Showing 6001 words to 9000 words out of 46889 words

Chapter 3 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

‘yan kasuwar gona, sannan da
makiyaya, Dandume tsohon gari ne dake cike
da tubarrakin manyan malamai na addinin
musulunci kamar dai mahaifin su Safiyyah.
Safiyyah ta taba bashi labarin cewa ita
FGGC Bakori tayi, kuma ta yi nasarar lashe
jarrabawar JAMB da tayi a boye bada sanin
mahaifinta ba, saboda ya sha alwashin shi
aure yakeso zai yi mata da zarar ta gama
karatun sakandire in dai miji ya bayyana,
saboda shi Malami ne na kwarai, bazai
lamunci komai ba sai tafiya gidan aure
bautar ubangiji.
Cikin ikon Allah kuma ta samu ta haye
Jamb din, da yakkyawan maki mai burgewa.
Tace hatta form din Jamb din, dan uwanta
“Yaya Shaikh” ne ya saya mata a boye.
Kasancewar ita da Yaya Sheikh kusan
a komai bakinsu daya cikin gidansu, sun saba
su kashe su rufe itada shi, ba tareda ko

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Malam da Ammi sun sani ba, sun kasance
aminai ne bayan ‘yan uwantakar jini mafi
kusanci dake tsakaninsu.
Itada Yaya Sheikh (‘yan maza zar
suke). Da mahaifinsa mai rasuwa Malam
Abubakar da mahaifinta Malam Usman uwar
su daya ubansu daya.
Bayan rasuwar mahaifinsa ne Malam
Usman ya dauke shi hannunsa, sai ya damka
shi a hannun Ammi, wato mahaifiyarsu
Safiyyah, kasancewar shikadai iyayensa suka
haifa. Daga ita har Yaya Sheikh, duk suna da
ra’ayin tayi karatu boko har zuwa jami’a,
akan passion dinda take so tun tana karama,
Safiyyah tana na yarinya ba abinda ta kware
a kai a makaranta irin ‘Zane’, kasancewar
Art class tayi, ba abunda bata iya zanawa
yayi kyau ya bada suffa mai ma’ana ba,
wanda yake sabanin ra’ayin mahaifinta, da
suke kira “Malam” wanda kasurgumin
Shaihun Malamin addini ne. Ya kan ce shi bai

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ga komai na amfani a cikin Zane-Zanen da
take cika musu bango dasu ba.
Safiyyah ta cigaba da bashi labarin
cewa, “saboda haka sabanin sauran
‘yammata irina da iyayensu ke raye har
zuwa wannan lokacin, zaka ga iyayen ne da
kansu suke fafutukar nema musu gurbin
karatu a jami’a bayan kammala sakandire,
don basa son ajiyesu a gabansu basa komai,
“amma ni Safiyyah abin ba haka ya kasance a
gareni ba, na san na shigo jami’a ne kawai
(by chance)”.
Wato ta samu shiga makarantar ne bisa
yardar Ubangiji, da ya riga ya rubuta mata
ita a kundin kaddarorinta, cewa zata yi boko
mai zurfi ko Malam baya so, da kuma karfin
addu’ar data kwana yi akan mahaifin nata,
kafin ta doshe shi da takardar samun
gurbinta a safiyar ranar da sakamako ya fito.
Tace tayi addu’a sosai, ta kuma sa
kananan kannenta uku mata Sabah, Rayyah
da Rayha sun tayata, wadanda akwai ratar
shekaru biyar tsakanin ta Sabah, sauran

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

biyun kuwa wajen shekaru bakwai da takwas
ta babbasu, tace sun taya ta addu’a ta basu
sadakar cakulet sukayi ta murna, akan Allah
ya dorata akan mahaifinta ya lamunce mata
zuwa jami’a a birnin Zazzau. Malam ya riga ya horesu da yin addu’a
da tsayuwar dare cikin talatainin dare, akan
kowanne lamari suke so Allah ya shige musu
gaba a kai, don haka shima Malam bai tsira
ba, a cewarta ta kai kararsa sunansa ne
gaban Ubangiji akan bukatarta da zazzafar
addu’a har da sadaqah wa kannenta.
Mahaifinta Shaikh Usman Ameen
Ladan Dandume, fitaccen malami ne na
addinin musulunci a kauyen Dandume, ba
malamin allo bane malamin buzu ne, dake
karantar da magidanta da samari, kowa ya
san zaiyi wuya a rikon addini irin na Malam
Usman ya bar babbar diyarsa taje jami’a har
wani gari wai Zazzau, ba tareda igiyar aure a
kanta ba. Tunda shi da kansa yake bada
fatawa ga iyaye maza dalibansa a kauyen

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Dandume, ta hanasu barin ‘ya’yansu mata
sakaka a jami’o’i batare da aure ba.
Malam Usman sananne ne a wurin
tsaurin tarbiyyah, mutum ne mai kokarin
kiyaye dokokin Ubangiji a gidansa, don ya
kiyaye hadisin da yace “in kuna tsoron
bazaku iya adalci ba, ku auri dai-daya”,
shiyasa har zuwa yanzu da ya cimma
shekarun girma, furfura ta sauka, bai kara
auren wata mace bayan Amminsu Safiyyah
ba, an sha kawo masa sadaqar ‘yammata iri
iri daga kauyukan Katsina daban daban baya
amsa, saboda Allah shaida ne akan Mallam
yana mutunta Ammi, yana martabata, yana
mutuwar sonta, duk da kasancewarta uwar
‘ya’ya mata zallah a gareshi. Bata taba
haihuwar masa Da namiji ba.
Tun kafin a haifi su Safiyyah malam na
rikon Dansa Ridhwan da suke kira “Yaya
Shaykh” wanda ya kasance da ga dan uwansa
Abubakar da ya rasu a hatsarin mota,
mahaifiyar Ridhwan kuwa tun wajen
haihuwarsa ta koma ga Ubangiji, don haka

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Sheikh maraya ne, Ammi ce ta raine shi da
nonon shanu. Bai tashi ya san wasu a
matsayin iyaye ba bayan Ammi da Malam.
Har ila yau Malam nada wani yaro
almajirinsa da ya rika kamar Da mai suna
Haroun, yaron da aka kawo masa almajirci
daga Geidam ta jihar Yobe.
Don haka a lokacin da tayi jarrabawar
(jamb) ta kuma ci, sai Yaya Sheikh ya nemo
mata gurbi a ABU ta hanyar wani almajirin
Malam mai yawan zuwa gidansu gun Malam
wanda ma'aikacin ABU ne (non-academic
staff), Malam bai sani ba haka Ammi daga
sanda taje ta rubuta jarrabawar har gashi ta
ci, daga ita har Yaya Sheikh sun san sun yi
karambani, amma sun yarda addu’a bata bar
kowa ba, basu taba tunanin Malam zai barta
zuwa jami’a har a wani gari can, bama cikin
Katsina ba, ba kuma nasu garin Dandume ba.
Ita kuma Safiyyah Allah ya sani, tun
tasowarta babu makarantar da take burgeta
take bata sha’awa a fadin Najeriya irin
Jami’ar Ahmadu Bello, wannan ya samo asali

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

daga kanwar mahaifiyarta Anti Dije dake
aure a Zaria, kuma tayi aiki a ABU kafin ta
bar aikin ta zauna a gida, a lokacin da Anti
Dije ke can tana yawan zuwa hutu wajenta,
Anti Dije na yawan bata labarin garin Zaria
da manyan makarantun dake kunshe cikin
garin. Ta kan ce “Zaria gidan ilmi ce
kacokam! In kin tashi karatu Safiyyah ki
taho Zaria, don samun kwali mai nagarta,
saboda babu jami’a mai tsohon tarihi a arewa
kamar Ahmadu Bello.
Ta san dai akwai taimakon addu’arta,
domin ta roki Allah idan karatunta alkhairi
ne ya baiwa mahaifinta ikon barinta
salin-alin cikin sauki, idan kuma babu
alkhairi kada Allah ya bata ikon tambayarsa
ma, ta yiwa Ubangijinta alkawarin kare
mutucinta dana addininta dana iyayenta, in
har Malam ya lamunce mata zuwa karatun,
ta hanyar yin shigar da zata kare martabarta
data addininta, ta tsarkake idanun maza a
kanta, wadda a cikinta suka taso itada
kannenta mata dama, wato shiga ta kamala
(Hijabs), ta yiwa Ubangiji wannan alkawarin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

tsakaninta dashi cewa karatu kadai zai kaita
Zaria, bata da wata manufa bayansa, muddin
ta samu yarjewar Mallam in ta shiga ABU
bazata canza halaye da dabi’unta daga yadda
suke a Dandume ba. ​ To shi Ubangiji a kullum niyya yake
dubawa da tsarkin zuciyar bawa kafin ya
amsa masa addu’a. Cikin hukuncin Ubangiji
Allah ya amshi rokonta, don yaga tsarkin
niyyarta karatun ne kawai a ranta. Malam
Usman Dandume ya sahale mata zuwa ABU
babu ja’in’ja.
Yace ba don komai ya amince ba sai
don cewa itace babba cikin ‘ya’yansa, kuma
dukkansu ‘ya’yansa mata ne, mata kuma
masu rauni ne da kaunar juna by nature
dinsu, don haka itace uwar kannenta da zata
dauki takalihunsu ranar da basa nan shi da
Ammi, ko ranar da karfinsu ya kare tunda
basu da Da namiji a cikinsu bayan Yaya
Sheikh, don haka dole ya bata damar yin
ilmin addini dana zamani, a matsayin jarin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

da zai iya bata kadai itama ta basu
(kannenta).
Malam ya rufe zancensa da cewa “kowa
yayi da kyau ya sani Safiyyah, in bana
ganinki Allah daya halicceki yana ganinki, ya
kuma san irin tarbiyyar dana baki da abinda
zaki je ki aikata a bayan idona”. ​ Wanan ne yasa Safiyya zama wata irin
Kamilah, khashi’ah, khalisah, kamammiya,
zaqaqura, zealous (mai himma) kuma smart a
jami’ar. Take yin rayuwarta daidai da ita, ba
rawar kai ba kidifiri. Ba karya ba kawayen
banza, ba sakin fuska ga kowa walau mace
walau namiji, Safiyyah taki sabo dakowa, don
ma kada a abokantaketa a bata mata tunani,
a shiga lokacinta, na abinda ya kawo ta, yasa
hatta matan ma bata kulawa ba maza kadai
ba, lokaci abu ne mai matukar muhimmanci
a gurin Safiyyah, da bazata iya karar dashi
akan kawancen makaranta ba, idan kuma
hanya ta kure kun hadu Safiyyah zata yi
maka sallama ta musulunci shikenan.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Kullum fatanta Allah ya fiddata kunyar
Mallam, da yardar da yayi ma tarbiyyar da
ya bata.
Safiyyah kyakkywar ba-katsina, kalar
fatarta kamar ruwa biyu, hancinta da
bakinta kamar na mutanen kasar Habasha
(Ethiopia) ga wadatar sumar kai data gira.
Ga lumsassun idanu masu matukar daukar
hankalin wanda duk ta kalla dasu ba maza
kadai ba.
In har bai manta ba, silar haduwarsu
kenan, watau zuwanta jami’ar Ahmadu Bello
da shekara daya da ‘yan watanni, tana
kokarin shiga aji na biyu wato (level two).
Daga wancan lokacin zuwa shekaru
goma da doriyar watannin da suka shude da
yasan Safiyyah, to a jami’ar Ahmadu Bello ya
fara saninta, ya kuma ganeta ne daga
uniqueness na sautin muryarta (in’ina ce da
ita), sautin da ya bambanta dana sauran
mata, har kuma zuwa inda yau ke motsi, bai
manta sautin in’inarta da yaji na farko shi
yasa shi juyowa ya kalleta ba.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

In’ina ba dadin saurare gareta ba,
amma shine sautinta daya fara shiga
kunnensa ya zauna, har gobe sautin yana nan
a kunnensa, yana shawagi a kwakwalwarsa,
yana masa amsa-kuwwa, don shi dadi sosai
in’inar tayi a kunnensa, his fondest memories
da ita kenan a kullum; (in’inarta).
Sautin da har yanzu ya kan sake yi
masa amsa-kuwwa, lokaci- zuwa lokaci, idan
ya tuno Safiyyah, bai mance shi ba, kuma
bazai mance din ba, domin dadin da sautin
in’inar yayi masa yaki bacewa daga cikin
memory dinsa. Wani irin sarkakken sauti Safiyyah
keda shi, mai ‘yar gargada (stammering)
wanda dai-daikun mutane kadai Allah yake
jarrabta da ita.
In’ina wata lalura ce ta furta magana
da kyar, ko kana yi tana makalewa, ko kuwa
hardewa da ‘yar gargada haka, kana yi kana
kwatota daga makoshinka da kyar, kamar
yadda Ubangiji ya jarrabci AnnabinSa Musa
(A.S).

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Sautin nata mai tashi ne da
rangwamen amo, kuma cike da zakin murya
irinna ganiyar ‘yammatanci, irin dai na
budurwar dake ji da kuruciyar
‘yammatancinta, (in her teens), hakika
Safiyyah ta yi nasarar shiga jami’a da wuri,
su ake kira JJC (Johnny just come).
Don a lokacin Safiyyah bata fice
shekaru goma sha takwas a duniya ba, inma
ta kai din.
Ranar da ya fara ganinta, tun kafin ya
ga fuskarta shi in’inar ya fara ji, shine abu na
farko da ya ja hankalinsa tamkar
maganadisun mayen karfe zuwa gareta a
ranar, saboda (peculiarity) din dake cikinsa,
‘yar gargadar maganarta ta masa dadin ji.
Inda yaji tana maimaitawa Librarian din
dake kula da (reserve section) cikin tukewa
da kokarin shanye fushinta, saboda cewa da
yayi wai shi baya gane me take cewa.
Kamar zata yi kuka ta sake cewa
taqarqarewa tana fizgo maganar da kyar, ta
ce cikin in’inarta….

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

“Malam…, nace-nace maka….
“Architecture, Form, Space, and Order (Frank
Ching, 1979)” zaka dauko min.
“Me kike cewa ne?”
“Kayi hak-kuri….ni…ni… stammerer
ce, I don’t feel repeating it again”.
Zayyan sai ya samu kansa da yin
murmushi daga kwancen da yake a rigingine,
yana iya hango fuskarta cikin damuwa a
lokacin cikin wani sako na kwakwalwarsa,
kamar a lokacin Sophie take furtawa
librarian din bazata maimaita ba. Exactly
over a decade now da faruwar hakan amma
komai dawo masa yake tamkar a yanzu yake
faruwa.
Ya juya ya sake gyara kwanciyarsa,
wannan karon akan ruwan cikinsa yayi
folding hannayensa a saman kansa ta baya, ya
kara nausawa cikin dogon tunanin nasa.
In’inar kawai yake tunawa da bege da
kewa mai yawa, kamar Safiyyah bata cikin
gidan nasa a halin yanzu, bayan shine da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kansa ya buyar mata cikin wani hali na
rashin yarda da hukuncinsa.
“She looks so naïve and innocent
budurwa tun a lokacin, amma kuma tawayar
tangardar harshen ya zame mata cikas ga
cika “Classy Babe (hadaddiyar budurwa”.
In ta fadi abu kuma aka ce ta maimaita
ba’a gane ba, bayan hararar da zata zabga
maka kamar idanunta zasu fado kasa, har
kwallahr bakin ciki take yi mai zafi. Don me
zaka ce baka gane ba? Ya fara son Safiyyah daga rana ta farko
da ya fara haduwa da ita. Wani abu kaman
dai “Love at First Sight” ko me? Wanda yayi
ta ‘nurturing’ dinsa yana nunar dashi a
kasan ransa shikadai, kuma har gobe bai
gama rainon nasa ba, don kullum kara tsiro
yake da fidda sabuwar yabanya, yana bude
sabbin rassa da sababbin ganyaryaki sabbi
gadagal! Na son Safiyyah a zuciyarsa.
Musamman a halin yanzu da yake tantama
kan ingancin abinda ya aikata mata, da sunan
nema mata maslaha a zaman aurensu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Shi da kansa ya san bai san da kalmar
da ya kamata ya suffanta ko ya kamanta ko
ya kintatawa mai karatu girman matsayin
soyayyar Safiyyah a zuciyarsa da cikin
rayuwarsa gabadaya ba, koda harshen da zai
iya bayyana girman son da yake yi mata ba
yadda mai karatu zai gane, da girman
matsayinta cikin rayuwarshi da duniyarshi
tun daga ranar ba.
Kawai ya san cewa duk wani so na
gaskiya da duk wata kauna ta hakika da Da
namiji na kwarai irinsa zai iya yiwa diya
mace, to shi Zayyan Bello, nashi son ya kare
ne akan Safiyyah Usman
Dandume. Saboda ya so ta ne a lokacin da
zuciyarsa babu nauyin komai a cikinta sai
zallar kuruciya, soyayyah ce ta samartaka
zallah irinta isowar shekarun hankali wato
cikakkun shekaru na cikar balaga, wadanda
a su ne namiji ke fara gina matakan
rayuwarsa, babu nauyin iyaye da ‘yan uwa da
yazo ya hau kansa daga baya.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Babu komai a ransa a lokacin sai katon
fili fetal! Wanda zuciyarsa ta shimfida ma
Safiyyah koriyar darduma akai, ta feshe
dardumar da turaren nan na kauna da
soyayya na “Sandalia” tayi mata maraba da
sauka, gurbi ne dama wanda ya tanada ya
ajiye musamman domin soyayyar iyalinsa
kadai, amma bayan wannan babu nauyin
kowa da komai a cikin zuciyarsa a daidai
lokacin.
‘Yar mutanen Dandume, ta shigo
rayuwar samartakarsa tun yana rubuta ‘final
project’ dinsa a jami’a.
Hakan ne yasa lokacin da Safiyyah ta
iso rayuwarsa daga haduwarsu ranar nan a
(University Library), nan da nan tayi maza ta
shige sukuf! Cikin ransa, ta baje kolinta ta
hanyar mamaye ko’ina ita kadai, bata bar
masa kowanne kankanin sako da zai sanya
tunanin komai bayan nata ba. Har wani
lokacin ya kan kirata da suna (Cinye Du) a
cikin ransa, don hakika duka zuciyarsa
Safiyyah ta cinye, ta mamaye ko’ina ita

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kadai. Ba wadda zai iya kara so kuma, bayan
so na farillah, wato na Mahaifiyarsa Mama
Fatu, da kannensa uku da Yayyensa biyu duk
mata.
Uwa-Uba ka cire son da yake yiwa
mahaifinsa (his beloved Baba Bello), wanda
bazai shiga cikin kwatancen bama to duk
sauran girbin dake zuciyarsa ‘yar mutanen
Dandume ta cinye. ​Ya fara son Safiyyah ne tun mahaifinsa
Arch. Bello yana raye, lokacin da shi kansa
daukar nauyinsa akeyi da komai na
karatunsa, wato Baba ke daukar takalihun
komai nasa, tunda dan lelen cikin mata ne
shi, abin nufi shikadai Mama Fatu ke da, a
matsayin Da namiji, Yayyensa biyu mata ne
haka kannensa uku duk mata ne, gashi da
tarin da basira a karatu, Zayyan nada
rawar kan kuruciyar samartaka ta samari
‘yan bana bakwai tsararrakinsa a wancan
lokacin, zaka ganshi kullum cikin
nutsuwarsa da tsafta da gayu, very reserved
and smart dashi, dalibin shekarar karshe a

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

karatun digiri na biyu a lokacin yana
rubuta thesis dinsa.
Dan kimanin shekaru ashirin da
bakwai da haihuwa.
Saboda irin gatan da Baba Bello ke
gwada masa, tunda ya gama digirin farko
ya saya masa wani lafiyayyen (Bike) na
yayin samari, mostly 'yan gata na lokacin
kadai ke iya hawa ‘Bike’ dinnan da ake kira
(LIFAN), wanda dashi yake shanawarsa
yana fantamawa da abokansa a tsakiyar
ABU.
Daga nesa in ka hango shi akan ‘bike’
dinnan yana zuga gudu a cikin harabar
makarantar, iska na cika rigarsa, ko idan ya
shigo farfajiyar tsangayarsu a kan babur
din, sai ka so kara yi masa kallo na biyu,
domin zaiyi maka matukar kama ne da
jarumin wasan kwaikwayon nan na kasar
Hindi; Bollywood actor, Abhishek
Bachchan. Saidai ace Abishekh ya fishi
zama jajawur ya fishi nannadadden gashin
kai. Shi Zayyan Ba-katsine ne kuma

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Ba-rume, wanda ya tsotso nasa ussin
kyawun da hasken fatar daga Rumawan
jihar Katsina.

Mahaifinsa Arch. Prof. Bello
Rafindadi, dan asalin shiyyar Rafindadi ne
ta jihar Katsina, shine (Chancellor) na
farko na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Adua,
sanda aka budeta. Mahaifinsa Prof. Bello Shi ya zaba
masa tafiya Jami’ar Ahmadu Bello, yana
kammala karatun sakandirensa a Barewa
College, babu bata lokaci ya samu
admission, don shima Baba Prof. can yayi
nasa digirin na farko, sauran kuma a
UDUS, Baba Bello yana da burin dan shi
Zayyan ya karanci abinda shima ya karanta
ya samu daukaka, arziki, shuhura da cigaba
mai yawa akan profession din, watau
“Architecture”.
Burinsa tun a lokacin shine Zayyan
dinsa ya gajeshi akan komai da yake kai,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kasancewarsa Da namiji tilo daya mallaka
cikin tarin ‘ya’yansa mata.
****

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login