Showing 15001 words to 18000 words out of 46889 words
Chapter 6 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf
keke-da-keke in dai akan
‘ya’yanta ne.
Rayuwa ake ta hakika wadda babu
karya a zaman Baba Bello da Mama Fatu.
In yana dashi ta sani, haka in babu ta sani.
Sun taso tun kuruciyarsu a haka cikin son
juna, ya hadu da Mama ne a garin Rumah
da yaje wani aikin koyarwa na sa-kai
(voluntary teaching) bayan kammala
sakandirensa kafin fitowar admission dinsa
zuwa jami’a. Baba yana matukar tattalin
Mama da tattalin farin cikinta, zamu iya
cewa a takaice Baba Bello shine komai dinta
a duniya.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Saboda Bello ya Aureta tun bata kare
makarantar gaba da firamare ba, amma da
taimakonshi da tsayuwarshi akanta sai da
ta kai har matakin NCE, tana karatun NCE
tana haihuwar yaranta a jejjere. Baba Zayyan baiyi wasa da tarbiyyar
yaranshi ba ko kadan, duk da anso a samu
matsala ta fannin Mama Fatu, ta kasance
me matukar rauni akan tarbiyyarsu saboda
soyayyarsu, don ko Baba ne yake musu fada
wani lokacin zaka ga ranta yana baci,
hancinta yana bubbudewa tana wani irin
canza fuska da cin magani. Baba ya karanci
halin matarshi tsab, don haka sauda dama
baya musu fada a gabanta saidai ya kebe
dasu, duk da baya son bata mata rai yana
yawan tsawatar mata akan sangartar da
take yiwa yaran, musamman auta Hatoon
da ta haifeta a shekarun girma, tana da
rauni akan tarbiyyarta, shiyasa yarinyar ta
tashi a sangarce, don zaki ga wani abun ma
tsoron idon Baba ne yasa takeyi ba tsoron
Mama ba.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ko akan zuwa islamiyyah Baba ya sha
tasa su Zahra a gaba ya kora su da dorina,
ko yaje makarantar yasa a zanesu tsaf,
amma fa a bayan idon Mama, don in sunce
wa Mama sun gaji bazasu je Islamiyya ba,
nan da nan zakaji Mama na fadin “to a
barwa gobe”, in kuwa makara sukayi nan
zaka ji tace bazasu je ba, ba gardin da zai
bugar mata diyoyinta, su zauna a gida suyi
bita su huta sai gobe. Zafin neman ilmi ba
shi ke sawa ayi kudi ko ilmin ba. Ita ai NCE
kawai tayi, me ta rasa a rayuwarta?
Mai cin abin hannun Mama kuwa sai
‘ya’yanta. Mama akwai rowa.
Baba duk inda zai taka a fadin kasar
nan da Mama Fatu yake zuwa, don haka ko
a cikin tsararrakinta zaki ga ita tana da
wayewar kai sosai, sakamakon zama da
rikakken dan boko irin Arch. Bello
Rafindadi, sun yi yawon bude ido ita dashi
sosai a gari-gari a cikin kasar Nijeriya, duk
wani wajen hutawa da buda ido a arewaci
da kudancin kasar nan Baba da Mama sun
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
taka shi. Haka siddan zasu dauki hanya su
tafi suyi sati a Yankari itada Baba in suna
son hutawa daga haniyar gari data
kacaniyar yaransu.
Rufin asiri daidai misali a lokacin Baba
Bello nada shi, kuma mutum ne da bai san
dadin abun hannunsa ba, me son ‘yan
uwanshi da na Mama Fatu, a wurin shi da
danginshi da nata duk daya ne. Gidanshi ya kasance ‘open house’ ga
kowa nata da nashi.
Kai tsaye bazaka ce Mama bata da
kirki ba sai ka zauna da ita, halinta ya
bambanta dana mijinta Baba Bello sosai.
Shi Arch. Bello kowa ya shaideshi da
hakuri, kuma mutum ne mai sanyin hali da
yawan kyauta, ma’abocin tawali’u, mai
faram-faram da rashin nuna bambanci
cikin mu’amalar shi da kowa da ya rabeshi.
Amma wani nakasun Mama Fatu shine,
mace ce mai nuna bambanci tsakanin mai
shi da mara shi cikin mu’amalarta, mai
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
nuna iko da mulki ga wadanda ke
karkashinta da dangin mijinta. Gata da
izza, fadin rai da saurin daukar zafi (saurin
fushi akan ‘ya’ya) bata kara ko kadan a
kansu, tamkar ba bafullatana ba. Har dai in aka zo batun lamarin
Baffanta, nan zaka ga rashin fulako gun
Mama. Mama bata kawaici a kansa sam,
duk yadda kake da Mama kada ka sake
kace ga laifin Baffa, gara ita ka bata mata
daka batawa Baffa, in har kana son zama
lafiya da ita. Kusan haka take behaving
akan auta Hatoon ma. Kada ka sake ka taba
auta in kana son Mama ta cigaba da bude
maka hakoranta.
Wannan yasa Hatoon ta tashi a yarinya
mai shegen ji da kai da tsokanar ‘yan
uwanta, ga yawan shagwaba da yawan raini
ga Yayyenta, da rashin jin maganar kowa
har Maman kuwa, Baba kadai take shakka
a gidan sa Yaya Baffa, sabida Mama ta
daure mata gindi, kowa yazo da korafi akan
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
auta yanzu zata tare mata fadan ta ara ta
yafa.
Mai dan dama-dama a hankali da
cikar tarbiyyah cikin ‘ya’yan Mama Fatu
mata to Yayarshi Zubaina ce, Zubaina ta
kan dade bata zo gida Rafindadi ba, don
mijin ta irin mazan nan ne masu mugun
kulle ga matansu, suka kuma isa dasu. In ka cire Zubaina kafatanin duka
‘yammatan Mama halayenta suka debo.
Yaya Zubaida kuwa ai makwafin Mama
kenan a halayya da dabi’a. Zubaina ce
kadai mai hangen nesa cikinsu saboda mijin
data aura malamin makaranta ne duk ya
canza halin Zubaina zuwa irin wanda
yakeso bayan ya aureta.
Mama ana yawan zugata da cewa
‘ya’yanta mata ai jarin ta ne, tunda Allah
ya bata su kyawawa tamkar ita ta kera
abinta don kyawun sura, wannan yasa
Mama ta dora buri sosai a kansu, da zuwan
aurensu Zahrah, burinta kadai suyi auren
hutu a inda zasu huta itama ta karu, ba irin
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
auren da Baba Bello yayima Zubaidah da
Zubaina ba, suma kuma su Zahran saboda
yawan hudubobin Mama na kada su sake su
kawo mata dan (I love you) ko mai fama da
alli yasa suka tashi da burin sai wanda ya
kama kasa ya tsaya da kafafunsa zasu aura,
wannan yasa har gobe ‘yammatan Mama
babu suna nan zube a gabanta, babu mai
tsayayyen saurayi, kowa yazo Mama zata ce
bai isa ba, me yaci balle ya basu? Gashi dai
har Zaitoon da Zahra sun fara jarrabawar
shiga aji na uku a jami’a yanzu babu
tsayayye.
Mama da ganin ta ka san an zuba kyau
a zamanin ‘yammatanci an kuma yi ruwan
idon samari kafina tsaya akan Bello
Rafindadi, kuma har yanzu in ka dubi
Mama zaka ganta da kyanta da gayunta, ga
koshin lafiya da kuzari, gata da ingarman
jiki, saboda samun kyakkyawar cima da
take yi da kulawa daga Baba Bello, wanda
zai iya kwana da yunwa ita ya bata, kyawun
surarta bai buya ba har yanzu, duk da a
halin yanzu Mama ta baiwa 60 baya.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama tayi aikin koyarwa na lokaci mai
tsaho a babbar makarantar ‘yammata ta
gwamnatin jihar Katsina, bayan ta haifi
auta Hatoon sai ta bar aikin, ta karkata kan
kasuwancin atamfofi da lesika da mayafai
na matan zamani, kuma kasuwancin sai ya
karbi Mama sosai fiyeda koyarwar. Don a
karshe daga shagon cikin gida har ta kai ga
bude shago a kasuwa, na atamfofi da lesika,
inda take harkokin kasuwanci bisa kulawar
ma’aikatanta.
Shi dai ya san babban nakasun
Mamansu Hajiya Fatu, wanda Babansu ya
sha gaya masa baya so, a matsayinsa na da
daya namiji garesu sai ya zama babban
aboki ga Baba wanda yake tattaunawa
dashi akan komai da ya dameshi, Baba ya
sha gaya masa abinda baya so a tareda
Mama shine halinta na raini da take
nunawa ga na kasa da ita, in har ta fika
arziki to kuwa dole zata rainaka, ko daga
kalaminta. Bazata taba hada kafada da kai
ba, wada ‘ya’yanta mata kusan duk sun dau
wannan halin, basu da mai tsawatar musu
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
su ji sai Baba Bello da kansa. Ko shi Zayyan
din in yayi yunkurin ladabtar da kannensa
nan da nan Mama zata taka masa burki.
Zayyan ya sake juyawa wani irin juyi
mara dadi akan makeken ni’imtaccen
gadonsa, sai ya ja numfashi ya sauke a
hankali cikin tunanin sha’anin gidansu, ya
kuma kara da lumshe idanunsa yana mai
fuskantar ceiling. Baya son tuno duk abinda
ya shafi Baba Bello yanzu, domin yana yi
masa fami akan warkakkeen gyambon
rashinsa dake ransa ne, amma ya zama dole
yake tuna Baba da rayuwarshi tare dasu
bakidaya, su kuma dinga dawowa cikin
tunaninsa lokaci zuwa lokaci saboda Baba
Uba ne da babu irinsa a wannan zamanin.
Daga nan Zayyan ya kara nausawa cikin
tunanin da ya samu kansa, duk a kokarinsa
na son nemo adalci ga kansa, da maidakinsa
Nana Safiyyah a daren yau ta hanyar yiwa
kansa (self-judgement and self-evaluation),
bayan tuni aikin gama ya rigada ya gama,
ko yace bakin alkalami ya gama bushewa.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
**** **** ****
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
A
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ranar, abinda ya faru bayan ya dawo daga
Dandume shine, ya dawo gida da farin cikin
amincewar iznin neman auren Safiyya da
mahaifinta Mallam Usman ya bashi, kai
tsaye bai tsaya ko’ina ba sai falon
Mamanshi Haj. Fatu. Yana saka kafa a falon Mama, bakinsa
dauke da sallama cikin doki da kaikayin
baki, da kafafun Hatoon ya fara cin uban
karo a bakin kofa, suka tadiye shi har suka
kusa fadar dashi a kasa. Haushi ya kama shi. Ya juya ya kalleta
da manyan idanunsa, tayi shame-shame a
bakin kofa wai ita tana azumin ramuwa,
lokacin ana gab da shan ruwa, autar Mama
ta kai makura wajen galabaita, don kuwa
azumin ma saida taji wa’azi a radio na
hukuncin marasa ramashi sannan ta fara
ramawa lokacin azumin bana saura kadan
ya kama.
Hatoon ta kusa kayar dashi a kasa
sosai, a fusace yasa kafa ya shureta da karfi,
nan da nan Hatoon ta saka karar kiran
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama, tace da karfi “Mama kizo. Yaya
Baffa na dukana!”
Sai ga Mama ta fito daga daki da sauri
jin sautin kukan Hatoon, kamar wadda
aketa duka, shurinta kawai yayi da kafarsa,
amma ta bare baki tana kukanta na
sangarta mai ban haushi, Mama tana ganin
sa a gaban Hatoon ta ce. “Ha’an! Tunda naji kukan Hatoon
alhalin tana azuminnan da sanyin
yammacinnan na san anci zalinta da
mangaribar fari, kuma ba kowa bane sai
kai Baffana, to juya ka bar min falo, tunda
bani na kiraka ba”. Zayyan bai damu da fadan da Mama ta
rufeshi dashi ba, don inda sabo sun saba,
haka bai ji gargadinta na ya koma inda ya
fito bata gayyatoshi ba, sai ya shigo falon ya
zauna ya harde kafafunsa yana hararar
Hatoon, yace “zaki tashi daga wannan
banzar kwanciyar a bakin kofa, ko sai na
babballaki in yaso kiyimin ihu da hujja?
Yanzun don Allah da kin kayar dani fa?”
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama tace “a’ah fa. Baffa ka san
Allah, tunda dai bamu kira ka ba, kuma ba
maganar arziki ce ta kawo ka ba, to ka
koma inda ka fito ka saurarama Hatoon,
bana son diban albarka akan yarana ka sani
daga kowa har su da kansu kuwa, me ta
tare maka haka kake neman cinyeta?
Ina dalilin wannan tsangwama? Azumi
fa take yi, in baka tausaya mata ba, ai baka
hantareta ka hau shurinta daga shigowarka
ba”.
Ba don Mama bace take maganar
nan, tabbas da ya kaiwa bakin Hatoon
kyakkyawar mahangurbar da zata
kumbura mata bakin, don yana kallonta
tana gatsina baki irin dai wanda ta saba
yiwa yayyenta in taji Mama na tare mata
fada a wurinsu.
Kwafa yayi, yayi shiru ya rabu da ita,
don in ya sake ya tabata zai fuskanci fushin
Mama, haka kawai tasa an gwasale masa
farin cikin da ya zo a cikinsa.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Don haka yace. “Mama kiyi hakuri, ni
ba maganar wannan sakaryar ‘yar taki ce
ta kawo ni ba, in fact, ko me zaki yimin yau
a kan ta bazan ji haushi ba, bazan kuma
wani damu ba, tunda ai na riga da nasan
kinfi sonta a kaina, to na me zan damu don
kin koreni a gabanta?
Ni ranar yau daban take a wajena; ina
cikin matsanancin farin cikin da sakarcin
Hatoon yayi kadan yasa inyi fushi yau.
Mama ta samu wuri ta zauna cikin
rashin kulawa da zancen tace “to yaya
akayi?” Yayi murmushi cikin ‘yar alkunya
da sosa keya kafin yace.
“Mama ni yau nayi gamon alkhairi fah,
irin albarka, tsatson martaba, yau dai Allah
ya nufa na isa ga gidansu “HIJABIE!!!
Na kuma gabatar da kaina ga
mahaifinta”.
Mama na wani irin yamutsa fuska da
baki cikin gatse tace “wacece haka? Wane
irin suna ne Hijabie ni ‘ya su? Sunan yanka
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
ne ko sunan rana ko hijab da ake sakawa
aje masallaci yin sallah?”
Ya sunkui da kai jin abubuwan da
Mama ta zano, kafin yace “Mama Yarinyar
nan mai hijabs da jilbaabs da nake yawan
baki labari ina haduwa da ita a school
Library? Kuma alhamdulillah mahaifinta ya
bani damar fara saka kai ga neman auren
ta”.
Budar bakin Mama Fatu sai cewa tayi
“lallai Baffa ka girma! Ni yau naga abinda
ya girmeni, kai nan har wani aure ka isa
Baffana? Nawa kake? Cewa nake ko 27
Baffa baka kai ga rufawa ba? Tukunnama,
diyar waye a Katsina ita Hijabie din? Ina
nufin WAYE UBANTA?”
Tunda a halin yanzu me ka aje, me
kuma kake dashi da zaka baiwa iyali, aikin
me kake yi da zai rike maka aure?”
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama Fatu ta tambaya da accent
dinta na Katsinawan Rumah. Cikin
balbaleshi da fada da tada jijiyar wuya.
Zayyan saida ya bari Mama ta kai aya,
tunda yasan halin kayarsu, sai ya kwantar
da murya don ya riga ya san halin Mama na
saurin daukar zafi da izgili, cikin lallashi
yace, “ba sunanta Hijabie ba Mama, nine na
saka mata hakan sabida kyawun da Hijab
da jilbab ke mata.
Sunanta Safiyyah, diyar Malam Usman
Dandume, mahaifinta babban Alaramma ne
(Shaihun malamin addini) mai bada
karatun addini ga magidanta da almajirai a
garin Dandume”. Abinda shi bai fahimta ba tun a lokacin
shine; wannan matsayin na mahaifin
Safiyyah da shi yake ganin abin alfahari ne
da bugun kirji wajen zaben abokiyar
rayuwa da yayi, a wurin Mama Fatu shine
first disappointment (sagewar guiwa na
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
farko) data fara samu akan Safiyyahrsa, na
kasancewarta ‘yar malamai, wanda ko kusa
baya cikin tsarinta kuma bai zo cikin
tunaninta ba, na irin surukan data ke burin
hada zuri’a dasu, sannan gata ba ‘yar
manyan ‘yan boko da sukayi shuhura a
bokon ko wasu masu dukiya ba, domin nan
take Mama cewa tayi tun kafin ya gama
rufe bakinsa.
“Hadin gambiza Baffa?! Wannan shi
ake kira hadin gambiza.
Me ya hada dan Furofesa da diyar
alaramma na kan buzu kuma?
Kai Baffana bana son rigima mai lasisi.
Haka kawai inje a tattofe min kai da
laqanquna a rubuceka a minjaye a shanye,
a mallake min kai ko a rabani da kai, kai
kadai dinnan namiji danake dashi a
cikinsu? To bada ni ba gada makabarta. In ka
ganni a lahira kaini aka yi. Kai kenan kwalli
dayan da Allah ya bani a matsayin da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
namiji, maimakon ka kawomin matar da
zan yi alfahari da tinkaho da ita da iyayenta
kai kuma ka samu ta sakawa a gaban mota,
a kara maka karfi, wadda zan dinga zuwa
da ita a gidan biki ina nunawa kawayena a
matsayin surukata, yarinya ‘yar hutu da
za’a cika mana gida da duma-duman ‘royal
furniture’ a dinga bamu kujerar Makkah
duk shekara nida kai, da yayyenka, ba tare
da la'akari da namu samun ba, a kuma
baka gwaggwaban jarin da zaka kafa kanka
kafin ka samu aikin yi, sai ka bige da kawon
diyar gidan alaramma?”.
(A saninsa wannan shine mafarin
rashin kaunar Mama da Safiyyahrsa.
Domin tun ba’a kai ga auro Safiyyah ba,
ba’a kai ga an zauna da ita anga kalar
halinta ba, kasancewarta diyar Alaramma
da yace kadai gidan da ba mamora (ta
bakin Mama), yasa Mama tun tashin farko
ta tsani zancen aurenta, ta kuma ki jinin
asalinta, ta gwasile shi nan take, ta sassage
masa gwuiwa a kanta.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Haka Mama ta cigaba da sakin
maganganu na ba’a da raini da shagube ga
zabinsa, irin wadanda zasu sa shi kansa yaji
Safiyyah ba ajin aurensa bace, amma ina!
Baffan Mama ya riga ya kamu iya wuya,
maimakon hakan sai ji yake Safiyyah tana
kara kawatuwa da kwanciya masa a rai,
tana kara burgeshi tareda kara nabba’a a
birnin ransa.
Hatoon dake gefe shame-shame a
kwance, amma tsaf ta kafa kunnenta a
kansu tana sauraronsu shi da Mama, tun
tana gintse dariya da ganin yadda Yaya
Baffa ya muzanta a gaban Mama, har a
karshe tace me zatayi ba fashewa da
shaqiyyar dariya ba! Ganin Yaya Baffa
yanata karkarwa don Mama tace diyar
Alaramma ba cikin zuri’arta ba.
Hatoon bata san sanda ta dinga tilliqa
dariya ba harda kwarewa, jin Mama na
cigaba da sakin maganganu na wulakanci
da nuna rashin aji (class) ga zabin da yayi.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Yana fama da kalaman Mama yana
kuma kara fusata da jin yadda Hatoon ke
babbaka masa dariyar shakiyanci daga
kwance, ya san jinsu take da kunne daya,
ita Hatoon abinda ya bata dariya da Mama
tace wai “diyar Alaramma ko? To ba dai a
gidana ba Baffa, haka kawai a saka min
sunanka a katon mimi (minjaye) a
shanyemin kanka tas, azo ana ce min saidai
in haifi