Showing 30001 words to 33000 words out of 46889 words

Chapter 11 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

gujewa tsoron
nata, don duk halin da zai shiga baya wuce
limit din da ya san Sophie bazata iya dauka
a lokacin ba, wannan shi yafi komai samo
masa kanta nan da nan, ta yarda dashi akan
hakuri da hadiye sha’awa dari bisa dari,
zata iya bugun kirji tace shi daban yake,
wato ya bambanta da sauran mazan da
Aunty Dije ke bada misalin rashin
hakurinsu akan matansu a cikin gida bayan
aure. Zayyan ya kasance namiji mai
tsananin wayau da hikimar iya sace zuciyar
matarsa....
A hankali yasan yadda yayi yasa
tsoron nasa ya fara barinta, har ta zama

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

addicted da yawan sumbar da yake mata, da
nau’ikan romancing dinsa kala-kala da
yake yawan aika mata a ko’ina suke cikin
gidansu, har a kitchen bai barinta, bai raba
ta da jikinsa, ta zama addicted to his
touches, koyaushe har jirace take daya
sumbacetan, ko ya rabi jikinta ko yaya ne.
Da haka soyayyar su ta aure ta
bunkasa, ta soma zama flamboyant.
Hatta wanke wanke Safiyyah nayi
Zayyan na dauraya, yana aika mata kiss a
kasan wuyanta yana zuba mata hira,
wannan ba damuwarsa bace wai don ya
tayata aikin kitchen (as long as) Safiyyah
zata daina tsoronsa da aka saka mata. Da kyar yake iya fita yanzu, ko ya fita
cikin makaranta baya jimawa. Sallah ma
shi yake musu jam'inta, sai yace wai tafi
lada. Duk don kada ya fita yayi nisa da
Safiyyahrsa. Hutun sati uku office suka bashi na
aure. Gashi ba wuya a wurin Allah har ya

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

lamushe su, cikin kulawa da tattalin
Safiyyah da inganta rayuwar aurensu da
soyayyah mai wuyar samu.
Ranar da Sophie tayi kwana ashirin
da daya da tarewa ne wato ranar da
hutunsa ya kare yace ta shirya ya kaita
Katsina ta gaida Baba Bello da Mama Fatu.
**** **** ****
Hausawa suka ce wai komai nisan jifa
kasa zai fado. Kuma sannu sannu bata hana
zuwa saidai a dade ba’a je ba. Sannan suka
ce wai komai wayon amarya….. watarana
irin wannan……na zuwa!!! Ranar mai dimbin tarihi a garesu ta
kama Asabar ce, kuma ta karshen wata.
Don haka ana sanitation a gari, wanda yasa
basu fita kofar gida da wuri ba, sai wajen
karfe goma na safe. Safiyyah ta shirya tsaf cikin wata
makubar Egyptian Jilbaab dinta. Ta kawo
bungles ta zubawa hannun hagunta ta fito

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

tsaf da ita, kamar baqar balarabiyar
Saudiyyah.
Tun jiya yayi musu shatar Taxi da
zata kaisu har Katsina, mai taxi ya iso kofar
gidan ya kirashi yace ya iso yana waje.
A daren ranar Safiyyah tayi wa
Mama dambun nama mai dan yawa da cake
da (milk doughnut), tun Asubah ta tashi
tana karasa aikinsu, ko Zayyan bai san
aikin me take tayi a kitchen tun duku-duku
ba. Da suka yi sallah barcinsa ya koma.
Saida gari yayi haske ya tashi yayi wanka a
gurguje, ya dauki wata dakakkkiyar
shaddarsa fara sol, getzner. Ya fesa turaren
sa dayake amfani dashi tun na lokacin wato
UltraViolet (Men) samfurin Paco Rabanne.
Har sun fito zasu shiga mota bayan
Zayyan ya saka kwanukan data shirya
abubuwan da zata kaiwa Mama a ciki a
bayan motar. Sai Safiyyah ta tuna tayi
mantuwa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Ba wani abu ta manta ba cajar
wayarta ce da kayan kwalliya data sayawa
autar Mama (Hatoon), tayi excusing dinsa
ta koma cikin gida, tana komawa daki ta
sunkuya a kasan kujera tana neman
charger dinta. Da Safiyyah ta juya baya tana tafiya
kamar wanda akayi wa wahayi a wannan
lokacin sai kawai ya ya samu kansa da
dagowa a slow ya kalli bayanta… tana
takawa bayanta yana kadawa dari da sittin,
dari da saba’in, duk da cikin jilbab take,
kirjinnan ya ciko kamar zai fashe, don har
wata ‘yar kyakkyawar kiba Sophie ta kara
a gidansa cikin sati uku, saboda samun
kyakkyawar kulawarsa da soyayyar mijin
da bai son ta wahala, duk wani aikin energy
zai karba yayi mata, tafiya take cikin
wannan takun nata mai kamar na mage mai
yanga (cat-walk). Zayyan ya hadiyi wani
whalallen miyau, ji kake, muqut, cikin
tasowar sha’awar da bai taba ji ba a
rayuwarsa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Amma a haka ya basar ya maida kai
ga wayar hannunsa yace a ransa “yarinyar
nan kin dade kina cin lokacin ki a kaina. Ko
maza nawa ne irina masu sadaukar da farin
ciki da jin dadinsu, ga samun kwanciyar
hankalin matansu? Sai kuma wani irin bakon tunani ya
zo masa, na idan suka mutu a hanya fa shi
ko Safiyyah, ba tareda ya taba tabbatar da
sunnar Manzo data rataya a wuyansu ba shi
da ita, kawai sabida gudun zuciyar matar
tasa? Wannan fa ya tashi daga neman hadin
kanta da kwanciyar hankalinta, ya koma
kamar shakkarta yake yi??
Shin Safiyyah zata rabu dashi ne idan
ya dabbaqa sunnar aurensu? Ko sakinsa
zata yi? A gidansa fa take. Iyakaci tayi fushi
dashi duk ranar da hakan ta faru. Sai wata
sabuwar sha’awa da fitina mai tsanani da
bai taba ji ba akan Safiyyah suka zo suka
rinjayi duk wani tunani da ‘self-control’ da
ya mallaka a lokacin.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Yayi kokarin ya shanye komai har
suje Katsina su dawo, amma ina! Al’amarin
nema yake ya zama out of his control a cikin
taxi. Ya kasa sukuni sam a zaunen da yake,
sai muskutawa yake yana sake muskutawa.
Da yaga haza, wato zaayi abin kunya in
Safiyyah ta fito sai kawai ya fito daga motar,
ya fidda kayansu daga bayan motar ya
sallami Mai taxi da kudi masu kauri, yace
yayi hakuri sun fasa tafiyar sai wani satin
ya dawo suje.
Ya dauko kayan girkin nata ya mayar
matasu kitchen daya bayan daya.
Sophie na dagowa daga leka kasan
kujera tana neman charger taga Zayyan
tsaye a bayanta kamar sojan badaqqare,
har sai da jikinsu ya gogu da na juna garin
dagowarta. Ganinsa a bayanta unexpectedly yasa
Safiyyah ta dan tsorata, musamman ganin
yanayinsa na lokacin, saida gabanta ya fadi,
mummunar faduwa domin ta dauka wani

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

abun ne ya faru a irin kallon da yake mata,
ta soma kokarin magana cikin in’inarta….
“Ah! Zay...,yan.. Habi-by…. Lafiya
dai ko? Ai da ka jirani yanzun….zan..
Yanzu zan fitoooo... ".
Sauran maganar makalewa tayi a
makoshin Safiyyah, sakamakon irin
rungumar da Zayyan ya kai mata intensely,
ba shiri ta hadiye sauran abarta, domin
idanun Zay--yyan dinda ta kasa karasa
ambatar cikakken sunansa yau saboda
firgita, sun tashi daga na normal Habiby
dinta data sani mai lallabata, ya fito mata a
namijin zakinsa sak! Yanayinsa ya nuna
muraran cikin yanayi na matsananciyar
bukatuwa yake da ita, yanayine da ita dai ta
kasa fassarawa, don bata taba ganinsa cikin
kwatankwacinsa ba. Wani yanayi ne da ko
me zata ce, kuma ko zata yi yau don son ya
daga mata kafa… zuwa wani lokaci, hakika
ba zaiyi wani tasiri ba.
A lokacin nan Zayyan ya hautsine
mata ya koma mata a namijin Kure,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

wadanda basa ji basa gani a lokaci irin
wannan.
Ko daga yanayin hot kisses dinsa na
yau, wanda ya sha bambam dana kullum
wajen daukar zafi, Sophie ta san yau dai ta
kare mata, karyarta ta kare a hannun dan
mutanen Rafindadi, shima tasa ta kare,
wanda hakan yasa ta tausayawa kanta da
kanta tun kafi mai afkuwa ta afku...
At the same time, Zayyan yayi
kokarin dan hadawa da lallashinta, yana
kuma bata baki da tausasan lafuzza na cewa
hakan bazai cutar da ita da komai ba, duk
cikin son da ya samu kansa da yi mata ne,
yana kokarin cimma burin gangar jikinsu.
Amma shima zufa yake. Shi kansa baya
cikin hayyacinsa, kamar wani wanda aka
yiwa wahayin lallai-lallai ya amshi
sadaqinsa a yau, kuma a yanzu, da farar
Safiya, in ba haka ba zai iya rasa ransa.
A cikin kalamanshi na ranar da
Safiyyah zata iya tunawa har cewa yayi ta yi
masa alfarma, ta bashi dama (koda ta iya

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

yau ce kadai) domin ya gwada mata girman
son da yake mata a aikace.
Manyan idanunsa da suka canza launi
suka kuma kankance sun gama gaya mata
manufarsa ta yau mai kankat ce, ba sauran
ragayya a tsakaninsu.
Koda bai fayyace da fatar bakinsa ba,
emotions dinsa sun gama nunawa.
Jin saukar dumin hawayenta kan
kafadunsa, gabadaya sai ya shiga damuwa,
da kyar ya iya cewa “Sophie, kiyi hakuri
kinji, kiyi min alfarmar yau kadai, haka
rayuwar kowacce mace ta gada ba rashin so
bane, ba rashin tausayi bane, shine cikar
manufar hakikanin son da nake miki.
Shine kuma hanyar da zata bamu
zurri’a tsarkakakka mai albarka nida ke.
Ji nake yau in ban sameki ba mutuwa
zanyi Nana Safiyyah!”
Shima sai nasa hawayen suka digo a
gadon bayanta.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Kalamanshi sun bata tsoro. Kuma
koda ace Zayyan bai furta hakan da
bakinsa gareta ba, idanunsa da rawar da
jikinsa keyi wajen shige mata, sun gaya
mata yau mai rabata da Habiby sai Allah
kadai, wanda ya kulla wannan zazzafar
soyayyar tasu.
Duk wata sha’awa da ya tara ta wata
da watanni, duk wani feeling daya dade da
zama tamkar gyambo ko tsatsa a gangar
jikinsa da zuciyarsa, sai yau ya samu suke
‘healing’ daya samu Safiyyah yadda yake so
a kan gadon aurensu. Maganganunsa na
karshe kafin ya maidata cikakkiyar matarsa
da zata iya tunawa shine da yace “tayi
hakuri” and he mean it. Ba abinda zai iya
mata a lokacin bayan ban hakurin.
Zayyan yace tayi hakurinnan sau ba
adadi yafi cikin carbi, tun tana kirga adadin
ban hakurin har ta daina, because he
cannot speak any fluent language today, sai
baragada, irin wannan;

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

“I neeed yhuhh badly today…I am so
so - sorry Sophieeeeeee”.
Gabadaya yau Habiby umarnin
jikinsa da zuciyarsa kawai yake bi, ba
abinda take so yayi ko ya bari ba….
Duk wani uzuri da kauda kai da
kawaici ya gama yi mata su a can baya.
Yayi mata bajinta da sadaukarwar da
maza matasa kamarsa da yawa bazasu yiwa
amarensu ba, musamman wadanda suka
aura da gumin soyayya.
Dole kanwar naki, Safiyyah yau tayi
saranda! Ba dogon musu ta mika wuya ga
bautar aure bautar Ubangiji.
Zayyan ya zama mijinta na hakika
yau, kamar yadda ya taba ce mata a soron
gidansu watarana zai zama .... In bata
manta ba ai dama ya taba ce mata bazasu
dawwama a haka ba tunda ba auren Yaya
da kanwa suka yi ba!

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Ya kuma taba cewa “akwai ranar da
bazai saurareta ba, kansa kawai zai
taimaka, kansa kadai zai tallafawa a
ranar”. To kenan ga ranar tazo.
Ya zamanto cewa rokonta da
magiyarta na ya tausaya mata, ya biyar da
ita a sannu ma ba ya bari zuwa wani lokaci
ba basu yi tasiri ba sam a tare da Habiby,
daga yadda gangar jikinsa yaso tafiyar da
ita, domin basu taimaka ba ko kankani
wajen samar mata rangwame ko yaya yake
daga Habibin nata.
And that was how their first night
happened, a very passionate night, they had
a wonderful love making, ever! Wanda daga
ranar yayi binding dinsu together suka zama
cikakkun Zayyan da Safiyyah da a yau yake
bada labari. Tarihin aurensu ya fara ne daga
wannan muhimmiyar ranar da ya karbi
budurcinta cikin girma da daraja.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Domin a ranar ne ya goge duk wanan
‘fear’ dinta akan aure, ya cire hijabin nan
na kunyar Safiyyah da take sawa tana
lullube tsakaninsu.
Safiyyah sai taga komai ba’a yadda
take zato da hasashe ba. Kuma ba’a yadda
Aunty Dije ta suffantashi gwanin ban tsoro
da saka fargaba a zuciyar amarya ba.
Bata sani ba Zayyan ya biyar da itane
(in a very gentle manner) har ya samu ya
gamsar da kansa, duk da irin kidimewa da
rikicewar da ya samu kansa a lokacin na
kasancewarsa virgin shima. Yet yana gayawa
kansa yabi a sannu (no matter how) ta
wahalar dashi, kada yayi hurting dinta is
her first night. He wouldn’t take it as a
revenge! A haka har ya samu ya karbi
abinda yake kulafucin karba, wanda duk
wani mijin kwarai ke burin karba daga
matar kwarai irin Safiyyarsa....
Macen kwarai data kai mutuncinta
gidan miji kadai zata gane irin yanayin da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

suka kasance ciki a wannan muhimmiyar
ranar shida Safiyyah.
Don haka tafiya Rafindadin da ba’ayi
kenan a ranar ba, a gidansu suka shiga
Rafindadinsu, sai a sati na gaba. In fact,
hakan ya janyo saida ya kara sati daya akan
hutunsa, domin satin sai ya koma na jinyar
amarya Safiyyah da cigaba da more romon
soyayyah tsagwaronta, amarci yake diba
son ransa, saida ya fanshe duka hakurinsa,
koko muce satin ya zamar masa satin
“Shahr Al-asal” (honeymoon) a larabce da
kuma turance.
A cikin kwana bakwannan gradually
dai Zayyan ya maida Safiyyah cikakkiyar
matarsa ta sunnah, wadda duk sanda ya zo
da bukatarsa da safe ne koda dare koda
yammaci, zai samu abinda yake so har da
kari, ayi masa welcome wholeheartedly babu
kailula.
Matsalarsa daya da Safiyyah taki
karbar irin sutturar da yake sha’awar
ganinta a ciki kullum, kuma bata masa irin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kwalliyar daren nan ko irin (dressing) din
da yake son gani a jikinta sabida kunyarta
da gidadancinta, ko muce saboda irin
‘orientation’ dinta da ‘background’ dinta
wato hakan ya samo asali ne da irin ‘decent
upbringing’ dinda ta samu. Zai wuni yana jinyar Sophie da
tarairayarta, in dare yayi kuma ya karbe
ladan jinyarsa in a loving and romantic
manner.
Zuwa lokacin Safiyyah ta ware, ta
karbi rayuwar aure ta reality. Ta daina
tsoron shi, tana cooperating dashi dari bisa
dari, tana kuma enjoying soyayyar kamar
kowacce mace, ta rungumi rayuwar auren
yadda ya kamata duk wata macen kwarai ta
yi, a shekarun girman diya mace.
Burinta kullum kasancewa tareda
Habiby da farantawa Habiby rai, fatanta na
yanzu shine samun ‘ya’ya masu irin
halayensa da kamanninsa daga gareshi.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

A duk sanda ya bukaceta yanzu a take
amsar gayyatarsa. Don ta gane wuyar
sha’anin ashe-ashe bata kisa, shu’umancin
Aunty Dije ne.
Tafiyarsu zuwa Katsina sai a sati na
gaba ta yiwu, ya zamanto cewa sati hudu cif
kenan rabon Zayyan da gidansu, wato tun
bayan tarewar Safiyyah. Saidai koyaushe
basa rabo da waya shi da Baba da Mama da
‘yan uwansa mata. Abinda bai sani ba ashe hakan da
yayi wato kwashe sati hudu cur bai zo gida
ba yayima Mama Fatu ciwo sosai, ya kuma
fusatata, don sanin kowa ne Mama ta
kallafa rai akan Zayyan, bata maraba da
duk abinda zai canza mata shi ko ya canza
tsarin rayuwarshi ta baya wajen kulawa
dasu, kasancewarsa da namiji kwal data ke
so fiyeda sauran yaranta, ta dai tsaya taga
iya gudun ruwansu shi da matar tasa, na sai
yaushe zai zo inda take saboda yayi aure.
Mama ta kasa yin uzuri akan hakan. Har
rannan take cema Yaya Zubaidah cikin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

damuwa, ranar Zubaidah tazo mata yini
kamar yadda ta saba zuwa gida ta wuni duk
sati.
“Zubaidah ko kin fahimci Baffana
mace ta janye min shi tun ba’a je ko’ina
ba?”.
Zubaidah tayi dariya kadan, tace “kai
habawa Mama! Har yaushe aka yi daren da
garin zai waye?
Ki barshi na dan lokaci ne, giyar
amarci ke kwasarshi in kwannafi ya kwanta
kanwa ta kar tsami zaki ganshi ne da
kafafunsa.
Amarya kota buzuzu ce sai an yi
dokinta Mama”.
Mama ta ce “umh” kawai.
Don bata so zancen yayi nisa ya kara
janyo mata bacin zuciya.
Wannan itace haduwar farko
tsakanin Sophie da surukuwarta Mama
Fatu, haduwa ta zahiri. Saboda a hoto

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kawai Mama ta taba ganin Safiyyah sai ko
yau data ganta a gabanta kuma a dakinta.
Nan Safiyyah taga inda Zayyan ya
debo ruwan kyawunsa na Rumawa. Bai
baro Mama a komai ba. Hatoon na
makarantar kwana haka su Zahra suna
jami'a. Cikin sa’a daga Mama har Baba suka
samu a gidan, dattijan suna shan hutun
karshen mako yadda suka saba. Baba Bello
da ‘yar lelensa Hajiya Fatimah (Mama
shalelen Baba) inji ‘ya’yanta. Kasancewar Asabar ce Baba yana
gida bai fita ba. Zayyan ne a gaba, Safiyyah
na biye dashi a baya, yayi sallama suka
shiga kasaitaccen falon Mama.
Mama dake hakimce cikin kujerar
falonta ta sha ado da (swiss lace) dan gaske,
ruwan zuma, kwalliyar ta musamman ce
yau ta karshen mako kasancewar Baba na
gida yau yace ba inda zashi, kai in ka ganta
a lokacin tamkar Hakimar Rafindadi, tana

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

jiran Baba ya gama wayar da yake yi tayi
masa korafin Zayyan, har yau bai zo ba tun
tarewar amaryarsa.
Yanzu ita dashi sai dai waya, yana
faman bata uzuri na zai zo, zai zo, sai kuma
katsahan taji sallamarsa.
Mama ta amsa sallamarsa ciki-ciki
don ta dau muryarsa tun daga waje, yana
shigowa tace cikin nuna mamaki.
“Muryar wa nake ji mai kama data
Baffana? Halan ka yi batan kai ne yau
Baffa?"
Watakila saboda haushin Zayyan yayi
sati hudu bai zo ba shiyasa Mama ta kasa
yiwa Safiyyah kallon kirki. Duk wani dan
canji yanzu ta cewa kanta sai tana kula, don
kada diyar Alaramma ta janye mata shi da
laqaninsu da tofinsu na ‘ya’yan
Alarammomi. Shi daya jal din da Allah ya
bata a matsayin namiji cikin ‘ya’yanta mata
kenan bata wasa da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login