Showing 36001 words to 39000 words out of 46889 words
Chapter 13 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf
dauka.
Library kuma bata fasa zuwa ba, ta
wuni tana karatu acan da ‘Pink Travel
Mug’ dinta na shan ‘hot coffee’. Allah ya
sani she is addicted ga shan coffee, yana
bude mata kwanya sosai. Musamman a
lokacin da jarrabawa ta kusanto, ko in zata
yi assignment, tana can library da pink
travel mug dinta mai cike da hot coffee, to
acan Zayyan yake samunta ya dauketa su
wuce gida.
Har Kano Zayyan ya kaita sada
zumunci wajen Yayarsa Zubaina, amma
basu kwana ba, sun yi zumunci da ita da
iyalanta suka dawo Zaria a ranar.
Sosai Safiyyah ta kwantawa Yaya
Zubaina a rai, ta yaba da hankalinta da
kamalarta, Zubaina ta kasa shiru har sanda
zasu tafi ta kira Zayyan zaure kafin su
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
wuce, ya dawo shikadai, sai ta rike
hannunsa tana murmushi tace.
“Gaskiya Baffan Mama, ka gama yin
dacen mata, ga kyau ga nutsuwa ga cikar
addini, ka riketa da kyau, kaji Baffa?
Domin na hango maka mace tagari
anan, wadda dukkan alamu sun gama nuna
ta fito daga babban gida na tarbiyyah da
addini, wadda zata baiwa ‘ya’yanka irin
tarbiyyar da akeson ‘ya’yan musulmi su
samu, a tareda Safiyyah”. Zayyan ya gyada kai yana murmushi,
ya kara jin son Yayarsa Zubaina, ita kadai
ce ta yabi Safiyyah a danginsa, su sai dai
suyi mockering dinta da diyar Alaramma
ko ‘stammerer’. Sai kace fitowa daga
tsatson Alaramman ba abun alfahari bane
ko in-inar ita ta baiwa kanta. Yace.
“Nagode Yaya Zubaina. Na san you
will always stand with me, akan duk abinda
na kawo nace inaso.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ko da kuwa ke abun bai yi miki ba
zaki tayani son shi, da kula dashi. Ke kadai
ce kika yaba da Safiyyah a cikinku. And I
truly appreciate.
In sha Allah zanyi duk yadda kika ce
akan Sophie, zan riketa amana, zamu
rufawa juna asiri mu zauna lafiya”.
Da aka kwana biyu kuma ya kaita
gidan Yaya Zubaidah a Batsari.
Tarbar ta sha banban tsakanin ta
gidan Zubaina data ta gidan Zubaida, ko
daga ruwan pure water biyu da aka ajiye
mata akan plate aka shanyata a falo aka ce
za’ayi magana da Baffa cikin daki, bayan
daga nesa suka zo ko abinci bata basu ba,
sai Baffa data janye uwardakinta tana masa
korafin Baban su Amal ya hanata aikin da
takeyi. Sabida yadda Mama ke yawan kiran
Safiyyah diyar Alaramma yasa itama Yaya
Zubaidah tuni tabi ta raina ajin Safiyyah
tun kafin ta ganta.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Nan Safiyah ta gama gane ‘clear
difference’ na halayen ‘ya’yan Mama, biyu
sun biyo Baba Bello sak a komai (Zayyan da
Zubaina), hudu sun kwashe Mama Fatu tsaf
(Zubaidah, Zahra, Zaytoon da Hatoon). Safiyyah a wannan dan tsakanin da
take karatun digirinta na farko a Zaria,
Zayyan na aikinsa na Lecturing, suna
yawan zuwa Katsina gaida iyayensu, duk
kuma sanda suka je Katsina sai sun shiga
Dandume, sun shiga shekara ta biyu da aure
yanzu, ta gama fahimtar halin dangin
mijinta tsaf, don basa wata daya Zayyan bai
kaita cikinsu ba. Musamman lokacin da
Baba Bello ya kwanta wata ‘yar jinya.
Baba ya jima yana fama da larurar
suga da hawan jini, amma basu taba
kwantar da shi ba sai a wannan lokacin,
kuma Zayyan ke kula da zarya da shi a
asibiti, kullum yana hanyar asibiti dashi,
don haka da aka baiwa Baba kwanciya don
samun (bed rest) sai yayi tunanin maido
Baba asibitin koyarwa na ABUTH kawai
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
don dai yafi samun damar kula dashi da
kansa, in yana kusa dashi saboda aikinsa, ya
kuma ragewa kansa zirga-zirgar da yakeyi
tsakanin Katsina da Zaria.
Sai hakan yasa takalihun abincin
Baba da ake yi masa na musamman irin na
masu ciwon suga a zaman asibitin ya dawo
wuyan Safiyyah, ita ke kula da yi masa
tsaftataccen abincin da ake masa na
musamman, kullum ita keyi safe, rana da
dare ta kai asibitin da kanta, to anan ne
suka cakude da dangin Zayyan suke wuni
tare har dare, wani lokacin Zahra da
Zaitoon su kan biyota gidanta su kwana, da
safe suyi wanka su koma asibiti tare, don
autar Mama Hatoon na makarantar kwana
har a lokacin.
A dan tsakaninnan kaf! Sophie ta
gama banbance halin yayye da kannen
Zayyan a kanta, dukkansu dinnan ra’ayinsu
ya tafi daya dana mahaifiyarsu Mama Fatu
akan rashin dacewar aurenta da Zayyan. A
wurinsu ita ba tsarar aurensa bace, kamar
wata alfarma aka yi mata da aka aureta, in
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
ka cire mai saukin halin cikinsu Yaya
Zubaina. Babu mai kallon kanta da gashi.
Abin mamaki ko a fuska Zubaina
kadai ke kama da Baba Bello, dukkansu da
kyakkyawa Mama Fatu suke kwasar kama
har Zayyan din, kuma ita kadai take da
halinsa na accommodating kowa ya rabeta,
irrespect of social status. Safiyyah ta fahimci
‘yan uwan Zayyan da mahaifiyarsa sun
raina ajawalinta, suna ganin bata isa ya
aureta ba, kamar ajinta yayi kadan da
auren Zayyan dinsu, matsayinta bai kai da
auren dan uwansu/dan ta ba, balle ta samu
matsayin shigowa cikin su ta hada kafada
dasu a matsayin surukarsu/matarsa. Ta kan
tambayi kanta to ko mai yasa ahalin Mama
suka raina ajawalinta haka? Ita
bawulakantacciya ba? Daga bisani ita da
kanta ta gane sabida ita ba ‘yar masu kudi
bace, kuma ba ‘yar gayu gangariya irinsu
ba, ko daga yanayin sutturarta sun raina
mata, wadda tasha bambam data ‘ya’yan
Mama da abokan huldarsu.
Har ila yau, a wannan zaman ne ta
fahimci tsakanin Zayyan da Zubaina akwai
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
fahimtar juna mai kyau fiyeda tsakaninsa
da babbar Yayarsu Zubaida.
Zubaina kamar ba sakuwarsa ba, tunda
kowa ya san sako da sako ba’a shiri. Amma
su shiri suke kamar aminai. Zubaina ita
Zayyan ke bi a haihuwa, wato ita ta saki
nono ya kama. Ita kadai ke taya shi son Safiyyah
bilhaqqi, take kuma girmama tushenta,
asalinta da nasabarta, saidai kuma ita a
nesa take, ko jinyar Baba da akeyi yanzu
sau daya ta samu Malam Mahi mijinta ya
barta tazo, kuma bata kwana ba a ranar ta
koma.
Zubaina ce kadai bata samu ilmin
zamani mai zurfi a cikinsu ba, kuma bata
aikin gwamnati, don daga sakandire aka yi
mata aure, mijinta kuma baya ra’ayin ta
cigaba, sai ya bata jari take sana’ar poultry,
amma hakika Zubaina tafi Zubaida
kyakkyawar alaqa da kowa.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Zubaida kuwa babbar ma’aikaciyace a
Batsari Local Government. Su kam su
Zubaida, Safiyyah kan fada a ranta, duk an
tsotso hali daga Mama, na raina mutanen
da basu kaisu a status na rayuwa ba, halinta
ba wanda suka bari sai ma wanda suka
dara ta.
Abin nufi, ‘ya’yan Mama kullum suna
kallon kansu da matsayin mahaifinsu da
shaharar sunansu a Katsina, cewa su iyalin
Bello Rafindadi ne, kamar diyan gwamna
haka su Zahra ke jin kansu, in kai ba kowa
bane a Katsina, iyayenka basu yi suna
kamar nasu uban ba, kuma basu taka wani
matsayi a boko ba, to 'ya'yan Mama da ita
kanta basa wata alaqa mai dadi da kai.
Ta gane wannan halinsu ne na cikin
jini, akwai girmama abun duniya da
daukaka sama da asali da nagarta.
Don haka Safiyyah ta zama kamar
wata ‘yar karere a cikinsu, saboda yadda
suke wareta gefe su manta da ita a wurin a
zaman asibitinnan, kamar wata ‘yar aikin
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama haka suka dauketa. Don haka sosai
Safiyyah ta kama kanta daga shiga
sha’aninsu.
Bayan ritayar Baba Bello daga jami’ar
Umaru Musa, kafin ciwon nan ya ci
karfinsa, Arch. Bello ashe ya tara duniya a
boye, domin ya koma ya kutsa sosai cikin
sha’anin (Real Estate Business). Baba Bello ya samu arziki ya kuma
samu budi mai yawa akan harkar zanen
Estate da ginasu da bada hayarsu cikin dan
lokaci, ya samu alkhairi akan real estate
nan da nan, har fiyeda lokacin da yake
shugabantar jami’ar Katsina bakidaya. Wannan budi da Baba ya samu rana
daya sai girman kai da fahari (pride and
arrogance) ya karu ga ‘ya’yansa mata, da
mai dakinsa Haj. Fatu Rafindadi, mulki da
zuba iko a cikin gida ya karu ga matarsa
Mama Fatu, kai kace itace first lady ta
lokacin watau “Turai ’Yar Aduwa”, don a
lokacin nan da yake tunowa in har bai
manta ba, kuma ya tuna daidai, marigayi
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Alhaji Umaru Musa ‘Yar Aduwa ne yake
mulkin kasar Najeriya.
Kodayake Mama ai first lady din ce,
amma ta Baba Bello kadai.
Da wuya tayi laifi a gun Baba, don ko
bata kyautatawa kowa ba, shi ya shaida
tana kyautata masa.
Arzikin da Baba Bello yaketa samu
farat daya akan harkar ‘real estate’ ya sa
competition ya shigo cikin sha’aninsu, ya
samu abokan hamayya na sana’a sosai,
saboda cikin dan lokaci Baba Bello ya
kudance yayi suna a harkar Real Estate, ya
zamana yanzu harkokinsa da zaman sa yafi
yawa a jihar Lagos.
Domin acan ne yafi karbar kwangilar
zanawa da gina Estates har daga
gwamnatin tarayya yana karba, daga baya
daga masu private companies ma irinsu
“Lange and Grant” da “Julius Berger
Nigeria” Baba na samun kwangilar zane da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
gini daga hannunsu da aka gane
shahararsa.
Rayuwa ta wani irin canzawa iyalin
Baba Bello rana daya, fiyeda sanda yake
aikin gwamnati a jami’ar Katsina.
Wani abu da zai burgeka ya kuma baka
mamaki da Zayyan Bello Rafindadi shine,
ko sau daya arzikin mahaifinsa na yanzu
bai taba canza tsarin rayuwarsa daga
wadda yakeyi a baya ba, kamar yadda ta
kannensa mata ta canza. Yana nan a yadda
yake. Zayyan mijin Nana Safiyyah. Don
hatta Zahra da Zaitoon yanzu motar kansu
suke ja mulmulalla, kalar da kowaccensu ta
zaba Baba ya sai mata.
Shi kam har lokacin yana nan a yadda
yake rayuwarsa tun fil azal, irinta malaman
jami’a ba yabo ba kuma fallasa. Karamin
Lecturer ne mai jini a jika da farin jini a
wurin aikinsa, irin malaman jami’ar nan ne
‘yan zamani da suka san ciwon kansu
matuka, suka san muhimmancin ilmi da
amfanin neman na kai. Wadanda basa taba
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
daukar samun wani a matsayin abin
tinkahonsu ko dogaronsu.
Shi bai dauki rayuwar nan ta duniya da
zafi ba, yana rayuwa within his own income,
ya yarda komai na dan adam lokaci yake
dashi, kuma arzikin Baba Bello ba nasa
bane. Gumin Baban ne. Arch. Zayyan Bello Rafindadi kenan.
Wanda kowa ya san shi ya san shi da babur
dinsa LIFAN mai lafiya guda daya da yake
matukar kula dashi, tun wanda Baba ya
bashi as gift din aure yau shekara uku
kenan yana kula da lafiyar abinsa, da
matarsa daya kamar ransa gimbiyar
zuciyar Zayyan “Mrs. Safiyyah Rafindadi.
Ya kan yawan gayawa Safiyyah yadda
yake matukar son ‘Bike’ din nasa da yake
kira ‘Lifany’.
Yace in yana tukashi tana bayansa ta
dafe masa suna tafiya wani irin nishadi yake
tsintar kansa a ciki, wanda yafi gaban
yadda zai iya fasaltashi. He feels himself on
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
top of the world’s greatest happiness and
excitedness. Safiyyah sai tayi ta dariya don
itama tana son ‘Lifany’ din nasa. Tana
wanke masa shi duk sati da kanta a harabar
flat dinsu. Don koda Baba yace zai canza masa da
mota lokacin da Mama tayi korafin an
sayawa su Zaitoon motocin kansu, yara
dasu, an bar Baffanta da fama da tsohon
Babur, shi da yake da nauyin iyali a kansa,
Zayyan ki yayi sam, yace, “Baba kyale Mama kawai ta tsani
Lifany na rasa dalili, ni kuma wannan Lifan
din na riga na saba da ita, ina sonta sosai
fiyeda zatonta, jinta nake kamar jirgin
sama, kuma ta isheni rayuwa a yanzu, ban
san gobe ba. Koda zan sayi mota nafi son ya
zama cewa da gumin aikina na sayeta. Baba
kayimin komai a rayuwa tunda ka bani iyali
to ka gama role dinka as a father, bai zama
dole sai ka saya min mota ba.
Daga gidana zuwa cikin makaranta dai
Allah na tuba babu wani nisa, in mun so ma
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
a kafa muke takawa nida Sophie don motsa
jiki da karin lafiya”.
A kullum Prof. Rafindadi yana
matukar jin alfahari da godewa Allah da ya
bashi Zayyan, Allah bai bashi wadatar
‘ya’ya maza ba sai Zayyan tilo a cikin mata,
ya kuma zama jarumi a cikinsu, daya
tamkar da goma. Halinsa duk na dattako ne da ya
banbanta dana sauran ‘yan uwansa mata,
masu son jin dadi da rayuwar high taste
anyhow, flamboyant life itace rayuwa a gun
‘ya’yan Mama. Mama saida ta san yadda tayi ta
kalallame Baba da lallami ya sayawa Zahra
da Zaitoon motocin da suke hawa yanzu ba
don ran Baba ya so ba, wadanda suke
shekarar karshe a jami’ar Katsina a
lokacin, don dai competition da kawayensu
‘ya’yan masu akwai.
Da wuya kuma Mama tayi umarni
Baba ya tsallake ko baya so. Don yakan ce
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
dasu komai ya samu a rayuwarsa tareda ita
(Mama) suka sameshi. So baya iya yi mata
iyaka da duk abinda ya mallaka.
Baba na matukar jin dadin yanayin
rayuwar Zayyan dinsa, bai dauki rayuwar
‘ya’yan masu kudin Katsina ya dorawa
kansa ba, wai don ganin budin da Babansa
yake samu a yanzu, kamar wanda aka yiwa
wahayin arziki ya sameshi a tsufansa. A kullum Zayyan sakawa yake a ransa
arzikin Baba ba nasa bane, gumin Baba ne,
daya rayu yana fafutukarsa, Allah kuma ya
rubuta bazai samu cin gajiyarsa ba sai a
shekarun tsufansa bayan ritayarsa. Irin manyan kwagilolin zanen Estates
da gine-ginensu da Baba yake samu yanzu a
Lagos, sanda yake aikin gwamnati bai samu
ko kwatan-kwatansu ba, don haka shikam
bashi da wani buri a kan dukiyar Baba, bai
sakawa ransa fahari ko amfani da dukiyar
Babanshi da ba guminshi ba.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Yafi maida hankali ga neman na kansa
ta hanyar murza albarkar bironsa. Kullum
yana gayawa kansa saida Baba ya sha irin
wannan wahalar a kuruciyarsa, sannan ya
samu nasibin da yake samu yanzu a
shekarun girmansa. Baba kuma nada yaqinin cewa,
kyawun turbar rayuwar da Zayyan yake
kai a yau, har da influence na auren macen
kwarai, wadda ke taka rawa sosai wajen
taya shi zama mutum nagari a cikin gida da
waje, wato maidakinsa Safiyyah Usman
Dandume, tana da hannu dumu-dumu
wajen kara dora shi a kan turba sahihiya.
Rana daya ciwon Baba ya rikice, aka
kuma rasa gane kan ciwon, tsakanin sugar
dinsa da hawan jini likitoci sun kasa gane
wanda ya kwantar dashi.
Baba Bello ya sha jinya mai tsayi a
ABUTH. Safiyyah kuma tasha hidima da
dawainiya da girke-girkensa da sauran
hidimarsa a kullum, ta sha albarka kwando
yafi dubu a gun Baba Bello, kullum ta kawo
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
masa abinci tace ya tashi yaci da irin kalar
addu’ar da zai yi mata mostly akan Allah ya
bata ‘ya’ya nagari masu irin halayenta.
Bazai taba manta yadda a jinyar nan
da Baba Bello yayi, kullum suka kebe shi da
Baban a bayan idon Safiyyah, sai ya
jaddada masa bukatarsa ta cewa ya kula da
matarsa Safiyyah. Don Baba shikadai yasan
wacece matarsa Mama Fatu? Macijin sari
ka noke ce, akan duk abinda bata ra’ayi. Ko
kuwa green snake under green grass idan
bata son abu.
Duk da cewa Arch. Bello yafi karfin
gidansa, kuma Mama na jin maganarsa,
amma kowa da halinsa bai isa ya canza
mata hali ba, shikadai yake iya tsawatar
mata in tayi ba daidai ba, ya san wasu
lokutan Mama sai a hankali, musamman in
mutum bai yi mata ba, wato baiyi daidai da
zabinta ba, yana sane da cewa tana ragawa
Safiyyah wani wulakancin sau tari saboda
ganin idonsa, don ta san bazai dauka ba,
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
baya bari tayi mata wani abu da bazata ji
dadi ba in dai yana wuri.
Baba yana iya kokarinsa wajen kulawa
da Mama, wajen yi mata nasiha da karkato
da hankalinta kan rayuwar duniya kalilan
ce, hatta zumuncinta da danginta na Rumah
sai ya tashi tsaye a kai take dan yi. Lokacin da ya fahimci sam bata damu
da alaqa da danginta ba, saboda basu da
shi, sai kwashe-kwashen matan manya
irinta, Baba bai kyale abin haka ba, haka
kawai sai ya shirya kayan abinci ya cika
bayan motarsa yace tazo su tafi Rumah su
gaishesu.
Baba shine kamar uwarta kuma shine
kadai ubanta mai sata a hanya, don
iyayenta sun jima da kwantawa dama.
Baba Bello shikadai yake iya shaping
din Mama Fatu ya tankwarata ta yi abu ko
bata so, ya san halin Mama sarai bataso
kowa ya rabeta sai ‘ya’yanta kawai, koda
kuwa nata danginne, shikadai yake iyawa
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
da halin Mama ya biyar da ita cikin lislama
su zauna lafiya, kuma shikadai ya iya zama
da ita, amma mutane da yawa musamman
danginta na Rumah basa jin dadinta, yafi
kowa sanin halinta ciki da bai dinsa, ya kan
ce. “Fatima zuma ce ga zaqi ga harbi”.
A zaman jinyar nan tasa da yayi a
ABUTH yana ganin yanda Mama da
‘ya’yanta ke ware Safiyyah su mayar da ita
bare a asibitin, sun mayar da ita kamar’yar
aikinsu, saidai ka ganta ita kadai a can
gefensu tana karatu a cikin wayar hannunta
kamar basu san da kasancewarta a wurin
tare dasu ba.
In har ba Zayyan yana nan ba, sai ya
shigo wurin take dan sakewa don shikadai
ke janta da zance, ko sakota cikin hirarsu.
Baba ya san shikadai yake iya yiwa
Mama magana taji, baya taba saka kara
Mama ta tsallake. To bai cika son yana mata
gargadi akan Safiyyah ba, tun bayan wanda
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
yayi mata na ranar haduwarsu ta farko,
don kada ta tsaneta.
Ita Safiyyah din dai