Showing 42001 words to 45000 words out of 46889 words

Chapter 15 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

lallashinsa, yace masa “kayi hakuri
Zayyanu, inna kira wayarka bana samunka,
Hajiya kanta tace bata samunka a waya wai
ta rasa lambar maidakinka cikin wayarta,
naso in gaya maka Habu ya koma garin su
tun bayan bakwai, wato mai kula da
shukokin gidan, shikuma Umaru mai
wankin motoci da share-share shima yace
ya samu wani aikin don haka ya tafi, Bala
direba kuwa ko sallama bai yimin ba na
daina ganinsa”.
Zayyan yace a ransa “dan adam kenan!
Babu komai, it is well. An gode”.
A fili kuma yace “kuma da babu Habu
ba Umaru ba Bala a gidan, saboda su
butulallun Allah ne, kai sai ka kasa share
harabar gidannan ko sau daya?”
Shi bai san ba su Habu kadai ba, duk
ma’aikatan cikin gida mata ma sun ware,
don Mama tace bata bukatar kowa, Ankudi
kawai tace ta zauna to itama tace zata ganin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

gida kafin sadaqar arba’in amma har yau
bata dawo ba.
Daga cikin gida Mama ta jiyo tashin
sautin Zayyan yana magana da Baba Ilya
cikin fada-fada, take cema Hatoon “ke duba
min ki gani naji kamar muryar Baffana
yana fada a waje, jeki gano min shi da
waye? Dama ashe Baffa ya iya fada haka?” Hatoon ta leka ta taga ta ganshi, tace da
Mama “ai kuwa shine. Baba Ilya ne maybe
ya taka sawun barawo”.
Ya tako zuwa cikin gidansu yana
gayawa kansa sai yayi da gaske, ya kuma
tsaya tsayin daka don ganin gidansu bai
mutu ba, a rashin Baba Bello.
​Dole ya dinga zuwa akai kai, fiyeda
baya don tabbatar da lafiyar gidansu,
lafiyar kannensa data mahaifiyarsu, da
bukatunsu na yau da kullum.​
​Yayi sallama a falon Mama Fatu,
Maman ta amsa daga zaune akan

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

sallayarta, bata dade da idar da sallahr
azahar ba ya shigo, ta ce.
“maraba lale da Baffan Mama, kuma
Baffa daga zuwa sai fada? Kai da waye
halan? Waya taba min Baffana magajin
gida haka?”
Zama Zayyan yayi, yana ajiyar zuciya,
ransa yana sanyi da ganin Mama, da
kalaman maraba da take yi masa cike da
murnar ganinsa, bai ce komai ba, sai sauke
ajiyar zuciya yake yana kallon Mama cikin
tausayi, ganin yadda duk kibar nan tata ta
jin dadi ta zaizaye rana daya yasa yaji
zuciyarsa ta dada tsinkewa, gabadaya ta
rame, alamu ne na har yanzu bata wartsake
daga dukan da rashin Baba Bello yayi mata
ba.
Idanuwanta duk sun yi ciki sun
kankance don yawan kuka, Mama ta koma
yellow kamar mai ciwon shawara daga fara,
kuma jajazir din Barumiyarta.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Gidan da kullum zaka samu kowa cikin
annuri ana raha da wasa da dariya, a shiga
nan a fita can, walwalar gidan data
mutanen gidan duk ta kaura yanzu, tabbas
Uba shine jigon gida, don haka Mama Fatu
kam ta ga mutuwa irin wadda bata taba
gani ba, saboda Baba Zayyan dinnan
shikadai ta sani ta kuma rika a duniya a
matsayin komai nata, bata gajiya da fadawa
‘ya’yanta “Bello ne uwarta shine ubanta”
tunda bata tashi tareda iyayenta ta san
dadinsu ba sai nasa, shine kuma danginta
don ba abinda dangi suka kulla mata a
rayuwarta, tun tana karama iyayenta suka
rasu, aka rasa mai daukarta sai wata
kanwar mahaifiyarta a Rumah, ya kuma
aureta ne da kananan shekarun da basu fice
goma sha biyar ba.
Sun yi zama na kauna da soyayya abar
buga misali ita dashi da ‘ya’yansu, na kusan
shekaru arba’in da doriya.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Zayyan yasa farin hankacinsa yana
share fuskarsa da tayi jajawur da gumi,
hawaye ya digo masa.
Mama ta taba ce ma Zubaina.
“Wannan shine hawayen Zayyan na
farko data yi witnessing a shekarun
girmansa”.
Ko ranar da Baba ya rasu, Zayyan yafi
kowa jarunta da nuna dakiya, amma a yau
ganin yadda gidan mahaifin nasa ma neman
mutuwa yake yi ya jefa shi cikin wani hali
na jin mutuwar Baba Zayyan fiye da
kullum. ​Da kyar Mama ta samu ya saki ransa
suka soma gaisawa, tace ina Safiyyah? Yace
a ransa yau wace rana Mama ta tambayeshi
Safiyyah? Ya gaya mata tana lafiya tana
kuma gaisheta. Yayi fatan Allah yasa Mama ta fara son
Safiyyah ne saboda rashin Baba Zayyan,
tunda ta san yadda shi Baban yake sonta

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kamar ‘yarsa, in ta cigaba da nuna rashin
kauna ga Safiyyah abin zaiyi masa yawa.
Sunyi hirarraki masu dama ranar,
Mama tace “dama inata jiran zuwanka
tunda kaki ko waya ka kunna, in gaya maka
sakon Babanku Alhaji Murtala.
Zuwansa har biyu kenan bai sameka
ba, kan maganar dukiyoyin Babanku dake
hannunsa da wadanda ya sani dake hannun
Lauyansa dama wadanda ke Banki, yazo ne
kan batun, don yanaso zai tattarosu a raba
gado ranar sadaqar arba’in, a raba
marigayin da wannan nauyin”.
Kamar yadda ya riga ya sani Arch.
Murtala shine babban aminin Baba Bello,
kuma kamar Ubangida yake a gareshi a
harkar Real Estate, shi ya fara budawa
Baba harkar ya shigeta sosai da
taimakonsa, bayan ritayarsa daga aikin
gwamnati, saboda Alh. Murtala yanada
connections sosai da gwamnatin tarayya, da
kuma gwamnatin jihar Lagos.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Arch. Murtala Babangida Masari,
abokin Baba Bello ne tun na kuruciya
(childhood friend) wanda tun zamanin
makarantar sakandire suke tare, kuma
sukayi karatun jami’a shima tare a fanni
guda, don haka lokacin da Baba yayi ritaya
sai ya jawoshi jikinsa ya tsundumashi a
harkar da yakeyi ta kwangilar gine-gine da
zanen gidaje.
Zayyan yace da Mama cikin raunin
murya da karaya.
“Kamar ana jiran matsawar Baba har
an soma zancen raba gadonsa? Hakan bai yi
wuri ba saboda Allah Mama?”
Mama tace “umarnin Allah ne ai na
raba gado cikin lokaci, ba umarni na bane,
ba kuma na Babanku Murtala ba, don a
raba mamaci da nauyinsa, ba don komai
ake rabawa da wuri ba ai don amfanin
mamaci ne, ba kuma ni nace dashi azo a
raba din ba, balle kace na fiya kankanba”.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Kafin Zayyan ya samu abun cewa sai
Hatoon ta fito daga daki, ta gaida shi, ta
wuce kitchen ta zubo abincin da Mama tayi
yau, ta dawo cikinsu ta zauna gefe tana ci,
Mama tayi mata kallon takaici tace. “Shi Yayanku da yayi sammako yayi
doguwar tafiya tun daga Zaria baki ga ya
kamata ki bashi abincin ba? Hatoon, na
rasa irin hakalinki, yaushe zaki girma ne?
Kullum sai kin nunawa mutane halinki na
rashin da’a da sanin yakamata da zaisa aga
laifina wajen baki tarbiyya kike jin dadi ko?
Cikinki kadai kika sani. amma na dan
uwanki ko oho ko?”
Karo na farko da zai iya cewa yaga
Mama tayiwa Hatoon dinta fada, kuma a
kan abinda ya kamata. Kullum saidai tayi
laifi in an yi yunkurin yi mata fada ko gyara
ta tare mata. Yau dai yanata ganin sauyi a tareda
Mama yayi fatan Allah yasa ta dore. Yana
matukar son ace halin uwarsa yafi na kowa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kyau. Ganin yadda Hatoon ta zumburo
baki, dama aka ce icce tun yana danye ake
tankwara shi…..
Hatoon zatayi shagwabarta yadda ta
saba sai suka hada ido da shi, irin kallon da
ya sakar mata yasa ba shiri ta mayar da
bakin data zumburo ya koma daidai, daga
yadda taga yanayinsa zai iya marinta yau,
don haka ba shiri ta tashi da sauri, ta koma
kitchen din ta zubo masa Sinasir, Waina da
miyar ganyen alayyahu da tantakwashin Sa,
da Mama tayi. Ta kawo gabansa ta lallaba
ta ajiye ta gudu dakinta bata kara fitowa
ba.
To dai da yake yana jin yunwar da
gasken gaske, shiyasa ya yarda da tayin
Mama, ya mike ya wanko hannunsa a sink
din falo, ya dawo ya zauna, ya yiwa Sinasir
da wainar nan kyakkyawan ci, ko babu
komai Mamansa ce tayi da kanta. Yayi kewar girkinta sosai, don Mama
ta iya girki na gargajiya, yana ci suna hira
da Mama, hirar da suka jima basu yi irinta

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ba, yace zai je gidan Baba Murtala din cikin
satinnan ya same shi har Lagos din.
Haka ya wuni sur tare dasu har la’asar
yana Rafindadi, har su Zahra suka dawo
daga makaranta suka sameshi a gidan suka
sha hira shida su, abinda bai cika yi dasu ba
a baya, amma yau ya zauna cikinsu ya saki
jiki da fuska ya ji damuwar kowaccensu da
sha’anin karatunta, ya basu abinda suke
bukata don tausayinsu yake ji su duka in ya
tuna yanzu sunansu marayu, musamman
sanin yadda Baba ke kula dasu, kafin
yamma tayi ya juyo Zaria. Sai dare can ya
iso gida.
Ya koma Zaria da kyakkyawan
kudurin ba zai sake nisa dasu Mama ba,
hakika suna bukatarsa a kusa dasu, domin
yaga yadda rashin Baba ya ragaita su.
Ya barwa ransa in sha Allah ba zai
kuma jimawa bai zo garesu ba.
Ya tafi da tausayin Mama fal a ransa,
da damuwar ganin su Zahra duk sun rage

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

karsashi da kidifiri, wannan fallin nasu na
gayu da iyayin ‘yammatancinsu duk babu
shi yanzu, walwala kanta ta kaura a gidan
Mama da ‘ya’yanta. In ka dauke Hatoon
babu wani mai walwala a cikinsu. To kafin ma Zayyan ya saka ranar
zuwa Lagos gun aminin mahaifinsa Baba
Murtala shi ya zo da kansa har Zaria ya
same shi tareda Lauyan Baba Barr. Abba
Gana Shattima. Sun tattauna extensively, an
kuma tattaro dukiyoyin Baba na gida dana
banki da wadanda ke hannun Baba Murtala
wadanda Zayyan kansa bai san dasu ba,
don haka ya sha mamakin jin abinda Baba
ya bari ya kuma jinjina amana irinta Baba
Murtala don shi ko sau daya Baba Bello bai
taba gaya masa yanada dukiya mai yawa
cikin dukiyar Murtala ba.
Ya kara jin gudun duniya ya shigeshi,
da tsoron tara dukiya.
Mutuwa mai tonon asiri! Ashe har
Estates Baba Zayyan ya gina ga gwamnatin
tarayyah da ba’a kai ga biyanshi kudin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kwangilarsa ba, sai yanzu da ya rasu, Baba
Murtala ya tsaya tsayin daka yayi fafutuka
aka biya magadansa.
Baba baya tattauna harkokin business
dinsa da shi dan sa Zayyan saida Baba
Murtala kadai, ko mai yasa? Ko don ya san
baya ra’ayin business din? Zayyan a lokacin
bai takura kansa da dogon nazari akan
dalilin da yasa Baba Bello baya gaya masa
samunsa ba, a take ya baiwa kansa amsa
don ya dade da sanin doctrines din Baba
Bello fiye da kowa;
Shi ya san ba don komai Baba yayi
hakan ba sai don yafi so ya koyi dogaro da
kansa, ta hanyar amfani da ilminsa bada
dukiyar da waninsa ya tara ba.
Kuma alhamdulillah Baba yayi nasarar
tsayar dashi akan kafufunsa, ta hanyar
bashi ilmin addini dana zamani, don tuni ya
tashi daga Asst. lecturer zuwa cikakken
lecturer a ABU yanzu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Aka tattara dukiyar baba Bello waje
daya da taimakon mai shari’a da lauyansa
aka rabawa iyalinsa gadonsu bisa tsarin
addinin musulunci.
Inda kamar yadda addini ya tsara shi
ya tashi da kason da ya rubanya na ‘yan
uwansa mata. Mama kuma ta karbi
tumunin takabarta.
To bayan gama rabon gadon ne Mama
ta tara yaranta mata duka suka yi (closed
door meeting), suka amince da shawarar da
Mama ta kawo musu.
Mama ta kira Zayyan a washegarin
ranar data zauna da yaranta mata, suka
zauna daga ita sai shi, bayan sun gaisa yaci
abincin data aje masa ta tabbatar ya samu
nutsuwa, sai tace masa. “Baffana, nida ‘yan uwanka Zubaida,
Zubaina, Zaitoon, Zahra da Hatton, mun
yanke shawarar damka maka ragamar
komai namu a hannunka, wato mun maido
kason kowaccenmu hannunka, a sake cure

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

dukiyar nan waje daya in yaso ka cigaba da
juyata kamar yadda Babanku ke yi a
harkar Real Estate.
Da sauri ya dago ya dubi Mama a
rikice, ta bude ido sosai tace “Eh, haka nake
nufi ka bar aikin gwamnati, muna son a
matsayin ka na Da namiji kai kadai a
cikinmu ka dora mana daga inda Babanku
ya bari”. Ta soma matsar kwalla da gefen
hijabinta.
Tana cewa “ni ban ga me kake samu a
koyarwar nan ba, ni ban saba da wahala ba
haka ‘ya’yana, dole ka taimaka mana kada
rashin Babanku yasa mu ragaita, kaga dai
dukiya in ba juyata ake ba bata da albarka,
nan da nan za’a nemeta a rasa. Ni dai ka
ajiye aikin gwamnati, kazo ka zame min
Bello Rafindadi tunda dai ga jari ya bar
mana”.
Zayyan a wannnan lokacin sai ya
karaya, har fiyeda kima, irin abunda yake
gudu kenan tun rasuwar Baba. Ya san duk

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

nauyin gidansu kansa zai dawo. Mama ta
manta kama da wane bata wane.
Dama har lokacin cikin dimuwar
yawan dukiyar da Baban ya bari yake. Yana
ganin bazai iya da wannan nauyin da Mama
da ‘yan uwanshi ke son dora mishi ba.
Arch. Bello Rafindadi, bayan
kasancewarsa tsohon dan boko tofa
rikakken dan gwagwarmayar kasuwancin
gine-gine ne. Baya taba tsugunnawa a waje
daya, duk inda ya samu kwangilar zane ko
gini zai je yayi a cikin Nigeria. Shikuwa ya riga ya san kansa cewa shi
malamin makaranta ne, wanda samunsa
duka ya ta’allaqa ne ga albashinsa na wata.
Bai taba mafarkin zama irin Babansa a
harkarsu ta kasuwanci ba, ko zama dan
gwagwarmayar neman kudi kamar Baba
Bello, wanda ba abu ne mai sauki da zai iya
ba a halin yanzu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Da karyayyar zuciya da kuma sanyin
murya Zayyan yace da Mama cikin
bijirewa.
“Mama naji bukatarki data ‘yan
uwana mata, amma ina baku hakuri,
wannan wani nauyi ne mai girma kuke son
dora min da bazan iya dauka a halin yanzu
dana samu Rauni a zuciyata ba, tunda
nauyi ne na dukiyar marayu kin ga, ina
tsoron wani abu ya samu dukiyar ‘yan
uwana a hannuna saboda tsautsayi ko
sakaci na, tunda kinga ba wai na iya harkar
bane, ban kuma taba gwadawa ba.
Ni a ra’ayina da dai kin bar kowaccen
su ta juya dukiyarta da kanta, tayi sana’ar
da take so da kasonta, nikuma zan taimaka
musu da shawarwari da goyon baya duk
sanda suka bukata”. Amma Mama tace “a’ah, sam ban
yarda ba, ni da kai kanka da su ‘yan uwan
ka mata duka abu guda ne, ba kuma ‘yan
Uba kuke ba balle kace min zasu zargeka,
hadin kanku nake so a duniya tunda baku

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

da wanda yafi muku junanku, shiyasa nace
a hade komai wuri daya a damka maka.
Da a samu riba, da ayi asara duk daya
ne a wajenmu, indai dukiyar nan a
hannunka take Baffana bamu da haufi
kaji?!”.
Zayyan ya buga ya raya akan bazai iya
ba, Mama Fatu ma ta kafe akan bakanta.
Tace “zamusa kafar wando guda nida kai in
ka ki jin maganata”.
Don haka da damuwar wannan
maganar da sukayi da Mama ya juyo Zaria
a ranar. Har yace sai ya kai kararta gun
Baba Murtala.
***** ***** ****
Kwana biyu kullum Safiyyah cikin
damuwar nan da kuma tunanin nan take
ganinsa ciki, tun dawowarsa daga Katsina,
ta kuma fahimci (family issue) dinsu ne,
shiyasa bata tsananta masa da tambayar
abinda ke damunsa ba, kuma bata saka

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

baki ba, tunda shima bai sakata a cikin
sha’anin ba.
Ko a daren ranar ma tana ji yana waya
da Yaya Zubaina akan wata bukata da
Mama ta saka shi da bazai iya ba, taji
Zubaina tana kara tabbatar masa sun riga
sun gama shawara shi zai ja ragamar
dukiyar Baba, bata son wata magana daga
gareshi bayan wannan, kada ya zama raggo
mana?
Zubaina ta kare da cewa “Ita ba haka
tasan Zayyan dinta ba, rashin Baba duk ya
salube jarumtakarsa”.
To sati biyu bayan nan, da ya dan samu
nutsuwa don Mama da ‘ya’yanta duka sun
dage akan bakansu, ya gayawa Safiyyah zai
je Lagos gun aminin Baba, kuma zai kwana
uku don bazai yiwu ya dawo a washegarin
ranar ba tafiyar motar haya ce. Tunaninsa a lokacin shine yaje wurin
Babansu Alh. Murtala, ya kai karar Mama
dasu Zubaidah, kan suna son dora masa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

nauyin da bai shirya dauka ba, ya kuma
nemi shawararsa kan batun.
Kasancewar ya san Baba Murtala a
matsayin mutum mai amana da rikonta,
mai son cigaban Baba Bello da zuriyarsa da
zuciya daya ko ba’a fada ba, duk shawarar
daya bashi zata zama mai amfani ce a gare
shi fiye da tasu Zubaina. Safiyyah ta kwana yi masa shirin tafiya
Lagos, a washegari sukayi sallama ya tafi
kamar bazasu rabu ba, soyayyar Safiyyah
da Zayyan kullum kamar a ranar suka fara
ta, basa taba gundura da juna da nuna ma
juna so da kulawa, sai ka zauna kusa dasu
zaka gane tamkar ‘tube’ da ‘tyre’ suke
rayuwa.
Koda Zayyan ya isa Lagos cikin motar
haya ta luxurious, unguwar Ikoyi ya nufa
wato inda gidan Baba Murtala Masari yake,
kyakkyawar tarba Baba Murtala yasa aka
shirya masa da masaukin da zai sauka tun
kafin isowarsa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Sauka irin ta Dan da ka haifa a
cikinka, ka kuma dade baka ganshi ba, ita
Baba Murtala ya shirya masa.
Aka kaishi dakin baki ya ci abinci ya
kintsa, tare da Baban suka yi sallahr
maghriba da isha’i a jam’I, sannan suka
zauna a falon Baba Murtala don
tattaunawa, ya fara gaya masa abinda ke
tafe dashi, wato rigimar Mama data ‘yan
uwanshi, na sai ya kwafe musu Baba, ya
koma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login