Showing 39001 words to 42000 words out of 46889 words
Chapter 14 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf
rannan yayiwa
magana cikin sirri cewa “tayi hakuri da
Mama, ta kasance mai hakuri da kowa
zama ko alaqa ya hadata dashi”.
Saboda tun wancan fadan da ya taba yi
mata akan Safiyyah din, lokacin da taci
fuskarta a gabansa, da tace Zayyan ya rasa
wadda zai dauko musu sai diyar
Alarammomi mai tsamin baki (stammerer). Baba da yayi mata fada batace komai
ba, sai lokacin kwanciya barcinsu tayi masa
martani, inda tace “ta lura yana son
Safiyyah dinnan da yawa. Ita kuma bazata
so su dinga samun matsala shi da ita akan
suruka ba”. Tun daga lokacin yake
kiyayewa da yi mata magana akan Safiyyah
kada ya sayo mata tsana a wurinta.
Haka duk abubuwan dake faruwa a
lokacin jinyarsa yana lura. Waretan da suke
yi shi yafi komai saka shi a damuwa. Shi ya
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
san Mama bata yin Safiyyah tun farko. In
kuma Mama bata yin ka, ba wanda ya isa
yasa ta yi ka.
Mafi a’ala gareka shine ka yi nesa da
shiga sha’aninta.
Zayyan ya kara rintse idonsa a lokacin
da tunaninsa yazo nan, ya ciza lebbansa na
kasa cikin tuno rayuwar Baba Bello. It was a
bitter past moment da baya ko son tunawa,
amma dole ya tuna presence din Baba cikin
rayuwarsu. Baba ya so Safiyyarsa, ya so
zamar mata bango abin jingina a cikin
iyalinsa.
Aka ce Allah baya barin wani don wani
yaji dadi, shekarar Zayyan uku da auren
Safiyyah Allah ya karbi ran mahaifinsa Arch.
Prof. Bello Rafindadi.
A wannan shekarar da Baba Bello ya
rasu, shugaban kasa ‘yar Aduwa shima ya
rasu. Jihar Katsina bakidaya ta gigita ta
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
girgiza. Katsinawan Dikko sun dimauta. Anyi
rashin da za’a dade ba’a mayar a Katsina ba.
Safiyyah ta rasa mai kaunarta da
gaskiya a family din Zayyan, wanda yake
tamkar ‘shield’ ko ‘savior’ a gareta, Late
Arch. Prof Bello Rafindadi.
Mutuwar data gigita iyalinsa, da
daukacin al’ummar jihar baki daya.
A ranar lafiya kalau yayi sallar isha’I
ya koma ya kishingida, kafin gari ya waye
sai barci mai nauyi ya daukeshi. Ashe Baba
tafiyar kenan, don ganin gari ya waye
hantsi na neman ya dubi ludayi Baba bai
juya ba bai motsa ba bai kuma tashi yayi
sallahr asubah ba, hakan yasa Mama shan
jinin jikinta, don ta san Baba ko ciwo baya
saka shi jinkirta sallah balle barci.
Ilai kuwa tana dubawa ta tabbatar
Baba anyi shahadar daren Juma’ah. Ta kira
Zayyan a waya a lokacin yana kan hanyar
isowa asibitin da abincin safensu. Yaji
muryar Mama cikin rishin kuka tana fadin.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
“Na rasa bango na Baffa, na rasa
komai na. Bello ya tafi ya barni daku!
Mazan duniya sunyi kaura, sun barni a
duniya da tarin marayunsu, sun amsa kiran
mahaliccinsu”. **** **** ****
Fadin halin da Zayyan ya shiga na
rashin Baba yayi kadan biro ya rubuta shi,
a ranar aka wuce da gawar Baba Katsina,
dimbin al’ummar ciki da wajen Rafindadi
sukayi jana’idarsa a washegari. In kaga Safiyyah da Zayyan lokacin
amsar makokin Baba suna daka koyaushe,
ko fitowa cikin jama’a basa yi, in ka gansu
duka sai sun baka tausayi, sun yi laushi
kamar an zare musu laka da bargo,
musamman Safiyyah, da take ji a jikinta
mai sonta kwalli daya cikin gidan Rafindadi
ya tafi ya barta cikin fitinannun iyalinsa,
wadanda ita da kanta ta shaida bata da
farinjini a wurinsu.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Malam da Ammi tare dasu Sabah sun
zo musu ta’aziyyah daga Dandume, sun
wuni sur tare da ita a gidan makokin,
Malam Usman ya girgiza kwarai da
gushewar surukinsa na kwarai wanda suka
zama tamkar abokai wato Baba Bello, saida
aka yi sadaqar bakwai ne mutane suka fara
watsewa Safiyyah da Zayyan ma suka koma
Zaria.
Tunda suka dawo gida kuma sai
Zayyan ya komawa Safiyyah tamkar yaron
goye, ya jangabe a kwance ya kasa tsinana
komai, komai sai ta kawo masa inda yake
har Ruwan alwala ta kuma saka masa naci
sannan zaiyi, abinci kuwa sai ta bashi a
baki, kafin ta fahimci tamkar ciwon
damuwa na wucin gadi ya kama shi
(depression) don shikadai yasan halin
rashin da yake ciki, shikadai yasan girman
rashin Baba da yayi, da kuma irin kewarsa
dake nukurkusar zuciyarsa da azabtar da
ruhinsa bayan ya kaishi makwancinsa na
gaskiya, don yasan rayuwa bazata kara
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
koma masa yadda take a baya ba, tunda
babu Baba.
Har ila yau, damuwarsa takan karu
idan yana kintato girman burden din da ya
hau kansa yanzu, na kula da mahaifiya da
marayun kanne mata wadanda Baba Allah
bai yi zai aurar dasu da hannunsa ba,
wannan ma ya taka muhimmiyar rawa
wajen jefa shi a halin da ya samu kansa na
zama depressed, ga wani zazzabi-zazzabin
damuwa da masassara dake sakadarsa cikin
dare, alamun son shiga lalurar ‘anxiety’ sun
gama bayyana kansu a tare dashi, sallah
kadai yake iya tashi yayi in Safiyyah ta
matsa masa, ko aiki Zayyan ya daina zuwa.
Safiyyah a kan haka saida ta dangana
da dauko Malam wato mahaifinta, tun daga
Dandume yazo har Zaria, tana kuka tace
Malam yazo ya taimaketa Zayyan ya zama
daddawar daka yafison ta barshi yayi ta
kwanciya a gado kamar ruwa, ya daina fita
aiki, karon Malam Usman na farko kenan
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
da taka kafarsa gidan diyarsa ta farko da
yake kira Nana Safiyyah.
Malam Usman ya samu Zayyan har
kan gadon Safiyyah, ya rufeshi da wa’azi da
nasiha mai shiga jiki da huda zuciyar
musulmi, akan ya karbi rashin mahaifinsa
da kyakkyawar zuciya da tawakkali cikin
godiya ga mahaliccinsa, yace hakan shine
cikar imanin bawa.
Har ila yau, Malam yace masa, ya tuna
nauyin da yake rataye kansa yanzu, na uwa
da ‘yan uwa, sai ya zama namijin duniya
sosai zai iya saukewa musaman sha’ani na
mata, yace ya tsaya akan zuciyarsa kada ya
bari ta rinjayeshi yayi fushi da yin Allah. Allah yafi shi son Baba Bello, shi yasa
ya dauke abinshi, a sanda kowa ke tsaka da
bukatarsa. Ko ya san cewa mafi yawan
mutanen kirki basu cika jimawa a gidan
duniya ba? Malam Usman bai tafi ba saida yasa
Zayyan ya shiga toilet yayi wanka, yayi
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
askin fuska da yanke akaifarsa, ya canza
kayan jikinsa daga jallabiyyar data jima a
jikinsa, ya kuma umarceshi da ya daure
yaje ya ga Mama don Safiyyah ta gaya masa
tun baya sadakar bakwai bai kuma
komawa Katsina ba, kuma baya kiran kowa
a waya, yama kashe wayarsa tun da jimawa,
Mama ko ta kira bata samunsa, fadin ranta
kuma ya hana ta kira Safiyyah tace ta
hadasu, Malam ya tuna masa cewa shine
karfinta a yanzu don haka ya dinga zuwa
ganinta akai-akai fiyeda baya.
Bayan tafiyar Malam Usman a daren
ranar Safiyyah itama kwana tayi lallashin
Zayyan, tana mai tunasar dashi
muhimmancin karbar kaddara kyakkyawa
ko mummuna. Tace. “Shi kam Baba ai kowa ya san tasa tayi
kyau, tunda ya rabu da kowa lafiya, ya
mutu bai yi satar dukiyar al’umma ba,
babu bashin kowa a kansa. Dubi yadda
al’ummar musulmi suka yi dafifi don raka
shi masaukinsa na gaskiya.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Hakika Baba ya samu kyakkyawar
shaida ta kwarai, irin wadda kowa ke burin
samu a karshen rayuwarsa Habiby.
Baba abin so ga Dalibansa, kada ka so
ka ga yadda dalibansa suka dinga
tuttudowa zuwa ta’aziyyarsa, da sauran
al’ummar Katsina bakidaya”.
Safiyyah bata gushe ba cikin lallashin,
tareda gaya masa kyawawan halayen
mahaifinsa da kowa ke fadi, wadanda
sukasa ake masa kyakkyawan zato.
Kawai sai ya mika hannnu ya janyota
jikinsa, tabi umarninsa ta kwanta lumm a
kirjinsa, su duka suna sauke ajiyar zuciyar
tuna Baba Bello.
A karshe sai da ta dangana da inganta
masa daren, yadda biro bazai iya
bayyanawa ba sannan ya fara regaining
consciousness, wani yanayine suka samu
kansu na tsantsar soyayya mai shiga rai da
farantawa juna rai, bayan nan haka suka
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
kasance manne da juna cikin duvet a tsayin
daren bakidayansa.
Fatan ta da burinta kadai Zayyan ya
dawo hayyacinsa, ya karbi rashin Baba in
good faith, so take ya koma Zayyan dinsa
data sani, mai karancin far’a da rashin
faram-faram, wato ya dawo normal Zayyan
dinsa na baya, shikuma Zayyan bata sani
ba, ya yanke tsammani da hakan, don ji
yake a jikinsa bazai taba warwarewa daga
rashin Baba har abada ba.
Baba ya tafi ya bar shi da wata irin
kewarsa, ga nauyin mahaifiyarsa, kanne
mata da ya yayye mata shi kadai namiji
kwal a cikinsu da ya hau kansa yanzu.
Wannan kadai in ya tuna yana kara
saka masa damuwa, don ya san yadda Baba
ya rayu wajen sonsu da nuna musu kauna
hadi da kyautatawa iyalin sa ba mai iya
maye musu wannan gurbin.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Iyalin Baba basu san babu ba, basu san
su nemi wani abu su rasa ba. Kome sukeso
shi yake basu in dai baifi karfinsa ba.
Baba tsayayye ne akan bukatun
gidansa da tarbiyyar su Hatoon, duk da ba
koyaushe yake samun yadda yake so daga
Mama akansu ba.
Shi kam har bai san ta ina za’a fara da
maye musu wannan babban gibin ba.
Maye gurbin Baba babban maye gurbi
ne mai wuyar samu. Ko yace wanda bazai
samu ba. Bazai taba mantawa da watarana
da Hatoon tace bata son abinda aka girka a
gidan, haka Baba ya dauki mota ya fita
cikin dare ya nemo mata abinda take so,
haka da Zaitoon bata cin Biredi sa Gurasa
Baba Gurasa yake saya mata kullum har
rasuwarsa bai fasa ba.
Duk sanda yaji mai zuwa kano sai
yayiwa Zaitoon sautun Gurasa. Ire-iren
kulawar Baba Bello kenan akan iyalinsa, in
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
dai akan farin cikinsu ne baida namba two,
ko ta ina zai kwatanta zama shi a garesu???
Baba Bello daya ne cikin dubu, ko a
cikin iyaye, ta fuskar kula da iyali, komai
cewa yake “my family first”.
Kasancewarsa shikadai namiji a cikin
su a ganinsa bazai isa hujjar da zai iya
zamewa ahalin Baba makwafinshi ba, ko
mayewa ‘yan uwansa da uwarsu
wawakeken gurbin da Baba ya bari.
Gabadaya wannan tunanin yasa ya
raunana, babu sauran jarumta ko kankani
a tare da shi, sabida tunanin halayen Baba
masu wuyar imitating.
Ba rabo da gwani ba, aka ce maida
kamarsa!
**** **** ****
Da wannan mutuwar jikin da raunin
zuciyar yake kwana yake tashi tun rasuwar
Baba Bello. Wanda shi ya kassara shi, ya
kuma karar da duk wani karsashin da yake
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
dashi, ya kusa sabbaba masa ‘anxiety
disorder’.
Duk kuwa da kokarin Safiyyah na son
(reviving mood) dinsa da yi masa addu’a a
ruwa ta bashi ya sha, hadi da nau’ikan
kulawa da soyayyarta na macen kwarai
wadda ta damu da situation din mijinta,
mijinta Zayyan da kusan suke sharing the
same feelings itada shi a komai. Soyayya
take gwada masa gangariya akan gadon
barcinsu, but he hardly respond. Komai ya
fita kansa fit, including soyayyar.
Shi kawai ya san bazai taba mayar da
farin cikin da ya samu a rayuwar da yayi
tare da mahaifinsa ba, tun daga haihuwarsa
har girmansa a jikin Baba Zayyan ya rayu.
Kalamansa ne da support dinsa suka
raineshi, har ya zama jarumin da ya zama.
Yanzu kuwa da Baba ya tafi ya barshi, ya
tabbata ya tafi harda jarumtarsa.
Sabida haka ba wani abu na farantawa
ko wata soyayya da wani ko wata zai nuna
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
masa yanzu da zata hana shi damuwa da
rashin Baba da yayi. Saidai ya kalleka
kawai. Har sai bayan zuwan Malam Usman
ne ya dan samu canjin yanayi kadan.
Da safe suna karya kumallo, ya kalli
Safiyyah, sai ya ga itama duk ta rame
saboda damuwar da yake ciki, kamar ma ya
fita kuzari yau, ya sa hannu a habarta yace
“Sophie”, sai ta dago a hankali ta dube shi
sai ga kwalla fal! A kwance cikin idonta. Zayyan yasa yatsarshi manuni ya tabo
kwallar ta idasa gangarowa, yayi mata
murmushi yace “haba Sophie na, ban sanki
da saurin karaya ba, in duk muka karaya
wa zai cigaba da karfafa wani? Kiyi hakuri
dani kinji, kici gaba da karfafani, ni nasan
situation dina ba mai wucewa bane in har
zan tuna Baba.
But I always pray that it will come to
pass idan ina ganin ki a tare dani cikin
walwala”.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Ya fadi hakan ne da ya yana tuno wasu
kalaman Baba Zayyan akan Safiyyah,
watarana suna hirarta yace dashi “Zayyan
ina fada maka ka riketa da kyau, wannan
matar kwarai ce, kada ka bari ta kubuce
maka, ita kadai ta isheka rayuwar duniya
kamar yadda Mamanku ta isheni, ni nasan
‘yar baiwa ce, tsatson albarka mai iya
tattalin farin cikin mijinta, ko a fuskarta
mutum zai karanci kaunarka, ka tattalata
ka sata farin ciki kullum wallahi kadara ce
ita babba gareka”. Sai yaji murmushi ya
subuce masa. Yana shafa habar Sophie yana
fadin “Sophie diyar Babanta, Baba Bello, I
truly love you!”.
Murmushin da Safiyyah ta dade bata
gani daga gareshi ba, watakila tun kafin
rashin Baba rabon da taga murmushinsa.
Yace.
“Zan wuce Katsina yanzu, amma
bazan kwana ba in sha Allah, ki daina
damuwa kinji Sophie na? Everything will be
alright da karfin tawakkali.
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
My mood will be restored soon, idan
wannan shine damuwarki. Zan yi kokari in
dawo Habiby dinki da kika sani, kin ji
Sophie?”
Safiyyah ta kusa shidewa don farin
ciki, domin taji dadin kalamansa sosai, ta
kasa boye jin dadin data yin ta hanyar
fadawa jikinsa ta rungume shi, ta sumbace
shi saman lips dinsa yayi maza ya kwaci
kansa yana dariya yace “kada ki karya min
alwalar walha” tace ba damuwa sai ka
daura wata, nasan wannan ta riga ta
kwance. I have no idea na yadda nayi
missing my man anan wurin…”.
Ta fada tana rufe idon da ya bashi
dariya, har yana tantama anya Sophien shi
yau take masa wannan soyayyar? Safiyyah
sarkin kunya sarauniyar ustazan
Dandume? Inama ta dore da hakan, da ya
zama dan sarki. Amma ya san mawuyaci ne
ta dore din, kunya a jininta take. Da kyar ta
bar shi ya tafi, don sai da aka yi alwala mai
dalili, sannan ta bashi sakon gaisuwarta ga
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Mama dasu Zaitoon, ta rako shi har kofar
gida.
Safiyyah bata koma gida ba sai da ya
hau okada (babur) din da zata kai shi
tashar da zai hau motar Katsina.
A farkon shiga unguwar Rafindadi ya
sauka daga kan Achaban da ya dauko shi
daga Tasha, ya taka a kafa, da dan nisa
kadan kafin ya isa gidansu, sannu kan
hankali yake takawa don isa zuwa kofar
gidansu. Ya sauka tun daga dan nesa da gidan
ne don kawai ya motsa kafarsa, don ya dan
dade bai taka ta sosai ba, hakan yasa ya
samu damar da ya gaggaisa da jama’ar
unguwarsu. Suna kara yi masa ta’aziyya.
“hakika Baba Bello na kowa ne, Allah
yabamu hakurin jure rashinsa” yadda ‘yan
shiyyar Rafindadi da suka hadu a hanya
suke yawan fada masa kenan.
Tun daga bakin kofar gidansu da ya
sako kai ya shigo cikin harabar gidan,
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Zayyan ya kara gayawa kansa “lallai
bangon gida ya fadi!” kamar yadda Mama
tace. Wato Baba Bello ya barsu. Ya
subhanallah! Meyasa yayi wannan dadewar
bai zo gida ba ina tawakkalinsa da imaninsa
suka je suka barshi? Saboda da shigowarsa harabar gidansu
yaga hatta fulawoyin gidan kansu, da grass
carpet duk sun fara bushewa, kamar an
shekara ba’a basu ruwa ba, alamu ne na
rashin samun kulawa kamar da. Abin mamaki ma’aikatan gidan sun
fara watsewa wai ace daga rasuwar Baba,
ko arba’in ba’a yi ba, ko a tunaninsu an
daina biyansu ne yanzu, oho! Ko kuma don
ya dade bai zo Katsina ba? Mama kuma ya
san bata tasu take ba a wannan lokacin da
take cikin alhini da Takaba. Maigadin Baba
Malam Ilyasu ne kadai bai tafi ba. Ko dama
can shi dan amanar Baba ne.
Busassun ganyaryaki duk sun cika
harabar wajen ba’a share ba. Hakanan
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
yake jin kararsu duk takun da yayi suna
bada kara rakakas-rakakas na bushewa.
Wannan abu ya yiwa Zayyan ciwo.
Yace yau gidansu ne za’a maida kango as
early after the demise of Baba? Malam
Ilyasu na gaisheshi bai ko amsa ba don
bacin rai, kawai zuciya ta kawo shi wuya, ya
fara fada ta inda yake shiga bata na yake
fita ba akan Dattijon, har ya manta da
shekarun Baba Ilya.
“Baba Ilya, yaya akayi aka bar gidan
haka babu shara, sai kace bola?
Yaya aka yi shukoki suka mummutu
haka ba kwa basu ruwa da taki ne? Motocin
Baba ne sukayi irin wanan kura haka?
Saboda babu Babana ko? Saboda ba’a biya
ku kudin wannan watan ba? Ko babu
mutane da suke rayuwa a cikin gidan ne?” Nan Malam Ilya ya sadda kai, ba ciwon
fadan da yaron ke masa yaji ba, a’a ya san
feeling dinsa na yanzu, kamar baya cikin
hayyacinsa yake maganar. Shima sai kewar
KAWAR ZUCIYA 1! TAKORI 2025
Alhajinnasu ta zo masa har saida ya share
kwalla, da kyar ya dafa kafadun Zayyan
yana