Showing 3001 words to 6000 words out of 46889 words
Chapter 2 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf
**** *****
“THE ARCHITECT”
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
T
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
saye yake jikin ‘railer’ din data kare wata
matattakala daga dan saman tudun katon jan
dutsen cikin ‘park’ din Sunset Estate, dutsen
yana bulbular da ruwa garai-garai
kodayaushe. Ruwan sai kaga yayi tsiriii zuwa
sama, sannan ya gangara ya sauka kasa a
hankali, one of the very fabulous moments
dinsa shine duk yammacin da yake
kasancewa a nan gurin, idan rana ta tafi zata
fadi cikin Estate dinsa.
A daidai wannan lokacin tunanin yadda
sabuwar rayuwarsu zata fara a yau kawai
yake yi, yana kuma kallon kudurar Ubangiji
dake cikin faduwar rana, wanda yayi daidai
da jin faduwar gabansa, in ya tuna me zai je
ya zo masa daren yau. Zuwa yanzu ya tabbata gidansa ya cika
makil, taf da mata, daga bangarori daban
daban.
Kusan zuwa wajennan ya zame masa
dabi’a ko in ce al’ada, tun tarewarsu a cikin
Estate din bayan kammaluwar gininsa da
bikin bude shi. Sau tari, a duk yammaci irin
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
wannan daga misalin karfe biyar na yamma
zuwa shidda da kwata, in dai har yana gari,
kuma baya wani muhimmin aiki a gida, ya
kan zo wannan wajen ne ya tsaya, yayi ta
kallon faduwar rana a cikin Estate dinsa,
yana reflecting rayuwarsa, sannan ya karewa
gidajen da ya zana da kansa kallo na sha’awa
da alfahari da kai, hakan yasa ya zama mai
yawan godiya ga Allah, a bisa baiwar da yayi
masa ta hikima da arzikin da ba kowa yayiwa
ba.
A dai-dai lokacin ya kai duba ga
agogon ‘Cartier’ na bakar fata dake daure a
damtsen hannunsa mai cike da lallausar
gargasa, agogon har dan nitsewa yayi cikin
gargasar data cika farar fatar hannunsa. To
haka yawan gargasar yake a duk ilahirin
jikinsa, shi mutum ne bafillace, mai yawan
sumar jiki, musamman a gashin kansa da
kirjinsa da zaka ga har dan murmurdewa
take yi irin na fulanin asali. Ma’ana dai ya
kasance kyakkyawan mutum mai wadatar
sumar jiki data gashin kai ne.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Kyallin da agogon dake daure a
hannunsa keyi kadai ya isheka kimanta
daraja da kimar agogon hannun nasa,
musamman ga maza irinsa ma’abota masu
amfani da dukiyar da Allah ya basu wajen
kawata kwalliyarsu da tsadaddun agogo a
jikinsu, yanada yawan tsafta da iya sanya
suttura ta kamala, ya iya ado da kwalliya ta
'yan gayun maza, mai burgewa da ban
sha’awa, amma a dressing dinsa da wuya ka
ganshi cikin kananan kaya ko ‘Suit’.
To yau ma sanye yake da wani
rantsatstsen (sky-blue filtex) yadi na
musamman na kasaitattun maza. Yayi
matukar yin kyau a cikinsa, kalar yadin ya
haska shi, ya fiddo kwarjininsa da ilhamarsa,
sai annuri yake fitarwa daga fararen
idanunsa. Tsammani zakayi saurayi ne mai
shekaru 27 ba magidancin da ya doshi
shekaru 40 ba.
Zuwa yanzu ya san gidansa ba masaka
tsinke, don haka ya yanke shawarar barin
Estate din gabadaya.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
A lokacin rana ta gama faduwa, gari ya
fara yin duhu, maghriba ta kawo kai.
Sai ya baro wajen da yake tsaye, a kasa
ya taka zuwa masallaci, da zummar ya samu
jam’in sallar magariba a masallacin Estate
din.
Daga nan zai dauki motarsa da ya baro
a parking lot na masallacin, tun bayan fitowa
sallar la’asar, gara ya wuce gidan Baban
Abdallah, don gujewa taron dandazon mata
da hayaniyar su a cikin gidansa. Bayan an idar da sallah sai ya fito ya
shiga motarsa da ya faka a kofar masallacin.
Ya juya kan sityari a hankali, sannna ya tuka
a tsanake ya hau bisa titi kafin ya saki motar
a guje. Yana tafe akan titin da zai kai shi
unguwar Life-Camp daga Guzape, a hanya
yake ‘making comparisons’ a cikin ransa da
idanunsa da zuciyasa. Wato yanzu da yake
wuce manyan unguwanni daban-daban na
cikin kwaryar Abuja, ya kasa ganin kamar,
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
ko misalin Estate dinsa a komai, balle wanda
ya kama kafarsa, ko ace ya dokeshi a
kyawun tsari da na fasali.
Ko don wannan kadai yana alfahari da
kasancewarsa mamallakin Sunset Estate, mai
ilmin zanen da babu na biyunsa a kwarewa a
Arewa, yana kuma godewa Ubangiji akan
baiwar nan da yayi masa, wadda ba duk
mazan arewa ba, kai ba duk kai ba, ba kuma
kowa ba!!!
**** **** ****
A gidan Habibu yasha zamansa. Suka
sha hirarsu ta tsoffin abokai, duk dai akan
lamarin iyalinsu. Bashi ya baro gidan ba sai
misalin karfe goma sha biyu na dare, ya san
dai zuwa yanzu kowa ya watse, na cikin gidan
kuma duk inda suke sun gaji da jiran
dawowarsa sun dade da kwantawa barci.
Maigadinsa ne ya bude masa kofa, ya shigar
da motar ciki a hankali, sannan ya adanata a
muhallinta na dindindin watau (parking lot
din gidansa).
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ya jima sosai zaune cikin motar, kamar
ba zai fito ba, har sai kayi tsammanin ko
barci ya dauke shi ne, domin tunda ya
kwantar da kansa bisa sityarin motar, bai
kara dagowa ba, saboda gajiya da damuwa
da sukazo lokaci daya suka yi masa rubdugu. Akalla ya dauki tsayin kusan awa daya
da rabi a wannan yanayin, cikin tunani da
damuwa da suka ziyarce shi nan take. Sannan
a hankali ya lumshe dara-daran idanunsa,
wadanda a yanzu gajiya ta canza launinsu
zuwa ‘brownish’ haka, daga farare kal dinsu
da kowa ya sani, kafin daga bisani ya daure
ya kashe injin motar, ya dan jingina bayansa
da kujerar motar kirar bakar Bugatti
(Centodieci).
Ya fito a kasalance, rike da babbar
rigarsa a hannun damansa, an yi mata dinki
da shudin zare mai turuwa na alfarma, a
kansa shudiyar hula ce (Tonak) ta yayin
samari da magidanta, kayan sun matukar
karbarshi, sun fiddo zahirin asalin kalar
kyakkyawar fatarsa, wadda ta kasance
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
wankan tarwada mai haske. Domin baza’a
kirashi fari sol ba.
Idanunsa saye cikin farin gilashi mara
mazagayi (Cassie Rimless) wanda bai boye
damuwar dake cikin idanunsa da suke
lumshewa da budewa da kansu ba, wanda
yanayi ne na halittarsu hakan. A tsanake ya doshi hanyar shiga cikin
gidansa, shiru kake ji kamar babu wani
mahaluki dake raye a cikin tsararren gidan,
mai lamba ta farko a unguwar ‘Sunset
Estate’ watau (No 1. Rafindadi Close). A daidai wannan lokacin baka jin
komai a Estate din sai haushin karnukan gadi
(Security Dogs) dake tashi nesa kadan dasu,
hakan yake kasancewa a Estate din kullum
idan dare ya tsala, karnukan sunta zuba
haushi kenan marar dadin ji, musamman ga
wanda ya debo gajiya da damuwa, yake
bukatar hutun jiki dana zuciya harma dana
kunne kamarsa. Wato yafi son yaji ko’ina
shiru.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
A haka ya cigaba da tafiya a hankali,
bayaso taji dawowarsa, domin ji yayi ya
rasa duk wani karsashi nasa na Da namiji,
tunda ya hango tagar dakinta a bude, duk
da ance faduwar gaba asarar namiji…. Shi
dai yau gabansa faduwa yake, don haka, so
yake ya kebe kansa kawai.
Ya kasance mutum ma’abocin iya
takun tafiya ta nutsuwa da aji na
musamman (classic gait), kasancewar sa
wankan tarwada mai haske yasa fatarsa ta
kasance mai santsi, kamar mai shiga
wankan inji, har wani dan jaja-jaja zaka ga
kalar fatar fuskarsa nayi na hutu zallah.
Abokansa na kuruciya idan yana tafiya
ta gabansu, wani kirari zakaji sun rufeshi
dashi.
“…Takunka dabam ne Baffan
Mamanshi…., Farar aniya da farar zuciya,
sai Baffah ..… Shalelen Mamanshi an buga
an barka Zakin duniya, kanin Zubaina da
Zubaidah, Yayan Zaytoonah da Zahrah, na
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
“Sophie” bada kanka a sare kaje gida kacewa
Mama ya fadi kawai!”.
Domin tun yana makarantar sakandire
Baffa mutum ne shi mai yawan taimako, da
yawan jin kan na kasa dashi, shine suke ce
masa Baffa mai farar aniya da farar zuciya.
Ga dai shi da rashin walwala a fuska, amma
hakan bai hana shi zamowa mutum mai
yawan kyauta da kyautatawa kowa da
nagartattun halayensa ba.
Tun kuma a wancan lokacin kowa ya
san irin yadda Mamansu ke son shi, Mama
bata kara a kan Baffanta, domin ya ci sunan
marigayin Babanta. Sannan shikadai ne
namiji cikin ‘ya’yanta. Arch. Zayyan Bello Rafindadi kenan,
wanda dan asalin jihar Katsina ne.
Kasancewar Zayyan sunan Kakansa na
wajen Uwa yaci, shine Mamansa da kanta
take kiransa “Baffa”. A wannan shekarar
Zayyan ya cika shekaru talatin da bakwai
da haihuwa.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Zayyan rabinsa Ba-rume ne rabi kuma
haihuwar asalin shiyyar Rafindadin birnin
Katsina.
Idan nace “Ba-rume” ina nufin Arch.
Zayyan, ta bangaren mahaifiyarsa Hajiya
Fatima da kowa ke kira (Mama Fatu),
Rumawa ne.
Shiyasa daga kallo na farko zaka ganshi
da zubin kyawunsu da fasalin tsayin mazan
Rumawa, amma Zayyan bashi da tsagin
gefen fuskarsu saboda ta dangin uwa ya
gado su bata uba ba, mutum ne mai cikar
zati da tarin kamalar dake bayyana yawan
sallah da kula da ibada, zaka shaida hakan
daga tabon sujjadah baki turarre dake
saman goshinsa, bazaka ce shi miskili bane,
don rashin walwalarsa ba yana nufin
miskilanci bane. Kawai za’a ce Baffa baida
far’a.
Mutum ne mai iya sarrafa kansa gaban
kowa, sannan mutum ne da ya iya jan zaren
'class' dinsa, watakila wannan shine abinda
ke hana a gane walwalarsa, amma dai Baffa
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
ya kanyi walwalar idan ta kama da ‘yan
uwansa mata, watau dai faram-faram dinsa
yana yinsa ne a inda yaga ya dace yayi
kawai.
Arch. Zayyan, mutum ne mai kiyaye
tsaftar jikinsa, zaka shaida yawan tsaftarsa
ko daga faratansa da kullum suke a gyare
tsaf-tsaf, Zayyan dan gayu ne sosai wanda
ya kware a iya daukar wanka, sannan da
iya karya hula akan goshinsa, kowa ya
shaida kuma mutum ne da ya iya zaben
sutturar data dace dashi a kowanne yanayi.
Kwalliyar da yayi yau kadai, ta gama
fallasa iya dressing dinsa.
A irin tafiyar da Baffa ke yi, sam baya
bari takun shi ya bada sauti, don baya so
Sophie tasan da shigowarsa ko dawowarsa
gidan a wannan lokacin. To balle kuma….
Kai tsaye sassan shi na cikin gidan ya
nufa, maimakon inda ya dace ya nufa a
yanzu, ba tare da ya kalli kowanne sashe na
bangarorin gidansa ba, wanda yake (fully
detached duplex), shi kansa ya san inda ya
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
nufa din, wato side dinsa, ba can ya kamata
ya dosa ba.
Amma Baffa ji yake ba abinda yake da
bukata yau irin kadaicewa, ba don komai
ba sai domin ya samu damar da zaiyi
sahihin tunani akan abinda ya aikatawa
rayuwarsu, a matsayin warwara ga tarin
matsalolinsu. Yana so ya nutsu, sannan ya
tantance, yayi kyakkyawan nazari akan
rayuwarsu shi da Safiyyah.
Babu wani doki ko farin ciki ko far’a a
tare da Baffa, irin na kowanne sabon ango,
wadanda dasu ya kamata ace ya shigo
gidan.
Idan ka lura sosai ma zaka gane
idanun Baffa a rufe suke don tsabar
damuwa, suna kara lumshe kansu da kansu
wanda nature dinshi ne haka.
Yazo zai shige sitting room dinsa kenan
sai yaji tamkar motsin bude tagar Sophie ta
falonta na sama.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Saidai kuma hakan baisa ya juyo ko ya
tsaya ba, saboda baya da kwarin guiwar yin
ko dayansu, wato tsakanin tsayawar ko
juyawar, saima cigaba yayi da tafiya harda
kara sassarfa saboda ya buya daga idanun
iyalin nasa. Yasa mukullin dake hannunsa ya bude
kofar bangarensa ya shige, sannan ne ya
samu ya saki ajiyar zuciya, tareda juyawa
ya kulle kofar shigowa katafaren falonsa
nasa. Baffa bai tsaya a falon ba, kai tsaye
(masterbedroom) dinsa ya wuce, ya fada
kan gadon dakin yayi dai-dai da kafafunsa
akan makeken gadon na alfarma, bayan ya
jefar da babbar rigarsa da jakar ‘laptop’
dinsa da ya riko a gefen gado. Ya juya ya sake gyara kwanciyarsa
sosai, wannan karon rigingine ya koma, ko
takalman kafarsa sau ciki da safar kafarsa
bai iya ya ciresu daga kafafunsa ba, a haka
ya kwanta.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Zuciyarsa cike da taraddadin da ya
ninka na baya, da ya tuna dole dai da safe
zai ga Safiyyah ya fuskanceta, wai meyasa
madadin ‘contentment’ irin na samun cikar
buri daya kamata ya kasance a ciki sai
taraddadi ya maye gurbi? Wadanda ba shi
ya kamata ace ya kasance cikinsa ba yau,
tunda dai gashi at long last, ya samo
maslaha ga matsalarsu shida Safiyyah.
A yau zai iya cewa ya ceci aurensa da
“Safiyyah” daga tangal-tangal din da
yakeyi, da kuma sauran matsalolinsu masu
zaman kansu. At long last, ya ceci aurensu
na tun tali-tali, aure mai tarin albarkar
iyaye irin nashi da Safiyyah. Shi da Safiyyah are more than husband
and wife, they are each others’ ALTER EGO,
sun riga sun yarda sirrin juna ne sannan
barin rayuwar junansu. To mai yasa zai
shiga damuwa kuma akan hukuncinsa?
Hukuncin da bisa yardarta ya aikata shi?
Tunda kuwa ko babu komai, daga yau ya
ceci wannan dadadden auren na tarihi da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
soyayyah daga rugujewa, da kuma duk
wata barazanar dake hanasu kwanciyar
hankali shi da Safiyyah?
Akalla dai zai iya cewa daga yau yayi
maganin duk wannnan bacin ran da
tsangwamar da Safiyyah ke kwankwada
dare da rana a gidansa.
Kuma insha Allah zai tsaya yaga cewa
ya cikama Safiyyah dukkan alkawuran da
ya daukar mata.
A tunaninsa yanzu kam ai za’a sakar
ma Sophie mara, tayi fitsarinta peacefully,
kamar kowacce mace mai iko a gidan
mijinta, a saka mata rigar ‘yanci, da bata
taba sakawa a idon Mama ba, shima kuma
zai samu kwanciyar hankalin da ya rasa
shekara da shekaru, a dalilin damuwar
Safiyyah data Mamansa, tunda finally yayi
abinda ake son yayi, kuma Safiyyah ta
amince.
Amma me??? Duk da yaqinin nan da
yake dashi na samun maslaha da warwarar
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
matsalolinsu na shekara da shekaru, ya rasa
meyasa hankalinsa yaki kwanciya da
al’amarin kuma, watau bayan
tabbatuwarsa. A lokacin da bakin alqalami
ya riga ya bushe. Duk juyin da Zayyan yayi a kan
gadonsa ya rasa me yasa sai yaji rashin
cikar kwalitin (ingancin) maslahar nan na
mintsininsa ta ko’ina….
Yana fata da addu’ar Allah yasa
maslahar da ya kawo din bai rikide ya
koma biggest mistake of his life ba, madadin
samo warwarar matsalarsu shi da Safiyyah.
Bai san meyasa yake ji a ransa kamar
wani babban al'amari ne ya tunkaroshi ba
kuma, wanda zai canza musu tsarin rayuwa
bakidaya, wato kamar ya ballo hadarin da
zai dokeshi daga sama, wanda zai sake
‘worsening’ komai ya dagula al’amuran,
maimakon kawo maslahar da ake nema.
Don dai shi ya san Sophie itace SOUL
dinshi (ruhinshi) bakidaya.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Sophie itace soyayyar dake zuciyarshi
gabadaya, tabbas kwanciyar hankalinsa
yana cikin nata kwanciyar hankalin.
Farin cikinsa har kullum, yana
danganta shi ne da farin cikin Safiyyah.
Sannan a kullum yana jingina sukunin
ransa da nata sukunin ran.
To amma anya Sophie na cikin sukunin
rai yau? A wane hali take? A rayuwarsu ta
aure kakaf! Basu taba raba shimfida ba in
dai yana gidan. Anya maslahar nan da ya
samo mai bullewa ce dasu duka? Kuma shin maslahar nan zata baima
Safiyyah hakikanin farin ciki da ‘yancin da
yake hango mata sanadinta? Sannan shin
maslahar zata haifar da Da mai ido a garesu
bakidaya??? A wannan gabar Zayyan ji yayi kansa
ya kara yi masa nauyi, kamar yadda
zuciyarsa ma tayi duhu, tayi nauyi cikin
rashin sanin abinda ya dace yayi kuma.
Domin tunanin halin da Safiyyah zata
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
kasance a daren yau kadai ya jefa shi a
rudani, wanda hakan ya jefashi a dogon
tunani da dogon nazari irin mai nisan
zango, irin wanda ya jima bai yi irinsa ba..
Daga wannan lokacin, a kwancen da
yake bisa makeken gadonsa, cikin wani hali
na kaka ni kayin zuciya da kwakwalwa,
Arch. Zayyan Bello Rafindadi, ya rintse
idanunsa ya shiga tunanin baya, komai ya
soma tariyowa cikin idanunsa daga
kwakwalwarsa, tamkar a majigin sinasinan
cinema rayuwarsu ta baya ke wulgawa a
idanunsa yanzu, tamkar wulgawar hotuna
cikin faifan bidiyo, komai ya shiga dawo
masa daki-daki tamkar a yanzu komai yake
faruwa…..
Zayyan ya tafi ‘down memory lane’
wato ya tafi ga tunani da tariyo dukkan
rayuwarsu ta baya shi da Safiyyah, tun
daga samartaka, dating dinsu, har zuwa
maganar aurensu da iyaye maza sukayi uwa
sukayi makarbiya, da abinda ya wakana
cikin rayuwar auren.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Watakila ta hakanne kadai zai samo
hakikanin maslahar da yake laluben nemo
musu, ta hanyar baiwa kansa assignment a
tsayin daren yau bakidaya, mai karatu
kuma yayi musu alkalanci na adalci shi da
Safiyyah, ta hanyar tarawa da debewa
tsakanin matsalarsu da maslahar da ya
samo.
Wadda har zuwa yanzu yake tantamar
cikar ingancinta koko yace still, maslaha
bata kai ga samuwa ba, in kuma aka ture
komai aka ce maslaha ta samu gareshi, to ga
ita Safiyyah din fa??? **** **** ****
FARKON FARI
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Garin Dandume gari ne da Allah yayiwa
albarkar noma da yalwar lafiyar kiwon
dabbobi. Galiban al’ummar Dandume
manoma ne da