Showing 9001 words to 12000 words out of 46889 words
Chapter 4 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf
*****
*****
Jim kadan bayan ritayarsa daga aikin
gwamnati, Baba (Prof) Bello Rafindadi, ya
koma harkar contract na zanen gidaje da
ginasu da bada hayarsu, harkar da ake kira
(Real Estate) irinna zamani a manyan
biranen kasar nan. Baba Bello ya samu tsundumawa a
wannan harkar ne ta hanyar amininsa
Arch. Murtala Babangida Masari, wanda
shi ya jima a harkar (Real Estate) da
gwamnatin Najeriya, Alh. Murtala bai taba
aiki a jami’a ba, sai a harkokin real estate.
Alh. Murtala Ya tara arziki mai yawa a real
estate business.
Baba Bello yana yawan cewa.
“Zayyan gashi dai shi daya a gabansa
tilo, amma daya ne tamkar da dubu”.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Kasancewarsa ya taso namiji daya a
cikin ‘ya’ya mata biyar, yasa Zayyan ya
tashi da dabi’ar yawan tausayawa ga mata,
duk inda ya ga mace babba ko yarinya yana
girmamata, in da halin taimako yana
taimaka mata, ya iya hakuri da halayensu
sannan duk dabi’un mata na rauni da
kyuya Zayyan ya sani, ya kuma iya tafiyar
dasu, tunda gabansa da bayansa duk ‘ya’ya
mata ne a dakin Mama Fatu. Mace daya tal
da Baba Bello ya aura a lokacin rayuwarsa.
Har Mama Fatu ta gama haife –
haifenta wato ta iso (menopause) bata taba
yin tsarin iyali ba, Zayyan kuma bai samu
kani namiji ba, sai kanne mata uku.
**** ***** *****
SHEKARA TA 2012
Itace shekarar da ya hadu da Safiyyah. A
wancan lokacin, wajejen shekarar ta dubu
biyu da goma sha biyu, mawuyaci ne ka
samu yarinya mai kananun shekaru mai
kamun kai da tsare mutuncin gidansu a
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
jami’ar Ahmadu Bello, kamar Safiyyah
Usman Dandume, wadda ake kira Safiyyah
Dandume, ta shigo jami’ar da shekaru
goma sha bakwai kacal. A halin yanzu
kuma ta shiga level 2 tana neman cika sha
tara. Safiyyah Dandume, ta riga ta siffanta
kanta da dabi’u na kamun kai a idon kowa,
da suttura ta mutunci, ta hanyar yin
kyakkyawar shiga ta kamala, don haka
mazan banza shakkar dosarta ma suke,
haka kawayen banza don babu fuskar
neman kawance da ita, a cikin ‘yammatan
dake tashen kokari a karatu a tsangayar
‘Architecture’ Safiyyah Usman Ladan,
tayiwa kowacce yarinya a department din
zarrah, ta yiwa tsararrakinta da abokan
karatunta da yawa fintinkau wajen maida
hankali ga abinda ya kaita, in akayi
jarrabawa ta karshen zango da (CGPA
4.50) take fita. Kullum addu’arta da fatanta
shine cikawa Malam alkawarin data daukar
masa, na cewa karatun jami’a bazai sa ta
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
canza dabi’un ta da halayenta masu kyau
daya riga ya santa dasu ba.
Kai shi bama wannan labarin da yake
yawan ji akanta bane abinda ya fara
attracting dinsa ga Safiyyah ba, irin saurin
maganarta dinnan (in’ina) da take masa
dadin ji, Safiyyah ga ga sassanyan kyau, ga
rangwada irin ta ‘yammata, wata irin
rangwada ta halitta Safiyyah keda ita cikin
Hijabi, komai nata Zayyan ya rasa mai
yasa, ko ba mai kyau bane shi kyau yake
masa, ya kuma burgeshi, ya kara kawatar
da ita a zuciyarsa.
Bai manta ba. A ranar da ya fara
ganinta Safiyyah a kule take, kuma a
harzuke da malamin labirare dinsu, amma
duk da haka tana kokarin shanye
harzukarta, saboda cewa da yayi bai gane
in’inarta ba, so take malamin labiraren ya
dauko mata wani littafi daya shafi abinda
take karantawa, tana so zata zauna a
labirare tayi Assignment, ta fada har sau
biyu amma mutuminnan yace wai ya kasa
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
gane me take fada da gangan da iya shege,
kyakkyawan bakinta kawai malamin
labiraren ya kurawa ido, sabida saurin
bakinta na halitta mai hade da hardewa da
tangardar harshe. Shikuma Zayyan dake bayansu yana
jira ta gama shima ya karbi nasa, tun bata
rufe baki ba shi ya gane me tace, ko don
shima littafin da ya zo nema din kenan?
Yana jin su itada malamin labiraren
suna magana, Safiyyah tana kara cewa
bazata maimaita ba, shikuma librarian
yana faman cewa “Na’am?? Hajiya sake
fade inji?” Hakan ya tunzura Safiyyah taji haushi
sosai, har kwallah ta cicciko a idonta, ta
kwanta a kasan kwayan idanun nata, kiris
take jira ta zubo akan kundukukinta, a can
baya Malam mahaifinta kullum da safe
yana karanta ayar;
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
“Rabbish’rahly sadry, wa yassirly amry,
wahlul uqdatan min lisany, yafqahu
qauly…..”.
Yana tofawa a ruwa yana bata tana sha
sanda tana yarinya, shine ma ta samu
saukin in’inar, amma duk da haka abin bai
tafi gabadaya ba, saidai ya ragu sosai.
Tunda har in ka saba da ita data fada zaka
gane. Tausayinta Zayyan yaji ya kama shi,
ganin tana neman barin wajen cikin kufula,
ya tuna wani abokinsa a sakandire mai suna
Saleh Wangara shima haka yake da in’ina
(stammerer), sai ya samu kansa da yanke
shawarar saka musu baki, wanda hakan ba
halinsa bane shiga maganar da bada shi
akeyi ba.Amma kwarai yarinyarta bahi
tausayi.
Zayyan sai ya samu kansa yana
maimaitama malamin labirare me yarinyar
nan take cewa, cikin nitsatstsen lafazin
Ingilishinsa.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ganin cewa yarinyar ta zo wuya har
tana hadiye hawaye da kyar, tana kuma
kokarin barin wajen don haushi, ba tareda
an bata littafin ba.
Kawai daga bayanta taji mutumin dake
tsaye a bayanta yace ma Librarian din cikin
nutsuwa; Tana son ka bata.
“Architecture, Form, Space, and Order”
na (Frank Ching, 1979)”.
Abinda bakinta ya kasa fada correctly.
Kuma abinda ta fada din kenan a
zahiri, sak babu bambanci, shida bada shi
take maganar ba, tsaye kawai yake a
bayanta, yana jira ta gama ya karbi nasa,
ya gane furucinta, amma librarian dinnan
don yasa ta tayi ta maimaita magana yana
karewa dan kyakkyawan bakinta da motsin
siraran labbanta da suka sha ‘wetlips’ mai
santsi kallo, suna sassarfa da hardewa da
juna, wajen yin furuci shiyasa yace wai bai
gane ba.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Aka dauko littafin aka miko mata,
kamar tace a mayar ta fasa, sai kuma ta
kasa musamman da suka hada ido da
wanda yayi mata ‘speech interpretation’
din. Kallon da yake mata na lallashi ne, mai
nuna cewa kada ta yi fushi, ta amsa tayi
karatunta.
Sai tayi masa kallon Rahma itama. Ta
kuma kasa tankwabe lallashin dake cikin
idanunsa. Ya fahimci hakan, sai yayi mata
murmushi na Sanya salama. Yace.
“ki karba ko?”
Ya tsareta da kyawawan Katsinawan
idanunshi, hakan yasa sai ta kasa kin karba,
domin zai zama kamar ta gwasile wannan
taimakon nasa da kulawar nasa ne.
A hankali ta amsa, bakinta na kokawa
da halshenta wajen motsin fizgo kalmar.
“Na - gode sosai fah!”.
Sai tasa kai ta wuce su, zuwa ainahin
cikin dakin karatun, kai tsaye Safiyyah ta
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
wuce zuwa wata corner a can kuryar library
din, inda a can ta saba zama duk sanda ta
shigo cikin dakin karatun.
**** **** ****
THE STAMMERER
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Y
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
au karo na biyu kenan da ganinsa da
“Stammerer” (sunan da yaji malamin
labiraren ya kirata kenan rannan bayan
wucewarta), yau ma tazo dakin karatun
kamar yadda ta saba, ta shige can kuryar da
take zama, ya riga ya gane yanayin
maganarta na halitta kenan (stammering) tun
daga ranar farko da ya fara ganinta, wanda
bazai gaji da cewa shi yafi komai daukar
hankalinsa a kanta ba, fiye da kyawun
surarta, ya kuma zame mata symbol a
wurinsa, wanda duk inda yaji sautinta nan da
nan yake gane itace, ko in yaji mai irinsa ya
tuno ta, ya kuma fahimci cewa a tsangayar da
yake ta ‘Architecture’ itama take karatu,
saidai undergraduate student ce ba kamar shi
da yake postgraduate student ba, ya gane
hakan ne daga wannan littafin da tasa aka
dauko mata rannan.
Kullum yana shiga library ne don yin
research da rubutu, baya son karatu cikin
hayaniya sam, idan ya shiga yana samun can
wata corner ne shima a can karshen dakin ya
zauna inda ba’a iya ko hango shi sosai, baya
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
son idan yana karatu a katse shi, shiyasa baya
yin karatu a (tutorial) da ‘yan ajinsu. Hakan
ya maida shi ‘regular visitor’ na library din,
saboda a lokacin yana bincike yana rubutun
(final project) dinsa na kammala digirinsa na
biyu. Yana matukar shiri da Librarians da
sauran ma’aikatan dakin karatun, idan ya
shiga karatu sallah kadai ke fito dashi, wani
lokacin zaka samu har gyangyadinsa yake yi
in ya gaji da karatun a corner dinsa, duk da
Zayyan mutum ne mara yawan sakin fuska
ga mutane da karancin far’a, amma fuskarsa
wani lokacin da walwala, ko babu far’a,
hakan kuma baya nufin shi miskili ne, a’ah,
kamewa ce kawai ta halitta da rashin son
daukar wargi, duk da haka in dai zai ga
ma’aikatan library din sai ya gaisa dasu cikin
sakin fuska, wannan ne yasa duk suka saba
da shi ya zama shima kamar ma’aikaci ne a
cikinsu ba dalibi ba.
Yanzu ya lura da wani abu, duk sanda
ya shigo library ya zauna a corner din
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
zamansa, yana yawan ganin wani (pink travel
mug) a desk din da yake gaban nasa,
mamallakiyar wannan ‘travel mug’ din itama
ya lura ‘regular visitor’ ce kamar shi.
Bayanta kawai yake iya hange kullum tana
sanye da Hijab ko jilbaab. Har a ransa ya
saka mata suna ‘Hijabie’ domin ya fuskanci
ma’abociyar suturta jikinta cikin Hijabi ce,
kullum cikin kyawawan Jilbaabs ko Hijabs
yake ganinta, wata shiga da kannensa su
Zahra sam basa yin kwatankwacinta. Kuma
shigar ba karamin kyau take yi mata ba (a
idonsa).
Ba koyaushe yake ganinta ba amma dai
tana yawan zuwa, idan ya hangi (pink travel
mug dinnan) ya san ta zo kenan, koda bata
wajen, to ta dan tashi zuwa sallah ne.
Da alama shayi ko coffee ne mai zafi a
ciki, kuma idan ta saka littafinta a gaba to
ko juyowa bata yi.
Ba ruwanta da duk abinda ke wakana a
cikin library din. Sai ya kasance shikuma a
rayuwarsa he’s in love with such kind of
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
serious and decent charcter, shiyasa take
burgeshi deep down inside him, yake
girmamata a kasan ransa, ba tare da ya san
kamannin fuskarta ba.
Watarana ya shiga research kamar
yadda ya saba, sai ya ga seat din ‘Hijabie’
babu kowa, sai ko ‘Pink Travel Mug’ dinta
na gado ajiye a wurin.
Sai yaji idanunsa na kewar ganin
bayanta da ya saba gani in tana karatu,
kawai yaji sha’awar zama a wajen nata, sai
ya zauna (for a change). Don shi dai a
duniya yarinyar nan da yanayin sutturarta
da decent nature dinta, duk suna matukar
tafiya dashi.
Yana tsaka da aikin gabanshi sai yaji
kamar tsayuwa a bayan shi. Ta zo zama a
gurinta, sai taga wani zaune a gun, bayan
kuma tayi shaida a wajen da littafinta da
Mug dinta, sai ta tsaya kyam, ya dago a
hankali ya dubeta.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Nan da nan ya ganeta ashe yarinyar
nan ce mai in’ina, ita keda Pink Travel Mug.
Yayi mata sallama hade da murmushi, yace
“na zauna miki a wajenki ko? Sorry!”
Yana dagowa dinnan nan take ta gane
shi, (her speech interpreter)!. Itama sai tayi
murmushi, da sasssarfar maganarta tace
“so, it is you?”
"Ashe baki da mantuwar fuska?”
Ta sake yin murmushi tace “Ba sai ka
tashi ba, tunda ai wajen na kowa ne, babu
mai (permanent seat) a wajennan, kawai
sabo ne yasa nake zama anan din, bakomai
Mr, bari na juya na nemi wani wajen,
Nagode”. Sai ya hau tattara takardunsa daga
kan desk din, yace mata “ayi haka? Hijabie,
zo kiyi zamanki. Mai waje ya zo mai
tabarma sai ya nade ko? Kayan aro baya
rufe katara”.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
'Yar dariya Safiyyah tayi tace. "bafa
sunana Hijabie ba Mr. Library. Sunana
Safiyyah Usman Dandume"
Zayyan yace "madallah da Nana
Safiyyah, ni kuma Zayyan nake, sunana
Zayyan Bello, ba Mr. Library ba".
Sosai ya bata dariya ta kuma yi zaman
ta a wajenta daman tafi son wajen, ta saba
da seat din sosai.
In bai manta ba, daga nan tushen
alaqarsu ya samo asali tsakaninsa da
Sophie. And in no time, sabo mai tsanani ya
shiga tsakaninsa da Safiyyah, kowanne ya
shiga yaki da halinsa akan dan uwansa;
abun nufi, Safiyyah ta cirewa kanta rashin
kula mutane da rashin son yin mu’amala
dasu akan Zayyan, shikuma ya cirewa
kansa fuskar rashin walwala da sakin fuska
in dai yana tare da Safiyyah a makaranta,
to kuwa zai nemo walwala duk inda take ya
sakawa kyakkyawar fuskarsa, a haka har
suka fara sabawa outside library.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Kasancewar duk suna karkashin
tsangaya guda hakan yasa suna yawan
haduwa shi da ita a department dinsu, kuma
gashi sun fito jiha daya, sai suka kara zama
abokan juna, kuma abokan karatu na sosai
ga junansu. Duk da haka Safiyyah na kaffa-kaffa
bata bari wata hira ta hadasu bata karatun
da ya kawota ba. Shima kuma Zayyan Bello
haka. Kullum kara wayar mata da kwanya
yake akan dabarun dake cikin ilmi Zane.
Har aka zo gejin da tafi jin dadin koyarwar
Zayyan, fiye data dukkan Mallamansu.
Bata san ma ya akayi shi ta saki jiki
dashi har haka ba, alfarmar da bata yiwa
kowanne da namiji a fadin jami’ar nan ba.
Kai har mata ‘yan uwanta, Safiyyah bata
sakewa dasu, kamar yadda ta samu kanta
dumu-dumu da sakewa da Zayyan Bello.
Wadanda sun riga sun nada mata rawanin
mai girman kai.
Har wasu ‘yammatan masu kishin irin
kyawun surar da Allah yayi matam, da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
yadda take jan attention din maza akanta
cikin Hijabi, su kan yi gulmarta da cewa,
ita ba ‘yar kowan kowa, ba sai kafirin
girman kai.
Rashin yawan far’arsa ko kadan baya
damunta, don ta gane nature na halittarshi
ne haka, ba kuma miskilanci bane, amma
akwai shi da dadin mu’amala ga wanda
zuciyarsa ta amincemawa yayi alaqa dashi
kamar yadda ta amince da ita Safiyyah.
Tarin nutsuwarsa da yawan kokarinsa a
karatu, sun taimaka gaya wajen sakewar
Safiyyah dashi, don ta tsani alaqa da
miskilin mutum ko dakikin dalibi.
Wani abu a halayyar Safiyyah shine; in
dai kana da kokarin da zata amfana dashi a
karatu, to kowanne irin hali gareka zata iya
tafiya tareda kai salin-alin.
To hakan ce ta faru tsakaninta da
Zayyan Bello, Zayyan bashi da far’a, baida
walwalar fuska ko kankani, babu kuma
fuskar wasa a tare dashi, amma akwai
tsantsar kokari da fasaha a ilminsu na
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Architecture, da ba duk dalibai keda su ba,
ga yawan kamewarsa daga kule-kulen
‘yammata da abokai barkatai shima,
wadannan sune manyan dabi’unsa da ke
burgeta dashi, suka kuma bashi (100%
acceptance) a wurinta. Dama an ce sai hali
yazo daya ake abota.
Ya zamana Zayyan na taimaka mata
sosai a harkar karatunta, a matsayinsa na
gaba da ita a shekaru da matakin karatu a
lokacin.
To shi dai Zayyan daga karshe bai tsaya
batawa kansa lokaci ba, ko yaudarar kansa
na tsayin lokaci, kamar yadda Safiyyah ke
yaudarar kanta da cewa abokantaka ce ta
karatu a tsakaninsu, ya tara hankalinsa
waje daya ya gayawa kansa gaskiyar cewa
ainahin son Safiyyah Dandume zuciyarsa ke
yi, so tsantsa kuma na zallar soyayyar Da
namiji ga ‘ya macen data dace da duka
burikansa, babu wani friendship ko
makamancinsa a zuciyarsa gameda
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Safiyyah, bayan So na sahihiyar soyayya a
ransa.
Da yaga zai Takura, da tunanin ta
yadda zai bullowa Safiyyah, saboda ba
fuskar hakan a wurinta, tunda har ta kai shi
ga kasa karatu yanzu da raba dare cikin
tunanin Safiyyah Dandume, haka zai kwana
yana juyi a kan gadonsa cikin shakkar
yadda zai tunkareta da zancen SO.
Kwarjinin da Safiyyah ke masa ba
kadan bane, ya yarda Hijabi sutturah ne
kuma kamala ne da Karin mutunci ga diya
mace, da ke saya mata martaba da kwarjini
a idon maza, in dai don Allah take saka shi,
daga lokacin ya fahimci cewa lallai son
Safiyyah azimun ne a ransa, kullum kuma
son nata karuwa yake yi cikin ransa.
Safiyyah ce kadai burinsa a halin
yanzu, kuma wani babban kuduri da yake
son cimmawa a rayuwa yanzu shine
aurenta.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
A zahiri, wani abu da bai taba planning
dinsa nan kusa ba shine “aure”, tunda ko a
makaranta yake har yanzu bai ko kammala
rubuta final project dinsa ba, balle ayi
batun neman aiki dana abun rike iyali,
wanda kullum Mama Fatu ke kwakwazon
sai ya samesu wato sai ya tsaya da
kafafunsa kafin ta samo masa matar aure
daidai da ra’ayinta.
Amma duk Safiyyah ta canza komai
yanzu, ta birkita lissafinsa ta yi katsalandan
cikin kowanne irin tunanin hankali daya
mallaka, da kutsowar cikin zuciyarsa da
rayuwarsa. Don haka bai wani tsaya
jinkirin da zai zama batawa kansa lokaci
ba, ya yanke mai fishsheshi ba tareda ya
nemi shawarar kowa ba.
Yaga gara ya badawa idonsa toka kawai
ya cire shayin Safiyyah da kwarjininta ke
saka masa daga idanunsa, ya