Showing 33001 words to 36000 words out of 46889 words
Chapter 12 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf
al’amarinsa, bazata
barwa wata mace kuma ‘yar talakawa da ta
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
zo daga sama tayi yadda taga dama da
rayuwarshi ba.
Idon Mama ya koma kan amarya
Safiyyah. Duk inda Zayyan ya cire kafa nan
take mayas da tata a falon, cikin yanayi na
nuna bakunta da surukuta.
To da yake Mama bata zaci zuwanta a
lokacin ba, yasata binta da kallo tana
shigowa, da takunta na nutsuwa kanta a
kasa. Ta lura wani kallon kurilla Maman
Zayyan take mata. Mama ta tsaida idonta a kanta tana
kallon ‘Hijabhie’ din Zayyan dinta, wato
Safiyyah Usman Dandume. Tun daga kallo
na farko ta hango macen kwarai, amma son
zuciya daya lullubeta da kyashin
kasancewata diyar talakawa yasa taji kawai
daga gani na farko Safiyyah bata yi mata
ba. kamar yadda tun farkon fara zancen
aurenta ma zancen bai mata ba.
Abun mamaki Mama ta kasa boye
haka a kan fuskarta, don sai yamutsa fuska
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
take yi kamar taga abun kyama. Kwarjinin
Safiyyah irinna cikar tarbiyyah da riko da
addini yaso ya dan rikita Mama, wadda a
baya take mata kallon raini tun kafin ta
ganta, just because an ce diyar Alaramma
ce, sai ba haka ta tsammaci ganinta ba,
wato dai ya zama cewa Safiyyah din ganinta
yafi jinta!
Ta so ganinta typical bakauyiyar
Dandume, yadda zata ji dadin raina mata
wayau. Amma ina! Wane mutum! Safiyyah
dai girman kauye ce amma bata da Ruwan
kauyawa, sannan ta wuce ido ya kalla ya
raina domin Safiyyah ta sha rubutun
kwarjini a gidansu ta koshi. Ashe ba duka
mazauna kauye keda appearace na
kauyawa ba inji Mama.
Sai tafi mata kama da kalar matan
manya ba yara ‘yan makaranta irin danta
Zayyan ba; she is looking extremely classy, a
cikin hijabin.
Yawanci mata masu tsayi da kyawun
surar fuska dana kirar jiki irinna Safiyyah
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
basu cika yawa a arewa ba, duk da za’a iya
cewa Safiyyah bata da zubin kalar
'yammatan da Mama ta saba gani tareda
‘ya’yanta, wato Safiyyah ba ‘yar gayu da
son kwalisa bace, kwatankwacin ‘ya’yanta
su Zaitoon da ire-iren kawayensu da ta sani,
ma'abota kawar zamani irinna ‘ya’yan
hutu, wadanda iyayensu wasu ne a Katsina,
sun kuma daure musu gindin yin shiga mai
tsada ta kece raini, ire-iren ‘yammatan da
ta so ace Zayyan ya aura kenan, amma
kuma ita Safiyyah nutsuwarta da kamewa,
da innocent looks dinta da zubin halittarta
na Alkyabbar mata yasa duk ta fisu
kwarjini da kamala.
Ko makiyinta in ya ganta a lokacin,
da irin shigar mutunci da tayi tazo gaban
surukanta zai ce “Safiyyah is decent and
classy”.
Duk da fatarta ba mai haske bace can,
yatsun hannunta duk sun sha adon jan lalle
na amarci har na kafarta, wanda bai gama
fita ba har lokacin. Domin kumshi ne mai
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
nagarta aka yi mata na aure. Kyakkyawar
round face (zagayayyar fuskarta) kawai
kake iya gani a jikinta da zara-zaran yatsun
hannunta, bata shafawa fuskarta komai ba
bayan ‘lip gloss’ data dan shafa kadan a
fatar bakinta mai sulbi kamar yankan reza,
zaka gane ita Safiyyah mai yalwar sumar
kai ce (mai yawan gashin kai) ta hanyar
tudun dankwalinta ta baya, nata tudun
kallabin natural ne ba irin wanda ake kira a
cuci samari bane.
Koko yace rashin haduwar jini na
farat daya shi ya kara afkuwa physically a
haduwar Sophie da Mama, tsakanin Mama
da surukarta Safiyyah.
Don sam Mama har ranta bata yi
farin ciki da zuwan Safiyyah gabanta ba, ta
so ace shikadai ma ya zo, su sake su wuni
hira abinsu.
Safiyyah tsugunne a gaban Mama
Fatu, tana gaisheta da dan sassarfar
halshenta na halitta, mai hade da in’ina
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
(stammering) wadda bata zama (worse) din
da za’a kasa gane me take cewa ba.
Mama data gane Safiyyah
(stammerer) ce sai ta kama baki cikin
kakabi tace.
“Allah Waahidun Ahadun! Yanzu
Baffana, ka rasa wadda zaka auro duk fadin
Katsina da wajenta sai mai tsamin baki da
in’ina haka?”
Bashi Zayyan ne kadai yaji kunyar
kalaman Mama ba, hatta Baba da ya ji
abinda Mama Fatu ke furtawa saida ya
kware da Ruwan da ya kurba a tambulan.
Yayi saurin kallon Safiyyah din, da
addu’ar Allah yasa bata ji ba, duk da ya san
addu’ar bata karbu ba, saboda Mama da
karfi ta fada ba sakayawa, sosai Baba ya ji
babu dadi hadi da kunya na wannan
kalaman baran-barama na matarsa Mama
Fatu akan surukarsu, a dai ranar
haduwarta ta farko da surukar tata.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Wadanda are more of cin fuska. He
felt embarrassed har fiye da Zayyan da
Safiyyan.
Duk da Safiyyah taji ta muzanta da
abinda Mama tace a kan yanayin
maganarta, amma ko a fuskarta bazaka ga
rashin jin dadin ba. Ta shanye hakan tsaf da
kyakkyawan murmushi. Saidai ta kasa kara
cewa komai bayan gaisuwar data yiwa
Mama, wadda Mama Fatu bata ko kai ga
amsawa ba har lokacin saboda takaicin ya
dauko musu stammerer. Don da farko
Safiyyah tayi niyyar tambayar Mama
lafiyar ‘yammatanta wato kannen Zayyan
su Hatoon, Zaitoon da Zahrah da bata gani
ba, amma sai taji bakinta ya dinke,
gwiwarta tayi sanyi kalau da yunkurin sake
magana kuma, tunda yanayin halittar
maganarta bata yiwa Mama dadin ji ba.…
Baba kam sai yayi funfurus dashi
kamar bai ji Mama ba, ya zama kamar
wani wanda baya jin yaren harshen Hausa,
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
yayi kamar bai fahimci me Mama tace da
Baffa din akan matarsa ba, sai ya fara,
"maraba lale da Nana Safiyyah, yau
gidan namu nada manyan baki, tunda
amarya Nana Safiyyah ce tazo da kanta ba
sako ba!”.
Ko dama can Baba Bello mutum ne
mai yawan raha ga iyalinsa. Mai saukin kai
a cikinsu. Nan da nan yasa Safiyyah ta kara
fadada murmushinta, ta duka ta gaisheshi
shima, tanata kokarin adjusting in’inar,
kada shima Baban Zayyan yace irin abinda
Mama tace akan in’inarta.
Sai ta baiwa Baba Bello tausayi sosai.
Yace yaya Zaria, bude baki Safiyyah muyi
hira kinji? Yaya karatun naku da kuma
wajensu Malam da Ammi a Dandume?
Ai kuwa Safiyyah taji dadi, ta
saketana amsawa with ease. Baba ya
tambayeta lafiyar sauran kannenta duka,
Safiyyah na amsawa da lafiya kalau suke
Baba. Baba Bello yayi duk yadda zaiyi cikin
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
hikima yake janta da hira (just to make
Safiyyah comfortable in his home) daga cin
fuskar da Mama tayi mata.
Zayyan kuma sai ya zama dan kallo a
hirar Baba da diyarsa Sophie, don Baba
baya ko sako shi cikin hirarsu, musamman
da yaji cewa Sophie ma dalibarsu ce wato
Architect student ce. Sai hirarsu tayi tsayi,
yana son sanin meye plans dinta bayan
gama karatun? Aikin gwamnati ko private
zane-zane?
Budar bakin Safiyyah sai cewa tayi,
tafi so ta zauna agida ta kula da yara, in
yaso ta dinga yin nata profession din daga
gida tareda Zayyan, wato tanaso ta dinga
yin nata Zanen a gida tana baiwa Zayyan,
su hadu su tara idea akai, su kayata shi. Ta
kuma dinga zama mataimakiyarsa ta cikin
gida tunda duk abu guda suke karanta.
Wannan zabi na Safiyyah ya burge
Baba Bello sosai, don da wuya ka samu
mace mai zurfin ilmin da zata ce maka wai
zata zauna a gida ta kula da yara, da
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
taimakawa mijinta, hakan yasa ya jinjinawa
integrity dinta cikin ransa.
Mama dai nata sauraren in’inar
Safiyyah daga gefe tana dada harzuka, a
kasan ranta tana ta maimaita mitar Zayyan
ya rasa wadda zai kwaso musu sai mai fama
da stammering, kamar ance kyawawan mata
masu kyawun lafazi a Katsina da kewaye
sun kare???
Saboda kokarin Baba na kyautatawa
da farantawa ga Safiyyah, yasa har suka
tashi tahowa gidansu a Zaria Safiyyah bata
fito gidansu Zayyan da bacin rai ba sam,
duk da Mama bata kara kula ta ba, ta dai sa
mai aiki ta bata abinci, Safiyyah bata ko ci
ba, don sai da shimfidar fuska kake iya cin
abinci, Zayyan kuma yace tare zasu ci a
gaban Mama, hakan yasa ta kasa ci don
tana ganin Mama na satar harararta, saida
Baffanta kadai take tadin hira. Shi kuma sai
yayi ta jefo Safiyyah cikin hirar, ita kuma
saidai tace eh ko a’ah.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Safiyyah bata kawo komai a ranta ba
na basar da ita da Mama tayi, amma a
ranta tace ga dukkan alamu bata samu
karbuwa gun Maman Zayyan ba, ta fahimci
halin Baba Bello Habibinta yabi ya dauke
gabadaya, na karrama dan adam ko yaya
yake bana Mamanshi mai fadin rai ba.
Ba wata far’a da ta samu daga Mama,
balle wata kulawa ta karbar bako.
Har suka bar gidan Mama bata
maida hankali akan Safiyyah ba, bata jata a
jikinta don ta sake da ita ba, bata nuna
mata kowacce irin kulawa da kauna ta
surukuwa ba. bata bata fuskar da zata ko
iya ce mata sannu bayan gaisuwa ba.
Wannan abu bai yiwa Zayyan dadi ba, ya
kuma sosa ran Safiyyah daga bisani, ganin
kirikiri Mama ta nuna Zayyan ne kawai
nata, kuma dashi kadai take maraba. Ita
Safiyyah bata san halin Mama bane rashin
kara akan yaranta.
Amma ko a fuska bazaka gane bata ji
dadin ba. kullum Ammi na nuna musu su
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
zama masu shanye facial expression dinsu
da hadiye rashin jin dadinsu akan duk wani
unfavorable treatment da wani yayi musu
wanda bai yi musu ba.
Ammi na yawan cewa ba kowa ne zai
so ka a rayuwa ba. Tunda kuma ga Baba
Bello da kansa yanata haba-haba da ita
name zata damu kanta.
Sai yamma suka bar Rafindadi, suka
kama hanyar komawa Zaria. Babu tsaraba
kota tsinke da Mama tayi mata. Tsarabar
da ita ta kawo mata kuwa Mama ba godi
bare an gode, tace da Ankudi (mai aikinta)
ta kai kitchen. Ranar nan da Baba ya koma gida
daga sallahr Isha’i ya samu Mama Fatu har
dakin barcinta, Mama ta sha fada, wanda
da wuya kaji Baba Zayyan nayi mata irin
shi, akan abinda ta fada akan in’inar
Safiyyah kuma a gabanta, daga bisani
wa'azi da nasiha Baba ya maida fadan, yace
“ba’a yiwa Allah izgili akan halittarsa, ta
koyi iya rike magana a bakinta don rike
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
girmanta, ba kowacce magana ce ta zo
ranka akan halittar wani zaka furta masa
ba, yace ta dinga tauna magana kafin ta
furta don gujewa tozarta dan adam da ci
masa fuska akan halittarsa, kalami mai dadi
ma ga musulmi kawai sadaqah ne. Cin
fuska akan nakasunsa kuwa zalinci ne ga
zuciyarsa.
Yace yanzu ina amfanin abinda tace
da Safiyyah a matsayinta na babba mai
hankali kuma Uwa agaresu wadda ta san
cewa in’ina halitta ce ta Allah?
Baba ya furzar da numfashi cikin
bacin rai, ya dubi Mama yace “Annabin
Allah ma yayi in’ina (Musa Alaihissalam)
na tabbata kinsan hakan a tarihin Annabi
Musa. Tashin farko a haduwarku ta farko
kin zubar da girmanki ga surukarki, matar
tilon danki. Wannan cin fuska ne kikayima
danki ba ita ba, tunda shi kika bari da ji
miki kunyar”.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama zancen ya fara isarta, ta shuno
baki gaba, tana son cewa wani abu sai ta
fasa, ta daure bata ce komai ba dai, har
Baba Bello ya gama fadansa da
bambaminsa da wa’azinsa da nasiharsa ya
gaji ya kyaleta. Koda suka kama hanyar komawa
gidansu a Zaria, shida ita duk suna bayan
motar hayar data kawo su Katsina sunyi
shiru, direban wanda shi yazo don ya
maidasu gida yanata sharara gudu dasu
bisa titi, a zaune suke dab da juna,
hannunsa cikin na Safiyyah.
Zayyan sai ya samu bakinsa da baima
Safiyyah hakuri kan abinda ya faru don ya
zama restless da ganin shirunta, sai yake
tunanin ko akan kalamin bakin Mama Fatu
ne yasa ta rage magana, ya damu sosai har
fiye da kima, ji yake kamar shi yayi mata
gorin.
Safiyyah hakurin da Zayyan yake
bata sai taji yafi abinda Mama tayi mata
nauyi. Saboda Mama ai Mamansu ce su
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
duka, ba abinda zata yi ko zata ce da zai
bata mata rai.
Shi kuma wannan Zayyan mijinta ne,
wanda Allah ya dora sama da ita, amma ya
kwantar da kai irin haka yana bata hakuri
akan laifin da bai aikata ba.
Sai tayi murmushin da zai kwantar da
hankalinsa ta ce. Shirun daka ga nayi ba
akan wannan maganar bane, tunanin su
Ammi da kewar su Rayyah nake yi.
Yanzu Habibi me aka yi da zaka yi ta
bani hakuri haka? Mama Mamana ce fa!
Ai gaskiyar Mama ne inada sassarfan
harshen. Nima na sani, kowa ma ya sani,
kuma ba so nake yi ba nima, nayi-nayi in
bari tun ina karama na kasa, nima bana
sonta ko kadan (in-inar), ina addu’a Allah
yasa watarana in bari…". Sai taji hawaye
ya taho mata. Ta sunkuyar da kai ido fal
kwallah don bata so ya gani, tace "this is
nothing to worry about Habiby! Please stop
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
it, hakurin da kake bani shi yafi komai
karya min zuciya”.
Zayyan yayi maza ya rungumota
jikinsa, (yama manta a motar haya suke),
yasa hannu ya dago habarta, yayi kokarin
saka idanunsa cikin na Safiyya, duk da tana
kokarin kaucewa haduwar kwayan
idanunsu saida yasan yadda yayi ya sarke
idanunsa cikin nata, tuni ya zuba mata
dafin dake cikin haduwar ‘eye contact’
dinsu, wanda ita kadai tasan irin tasirin da
suke mata cikin ruhi da gangar jikinta,
narka mata zuciya suke, su zuba mata
dalmar soyayyarsa. Zayyan yace cikin
shauki.
"My Dear Safiyyah, akwai abinda
baki sani ba, something you don't know ni
kuma bazan gaji da gaya miki shi ba.
Tsamin bakin (as Mama called it)
shine abu na biyu da ya fara inviting
zuciyata zuwa gareki, I love your
stammering! Kema kinsan haka. Ni son
in’inar nake. Dadi take yi min.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Wani lokacin har imitating dinta nake
yi nikadai kafin na mallake ki a gefena
Sophie.
Idan shaukinki ya dameni cikin dare
sai in yi ta kwaikwayon in’inar ina debewa
kaina kewarki, kafin Allah ya dube ni da
rahmarsa ya bani ke Safiyyahhh!".
Safiyyah ta dago da mamaki tana
kallonsa yace "yes, it's the sweetest voice I
ever heard. It sounds so special saboda zaki
ga ba kowa Allah yake yiwa baiwa da irinta
ba". Safiyyah tayi murmushi sosai har
saida barin kumatunta na hagu ya lotsa
sosai, feeling highly proud of her voice today,
(cikin jin alfahari da muryar tata yau),
tunda har muryar ta na yiwa masoyi
Zayyan dadi, a hakan yadda take, to ta
yarda don Allah kada ta yiwa kowa dadi.
Da wadannan kyawawan kalamai
Zayyan ya lallashi Safiyyah, suka rufe
chapter din in’inarta da Mama bata so,
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
basu kara tada zancen nan ba har inda yau
ke motsi.
**** **** ****
Safiyyah na level two a lokacin da
sukayi aure. Kullum tare suke shiga
makaranta in ta rigashi tashi ta jirashi har
sai ya tashi ya goyota a bayan LIFAN dinsa
su dawo gida tare. Rayuwar sa da Safiyyah ta cigaba da
tafiya a haka gwanin ban sha’awa ga duk
wanda ke gefensu, zaka shaida cewa rayuwar
aurensu cike take da so da kauna na hakika
zallah, wanda babu karya ba kuma kwadayin
duniya a cikinsa, suna masu yawan
tausayawa juna, da taimakekeniya a
tsakaninsu, ta fannin karatu da hidimar gida,
har zuwa shigar Safiyyah level three. Zayyan
shi ya cigaba da daukar nauyin karatunta
bayan aurensu.
Da yawan abokan karatun Safiyyah
basu san ma tana da aure ba, balle alaqar
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
aure dake tsakaninta da Assistant Lecturer
mai tashe a tsangayar zane-zane; Yaya
Brainlliant Architect, Zayyan Bello
Rafindadi.
Saboda babu wata alama da zata nuna
maka cewa Sophie tayi aure yanzu, tunda
dama kowa ya riga ya santa ne da shigarta ta
kamala wato hijab ko jilbab da kowa ya santa
cikinsu. Da wannan kalar ‘dressing’ din ta
riga ta suffantu, tun shigarta jami’ar
Ahmadu Bello. To da tayi aure ma ba abinda
ta canza illa shi Zayyan dake koraffin Hijabin
ya daina burgeshi yanzu, don har a cikin gida
fama yake da ita akan ta saka masa suttura
irin wadda yake sayo mata ya kawo mata,
amma saidai ta boyesu a kasan akwati. In
kayan kwalliya ya sayo ya kawo mata kuwa
don tayi masa kwalliya a gida to su Rayyah
da Sabah da Rayha take aikewa Dandume.
Har rannan wani coursemate dinta
mai karambani da shishshigi mai suna
Balarabe ya kasa shiru yake tambayarta,
shin ko Zayyan Rafindadi biological
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Yayanta ne? Don yaga suna tafiya gida tare
yanzu kullum, yana goyonta akan Lifan
dinsa.
Ko kusa bai kawo aure a tsakaninsu
ba, sabida Zayyan nada iya taku, baya bada
wata kafa da zaka gane akwai alaqar aure
tsakaninsa da Safiyyah Dandume, sai ta
karatu a makaranta. Ita kanta a makaranta “Malam” take
kiransa, sai sun dawo gida zaka ji ya koma
“Habiby”.
Safiyyah tayi murmushi tace da dan
ajinsu Balarabe "eh, Mallam Zayyan
Yayanta ne, kuma Malaminta ne".
Bata kuma kara tofa komai akai
bayan wannan ba, aka wuce wurin, wato
aka bar zancen a haka. Amma shi dai
Balarabe ya digawa abuna yar tambaya,
don in ba Yayanta bane a kamala irin tata,
bazata yarda ta dinga hawa bayan Lifan
dinsa ba
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Don haka take karatunta lafiya ba
idon 'yan ajinsu a kanta, musamman da
Zayyan din baya daukar 'yan level three.
Level 1&2 yake