Showing 1 words to 3000 words out of 46889 words

Chapter 1 - KAWAR ZUCIYA 1 BY SUMAYYA TAKORI KABARA.pdf

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

KAWAR ZUCIYA




1


Sumayyah AbdulQadir
​ 07030137870 (whatsapp only)
​ ​ babbangoro2015@yahoo.com
​ takorikabara@gmail.com

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025


Assalamu alaykum TAKORITES.
Kafin mu fara ina farin cikin tallata muku
Hajiya Aisha Umar Dauda mai A&A Incense &
Collections.
Dealers ne nadukkan kayan Oriflame Products & GHT
Products. Sanan suna da Room Freshener, Toilet Cleaner,
Tiles Cleaner, Glass Cleaner, Dish Wash, Hand Wash,
Shoes & Bags, Hand Made Shoes, Atamfa, Shadda,
Materials, Kid's Wears, Electronics, Perfumes and many
more.
Domin sayen daya ko sari ana iya tuntubarsu a;
No.1 Beside Lolo Dakare's Filling Station Hajj Camp,
Katsina State.
Suna aikawa ko'ina. Ko a tuntubesu kai tsaye a
wannan lambar waya don saka order.

08067303736
08054647489

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025



“Rabbana hablana min azwajina wa
dhuriyyatina qurratu a’ayunin wa ja’alna lil
muttaqina imaama”.

SADAUKARWA NE GA
“TAKORI’S LOUNGE”.
Ina alfahari da kasancewa tare daku har
tsayin wannan lokacin. Allah da ya hadamu
haka, a inuwar al’arshinsa ya barmu tare
cikin Alherinsa… har zuwa ranar da muka
daina numfashi. -Sumayyah
Abdulkadir
01/01/2025

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025


KAWAR ZUCIYA ( Littafi na 1)
MATASHIYA

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

G

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

arin Abuja, kamar yadda kowa ya sani, gari
ne da ya tara kerarru da kuma shahararrun
unguwanni (Estates) na gani a bada labari, a
matsayinta na babban birnin tarayyar kasar
Nijeriya, gari ne daya mallaki manyan
uguwanni kala-kala. Saidai duk yadda
kowanne Estate a garin ya kai ga tsaruwa da
girma, hadi da burge idanun mai kallonsa ko
maziyarcinsa, har yau ba’a samu shiryayyen
Estate da ya amsa sunansa kamar “Sunset
Estate” dake nan a tsakiyar unguwar Guzape
ba.
“Asokoro Extension” wadda aka fi
sani da unguwar “Guzape”, wasu na yi mata
kirari da (Beverly Hills of Nigeria) saboda
tsaruwarta da kyawun fasalin unguwanni da
gidajen cikinta, sannan da kawatattun
dogayen gine-ginenta da suke akan tudu. Kamar yadda mazauna wurin suka
sani, ita Guzape kacokam dinta a kan hayi
(hills) wato (tuddai) take tsugunne.
Kana dumfaro Guzape, Sunset Estate
zaka fara hangowa sabida tsayin gate dinsa,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

ya zamanto shine ‘landmark’ din da ya fito
da unguwar Guzape, dogon kyakkyawan gini
ne wanda aka yi shi a tsakiyar (Guzape
main).
Zai yi wuya farat daya ka yarda cikin
kasarmu ta gado ne wannan kyakkyawar
unguwa ta Sunset Estate take, musamman
idan a hoto ko a faifan bidiyo kaga Estate din,
wato dai idan ya kasance ba gani na zahiri
kayi ma Estate din ba. To balle kuma idan aka ce maka
fasahar wani dan asalin kasar ce ta samar da
zanen taswirar, wato in akace da kai dan
asalin kabilar hausa/fulani ne ya zana, ya
kuma tsara Sunset Estate. Ya kasance daya daga cikin daidaikun
matasa ‘yan baiwa na kabilar hausa-fulani
akan ilmin zane, sannan product din Arewa
ne gabansa da bayansa; kyankyasar daya
daga zaqaquran jami’o’in da kasar Najeriya
ke alfahari dasu. Wanda a tarihin rayuwarsa
kaf! Tun daga haihuwa har girmansa, da
tarihin ilminsa, bai taba fita ko (filin jirgin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

sama) da sunan yin karatunsa na ilmin
kimiyyar Zanen gidaje da tsara Estates din
birane ba.
Anyi ittifakin nagartar Ilminsa na Zane
ba wai ya samo asali daga shiga aji bane; a’ah
wata baiwa ce da hikima na musamman, da
Allah Subhana ya huwwace masa.
Hakika Allah yayi masa baiwa da
fasahar iya Zanen taswirar gidaje, da
kirkirar zanen kowanne irin abu ya durfafi
zanawa (yayi niyyar) zanawa. Abokan
karatunsa na jami’a da yawa kan masa kirari
da “rainon Zaha Hadid” saboda iya zanensa.
Wato (British-Iraqi Architect) dinnan da
sunanta yayi ficce a duniya akan ilmin
fasahar Zane, suna kwatanta shi da rainon ita
“Zaha Hadid” ne saboda iya sarrafa
alkalaminsa wajen Zanen taswira. Ta yadda
zaiyi wuya idan ka ganshi a zahiri (a fili)
ra’ayal ayni ka yarda tashin farko in aka ce
da kai shine wanda ya zauna ya zana “Sunset
Estate”, ya fidda ‘features’ na zubin ginin

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

yadda ya dade yana ‘imagining’
kasantuwarsa.
Akalla ya kwashe shekaru sama da
uku yana zanawa tareda sabunta ideas dinsa,
yadda zasu tafi da zamanin da ake ciki da
imaginations dinsa na kwararren fasihin
‘Architect’ akan Estate dinnan. Duk da cewa,
kowa ya san ya dade ana damawa dashi a
harkar Zanen gidajen zamani da Estates na
birnin tarayyah da kewayenta, abin nufi, har
a sauran jihohin kasar Najeriya an san da
zamansa akan harkar kwangilar Zane, a
kalla a kowanne satin Allah yana samun
kwangilar Zanen Estate dana tsara gidaje a
ko’ina cikin kasar Nijeriya.
Har a karshen shekara ta dubu biyu da
da ‘yan kai, Allah ya bashi ikon kammala
zanen taswirar ginin ‘Sunset Estate’, bayan
kwashe tsayin lokacin yana sarrafashi yadda
yake so da alkalaminsa, tsarin ginin da komai
dake cikinsa ya fito sak! Yadda yayi
hasashensa cikin kintace da tunaninsa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Zaka kara mamaki kwarai in kayi
la’akari da karancin shekarunsa a lokacin
zanen Sunset Estate da lokacin gininsa. Abun
zai matukar kara burgeka ne in kaji cewa
yayi zanen ne cikin shekarun kuruciyarsa in
his early thirties. Shi da kansa idan ya tuna cewa
fasaharsa ce ta samar ta kuma ajiye gidajen
‘Sunset Estate’ a muhallinsu, baya sanin
sanda yake yiwa Ubangijinsa tasbihi kan
wannan exceptional baiwa da yayi masa, yana
jin tarin alfaharin hakan a kasan ransa; yana
burge kansa da kansa shima, yana godewa
Ubangijin fasaha mai kyauta da kari a
gareshi.
Har wani lokacin yaji tafin hannunsa
sun tafi da kansu…, suna masu haduwa da
juna…., wato yaji hannunsa na motsawa
cikin tafawa kansa da kansa…….
Duk da cewa sanin kowa ne shi dan na
gada ne ta fannin ilmin Zane…. ba dan taka
haye bane, abin nufi gadon fasahar ilmin
zanen yayi, sannan ya zauna a aji ya karanta

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

shi. Kenan “Zaha Hadid” bata haifeshi ba
balle ta raineshi amma shima gado yayi, ya
gada ne daga nasa mahaifin, marigayi Arch.
Bello, wanda shima wani shahararren tsohon
(Architect Guru) ne. **** **** ****
SUNSET ESTATE
Estate din zagaye yake da wasu dogayen
shuke-shuke, bishiyoyi ne masu tsayi suka yi
masa rumfa, irin dogayen bishiyun da aka fi
sani da suna ‘palm trees’.
Idan dare yayi ko’ina ka juya hasken
fitilu ne na kayatattun kwayayen lantarki,
masu bada launi da kaloli daban-daban, su
maida Estate din kamar rana. A yawancin
lokuta musamman da maghriba yanayin
hasken fitilun Estate din komawa yake
tamkar wani yanki ko wani bangare na
‘Sharm El-Shaikh’ din kasar Misra.
Saboda babu yawan zafin rana sosai a
Estate din, sakamakon dogayen shukoki dake
lullube dashi.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

​Idan kuwa a lokacin damuna ne
bishiyun Estate din sun fi zama korra sharr,
da tashin kamshin furanni iri-iri. Kofofin
shiga ‘gate’ din wasu manyan kofofi ne na jan
karfe masu budewa da rufewa da kansu
(automatic gate), ko’ina na jikin katangar
ginin Estate din, an katange shi da (electric
fence).
A daidai tsakanin kofar shiga data fita
wato tsakanin kofar hagu da kofar dama, an
rubuta sunan Estate din da kalar ruwan gold
daga can samansa, inda aka maqala shi a
jikin wani farin bangon gilas mai garai-garai
da daukar ido, an rubuta shi rada-rada da
manyan baki kamar haka;
“Sunset Estate”.
Idan aka shigo akwai ‘lanes’ biyu na
shiga da na fita, an kawata ko’ina da ‘solar
lights’ da ‘security lights’ da ‘street lights’.
An shimfida bakar kwalta sambal a
gabakidaya titin da zai shigar da kai cikin
ainahin Estate din, da wanda zai fito da kai
wajensa.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Akwai gidaje kala-kala a ciki, kama
daga (blocks of flats), da (terraces), wanda a
ciki akwai (semi detached da fully detached
houses).
Kowane street/close na cikin Estate din
an saka mishi suna da ‘sign board’ mai dauke
da sunan sa, kuma wani abin burgewa shine
kowanne close/street ya samo asalin sunanshi
ne daga Local Governments din jihar
Katsina, saboda ainihin wanda ya zana kuma
mai Estate din dan asalin jihar Katsinan
Dikko ne.
Kishin jiha irin nasa yasa kana
shigowa zaka fara cin karo da local street
names da ba’a saba gani ba a wurare irin
wadannan, irin su Batsari Close, Bindawa
Close, Ingawa Close, Daura Close, Funtua
close, Jibia Close, Dutsinma Close, Dandume
Close, Bakori Close da sauransu.
Mafi girman Street din cikin “Sunset
Estate” shine Street na farko da zaka tadda
da zarar ka shiga layin farko, wanda duk
gidajen cikinsa (fully detached) ne, kuma sun

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

fi sauran girma da kyau, yana dauke da
sunan mahaifarsa ta ainahi watau
“RAFINDADI Close”.
A cikin Sunset Estate, har ila yau,
akwai supermarket, akwai local market
(kasuwar siyan kayan gwari/kayan miya dasu
(veggies), akwai masallaci, akwai (pharmacy)
sannan akwai saloon na maza dana mata. Daga can karshen Estate din akwai
wani katon dutse da ake hangowa daga
ko’ina kake cikin Estate din, irin duwatsun
Guzape Hills, anyi ‘park’ na shakatawa a
gurin, mazauna Estate din na zuwa da
yamma don hutawa da ishadi, suna kallon
faduwar rana. Gurin ba karamin kyan
daukan hoto yake yi da yammaci ba,
musamman idan rana ta tafi zata fadi.
Kwarai zaka so daukar hoto a Sunset
Estate, a irin wannan lokacin da rana ta tafi
zata fadi. Yanayi ne mai ban sha’awa dake
afkuwa kusan kullum a cikin Estate din,
kamar yanayin kasashen ketare (daya daga

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

cikin manyan dalilan da yasa ya zabi sakawa
‘Estate’ din suna Sunset Estate kenan).
A can wani gefe na park din, akwai
gurin wasan yara da aka kawata da kayan
wasa da liluna iri-iri na jin dadin kananan
yara.
Kai daga ganin tsari da zubin ‘Sunset
Estate’ kasan mamallakinsa kuma wanda ya
kirkireshi ya kashe dukiya da kwarewarsa ta
fitaccen mai ilmin zane (Architect) wajen
zana shi da tsara shi da gina shi, da gani
kuma zaka tabbatar da cewa Estate ne da
masu kambun susa kadai, ko masu babban
mukami a gwamnati zasu iya mallakar
muhallin zama ko na shiga haya a cikinsa.
**** **** ****
SHIMFIDAR LABARIN
“My Co-Architect!”.
Sunan da yake kiranta dashi kenan, a duk
lokacin da yake cikin shaukin begenta, da
lokutan da kewarta da tunaninta suka
addabeshi, ko in yana magana da wani a

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kanta ko ‘yan jarida in dai zai ambaceta to in
sha Allahu zaka ji yace “My co-architect”.
Wannan ya faru ne (bayan barinta
rayuwarsa) sai wannan inkiyar daya bata ta
zame masa abin ambatonta dashi, abin
tunawa da ita, idan yana zancenta, baya
ambatar sunanta na hakika saidai “My
co-architect”. Sau tari kuma ya kan ambaceta da
wannan sunan ne a duk lokacin da tunanin
gwagwarmayarsu tare a rayuwa yazo masa,
cikin fadi tashin neman ilmi, soyayyar
kuruciya (wadda ta kaisu ga aure), neman na
kai cikin aikin koyarwa da yayi a jami’a, ko
idan ya tuno ranar aurensu mai kyakkyawan
tarihi, aurensu mai asali da tushe mai kyau,
wanda aka yi tun cikin shekarunsu na
kuruciya, tun mahaifinsa na raye a can baya.
A rayuwarsa bai iya manta alherin
mutum ba, to balle alherin mutum mafi
kusanci dashi wato ita matarsa. Shiyasa ko
sau daya bai taba manta gudunmuwarta ga
nasarar samuwar gina “Sunset Estate” ba,

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

dama sauran nasarori masu girma data
taimaka masa (koda da shawara ne) ya
cimma a rayuwarsa. Duk wata daukaka da
tazo masa ya kn ce ya sameta ne tare da ita,
har bayan tafiyarta daga rayuwarsa yana
tuna ta da wannan kimar, ya kara jin ninkin
so da kaunarta.
Hakika ita wani ginshiki ce na dukkan
cigabansa, da kafuwarsa, da tsayuwarsa kan
tsinin kafafuwansa.
Bayan canzawar dukkan kaddarorinsu,
bai daina kallon komai na nasarar Estate din
a matsayin nasu su biyu ba……
Domin a cewarsa shi da ita ai ‘sharing
ideas’ sukayi, suka samar da (tangible final
draft) na taswirar Zanen ginin, a matsayinta
na (certified architect) itama.
Ta kasance mai yawan tallafa masa ta
kowacce fuska akan al’amuran profession
dinsa na Zane (mataimakiya ta cikin gida).
Duk wani jibi (gumi) na wahalar samar da
‘Sunset Estate’ da gudanar da ayyukanshi

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

kafin samuwarshi, a koyaushe ya kan ce ma
‘yan jarida.
“Shi da itane suka hadu suka yarfeshi”.
Wannan na daga cikin dalilan da suka
sa lokacin da aka fara bada hayar gidajen
Sunset, yayi mata kyautar ‘Terrace’ guda da
sunanta a cikin Estate din bayan wanda suke
ciki. Tsarin ginin Sunset Estate da
zamanatuwarsa, farin jininsa da ficen da
Estate din yayi a birnin tarayyah, yayi
matukar jan hankalin ‘yan jarida na cikin
gida dana waje, tare da manema labarai akan
ilmin fasaha, musamman masu son fito da
zallar fasahar ‘yan kasar da tallata baiwarsu
ga idon duniya, don duniya ta san da irin
fasaharsu, wannan dalilin yasa suna yawan
bibiyarshi, a gida ne ko ofis, da tambayoyi na
gani kasheni, akan son sanin tarihin
rayuwarshi, da sirrin nasarar Estate din.
Ana yawaita tambayarsa;

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

“Shin ko a ina ya samo tunani da
samfur din zanen Sunset Estate? Wai da gaske
ne shi da matarsa suka zana Sunset Estate?”
A irin wadannan tambayoyin zaka ji shi
yana fadin amsarsa a takaice ga ‘yan jarida
cewa.
“Yes! I got the samples from ‘Her!’
I mean (My Co-architect)”.
Idan kuma aka yi masa tambaya game
da sirrin nasarar “Sunset Estate” dana farin
jinin da ya samu yake kuma kan samu ko me
zai ce? Sabida a halin yanzu duk wani mai
babban mukami a gwamnatin kasa, ko ‘yan
kasuwa masu kumbar susa, ko ‘yan siyasa
mazauna FCT, kokari yake ya mallaki gidan
zama ko na haya a cikin Sunset Estate.
Baya gajiya da fadar cewa…...
“She is behind all these successes, My
co-architect!”.

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

Sannan akwai wani suna na
musamman da duniya ta shaida ya kan kirata
dashi a duk lokacin da yaso soyayya;
“My Alter Ego!”.
Hakika wannan sunan, ba dadi kadai
yake yi mata a zuciya da ruhi ba, yana sawa
ta ji kanta ya kumbura, taji ta tamkar tafi
sauran mata tana yawo akan gajimare, ta
kuma tambayi kanta ko a cikin mata ‘yan
uwanta, akwai wadda ta kaita sa’ar samun
soyayyar miji?
Domin hakika tayi sa’ar dasu basu yi
ba, na samun mijin da ke sonta da dukkan
zuciyarsa… har ya maida ita barin
rayuwarsa, dadin sunan da take ji in ya
ambaceta dashi yana wanke duk wani
dattinsa daya zo ya yabawa kansa a ruhinta,
wato bayan canzawar kaddarorinsu daga
positive zuwa negative.
Kalmar na tattaro duk wani nau’I na
farin ciki ta saka a ranta, zuciyarta kan zama
fara kal, kamar danyar madara, idan ta tuno

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

da sanda ya sha kiranta “His alter ego” a
lokuta mabanbanta na tarayyarsu da bazasu
lissafu ba. Don haka ita da take ce masa
“Habibyyy” ta san ai is not enough! Ta san
dai bata biyashi kalmar soyayyah ba, bata ko
kamanta ba, bata kuma da wata kalmar mai
tsada da zata iya bashi bayan wannan. Amma
ai yafi kowa sanin cewa shi ruhinta ne
gabadaya. Ya zama cewa, a duk sanda ta tuna
sunan nan da yakan kirata dashi (a lokutansu
na soyayyah) sai ya zama babu sauran
burbushin bakin cikinsa a cikin zuciyarta (a
lokacin da soyayyah ta canza).
A duk lokacin da ya kirata “alter ego”
dinsa….. hakan ce take kasancewa da ita!!!
Ko zata manta komai, saboda bacin rai,
da canzawar zamani, da kuma canzawar
zuciya, su wadannan kalaman nasa bata
manta su.
Ko na rana guda bata taba manta irin
tasirin da nau’ikan kalaman soyayyarsa suke
haifarwa gangar jikinta ba, a duk sanda ya
dubeta cikin ido dinnan ya ambaceta da

KAWAR ZUCIYA 1!​ TAKORI 2025

muryar nan tasa mai dakushe mata kunne da
kashe kuzarinta. Sannan ta sanyaya ruhinta
all at the same time. Wato idan yaso soyayyah
haka kawai ya kan kashe ido ya dage gira
yace. “You know you are my alter ego
koh?!”.
Yana daga cikin daidaikun tsofaffin
memories dinsu da basa fading! A gareta.
Kuma basa canzawa ko bayan canzawar
kaddararsu, har kuwa bayan ficewarta
kacokam daga gidansa da rayuwarsa……. *****

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login