a wasu abubuwan
daban, tunda Allah yasa akwai namiji a
cikinku”.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

A nan Baba Murtala ya shiga baiwa
Zayyan tarihin struggle din Babanshi Bello
Rafindadi, wajen gina abinda ya tara da
guminsa, yace bai dace ya yarfe wannan
gumin ya zubar ba, tun yana malamin
jami’a a mataki na farko Bello yake
koyarda Zanen gidaje mai ban mamaki ga
dalibansa, ya kara da bawa Zayyan
nagartattun shawarwari akan yadda ake
cimma nasarar harkar REAL ESTATE, ya
kuma ce ya zo su tsunduma cikin harkar
tare, zai kama hannunsa zai masa jagora.
Har zuwa sanda zai gama gane kan
harkar “Real Estate Business” bakidayanta
sannan ne zai saki hannunsa, ya barshi ya
cigaba da tsayawa akan kafarsa.
**** **** ****
A takaice wannan shine mafari, sila,
kuma tushen kafuwarsa, da silar arzikin da
yau yayi cikin dan lokaci da fitar sunansa a
harkar Real Estate.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Arch. Zayyan Bello, ya shiga harkar da
kafar dama kamar, koma fiye da mahaifinsa
Arch. Bello Rafindadi.
Duk wata hikima da baiwa ta
mahaifinsa sai ta yi hijira ta dawo cikin
kansa kamar yadda dukiyarsa ta dawo
hannunsa.
Don kuwa a gaba kadan, bayan kamar
shekaru biyu da farawarsa, Arch. Zayyan
yayi resigning daga aikin koyarwarsa da
jami’ar Ahmadu Bello.
A lokacin tuni Safiyyah tayi graduating
(ta kammala digirinta na farko) itama a
fannin nasu na Architecture, har tayi
hidimar kasa duka a Zarian. Safiyyah na
gama makaranta Zayyan ya bar Zazzau ya
koma Abuja, inda acan ne Baba Murtala
yake kokarin kafa Zayyan akan harkar
zanen Estate da karbar kwangilar gina su
da bada hayar su.
Kuma acan ne duka harkokinsu suka fi
karfi yanzu. Duk da Baba Murtala iyalinsa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

suna Lagos yana yawan zaman Abuja yin
harkokin kwangilar gine-ginensa.
Saida ya dan fara kwari a harkar ya
soma tunanin dawo da Safiyyah kusa dashi
don su bar Zaria gabadaya. Da farko
Zayyan ya fara da kama musu shida
Safiyyah dan madaidaicin gida flat a wani
(block of flats) mai daki uku da falo a Jabi. Estate din da Zayyan ya fara zanawa ya
kuma gina na farko mallakinsu ne shida
‘yan uwansa mata, wato hadakar dukiyarsu
ce su duka, a jihar Katsina suka samar
dashi, a can ya fara gina Estate, don akace
kowa ya bar gida gida ya barshi, wanda
suka sakawa suna; “BELLO RAFINDADI
ESTATE”.
Sai suka zuba ‘yan haya duk shekara
Mama da ‘yanuwanshi na damkar
makudan kudade, shi da Safiyyah ne suka
zauna sukayi ta musu, (debate), akan sunan
da ya dace a sakawa Estate dinsu na farko,
har a karshe suka ambaceta da ‘surname’

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

dinsu gabadayansu, watau “Bello Rafindadi
Estate”. Anan GRA Katsina.
Zayyan ya muskuta daga kwancen da
yake, yana cigaba da dogon tunanin da yake
yi…. wani lokacin har yana matse kwallah,
wani lokacin kuma yayi murmushi duk shi
kadai. Safiyyah have immensely contributed a
lot to his achievements and successes
(Safiyyah tayi matukar bada gudunmuwa
ga nasarorinsa da abubuwan da ya cimma
na nasara a rayuwarsa). Domin a duka
wadannan lokutan Safiyyah na tare dashi
cikin halin dadi dana babu dadi, against all
odds ta tsaya a gefensa, kuma tana kula da
rayuwarsa da cikinsa da lafiyarsa da
bukatunsa na Da namiji cikin kauna da
soyayyah.
Ta taya shi raba dare suna ‘sharing
idea’ da musayar fasaha, inda zaka gansu
sun zauna a falonsu sun baje takardun Zane
a gabansu cikin dare, kamar abokan aiki ba
mata da miji ba, suna tsara Zanen Estate

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

tare, tareda da shirya time-table na yadda
zasu gudanar da kwangilolin ginin gidajen
da suka samu su aiwatar dasu bi da bi cikin
tsari da sarrafa hikima.
**** **** ****
Bazai manta ba, shi da ita ne suka raba
dare a wani dogon dare mai dumbin tarihi
tarihi suka samar da ‘idea’ din kirkirar
“SUNSET ESTATE”.
Wanda zai zama mallakinsa ne shikadai
watau ba tareda dukiyar ‘yan uwansa a ciki
ko mahaifiyarsu ba. Cewa suka yi bari su
hada duk wata fasaha da suke da ita ta
ilmin Architecture a kan Estate din, da duk
abinda Zayyan mallaka ya sayar ya saka a
cikin capital dinsa ta ginin da zasu yi, su yi
Estate din amma wannan karon a matsayin
nasa shikadai.
Saboda shekaru uku bayan kama
harkar ‘real estate’ da yayi dukiyarsu
Zubaida ta rubanya a hannunsa, kusan
kashi hudun yadda ya karbeta daga

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

hannunsu, kowaccensu ta mallaki Estate
nata na kanta yanzu a Katsina, haka shima
yanada Estate sun kai hudu a Katsina,
hakika Allah ya sanya masa hannu da
nasibi a harkar ‘real estate’, da kuma
taimakon Baban kwarai Baban marayu,
Alhaji Murtala Babangida Masari.
Bayan ya tsayar da idea din yin nasa
Estate din na kansa, bisa shawara da
gudummuwar Safiyyah, sai yaje ya samu
Mama Fatu akan yana son gina Estate nasa
na kashin kansa a Abuja. Mama Fatu bata hanashi ba, ta dai ce
in dai zai cigaba da rikewa ‘yanuwansa
mata nasu Estates din, ita bazata hana shi
yin yadda yake so ba. In kuma Safiyyah ce
ta zugo shi akan ya ware dukiyarsa daga
Katsina ya mayar Abuja don tana bakin
cikin yana kulawa ‘yan uwansa da Estates
dinsu a Katsina, tana so ta janyeshi
gabadaya ya maida hakalinsa a Abuja, to
tayi a banza, tunda dukiyarsa dai zata taba
zama tata ba, tunda gata nan har yau sai

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

cika masai da kashi ta iya, ko gudan jini
bata taba ajiye masa a kasa da sunan dansa
ba.
Maganar ta dade tana masa yawo a kai,
amma bai ce komai ba. har yaushe akayi
auren da za’a soma cewa Sophie bata haihu
ba?
Bisa shaidun da suka kamata wato
Lauyan Baba Barr. Abba Gana Shettima da
Baba Murtala da Mama, Zayyan ya zame
komai nasa daga cikin na ‘yan uwansa su
Zubaidah, amma zai cigaba da kula musu
da komai nasu. Mafari kenan na fara
samuwar assasa tubalin ginin SUNSET
ESTATE a unguwar Guzape.
Bisa zane da tsari irinna zamani,
wanda yayi amanna bai taba yiwa kowa
irinsa ba. Kuma anyi ittifaqin bai dauko
samfurinsa daga ko’ina ba. A’ah, zallar idea
dinsu ce shi da Safiyyah. Domin sun kure duk wata fasaharsu ta
Zane a kansa shida Sophie. Shi da Safiyyah

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

suka samar da SUNSET ESTATE. Bayan
shekaru biyun da suka dauka suna raba
dare akan zanensa, tareda tsara proposal
din ginin, komai na shirye-shiryen ginin ya
kammala a shekara ta shidda da aurensu,
sai aka fara gina ‘Sunset Estate’. **** **** ****



Mu karasa a littafi na biyu.
Tare suke.
Sumayyah Abdulqadir
07030137870
(whtspp only).
PAID BOOK

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login