Showing 27001 words to 30000 words out of 46889 words

Chapter 10 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf


tafukan hannunta ya saka fuskarsa a
tsakaninsu, santsin sajensa dake kwance
gefe da gefe na kyakkyawar Barumiyar
fuskarsa yasa saida tsigar jikinta ya tashi
yarrr! Shikuma duk sai ya susuce, ya rikice
irin na rashin sabo da kusantar jikin mace,
tasowar wani sabon al’amari a tare dashi
yasa ya kai tafin hannunta saman lips dinsa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ya sumbata for the first time, idanunshi a
lumshe yace.
“baki bukatar bani hakuri, amarya ai
bata laifi ko ta kashe dan masu gida, that’s
my beloved Sophie, ni kadai na san irin
tanadin soyayyar da nake mana, nagode
Safiyyah kinji, once again nagode kuma in
sha Allah bazaki taba nadamar hada
rayuwa dani ba, nayi miki wannan
alkawarin, in sha Allah Safiyyah".
Tunda Zayyan ya samu wannan damar,
yau sai ya dukufa lallashin 'yan kayansa da
alkawura da kalamai masu dadi har
Safiyyah ta fara kwantar da hankalinta a
kan tarewarta, ta dan saki jikinta dashi
kadan, hannunsa sarke cikin tausasan
yatsunta suka shiga hira a hakan. Kai a
karshe ma basu rabu ba a ranar, saida
Zayyan ya san yadda yayi da dabara da
hikima ya raba jikinsu wuri guda karo na
farko a tarihin soyayyarsuda jikisa ya shiga
cikin nata, ya rungume Safiyyah tsam-tsam
a jikinsa lokacin da zai tafi, Safiyyah na iya

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

jin yadda kirjin Zayyan ke bugawa ba
sassauci yana gaya mata cikin kunnenta.
“Saurara Sophie kiji irin bugun da
kirjina ke yi, ba komai bane sonki da
tsananin sha’awarki ne”. Ko daga yadda
jikinsa ke bari cikin mararin samunta da
yayi cikin jikinsa yau, ta yarda da abinda
yake fadin. Zayyan ya samu gangara domin
gabadaya Sophie ta saki jikita dashi yau,
yayi kissing dinta sosai a kasan wuyanta,
kafin ya gangara zuwa saman lips dinta, ya
sumbaceta son ransa har cikin tsakiyar
bakinta da wani launin (French kiss) da shi
kansa bai san yadda ya aiwatar dashi ba,
karo na farko a soyayyarsu.
A ranar ya gaya mata ya san 'fear'
dinta, “I obviously know your fear” don na
karanceshi tsaf a tsakiyar idanunki, ko baki
fada ba na gane tsoron daren farko kike ji,
amma kullum Safiyyah kisa a ranki ni ba
abinda yasa na aureki kenan ba, kuma
soyayya ba cutarwa bace.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Na aureki ne don ina sonki Sophie, ba
don sha’awar wani abu a jikinki ba, ina so
in rayu dake ne, daga nan har karshen
rayuwata.
Ina fatan ki zama uwar ‘ya’yana a
duniya da lahira kuma matar dana ke so in
rayu da ita har a aljannah.
Da wannan nake so ki kwantar da
hankalinki ki tare a gidanki kinji Safiyyah,
nayi miki alkawarin bazanyi komai ba sai
ranar da kika shirya karbata a matsayin
mijinki, barin rayuwarki, kuma bisa
amincewarki da yardarki da goyon bayanki
kadai zan kusanceki”.
Bayan kunya da taji yau kamar tace
kasar ta tsage ta shige har da tausayinsa da
karin soyayyarsa. Sukayi wata irin rabuwa
mai sanyi a zuciyoyinsu, Zayyan yana kara
kashe mata zuciya da kalamai masu
sanyaya ruhi da Batasan ya iya bama. Ganin kwana biyu Safiyyah ta fara
samuwa ta amince ta kwantar da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

hankalinta, sai iyayenta suka durfafi shirin
kaita gidan mijinta a Zaria.
Malam yace baya son bidi’a mara
tushe. Don haka baya son taron biki.
Zayyan zuwa lokacin ya maida hankalinsa
ya kammala project dinsa yayi (defense,
both internal and viva). Ya fito a sahu na farko cikin
zakakuran dalibai da suka fita da (first
class) su uku kacal a tsangayar
Architecture, daga jami'ar Ahmadu Bello,
don haka yana gamawa ABU suka daukeshi
aiki sharp-sharp a matsayin Assistant
Lecturer.
Lecturing has been his dream career….
saboda a komai so yake ya gaji Babansa.
Don haka ba bata lokaci ya karbi offer din
da godiya.
Dan madaidaicin gidan da Baba ya
kama musu flat ne a Samaru daidai su. Two
bedroom flat da parlour daya, sai kitchen

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

da balcony da harabar adana mota guda
daya.
Akayi sa’a daga Zayyan har Safiyyah
masu saukin tunani na rayuwa ne. Iya
abinda mahaifinta yayi mata dashi taje
gidan mijinta. Ba abinda Zayyan ya saka a
gidan har ledar tsakar daki su suka saka
abinsu. Safiyyah ta shigo gidan Zayyan da
tsaftatacciyar zuciya, soyayyar su gwanin
sha’awa, takamaimai in za’a dora mata
wuka a makoshi, bazata ce ga abinda ya
sata son Zayyan ba da bashi matsayin barin
rayuwarta (miji) da gaggawa haka ba, cikin
abinda bai gaza shekara ba, kawai tana son
duka halayensa. A wannan lokacin kam
shima da kansa ya san Sophie babu
soyayyarsa irinta aure mai girma a ranta,
sai ko halayensa da kamalarsa data ke so
fiyeda komai nasa.
Sai ya fara da koyawa Safiyyah yadda
zata yi masa so na soyayyar aure gradually.
Saboda aurensu yazo ne unexpectedly daga

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Allah, wato daga zuwa gabatarwa tsakanin
iyaye sai Ubangiji ya aiwatar da kirarinsa
na “kun fa ya kun” a kansu.
Don haka da Safiyyah ta tare abu na
farko da Zayyan ya fara yi shine ya fara da
janta a jiki, ya maida kansa dan aikinta,
komai tare sukeyi na ayyukan gida, suna yi
suna hira yana bata dariya kamar ba shine
mara far’ar nan a filin Allah ba. A hankali ya fara koya mata yanda
zata zauna dashi cikin tarairayar abinda
yake so da gujema wanda baya so, Zayyan
ya koya mata sakin jiki dashi cikin launin
soyayyahrsa mai shiga rai. Alal misali a ranar da Safiyyah ta tare
da yake Zayyan ya riga ya lura da fear dinta
akan first night.
Sai ya hadiye duk wata zalamarsa irin
ta kowanne sabon ango a wannan ranar, ya
dinga lallaba Sophie da tatsuniya da labarin
Magana Jari ce, saboda shi yayi
karance-karance na adabin Hausa tun yana

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

secondary school, ya bata labarin cewa yana
cikin Hausa Club and Society har Debate na
harshen Hausa ya sha zuwa ya wakilci
makarantarsu. A haka labari ya kaiwa
Sophie karo a ranar har tayi barci a jikinsa
bata san lokacin da tayi ba. Hakika ta sara ma Zayyan wajen iya
sadaukarwa, ga iya kalaman soyayya da
lallashin mace, irin kalaman da ya
baibayeta dasu da asubahin ranar bayan
sun sallaci sallar asubah a jam’I su biyu.
Suka koma gado suka kwanta idonta cike
da barcin gajiya amma hankalinta bai
kwanta ba, ganin shi bashi da niyyar yin
barcin safen, sai ma yaja duvet ya rufe ta
har zuwa kirjinta, ya sukuya saman kanta
yana mata kalamai masu kwantar da
hankali da nuna mata cewa shi bashi da
matsalar komai yau a kan hakan. Bama ya
jin sha’awar komai (he’s overwhelmed with
happiness and excitedness) da shigowarta
rayuwarsa, yace ta saki jikinta tayi barcinta
ta huta Zayyan zai mata tausar kafar da
zata sat aji dadin barci. Tun tana dar-dar da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

shi har ta yarda da gaske yake, ya soma yi
mata tausar ta hanyar jan zara-zaran
yatsun kafarta a hankali, tausar namiji na
ratsa Safiyyah bata san yaushe barci ya
soma fizgarta ba. Daga bisani da ya tabbatar tayi nisa a
barcinta sai ya jefa pillow a kan kilishi ya
koma can ya kwanta, yana kallon barcin
Safiyyah da yadda take sauke numfashin
barcinta cikin nutsuwa. Da gaske da akace
wai wasu matan, sun fi kyau idan suna
barci, ya yarda da hakan yau akan ‘Sophie’,
wato Safiyyah is a sleeping beauty”.
Yayi ta jinjinawa kansa yana sarawa
kansa da kansa tareda kissimawa a ransa,
ko yaya akayi ya iya yima Sophie wannan
bajintar? A dai wannan daren mai dumbin
tarihi da ya dade yana jiran isowarsa, wato
a darensu na farko? Ya jure bai kusanceta
ba duk karfin sonsa gareta, da dokinsa na
zuwan wannan ranar?!
Shi da kansa sai ya baiwa kansa amsa
da cewa saboda sonta da kaunarta da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

yakeyi sun rinjayi sha’awar. Kasancewarta
cikin kwanciyar hankali rana ta farko a
gidansa zai fiye masa duk wani pleasure da
zai samu a cikin daren.
Bai auri Safiyyah don biyan bukatar
gangar jikinsa ba, kaunarta yake yi har
cikin bargonsa, wata irin kauna mai yawa,
don haka son farin cikinta tareda shi a
zaman aurensu ya rinjayi komai. Kuma yana so ya zama mai fada da
cikawa a gareta. Wato in yace zaiyi abu, ya
tsaya ya tabbatar yayi, in yace bazai yi ba,
kada ya canza. Kwanciyar hankalinta dashi
yana gaba da komai. Washegari daga shi
har ita, a ranar sai suka zamewa juna
kamar wasu bakin juna, ta kasa hada ido
dashi tana ji a jikinta kamar tayi masa laifi
data ganshi kwance akan carpet, wato ya
bar mata gadon ta kwana ita kadai cikin
sakewa.
Tare sukayi girkin breakfast, Zayyan
na firar dankali Safiya na juye Ruwan zafi a
tea flask, tana masa dariyar wai ya iya firar

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

dankali, yace “meye abin mamaki? Wai
baki san ni kanin mata bane, kuma Yayan
mata ba? In kawayen Mama suka zo
gidanmu ce min suke na mata-na matan
Mama. Don haka ki daina mamaki don kin
samu kwararren mai firar Dankali a
gidanki, ba abinda ban iya ba na kitchen, in
gaya miki.
Kafin a yiwa su Yaya Zubaida aure duk
makyuyata ne. Mama tafi sakani tayata
aikin kitchen fiye dasu”.
Nan ya shiga bata labarin halayen
‘yanmatan gidansu daya bayan daya, cewa
Zaitoon da Zahra sun fi baiwa gayu da
kwalliya muhimmanci fiyeda aikin gida,
Hatoon kuwa auta ce sangartacciyar Mama,
da irin kyuyar Yaya Zubaida akan aikin
gida, yanzu zata kirkiro ciwon ciki na karya
don Mama tace ya karba ya mata aikin, don
haka duk wani aikin kitchen na Yaya
Zubaida kusan shi yake yiwa Mama Fatu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Yace Yaya Zubaina ce kadai ke dan
tabukawa, kafin a aurar dasu, itama sai in
baya nan”.
A haka suka soya dankalin turawa
(irish) da kwai, suka dafa shayinsu yaji
kayan kamshin gargajiya kanumfari da
citta, suka juye komai a plate guda, suka
dauka zuwa falo, yana sakale da ita a
kugunsa tanata jin kunya. A plate daya suke ci, Zayyan ya cako
irish da fork ya kai bakin Safiyyah “ha’an,
bude nan in baki a baki!” Kunya sosai ta
kamata, ta rufe ido tana ‘yar dariya ta
rashin sabo, wani abu da wani namiji bai
taba yi mata ba, bayan Yayanta Yaya
Sheikh, wato bata abinci a baki.
Shima Yaya Sheikh din tun tana ‘yar
kankanuwa ne, sanda tana junior
secondary, Yaya Sheikh na yawan bata
abinci a baki, kuma a gaban Ammi,
musamman in tana fushi, ko Ammi ta bata
mata rai. Zayyan ya lura ta tafi tunani,
yace.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

"Sophie tunanin me kike haka? Bude
idonki ki dubeni, wannan kunyar fa dole ki
ajiyemin ita a gefe zuwa sanda zan
bukaceta, amma ba na bukatarta yanzu
sam. Ta yi min yawa. Yanzu so nake in zama ke ki zama ni,
mu gina trust a tsakaninmu, mu zama
confident din junanmu, muyi rayuwa ta
shakuwa, fahimtar juna, amana da soyayya.
Sophie kin san daga jiya na zama naki
kin zama tawa? To kiyi wa Allah ki daina
yimin rowar kyawawan idanunki in muna
tare, kina wannan boye sun, domin su nafi
son gani koyaushe, inta tozali da (silverish
eye ball) dinki. Daga su sai in’inar
(stammering), su nafi so fiyeda komai naki.
So open your eyes and look straight into my
eyes ko naji dadi, ki kuma bude min dan
bakin nan ina so in ciyar dake yau da
hannuna, ki kuma yimin ‘yar in’inar ko
kadan ce inji mana?".
Ai bata san sanda tasa dariya ba. Shi
kuma daman hakan yake so, ya dawo da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

attention dinta gareshi, don ta tafi tunani,
sam ta manta yana wurin, sai ya cigaba da
kambama dadin in’inar tata, wadda yace
tafi masa duk wata muryar zabiyoyin
larabawan da ya sani dadi (Arab musicians)
su Nancy Agram. Dariya take yi sosai, ta shagaltu da
dariyar shima ta shagaltar dashi cikin
kallonta da shaukinta, tace “wannan kuma
“C” ce Malam, don ka san bazan iya waka
bane kake mun ba’a”. Da rana ma tare suka yi girkinsu inda
sukayi lunch mai saukin girkawa, jollof din
shinkafa tayi musu da taji daddawa da
naman saniya. Tun anan Zayyan ya fara
gane kwarewar Safiyyah a girkin hausawa
ne, ba girkin turawa ba, tunda har tasa
daudawa a jollof. Sai ya bashi wani irin
aroma da dandano, da bai saba ji ba, kuma
ya masa dadi, Ammi ta musu wannan horon
bakidayansu ita da kannenta su Rayyah,
sau da dama Ammi in suna gida basa
makaranta sam bata shiga kitchen. Su take

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

barwa komai na girkin gidansu da hidimar
tsaftar gidansu.
Tun Safiyyah na dar-dar da angon
nata Zayyan Bello Rafindadi, har ta gama
sakankancewa Zayyan dai baya neman
komai daga gareta sai sabo, shakuwa da
soyayyah, wato so yake su saba a wannan
lokacin, kwanciyar hankalinta da sakin
jikinta dashi yafi bukata fiyeda gangar
jikinta.
Soyayyar da bai nuna mata kafin
aurensu ba, ita yake nuna mata yanzu
gangariya, a halin yanzu baya jin kunyar ya
zauna daga shi sai (shorts) a gabanta, tayi ta
jin kunya kamar tace kasar ta tsage ta shige
ta kuma kasa sakewa, fitsarar Da namiji da
bai nuna mata a makaranta ba yake zuba
mata gangariyarta yanzu, a tsakar gidansu
cikin dakin aurensu. Misali yace ta zo ta
cuda shi a wanka, ko sai sun yi wanka tare,
amma sai ta gudu ta buya ko tace girki take
zai kone in ta tafi.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Tafi-tafi daga kwana bisa kilishi har
suka koma kwana gado daya, ba tareda ta
gano wani abu makamancin faruwar
wannan tsoron nata daga Zayyan dinta ba.
Gabadaya ta soma sakewa dashi
yanzu, ta kuma sakankance ta saki jikinta
sosai dashi dari bisa dari, ta yarda da angon
nata, cewa shi daban yake, baya cikin layin
irin mazan da Anti Dije ke lissafin Ustazai a
waje, Devilish a cikin gida, ita mijinta
bawan Allah ne mai son ta da yawan
tausayinta, da gudun duk abinda zai
wahalar da ita bazai iya wannan al’amarin
da ita ba. Ke dai barshi da yawan tubewa a
gabanta batareda yaji komai ba.
Cikin sati biyu kacal Zayyan da
Safiyyah suka wani irin dinke tamkar sun
shekara da aure.
Sai ga Sophie har ta kan rabi jikinsa
ta kwanta ba tareda ta san lokacin da tayi
hakan ba, in hirar falo tayi dadi kenan.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Shikuma ya fara amfani da wannan
damar yace kitso zai yi mata, duk yabi ya
cukurkude mata sassalkan gashinta ya
cukuikuiyeshi da kalba. Ga Safiyyah Masha
Allah da gashin Katsinawan Dikko. Suka
manne da juna tamkar tube da tyre, sallah
kadai ke rabasu, in zai tafi masallaci, shima
sai taji wani iri kamar in ya fitan bazai
dawo ba. In ya fita din kuma zuciyarta na
kansa. Allah-Allah kawai take taji motsin
taba kofarsa ya dawo gida.
Tafi-tafi daga sanda suka samu kansu
dumu-dumu cikin sumbatar juna ma su
duka biyun basu ankare ba, sabida feeling
irinna kowanne lafiyayyen dan adam da ya
soma aiki a jikin kowannensu. Safiyyah bata farga data fara
kamuwa a tarkon angon nata Zayyan ba,
sai ranar da kiss mai zafi irin (hot kiss) ya
ratsa a tsakaninsu….
Daga shi ya zarce da shafar sassan
jikinta kota ina da kyar ta iya kwatar kanta
a ranar.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Wata ranar Asabar wani (accidental
French kiss) ya faru tsakaninsu na wucin
gadi. Hakan ya faru dasu ne ranar bisa
dining area, ta kona mishi dan yatsa da
ruwan zafi garin zuba mishi tea bata sani
ba. Nan Malaminki Zayyan ya samu hanyar
da ya dade yana neman samu bai samu ba,
ya jangabe rike da hannunsa yace sai ta
tsotse dan yatsan zai daina masa zafi, “zafi
yake mun sosai kamar fatar ta daye
Sophie”. Ai kuwa Safiyyah a rikice, ta
taqarqare ta kai dan yatsan bakinta ta hau
tsotson babban dan yatsan ba tareda ta san
tarko ne ya dana mata ba, kiss din da ita ta
fara jinsa a jikinta kafin shi, tasirinsa ya tafi
abruptly ya ratsa har tsakiyar kwakwalwar
Safiyyah data Zayyan din kansa.
Lokacin da tsotson y afara yin tsotso,
sai jikin kowannensu ya fara dauka, suka
dubi juna a rikice, a gigice, idanuwa sun
birkice da sha’awar juna, duk tayi arousing
dinsu, kallon da yayi mata a lokacin da
barauniyar rungumar da ya yi mata ba
shiri, shi ya tayar da dukkan emotions dinta

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

na diya mace, ta kasa koda wani
kwakkwaran motsi na kwatar kai.
Shi kuma haduwar fatar jikinsu wuri
guda ya kara birkita shi, nan suka bige da
sumbatar juna a urunce, a yunwace kuma a
susuce….
A wannan ranar dai da kyar suka
kwaci kawunansu a hannun juna, ba tareda
komai ya wakana ba.
Matsananciyar kunyar shi data biyo
bayan hakan ta hanata sakat har wayewar
gari.
Daga ranar ta saki jiki aka soma
shan zumar soyayyah, har Zayyan ya soma
aika manyan sakonninsa kadan-kadan cikin
dabara irin tasa.
Soyayyar sa mai sanyi, wani lokacin
zazzafa, ta tsayawa Safiyyah a rai, ta rike
ran Sophie akan mijin nata, soyayyah ta
wasannin ma’aurata (romancing) kawai
yake gwada mata zallarta, mai tsayawa a
ran diya mace, irin ta namijin da ya san kan

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

love, ya kuma yarda da kansa da
matsayinsa a zuciyar matarsa, cewa shi abin
so ne ga matarshi, da kowacce irin mace
data fada komarsa.
A wannan dan tsakanin Zayyan ya
nunawa Safiyyah cewa shi mai tsananin
sonta ne, kuma yayi hakuri mai yawa da ba
duk maza zasu iya kamarsa ba, tunda ya
aureta yake tattalinta da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login