Showing 12001 words to 15000 words out of 46889 words

Chapter 5 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

furta mata
zahirin abinda ke zuciyarsa in yaso duk
yadda Safiyyah ta karbi al’amarin zai jure
ya iya karba.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

A washegarin ranar da ya yanke
wannan shawarar da zuciyarsa suna tafe shi
da Safiyyah a hanyar zuwa tsangayarsu
bayan sun fito daga library, labarin
kannenta take bashi da suka zana
jarrabawar (jsce) a yau wato Sabah da
Rayha, Zayyan ya dubeta admiringly ko
yadda take labarin cikin wahalar in-ina
kara sonta yake yi, bai iya ya bari ta gama
bashi labarin ba ya katseta.
“Hijabie, ina son zuwa gidan ku fa!”.
Safiyyah ta dubeshi da dan mamaki da dan
tsoro a idanunta, saida yaji tsigar jikinsa ta
tashi, tace “gidanmu? To me akeyi a
gidanmu Mr. Library?” Ta bashi dariya sabida tsakaninta da
Allah ta shiga damuwa da jimami. Don ta
san halin Malam sarai, sanadin haka zai iya
katse karatun, don wannan ba shine
alkawarin data daukar masa ba kafin ya
barta tazo makaranta. Zayyan ya samu sa’a mai ban mamaki
a kanta da ita kanta take mamaki. Yayi

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

magana cikin sauti na kwantar da hankali,
ganin yadda kalamanshi suka sa ta shiga
rudu, yace,
“Safiyyah, mu zama frank da junanmu,
zumuncinmu nida ke mai ma’ana ne a
wurina, mai nufin yada kyakkyawar
yabanya, kuma shine abinda zai kawo ni
gidanku gaban iyayenmu”. Safiyyah ta gyara zaman hijab dinta a
kanta, ta langabar da kai tace “idan kuma
Malam yace wanene kai? Ko meye
tsakaninmu idan kaje me zan ce masa? Ka
dai bari sai na sanar dasu a gida tukunna,
don Babana Malami ne babba, baya bari
azo masa gida haka kawai babu dalili”.
Zayyan ya kankance ido yayi mata
wani shanyayyen kallo da bai taba yi mata
ba, yace “ai nima ba hakanan zan zo ba
Hijabhie, ba haka kawai ce zata kawo ni
gaban Malam ba, banza tana kai zomo
kasuwa ne?

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Safiyyah stop kidding and joke apart
pls, Hijabi na dake ajiye a gidansa nake so
in dauke abina.
A takaice zan iya cewa soyayyah ce ‘yar
gaske, wadda ta dabaibaye ni, da neman
irinsa mai albarka zai kawoni gidansa.
In kika ga kare na sunsunar takalmi ki
tabbata dauka yake so yayi Safiyyah!?"
Safiyyah ta rufe ido da hannayenta da
suka sha adon jan lalle, taji kunya matukar
gaske ta lullubeta, rana ta farko da wani
namiji da zuciyarta ta riga tayi na’am dashi
ya furta mata kalmar SO a tsanake, tace
cikin jin nauyi da farin cikin da take
kokarin dannewa, don gabadaya sai yau
tasan ashe itama ta fara kamuwa da son
dan ‘little gentle’ saurayi Zayyan din, ba
haka kawai zuciyarta da ruhinta suka sake
dashi cikin dan kankanin lokaci ba, SO ne
gangariya, dan asali na hakika Allah ya
gittar a tsakaninsu.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Don haka cike da jin kunya Safiyyah ta
sunkuyar da kai tana kokarin hada kalmar
da zata bashi amsa wadda bazata nuna
eager dinta ko amincewarta farat daya ba,
tace a hankali. “Amma dai ka fara bari in sanar a gida
first, cewa kana so kazo ka gaida Malam, in
yaso ya baka iznin zuwan, saboda kafin
Malam ya barka ka zo wajena fa sai ka je
ka fara samunsa takanas, ka zuba gwuiwa a
kasa ka gabatar da kanka da dalilin
zuwanka, ya baka yardarsa, da lokacin da
zaka dinga zuwa, wannan shine, bisa tsarin
gidanmu.
In ba haka ba zuwanka kai tsaye zai
zame min matsalar da zata iya yin sanadin
karatuna”.
​Zayyan dai ya fahimci ya zo gida na
mutunci da tarbiyyah irin wanda yake fatan
samarwa ‘ya’yansa. Kuma aka ce labarin
zuciya a tambayi fuska, ko daga idanunnan
na Safiyyah masu nuna yawan jin kunyarsa
yanzu, da jin nauyinsa tuntuni, yau kuma

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

gabadaya sun kara canzawa da yawan
kaucewa haduwar idanunsu. Uwa Uba,
amsar da ya samu daga gareta yanzu, ya
san Safiyyah tayi na’am da shi dari bisa
dari ko bata furta kai tsaye ba. Don haka shikuma bai yi kasa a
gwiwa ba, ranar Juma’ah kwana uku da yin
wannan maganar tasu, bayan an sauko daga
masallaci ya sake daukar wanka na
musamman, daman dai shi Zayyan kowa ya
shaida ma’abocin iya daukar wanka ne, ga
iya sanya hula a kan goshinsa, ya dauki
karin hular Zanna Bukar da ake yayi a
lokacin, da karin gugar shaddarsa ta yayi,
ya fesa turare sannan ya fito daga dakinsa
ya nufi cikin gidansu, nan yayima Mama
sallama kan zai je unguwa, har Mama tana
tsokanarsa ko daurin auren babban amini
Habibu zai je ne? Irin wannan kashe hula a
goshi Baffana? Murmushi yayi bai ce komai
ba, don abu na karshe da Mama zata kawo
a ranta shine Zayyan dinta zai iya kallon
wata mace da sigar soyayyah balle har yace
yana so, sabida kamewarsa da dattakunsa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

na halin manya irinna mahaifinsa, ya fita ya
kama hanyar Dandume a motar haya bayan
ya rufe dakinsa dake BQ na gidansu.
​A ranar Safiyya na gida tazo yin hutun
karshen mako, tunda bata da lecture ranar
Juma’ah tun sassafe ta kamo hanya ta taho
gida, kasancewar a Zarian tana zama ne a
hannun Antinta Dije dake aure a Tudun
Wadar Zaria. To kusan duk bayan sati biyu
zata taho Katsina a ranar Juma’ah, ta dawo
Zaria Lahadi da yamma.
Zayyan koda kuskure bai gaya mata a
wannan satin zai zo ganin mahaifinta ba.
Don haka ita kanta bata san da zuwansa ba
ko alama. Tama manta da zancen da sukayi
dashi kwanaki uku da suka gabata. Tun daga zauren farko da ya iso
Safiyyah ta shaki wani kamshin turare data
yiwa farin sani amma ko kusa bata kawo shi
bane a zauren gidansu, har cikin gidansu
turaren Zayyan ne mai dadin kamshi na
Ultraviolet (Paco Rabanne), Zayyan Bello
ya iso gidan ne ta hanyar bin adireshin da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Safiyya ta kwatanta masa tun daga tashar
Dandume aka dauko shi a babur har kofar
gidan, don haka bai sha wahalar samun
gidan Alaramma Usman Ladan ba.
Kasancewar mahaifinsu Safiyya
sananne ne kuma fitaccen malamin addini a
ciki da wajen garin Dandume, don haka
Zayyan yana sauka a tasha yayi tambaya sai
aka hadashi da mai babur ya dauko shi, bai
sauke shi a ko’ina ba sai kofar gidansu
Safiyyah.
​Da yake yammaci ne na Juma’ah
magidanta na unguwar ya tarar tare da
Malam din, suna daukar karatun yammacin
Juma’a yadda suka saba, kowanne
magidanci da irin littafin da Malam yake
karantar da shi. Zayyan sai ya shige cikin
daliban malam masu daukar karatu ya
zauna ya saje dasu abinsa, duk da shine
kadai yaro matashi a cikinsu, saika rantse
dalibin malam ne saboda yadda ya nutsu
yana sauraren karatun da Malam ke
badawa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Malam na lura da bakuwar fuskar, mai
zubin kyawun fulanin Rumah daya cakude
da kamannin ‘yan Rafindadi ma’abociyar
kuruciya a cikinsu, ya ga kuma shi bashi da
littafi a gabansa amma ya tattara
hankalinsa ya nutsu yana sauraronsu.
Hakan yasa lokaci zuwa lokaci Malam na
daga ido yana kallonsa yana cigaba da bada
karatu. Bai kula shi ba, har sai da ya gama
da dalibansa gabadaya.
A karshe aka yi tamabayoyi akan
darussa daban daban da aka karantar,
sannan aka yi addu’a ga iyali da al’ummar
musulmi da kasar bakidaya, aka shafa tare,
yadda Malam da dalibansa suka saba
kullum, kowa ya soma kokarin saka
takalminshi don barin zauren gidan
Mallam.
Shi kam Malam har lokacin yana
zaune akan buzunsa yana musabihar
sallama da dalibai masu ficewa, Zayyan
yana zaune gefe a inda yake tun shigowarsa,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

bai yi niyyar tashi ya karasa gaban Malam
ba, kuma bashida niyyar tafiya.
Ya rasa ta ina zai fara, gabatar da kan
nasa ko gaida Mallam din? Kamar yadda
Safiyyah ta gaya masa ko waye Babanta,
yaga har fiyeda hakan, yaga dattaku da
tarin ilmin addini, don gabadaya kamilin
dattijon Malam Usman wanda fuskarsa ke
cike da farin gemu zagaye da farin saje yayi
masa kwarjinin da ya hana shi ko motsi. A
hakan kuma duk da alamun tsufa mai
nagarta dake tareda Mallam, wanda bai yi
yawan da za’a kira shi tsoho can ba, sai
farin gemun da ya nuna shekaru sun tura,
duk da hakan Alaramma yana dan diban
kama da kyakkyawar diyarsa Safiyyah
sosai.
Har saida Malam ya gaji da
sauraronsa yayi magana don yana so ya
shiga cikin gida, yace dashi cikin
mutuntawa da tausasawa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

“Samari, ina fatan lafiya? Ko zan san
daga ina kake? Ban wanye da kai sosai ba,
kuma naga kai baka dauki karatu ba”.
​Zayyan ya muskuta ya gurfana gaban
Mallam, kamar mai neman gafara, yayi ta
maza kansa a sunkuye cikin kunya yace,
“Allah gafarta Mallam ni Danka ne,
sunana Zayyan Bello, nazo daga unguwar
Rafindadi ta nan cikin Katsina, musamman
don in gaisheku in samu albarkarku, in
kuma gabatar da kaina a matsayin mai So
da kauna ga irinku dana tsinta a jami’a mai
albarka, wato diyar wajenku Safiyyah,
wanda nake fatan ya kaimu ga zama abu
guda, cikin yarda da amincewar ku, da
sanya albarkar ku.
Idan Mallam yayi min izni, ina so na
saka kai ga fara neman aurenta”.
Ya kara dukar da kai cikin dar-dar, na
fargabar amsar da zai samu daga dattijon.
​Malam Usman ya dubi Zayyan wanda
kansa ke sunkuye, tsantsar hankali da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ladabin da ya nuna masa, da nutsuwar dake
tattare da zancensa, sannan appearance
dinsa bai nuna duniyanci ba, a’ah
appearance ne na samari masu tarbiyya da
kula da addini ya gani a tare da Zayyan,
sune kuma abinda suka dauki hankalinsa
matuka akan yaron, suka canza tsohon
tunaninsa nan da nan suka juya kudirin
daya dade dashi a ransa bai taba gayawa
kowa ba.
Ga yaron da kyawun fuska dana kirar
jiki irin na zaratan mazan Rafindadi son
kowa. Masha Allah dashi.
​Mallam ya nisa sannan yace “samari na
ji bayanin ka, madallah da hankali irin
naka da baka tare Safiyyah a hanya da
maganar soyayya ba, a’ah sai kayi tunanin
ka zo gare ni, ni mahaifinta ka nemi iznina. Wannan ya nunamin kalar tarbiyyarka.
Da wannan halin kwarai daka nuna na
ladabi da sanin girman iyaye, ni kuma na
baka iznin ka dinga zuwa ganin Safiyyah
sau daya a sati, idan ta zo nan gida hutun

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

karshen mako da take zuwa har ku daidata
kanku.
Samari ban yarda ka dinga tareta a
wurin karatunta ba, yin hakan karya
dokata ne, sai a nan gidansu kadai,
kodayake ta kan yi sati biyu bata zo ba,
amma dai in har ta zo gida, na yarje maka
ka dinga zuwa wajenta, anan zauren na
yarda ku dinga zantawa, idan kuka daidaita
kanku na kuma gamsu da nasabarka, to ni
bani da abin cewa sai binku da kyakkyawar
addu’a da fatan alkhairi”.
​Dattakun mahaifin Safiyyah da wannan
tsaftatattar Malanta da ya gani mai girma,
ya kara masa kaimi da ninkin son hada iri
da mahaifin Safiyyah.
Don haka a ranar bai ko nemi ganin
Safiyyah dake cikin gidan ba, bayan sun
gama magana da Alaramma Usman sai
kawai ya juyo gida cike da wani irin farin
ciki, da doki da zumudi mai yawan gaske,
ya isa gidan iyayensa a Rafindadi. Ya san

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

daga Baba har Mama zasu yi farin ciki da
irin gidan daya nemo aure.
​**** **** ****
​ WANENE ZAYYAN?

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

T

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

unaninsa ya mika ya tafi ga ainahin
asalinsa, tushensa da tarihin iyayensa.
Iyayensa duka Katsinawan Dikko ne
na asali, gidan mahaifinsa babban gida ne
ginin zamani, yana nan daga farkon
shigarka shiyyar Rafindadi, wanda a yanzu
ya zama ‘landmark’ na kwatancen kowanne
gida a unguwar, misali da ka ce “layin gidan
Bello Rafindadi” ko yaro karami zai nuna
maka.
​Mahaifinsa Arch. Bello dan asalin
shiyyar Rafindadi ne, gabansa da bayansa
can aka haifeshi, iyayensu da kakanninsu
sune tushen kafa/assasa Rafindadi a
Charanchi. Gidan Bello Rafindadi ya fita dabam ne
a unguwar kasancewar yafi duk wani gida a
unguwar girma da fadi da daukar hankali,
kai har ma da kyawun tsarin gini, wanda
akayi bisa doron ilmin abin, don hatta ginin
gidan, Prof. Bello Rafindadi shi da kansa ya
zauna ya zana ya tsara ya kuma gina abinsa

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

daidai da yadda yake so, kuma daidai da
yawan ‘size’ din iyalinsa.
Tsohon dan bokon da a halin yanzu
yayi ritaya. A can baya kafin ya mallaki
wannan gidan da suke ciki shida iyalinsa
suna zaune a karamin gidansa na gado duk
a unguwar ta Rafindadi. ​Arch. (Prof.) Bello Rafindadi ya rike
mukamai iri-iri a jami’o’in arewa, mukami
na karshe da Baba Bello ya rike shine na
“Chancellor” a jami’ar Umaru Musa ‘Yar
Aduwa, Katsina. A lokacin nan da Zayyan ya gano
Safiyyah, Baba Bello bai jima da yin ritaya
daga aikin gwamnati ba.
Bayan ritayarsa, Baba Bello bai zauna
a gida ba kamar sauran retirees, don har
lokacin da sauran karfinsa da koshin lafiya,
in ka ganshi ma bazaka yi tsammanin
yanada shekarunsa ba sabida yadda yake
kula da lafiyarsa, yana barin koyarwar
jami’a sai ya koma kacokam ga harkar

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

karbar kwangilar gini data zana gidaje,
ginin ma’aikatu da ginin Estates ga
gwamnati.
A hankali ya soma samun kwangila
sosai daga gwamnatin tarayya da
gwamnatin jihar Katsina, bisa taimakon
abokinsa amininsa tun na kuruciya kuma
ubangidansa a harkar Zane da gini, wanda
shi ya tsunduma shi a harkar kwangilar
gine-gine, kuma shi yake taimaka masa
wajen samun wadannan kwangilolin, wato
Alhaji Murtala Masari.
Bada jimawa sunan Baba Bello ya kara
fita a Katsina a matsayin babban contractor
na gine-gine da zane-zane ga gwamnatin
jiha data tarayya.
Arch. Bello da maidakinsa Hajiya
Fatima, wadda kowa yake kira da “Mama
Fatu”, suna tare tun aurensu na saurayi da
budurwa, duk wani fadi tashin rayuwa na
Baba ya sameshi ne tareda Mama Fatu.
Haihuwarsu ta farko sun fara ne da
haihuwar yara mata har biyu, kafin su

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

samu haihuwar Zayyan a matsayin namiji
na farko, kuma Da na uku a gidansu.
Babbar Yayarsu Zayyan Yaya
Zubaidah tana aure ne a garin Batsari, sai
Yaya Zubaina ita kuma a Kano take aure.
Zaituna da Zahra da Hatoon ‘yammatan
Mama duka suna gaban ta, Zaitoon da
Zahra suna jami’ar Umaru Musa, a mataki
da tsangaya daban-daban yayinda autar
Mama Hatoon take ajin karshe a
sakandiren ‘yammata ta FGGC Gusau.
​Shine Da na uku kenan a gidansu,
wanda ya biyo ‘ya’ya mata biyu a haihuwa,
uku kuma suka rufa masa baya shikuma.
Mama Fatu sautari in tana hira da
manyan kawayenta zaka ji tana fadin Baffa
wato (Zayyan) ya iya zama da mata, don
cikinsu aka haifeshi, cikinsu ya tashi, ya
san halinsu ya san rauninsu, yana yawan
tausaya musu”. Wani Zubin kuma Mama kan ce “ko
wacece tayi sa’ar zama matar Baffa ta huta.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Don zata ji dadin zama da shi, ya iya kula
da mata tun yana yaro. A cewar Mama da
wuya ya zama mijin mace daya, wato bazai
iya zama da mace daya ba, don ya riga ya
saba da zama da mata da yawa. Wannan
hasashen Mama ne a matsayinta na Uwa,
domin hakika Zayyan yanason sisters
dinshi, yana tarairayar bukatun ‘yan
uwansa mata fiyeda komai. Duk wani aiki
mai wahala na kitchen ma baya barinsu
suyi, shi yake karba yayi mata, daga yayyen
nasa har kannen nasa sunada matsayi mai
girma a gunsa.
Ya zamanto tun daga kan Hatoon
Mama Fatu bata sake ko batan wata ba,
gashi Hatoon nada shekaru 18 a halin
yanzu.
Tun fil azal a bayyane yake ga kowa
cewa Baba Bello na matukar son Mama
Fatu. ‘Yar lelen shi ce ta ko’ina, yana ji da
Mama Fatu ya tsoka daya a miya, bai taba
tunanin yi mata kishiya ba kuma bai hada

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

matsayinta dana kowacce mace a gurinshi
ba.
Mata irin Mama ake kira shalelen
maigida, bata laifi a gun Baba Bello, saidai
kuskure, wanda yake mata uzurin shi komai
girmansa a koda yaushe.
Baba baya yiwa Mama iyaka da duk
abinda ya mallaka. Komai ya samo nata ne
da ‘ya’yanta, danginsa duka a cewarsu sun
gama sallamawa Haj. Fatu Prof. Bello ta
mallakeshi daga kai har kafa. Kowa dai ya
san yadda matan Rumawan Katsina suke
dauke hankalin mazajensu da yadda suka
iya biyar da mazajensu ta hanyar mulkar
gidajen aurensu tsaf.
To Mama Fatu ta kasance daya daga
cikinsu, irin matannan ne ‘yan hutu wanke
goma tsoma biyar a gidanta, dari bisa dari
mijinta Baba Bello ya tsaya mata saboda
son da yake yi mata yasa ya sakar mata
komai nasa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Kowa ya shaida cewa sun fahimci juna
itada Baba fiyeda duk yadda ake zato, ba
wanda ya isa ya kushe halin Mama a gun
Baba Bello yanzu za iyi hannun riga dashi,
Mama tana da kirki iya kirki, amma fa a
zahiri, Mama Fatu macece mai son kanta
kwarai da son ‘ya’ya har ya wuce kima, in
kana son zaman lafiya da ita kada ka taba
mata ‘ya’yanta ko kace ga laifinsu,
‘ya’yanta sun fi na kowa matsayi a gunta.
Bata da kara sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login